Showing 15001 words to 18000 words out of 57484 words

Chapter 6 - AURE DA KARATU Book Complete Rumaisa Sidi.txt

26 Jan 2025

6705

ke kike yi tare da taimakon ƴan uwanki kuma ina godiya sosai amma nima inaso in ɗauki nauyin ƴaƴana kamar yanda kowane uba ke yi shekaranjiya mama ta kirani ta bani kuɗi dubu ɗari biyu tace wai in samu ko ƙaramar sana'a inyi ita a shawararta ma in sari takalma a gurinki ko ba yawa in aza a shagon bilya ɗan yayarta tayi magana dashi" murmushine ya faɗaɗa a fuskata "Kai Alhamdulillah wallahi mama mungode sosai Allah ya sanya alkhairi yasa arzikinmu a sana'ar"


Gyara zamanshi yayi "to maganar gaskiya ni bazan iya wani saida takalmi ina ma laifin ace gurina ake sarowa? ni wallahi farko da tace zata bani kuɗi inyi jari na ɗauka kuɗin sun kai miliyan ɗaya tunda filinta na gado ta saida to yanzu abinda nake nema gurinki ki rantamin dubu ɗari biyar sai ki haɗani da inda kike sarowa ina rabama mutane don ni bazan iya wannan zaman na kasa takalmi a kasuwa ba" galala na saki baki ina kallonshi kenan dai shi bazai canja ba kasa haƙuri nayi saida na magantu"wai abban safwan kai har yanzu zaman gidan bai isheka ba? meye laifin mama? kodon tana tausayama ai ba kai kaɗai ta haifa ba kuma kace bazaka yi sana'ar takalmi ba kafi ƙarfinta ne? wai me kake so ka maida kanka? yaushe za............"


"Ya isheki malama" ya dakamin tsawa tare da miƙewa tsaye yana ci gaba da magana "karki so ki gayamin magana wallahi ranki zaiyi mugun ɓaci bazan ɗauki wannan ba duk da kike kallona a haka har yanzu banyi lalacewar da za ki gayamin magana in ƙyale ki ba kuɗi na ce ki aramin kuma shima ba dole" ji nai kamar in maƙure shi a hasale nima na miƙe "to banida kuɗin ranta ma kuma wallahi idan har kace haka za ka cigaba da rayuwarka wallahi akwai matsala ko ni da nake mace bazan iya zaman da kake ba sana'a ba yanzu kuma ka samu ta baka za ka wulaƙanta" tasssssssssss naji sautin mari tare da wata guduma a cikin kwanyar kaina tare da gilmawar wasu taurari


Suman wucin gadi na tafi maganar shi ta dawo da ni a duniyar da nake "kinyi kaɗankiyi tsaye a gabana kina gayamin magana kuɗin ki na banza wallahi wahala za kiyi a wannan halayyar da kika tsiro da ita" bansan fitar shi ba saboda ina tunanin suma nayi a wannan lokacin na ɗau dogon lokaci kwance tsakar ɗakina


Kamar wacca ta shekara a kwance haka nake komai jina nake kamar ba ni bace kamar an canja ni wai yau ni ce lawal ya mara marifa uban ƴaƴana sai a lokacinne na fashe da kuka tare da shafa fuskata da lawal ya gama wulaƙantawa kallon kaina nayi a madubi kamar wadda aka tsikara na isa ga hijab ɗina da ke aje na ɗauka tare da mukullin mota ta fita nayi na rufo ɗakina ban damu da yanda fuskata ta kumbura ba haka na shiga mota ta na ja


Kai tsaye gidanmu na nufa kamar yanda na tsammananta ba kowa a falon ummi tana ɗakinta ɗakina na wuce wanda na zauna a lokacin da nake gida komai yana nan tsaf-tsaf saboda kullum sai an gyara shi kan gadon na faɗa tare da fashewa da kuka da sauri na rufe bakina jin kamar sautin kukana zai iya fita waje daga kukan bansan lokacin da bacci ya ɗauke ni ba




Daga yanda naga rana ta fito ta window ɗina na tabbata na daɗe ina bacci tashi nayi na duba agogo ganin lokacin sallah yayi yasa na shiga toilet na ɗauro alwala na tada sallah saida na ƙare nayi addu'a sannan na buɗe kofar tare da fita falo


Bayan ummi na hanga tana zaune a falon da hijabi ajikinta da kuma carbi a hannunta alamun sallah ta gama saida na kusa isa nayi sallama waigowa tayi da sauri tare da miƙewa tsaye da sauri ta ƙaraso wurina "Lafiya? yaushe kika zo? meya same ki a fuska haka? ina yaran?












Ayi hakuri da wannan






*AURE DA KARATU*


*NA*
*RUMAISA'U SIDI*






Page 14




Haɗiye kukan da naji ya tasomin nayi sannan nayi gyaran murya ina ƙoƙarin saisaita muryata kar ta hango wani abin "Yau na tashi banjin daɗin jikina ne ummi shiyasa nace bari inzo nan" saki na tayi daga riƙon da ta min tana min wani kallo "kar ki raina min hankali zainab dubi fuskarki yanda ta kumbura alamun kin ɗau lokaci kina kuka sannan kin shigo baki neme ni ba wai kashe kanki za kiyi zainab?" ta ƙarasa muryarta na karyewa kamar za tayi kuka rungumeta nayi tare da fashewa da kuka hannuna ta riƙa ta zaunadda ni akan doyuwar kujera ita ma ta zauna tare da ɗora kaina a kan cinyarta tana shafa bayana alamun rarrashi


"Kiyi haƙuri kowane bawa da kalar ta sa ƙaddarar zainab ba wanda aka saki haka kawai saidai ƙaddarar wani tafi ta wani nauyi ni bazance ki kashe aurenki ba don ba ni na haɗaku ba bale na rabaku an riga da an ƙaddara lawal mijinki ne kuma ba wanda ya isa ya tsinke igiyar aurenku sai in an rubuta wannan a ƙaddarar ku kiyi haƙuri nasan kina yi ki ƙara kuma ki rage saka damuwa a ranki kodon ceton lafiyarki Alƙur'ani da kike gani maganin damuwane zainab ki rage baccin dare ki tashi ki gayawa Allah kukan ki shi kaɗai zai miki maganin matsalarki duk wanda yace zai miki wallahi ƙarya yake"


Ajiyar zuciya na shiga saukewa ita kuma tana shafamin kaina Asabe ta kira tace ta haɗamin abu mai ɗan ruwa-ruwa kamar yanda nace inaso ganin yanda ta sakani gaba na daure na ci abincin shawarwari ta shiga bani tare da addu'o'in da zan riƙa yi sai gani na ware ina zuba shagwaɓata a jikin ummina duk da tunanin yarana yana nan maƙale a raina


Sallame sallar la'asar ɗina yayi daidai da fara ringing ɗin wayata ban miƙe na ɗauko ba na cigaba da salatina da addu'o'in da ake yi bayan ƙare sallah saida na kammala na janyo wayar tare da dubawa tsaki na ja ganin number lawal ce ina ƙoƙarin maidata na aje kira ya sake shigowa wannan karon ma shine ina kallo ta gama ringing har ta tsinke ban ɗaga ba ringing ɗin na ƙarewa wani yana shigowa ɗaga wayar nayi tare da karawa a kunne na ba tare da nayi magana ba" ina kika je na dawo ban same ki ba" wannan ita ce sallamar shi gyara zamana nayi sannan nace " inda aka san daraja ta inda kuma har gobe lafiyata tanada amfani a gurinsu ko so kayi ka dawo ka sameni ka ci gaba da jibga kamar yanda kake so"


ajiyar zuciya ya sauke tare da yin shiru na sakanni " kiyi hakuri wallahi raina ne ya ɓaci amma na miki alkawarin hakan ba zata sake faruwa ba" taɓe bakina nayi kamar yana gabana " bazan iya ci gaba da zama dakai a duk lokacin da ranka ya ɓaci ka dinga sauke fushinka a jikina ba wallahi bazai yu ba"tausasa yaudararriyar muryarshi yayi "nasan nayi kuskure amma kiyi hakuri" katseshi nayi"na gaji da haƙuri da kai ina cutuwa lawal na gaji ni shikenan banida damuwa sai kai? kullum kaine matsala ta? to na gaji wallahi"mamakine ya kamani jin bai ɗaga murya ko yayi fushi ba sai ma ƙara kwantarda murya da yayi "kiyi haƙuri zainab ko ba don ni ba ko don yarannan kinsan halin kayanki ga su can falo amna tunda suka dawo ta neme ki nace musu kina makaranta yanzu kuma sunga lokacin dawowar ki ya wuce sun samin rigimar in kiraki su yi magana da ke wallahi yanzu haka ko abinci ba su ci ba"




Miƙewa na yi daga kishingiɗen da nayi ina saurarenshi da sauri na ce mishi"Ina yarana" ina jin alamun yana tafiya da alama shi yana ɗakine su kuma suna falo ina jin lokacin da yake ce musu ga mommynku ku ce ta dawo da wuri "mommmmmmy" naji muryar Amna tana kirana cikin muryar da ke nuna tasha kuka ta ƙoshi "na'am shalelena"na amsa mata nima "mommy ki dawo gidan ba daɗi idan bakya nan"wannan karon Aysha ce mai maganar "zan dawo Aysha amma sai kun min alƙawarin yanzu za ku ci abinci" alƙawarin su ka min sannan na kashe wayata text ɗinshi ne ya shigo wayata "bayan magrib za mu zo mu ɗaukoki ni da yara" aje wayar nayi


Muna falo ni da ummi bayan ƙare sallar magrib muna firar yaya mubarak da muke saka ran dawowarshi a sati mai zuwa muka ji tsayuwar mota ba jimawa kuma sai gasu sun shigo a guje kowa yana kirana rungumeni su ka yi dukansu kowa yana gayamin yanda yaji da ya dawo ya tarar na fita sallamar shi naji a bakin ƙofar falon amsawa mu kayi sannan ya shigo ya duƙa gefen kujera kamar wani mutumen arziki yana gaida ummi cikin mutunta juna suka gaisa sannan ya fita


Kiran sunana tayi lokacin da nake ƙoƙarin saka turarukan da ta bani a cikin ƴar ƙaramar jaka "ina mai ƙara jan hankalinki da ki kula kinsan dai wannan karon yayunki ba za su miki kowane kalar uzuri ba in har tarihi ya maimaita kansa" bana buƙatar ta faɗaɗa min bayani don na fahimci inda zancenta ya dosa


Har muka isa gida duk yanda ya so sakani fira ban tanka shi ba Ina goge kaina da na wanke wurin wanka ya shigo "ga abincinki can idan kin tashi"ganin ya doshi ƙofa alamun barin ɗakin zaiyi yasa na ɗan ɗaga muryata na bashi amsa "baka taɓa ganin na je gidanmu na dawo gidanka da yunwa ba" ɗan tsayawa yayi na minti ɗaya sannan ya ɗaga ƙafarshi ya bar ɗakin


Kwanakin da suka biyo baya wata rayuwa muke yi a gidan ni da shi ya daina shiga harkata saboda da ya shiga zanyi fata-fata dashi to sai ya kama kanshi ya canja gaba ɗaya an siyo sabuwar waya ƴar yayi ga sababbin shaddodin da yake bugu ga kayan daɗin da yake haɗiya ni dai ina daga gefe ina shan kallo don ko nasan kuɗin mama ne ake wulaƙantawa yanzu zai ɗau wanka ya fita kamar wani alhajin nera wani abin ma abin dariya idan naga yanda ya ke shan ƙamshi shi a dole yayi arziki ya wuce wulaƙanci na


Yau ma ina kwance a kan doguwar kujerata safwan da aysha kuma suna riƙe da hannun amna suna koya mata hand writing ya shigo da uwar shadda har maiƙo ta ke ga hular da aka kafa kamar wani ango hannunshi ɗaya riƙe da haɗaɗɗiyar wayarshi ɗayan kuma yana riƙe da leda ta gefen ido nake gulma saboda banga fitarshi ba ina makaranta ɗaki ya wuce ya ɗanja lokaci a ɗakin har na fara shawarar tashi na bishi ɗakin kamar zan ɗau wani abu don inga abinda yake a ciki


Har idona ya fara ciwo da leƙe ya fito wannan karon da sabuwar jallabiyya ya fito a raina nace "Malam lawal saboda bawa bacci haƙƙinshi shima an sabunta mishi" kitchen ya wuce yana wata taƙama ni idan dai ba idona ne ke gayamin ƙarya ba har wani ɗaga kafaɗa naga yana yi kwanannan bai jima a kitchen ɗin ba ya fito riƙe da plate saida ya ƙaraso tsakiyar falon naga ashe kifine irin manyannan ya gasu iya gasuwa komawa yayi kitchen ɗin sai gashi ya dawo da ƙaton kwalin lemu da kuma kofi ɗaya


Janyo center table din falon yayi tare da kaishi gabanshi ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya ya janyo waya ya kunna yana ɗibar kifin a hankali kamar mai cin ɗawisu fahimtar abinda ya ke nufi yasa na umurci su safwan da su je su kwanta ina kallon amna tana kallonshi kunsan halin yaro da kwaɗayi musamman abinda yasan bazai samu ba itama ina watsa mata harara ta bisu su ka tafi gyara zamana nayi tare da ɗora ƙafa ta ɗaya kan ɗaya kamar yanda yayi saida ya kammala sannan ya tashi yana gyatsa ya kwashe kayan ya wuce ɗakinshi da kallo na bishi ina kissima yanda zan rama abinda ya min saboda na sanshi tun dama ba dai kwaɗayi ba duk abinda yasan zaiyi ɗanɗano to yana ƙaunarshi "nasan maganinka" na faɗa a fili tare da tashi na wuce ɗaki


Duk abinda nasan zai ƙarawa girkina ɗanɗano ko ƙamshi saida na zuba shi a dahuwar lafiyayyar kazata da nake wa farfesu harga Allah ban tashi cinta ba amma saboda lawal na ɓanɓarota daga freezer na shiga mata haɗin da nasan ba'a bawa marowaci daga yanda ya fito ya zauna falo nasan ƙamshinne ya fito da shi dama can hakan yake ko ya nake girki indai yana ɗaki sai ya fito yace bazai iya haƙurin jira a ɗaki ba kamewa yayi a kujera yana canja channel saida na ganshi sannan na shiga kitchen na zubo wa yara safwan na kira "ka ɗauka ku je ɗaki ku ci" ba don komai na tura su ciki ba sai don za su iya canko wani abu zubawa nayi a wani plate na ɗauka na nufo falon




Da gayya na yi saitin lawal kamar wurinshi zanje saida naje dab dashi sosai sannan na duƙa na ɗauki remote ɗin da ke kan cinyar shi ƙiris ya rage dariya ta ƙwacemin ganin har yana ƙoƙarin ɗaga hannunshi kamar zai karɓa ganin na goce sai ya fara muzurai yana raba ido ba ƙaramin ƙoƙari nayi ba wurin taushe dariyata saboda nasan ƙiris ya rageyawunshi su zubo


Tun dama Allah ya sa mishi son kaza ni kuma na fi son kifi ina da tabbacin shiyasa ya min abinda ya min jiya saboda har ga Allah kifin ya burgeni ga yanda aka gasa shi kuma nqce sai na rama don yanzu na daina yarda ina bar mishi bashi da ya min zan rama na daina ajiyar wutar damuwarshi zan riƙa fitarwa ta shafi kowa


Har na kammala suɗe dabgena ban ragawa komai ba kai hatta ƙassa ban ragawa ba sai lumshe ido nake ina tanɗar baki a fili kuma ina faɗin "Allah ka ƙara mana lafiyar cin dajaja" tsaki ya buga tare da tashi ya shige ɗaki dariya na tuntsire da ita har ina dafe cikina saboda yaban dariya wallahi lawal ba dai kwaɗayi ba yaran nasa suka shirya na ce Amna taje ta ce idan abbansu zai fita ya biya da su wurin mama saboda sun ɗan jima basu je ba


Ban ɗauka zai fita da su ba saida ya shiryo ya fito cikin dakakkiyar shaddarshi sai maiƙo ta ke ya ce su fito hannu su ka shiga ɗagamin nima na ɗaga mu su har ya kai ƙofa ya ɗan dakata batare da ya waigo ba yace "Nifa mashin zan hau ko napep"na fahimci abinda ya ke nufi ya ɗauka tunda na haɗashi da yarana in bashi key ɗin motata yayi yanda ya ke so da ita kawadda kaina nayi sannan na bashi amsa "ko a baro za ka tafi ai ba matsala bace yaranka ne kai ko a ƙafa ka jasu dai-dai ne" bai ƙara yin magana ba yayi fuuuuuuu ya fita


Ina bedroom ɗina naji sallamar maman haidar sai yanzu ma na tuna da mun haɗu shekaranjiya tace za ta zo nace kar ta zo ta bari sai yau kai wannan matar badai son gulma ba fitowa nayi muka gaisa ta zauna a ɗaya daga cikin kujerun falon lemu na kawo mata sannan na zauna gyara zamanta tayi tana fuskantata "tun lokacin da kika ban labarinki hankalina ya kasa kwanciya inaso inji yanda rayuwar aurenku za ta kasance duba da irin soyayya da kuma halaccin da kika nunawa abban safwan" dubanta nayi sannan na ɗan ya mutsa fuska "to ai ni nama manta inda na tsaya" da sauri ta katseni "yanda rayuwar aurenku ta kasance keda abban safwan" gyara zamana nayi sannan na ci gaba da bata labarin yanda rayuwar aurena ta kasance


Da farko rayuwar auren mu da lawal..............
























Hhhhhhhhhhh Allah sarki lawal😄




Shin kuma kun iya gulma kamar maman haidar😂









AURE DA KARATU


NA


RUMAISA'U SIDI




Page 15


Da farko rayuwar aurena da lawal rayuwa ce irin ta soyayya kamar yanda muka daɗe muna tsarawa ina samun kulawa da kuma tattali daga gare shi zallar soyayya na ke gani a wurin angona


Matsalar mu ta fara ne daga lokacin da garar da nazo da ita daga gidanmu ta ƙare buhu ashirin mahaifina ya baiwa lawal tare da naira dubu ɗari na cefane a matsayin kayan GARAR AURE na(littafina na farko) bayan an kai kayan gidansu buhu biyu ne kawai su ka shigo gidana bansan inda sauran su ka shiga ba


Tunda naga kayan abincin sun yi ƙasa na gayamishi yace min zai siyo yau koda muka wayi gari bamuda ko ƙwarar shinkafa a gidan yana ɗaki yana shiri na same shi gefen gadon na zauna ina kallonshi "Nisful yau fa kayan abincin duk sun ƙare ko abin kari babu bale kuma shinkafar da za mu dafa anjima"


"ohhhhhhhhh wallahi kina da matsala my zee ko jiya kin gayamin maganar nan nace miki zan siyo da inada kuɗi zan ƙi siyowa ne? kina kallon yanda nake fita kasuwar nan haka nake dawowa wallahi ni in banda mama bazan koma wurin mutumennan ba malam mutum don yana ganin kamar kana ƙarƙashin shi sai an tashi kasuwa ya ɗauko wata banzar dubu biyu ya baka kamar almajiri"


Raina naji baimin daɗi ba yanda naga ranshi ya ɓaci akan maganar da na mishi"kayi haƙuri nisful ba wai don in ɓata maka rai yasa nayi maganar ba"miƙewa nayi na isa ga wadrobe ɗita ƴar ƙaramar jaka na ɗakko a ciki kuɗin da ke ciki na fiddo za su kai dubu hamsin ko ma su fi kusa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login