Showing 33001 words to 36000 words out of 57484 words

Chapter 12 - AURE DA KARATU Book Complete Rumaisa Sidi.txt

26 Jan 2025

6689

ne,na hana Aysha ci ganin ya na cutar da ita.Da kuɗin da kike ba Amna ta bamu a makaranta na ke siya mata abinci ni in ci wanda ya bamu,don kar ya zane ni,yau muna a makaranta tace min cikinta ke ciwo,na karɓo mata magani amma koda aka tashi ya lafa,muna zuwa gida abin ya dawo"




Hannuwan shi ya haɗe wuri guda alamar roƙo "Don Allah Mommy idan aka sallami Aysha ki tafi da ita,ko da ni ba za ki je da ni ba,wallahi kullum sai ta yi kukan rashin ki a tare da mu.Mommy don Allah" ya ƙarasa yana rungume ni da ƙarfi tare da fashewa da kuka nima kukan na ke amma sai na danne nawa na shiga lallashin shi.




Sai dare Ummi tayi shirin komawa bayan su Yaya sunzo duba Aysha,tuburewa na yi kan ba inda zani,nan zan kwana tare da ƴata.Mama ce tace a ƙyale ni tun da ina so ba dan Ummi ta so ba suka tafi suka barni tare da alƙawarin shigowa kafin a shiga Theater da ita.




A zaune na kwana riƙe da hannunta ina jin wannan karon dole in yi amfani da shawarar Safwan,amma duka ƴaƴana zan karɓe ba zan yarda sakacin Lawal ya gurgunta ni ba,Mama ma anan ta kwana tare da mu.




Washe gari tun ƙarfe 8:00 su Ummi na asibitin,Kayan kari suka kawo na zubawa Mama don nikam banajin zan iya saka loma a cikina har sai naga an fito da Ayshata.Su Ummi basu jima da zuwa ba Lawal ya iso tare da Safwan.




Ina kwana ya min kamar wani mutumin kirki na amsa mishi saboda idon Mama da kuma Safwan da ke wurin. Tambaya ta ya yi ina Amna? nace ni na faɗawa Ummi ta barta wurin su Nihal kawai.




Lokacin da za a shiga da ita tana riƙe da hannuna ɗayan hannunta kuma tana riƙe da hannun Safwan a hankali tace "Mommy Ya Safwan yace da na warke wurinki zan koma wai?




Kaina na gyaɗa mata "In sha Allah Indo na,tare da ke zan tafi"Murmushi ta yi wanda ya ƙara bayyanar da kyawunta sanna ta dubi Safwan "Yaya kaima da kai zamu tafi mu zauna tare da Amna"


Haɗesu na yi na rungume ina jin wata ƙaunar su na shiga ta "Da ku zan tafi dukanku,Allah ya baki lafiya kawai"




Hankalina bai ƙara tashi ba sai da na ga ana tura ta a gadon da zai shigar da ita zuwa ɗakin theater kuka na fashe da shi bayan ɓullewar su "Ya Ilahi ka rufamin asiri,Allah ya baki lafiya Aysha" na faɗa a fili tare da zubewa daɓas a wurin.




Kaina da ke saramin na dafe,ina kiran sunan Allah a bakina.Mama ce ta shiga lallashina tare da kaini kan benci ta zaunar da ni.




"Kiyi haƙuri Zainabu,ki kwantar da hankalinki,In sha Allah A'isha za ta samu lafiya.Ki mata addu'a ita take buƙata.Ki daure ko kaɗan ne ki saka wani abu a cikin ki,rabonki da abinci fa tun jiya"




"Mama ba zan iya cin komai ba,zuciyata zafi ta ke min"Safwan da ya makure na duba "Je ka ɗakko min pure water a ciki in yi alwala"




Ina alwalar ya same ni "Mommy nima zan yi in yiwa Aysha addu'a" tare muka shiga jera salloli tun ina ƙarda abin da nake faɗa har na kasa tantance abin da na ke yi.






Carbin da ke hannuna na ke izawa batare da tantance abin da nake faɗa ba,na ji dawowar Safwan wurin ya zauna a kusa da ni.


Sakanni suka shuɗe,mintuna ma suka zo suka wuce,har muka kwashe awanni a zaman jiran tsammani.Dukan mu munyi jugum,ba wanda ya iya kai lomar abinci a bakinshi,hatta Lawal har wata rama ya yi.




Zabura mu ka yi dukanmu ganin fitowar likitan da muke dakon, jira,rige-rigen isa wurinshi mu ka yi tsakanin ni da Lawal.




"Doctor yaya? An yi nasara dai ko?" Lawal ya tambaya cikin wata iriyar murya da ban taɓa sanin shi da ita ba,Ido na zubawa likitan ganin ya yi shiru yana kallon mu.




Yaya Isma'il ne ya matso shima a sanyaye yace "Lafiya dai Doctor? Ina yarinyar?"




"Sai dai kuyi haƙuri,uban gijin da ya fi mu sonta ya ƙarɓi abar shi" na ji wani kalar sauti mara daɗi na faɗa,yawun bakina suka kafe,bugun zuciyata ya rikiɗe,jiri naji ya fara ɗiba ta,lalube na dinga yi don in sami wanda zan jingina da shi.




"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" naji muryoyi mabanbanta suna shiga dodon kunnena.




"Subhanallah ku tare ta, Zainab,Zainab Innalillahi" na ji ana faɗa bayan gilmawar wani baƙin ƙyalle a ido na,tare da kasa samun nasarar riƙe numfashina.




Bansan ya na kasance ba tsawon lokaci,sai dai na farka ne a wani irin mugun yanayi.Zabura na yi bayan dawowar numfashina tare da motsawar gangar jikina.




Waige-waige na shiga yi sannan na sauke ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ina dafe ƙirjina da ya min nauyi Ummi da ƴan uwana da ke zagaye da ni na kalla.




"Wai...Alhamdulillah,na gode Allah da ya kasance mafarki na ke yi" na faɗa ina jimƙe hannuwana wuri ɗaya sannan na dubi Ummi ina zare idona "Wai fa Ummi mafarki na yi wai Aysha ta rasu,Ayshata fa Ummi wai ita ta rasu" Na ƙarasa wasu hawaye na zubomin tare da Wani murmushi.




Rungumeni Anty Halima tayi tana bubbuga bayana ina jin yadda hawayenta ke zubomin a kafaɗata.Ni sai yanzu ma na lura ba gida ba ne,hannuna na duba da ke ɗaure da drip,hannuna da ba a sawa drip ba na ɗaga tare da ture ta daga kafaɗata ina nuna mata hannuna "Me nene wannan Anty? Me kuma ya same ni da aka kawo ni asibiti? Ai yanzu na rabu da Lawal ko? Dama shine kullum ya ke zama silar zuwana asibiti,don Allah ku faɗa min me ke faruwa"




Shiru kowa ya min sai hawayen da wasu ke zubarwa,cikin raunin muryar da ke gab da fashewa da kuka na ce "Kar ku cemin mafarkina ne ya tabbata,ina Aysha? ko dagaske ta rasu?




Ganin wannan karon ma kowa yana sharar hawaye yasa na fizge allurar ruwan da ke jikina tare da ƙoƙarin sauka daga gadon.Riƙe ni Anty Halima tayi,cikin wani irin kuzari na shiga ƙoƙarin fizgewa daga jikinta,ganin kamar ba za ta iya ba yasa Anty Nasma matsowa suka riƙeni.




"Ku sake ni,don girman Allah ku barni naje na dubo ƴata,batada lafiya,Aiki za a mata,kuma na mata alƙawarin tafiya da ita da zarar ta ji sauƙi.Ku daina riƙeni,kar ta mutu dagaske,don Allah" na ƙarasa tare da sauke kaina a kafaɗar Anty Halima.






Banason sauraren zuciyata da ke son tunatar da ni Aysha ta mutu,dagaske kenan Aysha tafiya ta yi ta barni bayan tasha faɗa min tana ƙaunata,shikenan na rasa ƴata,ƴaƴana su ne farin cikina.




A hankali na taka gaban Ummi da ke zaune kan kujera tana sharar hawaye da gefen hijabinta.Guiwowina na zube tare da ɗora kaina akan cinyar ta "Ke gani ko Ummi? Aysha tafiya ta yi ta barni,Ummi,kimin addu'a,zuciyata zafi ta ke min Ummi"






Hannunta ta ɗora akan bayana "Kiyi haƙuri Zainab,kiyi haƙuri,ba ke kaɗai ki ka yi rashin A'isha ba,dukanmu mun yi rashi,amma ki daure ki bita da addu'a kawai kinji"




Wani irin kuka na fashe da shi,ta tabbata na rasa Aysha kenan? Kalaman Ummi sun tabbatar min.Mutuwar Aysha ta girgiza ni ba kaɗan ba,lokaci ɗaya na zabge na fita hayyacina.




Daƙyar na karɓi loma biyu a hannun Gwaggo na saka a cikina bayan lallashin da ta min kafin na ci.ƙoƙarin kwanciya na ke Ya Bashir ya shigo tare da matar shi,ashe tare suka zo,ɗazun shi kaɗai ya zo sai Gwaggo.




Sannu ya min cikin matuƙar tausayawa tare da miƙawa Gwaggo ledar da ya shigo da ita "Ki bata ko fruit ɗinnan ta sha zama da yunwa ba daɗi"ya faɗa tare da kallon matar shi da ta kame a tsaye ta naɗe hannuwa.






Kamar wadda aka yiwa dole tace "Sannu,Allah ya gafarta mata"




"Amin" na amsa daƙyar saboda zuciyata da ke min zafi sosai,gyara kwanciyata na yi akan gadon ina jin kamar nayi tsuntsuwa na ganni a gida,na gaji da asibitin,gida nake buƙata.






"Kaina na ɗago daga kwancen nace "Ummi ina Safwan?






Matsowa tayi tare da kama hannuna "Safwan yana nan lafiya Zainab yana can tare da Mahaifnshi,shima Lawal ɗin ba lafiyar ce da shi ba,na so ya dawo wurin mu kafin a gama makoki amma ya roƙi alfarmar a bar mishi shi"




Cikin raunin muryar da ke gab da fashewa da kuka nace "Ummi don Allah ki min izini in karɓo Safwan,wallahi Ummi kashe shi zai yi shima,don Allah Ummi ki taimaka ki bari in karɓo shi" na ƙarasa ina ɓarkewa da kuka.


















RUMAISA'U SIDI




AURE DA KARATU

NA


RUMAISA'U SIDI






Page 26




A bazata na ji ta fara magana "Ki daina kuka In sha Allah Safwan zai dawo hannunki,ko yanzu koma ba yanzu ba.Ina so ki cire tunanin Lawal ne silar mutuwar A'isha,ko da wannan ciwon ko ba da shi ba lokacin ta ya riga yayi,kuma yadda kike iƙirarin A'isha ƴarki ce,kar ki manta shima fa Lawal ƴarshi ce.Don haka ki cire tunanin wani abu zai sami Safwan itama A'isha lokacin ta ne yayi"




Jagwab na maida kaina na kwantar,hawaye na bin gefen idona yana sauka kan filon da nake kwance.Shikenan ni ba zan yi farin ciki ba? Yanzu shima Safwan ina kallo zan rasa shi?Eh naji kamar yadda Ummi tace ba Lawal ne ya kashe Aysha ba,amma ai da gudummawar shi komai ya faru.




Saida na ƙara kwana a ka sallameni,na koma gida domin in ci gaba da jinyar zuciyata.Bayan mutuwar mahaifina ko mutuwar aurena bai girgiza ni kamar mutuwar Aysha ba,da nasan haka zai faru da ban baro su ba,da nasan haka zai faru da ita zan karɓo,da nasan...............






kuka na fashe da shi a fili nace "Da nasan haka zai faru da ban auri Lawal ba" haka na dinga gunjin kuka ina kallon fuskata da ta kumbura a jikin mirrow da ke toilet ɗin ɗakin.






"Subhanallah,Zainab kuka kuma? Ki buɗe don Allah" daƙyar na isa na buɗe ƙofar tare da rungume Anty Halima.A bakin gado ta zaunar da ni tare da isa kan mirrow na ta yago tissue ta zo tana share min hawaye da ke min malala.




"Ki daina kuka don Allah Zainab,haba kar ki bari imaninki ya taɓu don Allah" haka ta ci gaba da lallashina har na samu na taushe abin da ke tasomin.




Kaina na ɗago ina dubanta "Don Allah Anty kimin wata alfarma"






"Wace alfarma kenan?Ki faɗi duk alfarmar da kike so,in har bata fi ƙarfina ba zan miki"




Hannuwanta na riƙe "So nake ki rakani wani gurin,ba zan iya tuƙi ba" cikin sauri na shirya tare da zuba hijab ɗina muka fito.




Wurin Ummi na je cikin sanyayyar murya nace "Ummi fita za muyi tare da Anty Halima,ba jimawa za muyi ba" goshina ta taɓa "Har yanzu jikinki da zafi Zainab,ina za ki je bayan mutane na shigowa yi miki gaisuwa"




Hannun nata na riƙe "Ummi dagaske ba jimawa zamu yi ba,yanzu nan zamu dawo"




Hararar Anty Halima Ya Bashir yayi "Kina ganin bata da lafiya,za ki wani jata yawo ko?




Bakinta ta dafe "Nifa Yaya rakiya kawai zanyi"




Sai da muka lula a titin sannan ta dube ni "Ina muka nufa shalelen Ya Bashir?




"Gidan Lawal zaki kaini" na faɗa cikin dakakkiyar muryar da ke bayyanar da ƙunar da ke cin zuciyata.Kallo ɗaya ta min ta juya ta ci gaba da tuƙinta.






A ƙofar gidan muka yi parking ita ta fara fita sannan na buɗe gaban motar nima na fito.Ƙofar gidan Anty Halima ta nufa tare da tura get ɗin,waigowa tayi ta dube ni "Muje a buɗe ya ke"




Bayanta na bi muka shiga,tsakar gidan tarr da hasken wutar lantarki.ƙofar falon muka isa,ita ta ƙwanƙwasa,amma shiru ba motsi sai da muka ƙara yi sannan naji alamar ana buɗe ƙofar.




Kallon mamaki ya tsaya yana min bayan ya buɗe mana ƙofar,hanya ya bani ganin ina shirin bangaje shi in wuce.Sai da nazo tsakiyar falon sannan na fara magana ina kallonshi






"Ina ɗana? Yau zuwa nayi ko ni ko kai Lawal,amma yau ba zan bar Safwan a hannunka shima ka kashe shi kamar yadda ka kashe Aysha ba.Dole ka bani ɗana" na ƙarasa da hargowa tare da yi cikin shi kamar wadda zata dake shi.






Wani kallo ya ke bina da shi mai kamada na tsoro da kuma nadama "Kema kin yarda ni na kashe Aysha ko Zainab?Dagaske ni na kashe ta ko? Mama tace ni na kasheta,hakama Safwan yace baya sona saboda ni na kashe Aysha" ya ƙarasa yana nuna kanshi,ƙwalla na taruwa a idanunshi






Zubewa yayi akan guiwowinshi tare da haɗe hannayenshi "Ina roƙonki ki yafemin Zainab,kuma ki roƙamin ƴaƴana su yafemin,na yarda,wallahi na yarda ni na kashe Aysha,sakacina ne ya jefa ƴarmu a halinda ta shiga.Tun bayan tafiyarki ban ƙara bacci mai daɗi ba,ban ƙara yin nadama ba sai da na rasa Aysha.Na rasa Aysha ne a bisa sakacina,da ace ina kula da ƴaƴana da hakan bata faru ba,nayi nadama,wallahi nayi nadama marar iyaka.Na rasa Aysha,shima Safwan ya faɗa min baya sona wurinki zai koma saboda kinfi kula da su,alfarma ɗaya zan roƙa a wurinki Zainab,don Allah kar ki rabani da Safwan,na ɗaun alƙawarin shiga kasuwa koda da dako ne in ciyadda shi da abinci mai gina jiki,zan yi haƙuri in jure wulaƙancin koma wanene saboda in kyautata rayuwar yarana.Laifina a gareki mai girma ne Zainab,na cutar da ke,na cutar da yaranmu ki yafemin don Allah" ya ƙarasa tare da fashewa da kuka.






Zubewa na yi tsakiyar falon "Ka cuce ni Lawal,kaine silar komai,kai ka tarwatsa komai,bana jin zan iya yafema Lawal kuma bazan iya barma yarona ba" hannuna Anty Halima ta riƙo "Tashi mu tafi Zainab"




Hannun na fizge "Ba inda zan je Anty sai ya bani ɗana,bazan taɓa yarda da ƙaryar Lawal ba,mutumin da ya kasa zaman kasuwa ya nema shine zai faɗa miki zai yi dako ki yarda?Wallahi na ƙare yarda da Lawal Anty"




Gunjin kuka ya ke kamar wani ƙaramin yaro,abin da ban taɓa gani ba a iya tsawon zaman mu da shi "Na gane kuskurena,wallahi na gane"haka ya dinga maimaitawa har na yi nisa da ƙofar falon.






Kuka nake har muka doshi isa gida,sannan Anty Halima tayi parking ɗin motar ta waigo ta dube ni "Ban taɓa tunanin akwai abinda zai zo naji tausayin Lawal ba,amma yau daga yadda ya




koma ya isa ka fahimci nadamar da ya ke ciki.Zainab,ko kina so,ko bakya so Lawal uban ƴaƴanki ne,duk abin da ya same shi kamar ya same ki ne walau na farin ciki ko akasin hakan,a ganina tunda har ya nuna yayi nadama kuma ya gane kuskurenshi,to ki bashi lokaci ki gani.Ko ba komai shi mahaifin Safwan ne yana da ikon riƙonshi a hannunshi kuma yana da ikon hanaki har Amna da ke hannunki.Shawarar da zan baki,ki bar Safwan a hannunshi na ɗan lokaci ki gani,ki ba shi dama kamar yadda ya roƙa"






Har dare yayi na kasa bacci ina tunanin shawarar da Anty Halima ta bani,da kuma halin da na sami Lawal a ciki.Anya kwa Lawal zai yi nadama?




Ba dan na so ba na ƙyale Safwan a hannun Lawal,ina ci gaba da kula da Amna da kuma jinyar zuciyata akan rashin ƴata.Ga karatuna da muka zo gargara dole na mayadda hankalina.






Rufe gambun motata na yi,ina kallon motar Ya Bashir da ke fake a wurin ajiye motoci.To duka yaushe ya koma?




"Allah dai yasa lafiya" na faɗa ina nufar cikin gidan da kuma fargabar abin da zan tarar.






Daga yadda na same su a falon suna fira na sauke ajiyar zuciya don nasan lafiya. Gaida shi na yi da tambayar su Gwaggo da takwarata.






"Dukansu suna lafiya,sun ce a gaida ki" ya bani amsa yana bina da kallo.Ummi na gaida tare da nufar ɗakina,wanka na yi na sauya kaya,ina duba wayata Ummi ta shigo.






"Kiyi ki kammala shirinki,wurinki ya zo" Ummi ta faɗa ba alamar wasa a fuskarta.






"Wurina kuma Ummi?"na faɗa ina zare idona.Ƙara ɗaure fuska ta yi "Eh wurinki kuma wallahi in za kiyi hankali wannan karon kiyi,idan kuma ba za kiyi ba,kije kiyi duk yadda kike so.Ni dai iyakata da ke in faɗa miki gaskiya,a baya kinƙi Bashir ne saboda kina da Lawal,to yanzu ya rage na ki,ki zaɓi abin da ya cancanta a rayuwarki ko akasin hakan" daga haka ta juya ta bar ɗakin.






"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"na faɗa tare da dafe kaina,ya ake so na yi wai ina zan saka kaina????????










RUMAISA'U SIDI






AURE DA KARATU


NA


RUMAISA'U SIDI


FARAR ANIYA WRITERS


Page 27




A gurguje na shirya cikin riga da sket ɗin atamfa da suka min cif tare da mayafin da ya dace da shi,kallon kaina na yi a madubi,wai ni ce zan fita,kuma a matsayin bazawarar da za ta fita zance.




Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi " Allah ka shiga lamarina"




Bayan gida na fita ganin ba ya falon,tun daga nesa na hange shi yana zaune kan ɗaya daga cikin kujerun da ke gidan da wayarshi a hannunshi yana latsawa,ga kuma kayan motsa baki a gabanshi.






Sallama na mishi sannan na ja kujerar nima na zauna,kallona ya dinga yi bayan ya amsa min sallamata "Ya ƙarin haƙuri?




"Alhamdulillah"na bashi amsa a taƙaice.Zamanshi ya gyara sannan ya fuskance ni "Har na tafi hankalina ya kasa kwanciya,na ga ya dace dukanmu mu san inda muka nufa.Daga ni har ke ba ƙananan yara ba ne,mun wuce wannan Zainab,shi ya sa kawai na yanke in zo don in san matsayina,ki faɗa min Zainab,wannan karon za ki karɓe ni ko kuma yanzu ma ki na da wanda ki ke so?






Shiru na yi ina wasa da gefen gyalena a hankali na ɗago na watsa mishi fararen idanuwana sannan na sauke kaina ƙasa "Ka daina tunanin bana ƙaunar ka Ya Bashir,kai ɗan uwana ne ina ƙaunarka kamar yadda na ke ƙaunar su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login