Showing 33001 words to 36000 words out of 80263 words
shiga waresu ahankali, he was still staring at her ya durk'usa gefen fuskarta wearing a killer smile, wanda shi kanshi ba zai ce na menene ba.
Ahankali yasa two soft hands d'inshi ya d'an gyara mata kwanciyarta.
"Ya zagaya gefenta ya kwanta ya dauki three pillows ya yi musu tsakani, kamar jira take ya rufe idanunshi tafara wani shegen snoring a firgice Aliyu ya bud'e idanuwanshi, don tabbatar ita ce take snoring ya lek'a fuskarta duk da d'akin diff light ne bai hanashi, hango yadda snoring d'in ke fita daga bakinta ba.
A tsoro ce ya janye yana dafe goshi mik'ewa ya yi ya nemo auduga ya toshe kunnayenshi, ya ja duvet ya rufe jikinshi can cikin bacci ya ji ta fincike duvet d'in ta rufawa nata jiki, hakan ba k'aramin k'ona mishi rai ya yi ba.
Afusace ya fizge duvet ya girgiza shoulders ta ya ce ke tashi maza ki barmin d'akin.
Ba zai yu ki hanani bacci ba nida d'akina.
wani juyi ta yi ta cigaba da baccinta.
"Mtsss....ya ja tsaki yana hararata ya kwanta can tsakiyar dare har baccinshi yafara d'adi yaji wani shegen kick a d'uwawunshi, ya tashi atsoroce cikin angry face yake kallonta.
"Ya rabbi help me this girl gonna kill me, yafad'a dafe da goshi ya sauka daga gado ya jefa mata bargon yana fad'i gashinan ki cinye duvet d'in mayya kawai.
Kan resting chair ya koma ya kwanta sannan ya sami bacci saidai ba mai dad'i ba
Kiran sallar asuba ne ya tashe shi, ya tashi yana dafe goshi, sakamakon rashin samu wadattace bacci ya jawo mishi headache ya juya ya kalli kan gado sai sharar baccinta take yi.
Ta rungume pillow a k'irjinta.
Dauke idanuwanshi ya yi daga kallonta, ya mik'e tsaye da kyar yana rangaji ya shiga bathroom.
Ya dauro alwala canza kayan jikinshi zuwa farar jallabiya, da farko har ya yi niyar ya yi tafiyarshi masjid ba zai tashe ta ba, sai kuma ya ga rashin dacewar hakan.
"Cike da mugunta ya zuba mata wani shegen duka a gadon baya, saida ta gantsare kafin tayi nasarar kwalla jahilin ihu mai barazanar doshen dodon kunne Aliyu.
"Da sauri ya fice daga d'akin yana murmushin mugunta.
Fitarshi yasa tadawo da natsuwarta ta fahimci idan take, sosai mamaki ya rufeta da ta tuna abinda ya kawota d'akinshi har bacci ya dauketa.
"K'ayattace murmushi ta yi ta d'an bige bayan k'eyarta, sai kawai take ji wani irin nishad'i ta jima sosai tana blushing kamar wacce aka yi wa albishir da mallakar zuciyar Aliyu....lol.
Jin footsteps dinshi ya nufo d'akin yasa ta mik'e da gudu ta shiga bathroom, koda tafito har ya shigo yana zaune akan resting chair closing his two eye's ta kalle shi asanyayye kafin ta dauki hijab da praymat ta yi sallah, tana gama sallah ta ce "Ina kwana Yalla6ai?"
Ya bud'e idanuwanshi masu cike da bacci, saida ya yatsine fuska kafin ya ce banganshi ba.
Zaro manyan idanuwanta tayi masu kamar da an diga mata zaiba, tana kallonshi ba ki bud'e.
Kafin tayi magana ya katseta ta hanyar cewa tashi ki je had'a mana breakfast, idan kin kammala ki zo ki tasheni.
Ta mik'e tana murmushi ta nufi k'ofar fita ya bi ta da kallo, tana ficewa ya sauke k'atuwar ajiyar zuciya.
Ya haye bed had'e da switch off d'in bulb.
Ga mamankinshi a maimakon ya yi bacci sai ya tsince kanshi da tunaninta, tsawon lokaci ya dauka kafin ya samu bacci ya dauke shi.
Tana bari d'akin ta shiga nata ta canza kayan jikinta, ta shiga kitchen a gaggauce ta had'a breakfast, ta shirya table, sannan ta koma d'akinta tayi wanka ta shirya tsaf.....cikin atamfar super exclusive d'ikin skirt and blouse kayan sun kar6i jikinta sosai tayi kyau na ban mamaki tayi dauri d'an kwali Zarah buhari, ta kammala komai sannan ta nufi d'akinshi, ta samu ya tashi har ya shiga wanka, ta isa ga gadonshi ta shiga gyarawa, tana cikin gyara gadon ya fito daga bathroom sanye da bathrobe ta dauke kanta daga gefen da yake tsaye, tana gama gyarawa ta fice daga d'akin.
misalin k'arfe 11:00 na safe suka bar gidansu zuwa Airports, Isah direba na sauke su ya yi sallama da Aliyu saboda zai shi yi driving motar barrister A zuwa Abuja.
"Lokaci da flight d'insu ya yi landing direban Daddy ne ya dauko su.
Tun da suka fito daga Airports take kallon hanyoyin da direban yake bi, har suka iso Ardo mansion.
Da gudu gateman da security d'in gidan suka iso wajensu, suna gaida su ta amsa fuska sake har ma da wani d'an siririn murmushi.
Ta fito daga mota tabi bayan Aliyu sun iso flat dinshi ya ciro keys ya bud'e k'ofa suka shiga daga ciki.
Gate man ya shigo musu da kayansu, cikin mintuna k'alilan ta d'anyi nazarin falon k'asa duk abinda ke ciki kama daga cushion har zuwa painting falon white colour ne, kamar dai yadda gidansu na Yola yake saidai wannan yafi na Yola had'uwa.
"Ki hau sama mana"
Muryarshi ta daki dodon kunnenta, ta juya cikin salon tafiyarta ta bi steps ta hau saman saidai ta ja ta yi tsaye sakamakon rashin sani wane daga cikin k'ofufin da ta samu ne, nata.
Bata jima da tsayuwa ba ya shigo ya ra6ata ya nufi wata k'ofa ya bud'e, ta bi bayanshi.
Nan ma parlour ne ya sha kayan alatu na more rayuwa.
"Ya nuna mata wata k'ofa can k'asan mak'oshi ya ce ga sasshenki anan, yak'arasa magana had'e da mik'a mata key, ya shige d'akin da take tunanin shine na baccinshi.
"Ta kad'a kanta ta bud'e falon ta shiga ta wuce bedroom, ta ajiye jakkarta da mayafi ta shiga gyara wurin saida ta gama, tanufi nashi ta gyara taji motsinshi a bathroom, agaggauce ta shiga gyara d'akin koda yafito har ta kammala ta fice, ta gyara mishi falo, sannan ta sauka k'asa nan ma ta gyare shi tass....ta shiga kitchen ta yi nazarinshi nan ma ta tsafta ce shi, gaba d'aya gidan ya dauki k'amshi na fitar hankali.
Ta koma d'akinta ta yi wanka ta had'o da alwala, da yake lokacin sallar azhar ya yi ta yi sallah.
Sannan ta tsantsara simple makeup, ta dauko luggage d'inta ta ciro Arabian gown purple colour, tasaka tayi rolling da white veil.
"Tana cikin fesa perfume ya turo k'ofa ya shigo shima ya sauya kayan jikinshi, zuwa white chino trouser had'e da mandarin long sleeve, ya nad'e hannayen rigar.
"K'amshinta ya had'e da nashi ya k'ara k'amsasa d'akin.
Kallo d'aya ya yi mata ya dauke kai, tayi mishi kyau ba k'adan musanmman da tayi rolling da white veil favorite colour d'inshi.
"Mu je flat d'in momma ki gaisa da su ga alama basu san mun iso ba.
Yana k'arasa magana ya juya ta biyo shi abaya tana k'arewa compound d'in gidan kallo.
A downstairs falo suka iske momma da Zee-Zee momma na waya yayin da zee-zee ke kallon movie.
"Sallamar Aliyu ya dawo da hankalinsu akansu, zee-zee ta tashi cikin farin cikin tayi hugging barrister A.
Lokaci da momma tayi arba da barrister ta ji gabanta, ya yi mummunan fad'uwa da had'ye wasu mushirkai miyau.
"Barrister A ce tafara janye zee-zee daga jikinta, ta durk'usa ta gaida momma ta amsa cikin fara'a saboda tsabar makirci hadda su rungume barrister tana fad'i welcome to the family my daughter ya gajiyar hanya?"
Murmushin jin dad'i barrister A tayi duk tasan wannan welcoming da momma tayi mata bai gansheta ba
Aliyu ya nufi one sitter ya zauna ya yi crossing legs d'inshi, shi ma ya gaida momma ta amsa tana washe hak'ora.
"Sultan ashe kuna hanya?"
Uhm....!
Yafad'a kamar an mishi dole.
To miyasa jiya da dare da mu kayi waya ba ka fad'amin yau za ku zo ba?"
"Na manta ne!
Ya fad'a yana yatsina.
Kodai ka fad'awa Daddynka, ni ce da ka rena ba ka fad'awa ba?
Omg.....momma please banaso irin tambayoyin nan naki, sosai suke haifa min da ciwon kai.
Ya k'arasa magana yana turo miki.
"K'atuwar harara momma ta wulga masa afakace, a fili Kuma ta k'ikk'iro murmushin dole ta ce haba gadangana don nuna damuwa na akanka laifi ne?"
"Wani shegen murmushi Aliyu ya yi kafin ya ce kai....momma na fahimci yau K'orafi ki ke ji, to Allah ya ba ki hak'uri.
"Zee-zee ta rik'o hannun barrister A zo mu tafi matar Yaya d'akinmu mu yi fira, wallahi ina cike da farin ciki zuwanki gidanan ba k'adan ba.
"Nasan ko Meenat idan tadawo daga school ta ganki, haukace mana za tayi, saboda tun lokaci bikinku bakinta bai huta da zance ki ba.
"Teema ma za tayi farin cikin ganinki.
Barrister A tayi murmushi ta sace kallon Aliyu, karaf.....suka had'a idanu ya kashe mata idonshi d'aya batasan lokaci da ta lumshe golden eyes d'inta, daga bisani ta bud'e su fesss......akanshi tayi mishi k'ayatattce murmushi, sannan ta bi bayan Zee-zee har suka shige d'akin idanuwan Aliyu suna kanta.
"A lokaci da za'a auna Bp momma za'a iske ya haura d'ari biyu da tamani, tsabar kad'uwa gani abinda Aliyu yake yi wa barrister babban tashin hankalinta bai wuce mayatattace kallon da ya bi ta da shi ba.
"Da kyar ta tattaro 'yar raguwar natsuwarta ta had'a da k'arfin hali ta dube Aliyu da idanuwanta ba bu komai ciki face tashin hankali.
"Sul....tan....!
Ta kira sunanshi cikin rawar murya.
Na'am!"
Ya amsa yana kallonta.
Da fatar kana zaune lafiya da iyalinka?"
"Lafiya qalau momma ba wani matsala.
Shiru ya biyo baya jikin momma ya yi sanyi tana so ta tambayeshi yana had'a shinfid'a da barrister, tana jin tsoron amsar da zai bata.
"Sai kawai tayi ta maza ta gyara zamanta, tana mushirikin murmushi ta ce ina fatar kana sauke hakkinta yadda ya kamata?"
Kallon mamaki yake mata sai kuma ya murmusa tsaff....ya gane idan ta dosa sai ya ce sosai ma kuwa momma duk abinda takeso ina mata.
"Gaban momma ya cigaba da dukan tara-tara babban tashin hankalinta bai wuce asiri da Jarumi ya bata na kashewa Aliyu mazak'uta, sai gashi Aliyu yana fad'a mata yana shagalinshi to.....ina zance asiri da suka yi mishi ana nufi ya karye.
"Gani yadda ta k'ura mishi idanu ba ko kaftawa yasa ya ce lafiya momma naga kin tsareni da ido, kuma kinyi shiru?"
"Ta shiga kame-kame daga bisani ta yi nasarar cewa anyya kuwa Gadanga kana had'a shinfid'a da yarinyar nan?"
Sam banga jikinta ya nuna hakan ba.
Tafad'a tana tsare shi da idanu, sosai wannan tambayarta ta tabashi haushi da takaici ya 6ata fuska ya ce ki tambayeta momma za ta fad'a miki ko yau kafin mu baro Yola muna tare a d'aki d'aya.
"Please....momma ki daina irin wannan bincike bashida amfani, ni fa ba k'aramin yaro bane duk wani hakke aure nasani.
Kuma ina k'ok'arin sauke shi.
"Ni zan fita sai na dawo."
Ya k'arasa magana had'e da mik'ewa.
A dawo lafiya!
Cewar momma cikin yana yi na tsoro.
"Kaitsaye d'akinsu Zee-ze ya wuce ya tararda su suna fira yayin da Teema na kwance a jikin barrister, sai wasa take da dogon bak'in gashinta.
"Sosai hakan ya yi mishi dad'i saboda yana k'aunar siblings d'inshi ba kad'an ba miskilancinshi ke hanashi nuna musu hakan.
"Tsaye ya yi a bakin k'ofa yana kallonsu da girar ido d'age, Teema na arba da shi ta sha jinin jikinta saboda Allah ya zuba mata tsoronshi.
"Zan fita"
Yafad'a k'asan mak'oshi.
Atsanake tad'ago tana fad'i adawo lafiya Allah ya bada sa'a!
Amin nagode!
Har juya ya sake waigowa ya ce Zainab ba abinci agidan naku ne da ba ki kawo mata ba?"
Ko tsabar rashin iya tar6o guest ne?"
"Cike da tsoro Zee-zee ta ce Yaya kasan momma bata bari adafa abinci da yawa.
Mtsss.....ya ja tsaki had'e da barin d'akin yana cewa ki tabbata kin gayawa chef Emmanuel ya girka mata abinda za ta ci.
Jeeddah Aliyu
[7/27, 12:02 AM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619
DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA
*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```
*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```
*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``
*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN
*SLIMZY*:- IZZATA
*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO
*GIDAN RINA*
Not edited!
*23*
Yana k'arasa fita zee-zee ta kalleta tana dariya ta ce gaskiya matar Yaya Yayanmu yana ji da ke, Allah yasa kema haka ki ke ji da shi.
'Yar siriryar dariya tayi ta ce sosai ma kuwa.
Momma wacce tun fitar Aliyu take la6e tana sauraren firar tasu, ta zaro manyan idanuta tana huci, bankad'o k'ofar tayi ba ko sallama ta bi su da kallo.
Gani yadda suma suke kallonta yasa ta wayace ta ce Emmanuel girkin Alhaji zai doura yanzu, Zee-zee ta bi ki ku je flat dinku ta tayaki ki girkawa mijinki abinda zai ci.
"Da sauri Zee-zee ta d'ago tana kallon momma cike da zallan mamaki, ta ce "momma yaushe na iya girki da har zan tayata?"
ki bar Emma ya dafa mata koda noodles ne.
makirin murmushi momma tayi kafin ta ce "miye amfaninta idan bata girkawa mijinta abinci ba?"
Idan ke ba ki iya ba ai ita ta iya
daga yau ki fara girkawa mijinki abinci kinji my daughter?"
Ajiyar zuciya barrister A tayi tana mai cigaba da kallon momma tana karanta yana yinta.
"Har zee-zee za ta sake yin magana barrister A ta katseta da sauri ta hanyar cewa, to momma!
"Momma tayi murmushin mugunta saboda ganinta barrister A ta taso gidan huta uwa-uba yana yin aikinta yaushe take da lokaci shiga kitchen har ta iya wani abu wai shi girki.
Atunaninta tun daga wurin girki za su fara samun matsala da Aliyu saboda ta san halinshi da tsirfa, ba ko ne irin abinci yake ci ba.
Saboda haka shiyasa tayi amfani da wannan damar tafara aiwatar da nufinta akansu.
"Shikenan my daughter tashi maza ku tafi ki had'awa yarona delicious, yana ci kunnenshi na motsi.
Ta k'arasa magana tana washe hak'ora na kissa da kissisina.
Hannun Zee-zee barrister A ta rik'o zo mu je Zee ki tayani kema daga yau ki fara learning.
"Ni ma zan je matar Yayanmu!
Cewar Teema tana sosa gashin kanta.
Kafin barrister A tayi magana har momma ta rigata cewa kema bi su ki koya.
"Har suka fice daga d'akin momma tana murmushinta na zallan mugunta.
Da suke iso compound idanuwan barrister A suka hango apartment d'in Maryam, ta k'urawa wurin idanu tana mamaki yadda aka bar barandar wurin tayi k'ura, musanmman da tayi la'akari ko ina na gidan tsaf-tsaf yake idan ka cire wurin.
Ajiyar zuciya ta yi ta kauda ganinta suka k'arasa flat d'inta.
A falon k'asa suka zauna zee-zee ta had'a kayan kallo, suna cikin kallo aka yi kiran sallar la'asar, har barrister A tayi sallah ta dawo bata ga alamar Zee-zee da Teema zasu tashi suyi sallah ba.
Sai tunanin dukansu suna period ne, don haka ta share su suka cigaba da kallonsu.
"K'arfe 5:00 ta buga Zee-zee ta kalli barrister A ta ce matar Yaya kin ce sai kin yi sallah, za mu doura girki gashi har 5:00 o'clock ya yi.
"Barrister A tayi murmushi tana fad'i ko za mu fara girki nan zee-zee saidai gobe, saboda na duba a store ba foodstuffs, kinga zuwa gobe Yayanki zai siyo.
"Shikenan matar Yaya bari na je sai na fad'awa momma tunda ita store d'inta akwai sai, tasa akawo muku.
"Ba sai kin fad'a mata ba maybe fitarnan da ya yi zai dawo da su.
Daga haka su ka cigaba da firarsu har meenat ta dawo daga school, ta shigo da murnarta na gani matar yayan nata.
"Lokaci sallar magarib ya yi still barrister A ce kawai tayi sallah, sosai abin ya daure mata kai matuk'a ana nufi su duka uku suna menstruation period.
Sai kuma tabar tambayar k'asan zuciyarta.
Saida momma ta kira wayar meenat sannan suka koma flat dinsu, amma ba don ransu yaso ba sun so tabarsu sai Aliyu ya dawo.
"Bayan tafiyarsu barrister A ta haura sama tayi wanka, ta shirya cikin California candy strip ba k'aramin kyau rigar tayi mata ba.
Zanin ta doura akan rigar sakamakon tsagar da rigar take da a side by side, tayi sallar isha'i tana gama sallah ta cire zanin ta like ta mayar a closet ta fice zuwa downstairs falo.
"Misalin k'arfe 9:00 na dare Aliyu ya murd'a k'ofa ya shigo cikin sallama, ta mik'e tsaye tana amsa mashi tare da yi mishi sannu da zuwa, sannan ta isa wajen shi ta kar6i ledojin da ya shigo da su.
"Ya amsa gaisuwarta yana kallonta kallo ne irin na kwalliyarki ta ban sha'awa, d'an zaman da ya yi da ita akwai abubuwa da dama da ta mallaka da ke matuk'ar d'aukar hankalinshi, abu na farko ta iya kwaliyya ko yaya ta sanya kaya sai sun kar6i jikinta, sun fito da kyakyawar surarta.
"Hakan na dauke mishi hankali ba kad'an ba.
Gashi ta iya tafiya ta jan hankali duk lokaci da take tafiya yana lura da yadda take rausaya, ga66o6in jikinta na motsawa especially hips da boobs d'inta.
Idan kuma ya tsareta da lulu eye's dinshi, k'irjinta da fuskarta suna daukar hankalinshi, idan kuma ya kusanceta k'amshinta yana tafiyarta ruhi da gangar jikinshi, saidai yak'i bari ta gano hakan sau da yawa yana satar kallonta ne batare da saninta ba.
Tana zuba sanyayye murmushinta mai tsada ta wuce kitchen da ledojin da ta kar6a daga hannunshi, ta duba abinda ke ciki kayan tea ne had'e da bread sai shawarma , ice cream da kuma gassassun kaji sai k'amshi ke tashi.
Sai leda ta k'arshe mai dauke da tambari chicken republic