Showing 12001 words to 15000 words out of 80263 words

Chapter 5 - Gidan Rina Book Complete Jidda Aliyu.txt

31 Jan 2025

9437

kalli Amina ya ce please 2 minutes.
Uhmm.....Tafad'a tana mai wasa da zoben hannunta.
Nesa da ita ya yi ya amsa wayar, yana receiving ya kara wayar a kunnenshi hello....momma!
Ya hanya yaron momma?"
"Alhamdulillah....momma mun iso lafiya har muna shiri wucewa sai ga kiranki.
"Uhmm!
Da fatar yarinyar ta yi maka?"
Murmushi ya yi mai sautin gaske had'e da shafar sumar kanshi, ya ce momma za mu yi magana idan na dawo gida lokaci yana k'urewa kada mu yi missing flight d'inmu.
"Daga haka ya katse kira saboda yasan halinta sarai sai tasake, watsu masa wata tambaya.
Daga chan gefe kuma Barrister Amina ta k'ura masa ido tana nazarinsa daga sama har k'asa, tabbas ya amsa sunanshi cikkake namiji domin ya mallaki komai na cikar halitta, ta d'an namiji wanda kowace lafiyayyar mace za ta yi burin mallakarshi a matsayin life partner.
"Ganin ya juyo gareta yasa ta yi gaggawar kauda kanta, ya k'araso daf da ita shi ma kallonta ya yi sosai sannan ya yi gyaran murya tare da kiran sunanta Aminaaa......!
Yadda ya ja sunanta yasa tsigar jikinta tashi yarrrr.....
Ta d'ago ta kalleshi ya ce mu za mu wuce saboda yau za mu koma Abuja, gashi ban yo miki tsarabar komai ba, sai wani lokaci idan Allah yasake had'a mu.
"Murmushi ta yi wanda yak'ara mata kyau ta ce ba komai, nagode da ziyara Allah yakai ku lafiya, ka gaidamin da su mommy.
"Amin...
Ya furta chan k'asan mak'oshi.
Ta juya wajen Jamal ta ce malam Jamal nagode Allah ya kiyayye hanya ka gaida iyali.
"Mu ke da godiya barrister.
Cewar Jamal.
Daga haka ta juya ta nufi cikin gida.
Yayin da Aliyu da Jamal suka shiga mota direba ya ja aka bude musu gate direct Airports ya kai su, ko gidan Uncle Suraj ba su koma ba.
****---****----****
*ABUJA*

Momma zaune akan sofa abin duniya ya taro ya yi mata yawa, tun jiya da Aliyu ya dawo daga Yola har zuwa yau bai bari ta had'u da shi ba.
Yau tun da sassafe ya fice kuma har yanzu yamma lis bai dawo gida ba, ta kira phone d'inshi yafi a kirga saidai ta ji P.A shi ya dauka ya ce yana meeting.
"Mtss...ta ja tsaki daga bisani ta dauki wayarta ta yi dialling, d'aya daga cikin contacts d'inta sunanshi ya bayyana akan wayarta, kamar haka Jarumi!"
Wayar ta shiga ringing kamar ba za'a dauka ba saboda saida ta yi kusan tsikewa, ya yi picking Hello....
Yafad'a ahankali.
"Cikin rawar murya momma ta ce Jarumi akwai gaggarumar matsala da ke shirin tunk'aro mu, idan har mu ka yi sake ta afku shikenan mafalkinmu ya zo karshe.
"Har ta dasa aya a zance ta Jarumi yana saurareta, huce ya yi ya fesar da iska mai zafi daga bakinshi, cike da tafarfasar zuciya ya ce duk abinda yake faruwa nasani kema kuma kin san nasani, yanzu haka ina cikin garin Abuja domin mu nemowa kanmu mafita.
"Ki zo Ina westerns dreams hotel room 402, saboda wannan magana ba ta waya bace gudun kada wani ya jiyo ki lokaci da mu ke magana.
Yana gama magana ya katsi kiran.
A gurguje momma ta nufi bedroom d'inta ta shirya key motarta ta dauka had'e da handbag, ta nufi k'ofar fita kicibuss....ta yi da Tima zaune a k'ofar fita daga main parlour ta wargaje gashi kanta, ya rufe mata fuska.
"Gaban momma ya fad'i....rass!
Cikin sark'ewar halshe momma ta ce Ti....Ti...ma me ki ke yi anan?"
Tashi maza ki koma bedroom d'inki.
"Wata mushirika dariya Tima ta yi mai amon gaske ta ce ba Tima ba ce, rijiya ce mai dauke da kunamu da macizai sun lullu6e wata 'yar jakka mai dauke da kundin sirri.
"kafin kyaftawa ido har Tima ta mik'e kamar walk'iya, ta kai k'ofar d'akinta.
Da mugun tsoro momma ta bi ta da kallo, da kyar ta hadiye yawu sakamakon yadda mak'oshinta ya bushe.
"Har Tima ta kama handle d'in k'ofa ta juyo tasake
Kyalkyalewa da dariya ta ce je ki momma je ki maza kada jirgi ya tashi ya barki ba lalle bane ya dawo daukarki.
"Kafin momma ta yi yunk'uri furta wani abu har Tima ta shige d'akinta.
Mtsss.....!
Momma ta ja tsaki ta girgiza kai tai ficewarta hankali kwance.
Abinda zai ba ka mamaki momma na isa Hotel d'in ta ciro bak'ar jallabiya daga k'asan seat din motarta ta sanya had'e da yane kusan rabin fuskarta, da mayafin rigar, ta ciro wani k'ato black shade ta lullu6e kwayar idonta duk sani da kayi mata ba za ka gane ta ba nan take ba.
"Kaitsaye ta wuce receptionist ta yi magana da ba za ta wuce ta 60 seconds da wanda yake kula da dakunan hotel din.
Sannan ta nufi upstairs ba ta yi wata doguwar tafiya ba ta iso wani dogon corridor, rooms ne birjik.....suna facing juna ahankali take duba d'an k'aramin allo da ke dauke da rooms numbers, har ta yi nasarar gani room 402 hankali kwance ta yi knocking, wani mutum mai matsakanci tsawo fuskarshi lullu6e da face masks kwayar idanuwanshi kawai ka ke iya hangowa ya bude mata k'ofa ta shiga d'akin.






Jeeddah Aliyu
[7/26, 11:50 PM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619


DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA


*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```


*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```


*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``


*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYYATUDEEN


*SLIMZY*:- IZZATA


*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO




*GIDAN RINA*


*9*




Rigar jikinta ta fara cirewa ta jefa bisa gado, ta nemi gefen gadon ta zauna yayin da Jarumi ke safawa da marwa daga farkon bangon gabas zuwa bangon yamma, ya nad'e hannaye a bayanshi.
"Zai kyau ka nemi wuri ka zauna mu yi magana da ke gabanmu.
Cewar Momma tana nuna masa kusa da ita da d'an yatsanta.
Cikin kaukkausar muryarsa mai cike da ban tsoro ya ce ba zan zauna ba Zaituna har sai kin fad'a min ta ya ki ka yi sakaci har asiri da ke jikin Muhammad ya karye, har yake da gwari gwiwar nemowa Aliyu aure?"
"Karka yi min wannan tambayar banza Jarumi saboda banida amsarta, kawai ka nemo mafita ba wai ka tsaya kana dawo da hannun agogo baya ba.
Kukan kura ya yi ya chafke mak'oshinta, ya shek'eta kamar zai rabata da ranta tsananin azaba yasa momma kwantawa ya bi ta ya haye ruwan cikinta, sai da ya ga ta kusa daina motsi sannan yasake ta ya sauka daga kanta.
Yayin da tari ya turnuk'e ta, da kyar ta iya tashi zaune robar ruwan Faro ya dauko a fridge ya jefa mata.
Jikinta na rawa ta balle murfi ta kafa baki tasha rabin ruwan duk ya zube mata a jiki.
Cikin angry Voice ya ce ki shiga taitayinki da ni kinsani sarai banida mutunci, bana d'aya daga cikin mutane da ke jure rainin hankalin tsohuwar kilaki irinki, don haka ki natsu ki saurari irin hasara da ki ka janyo mana.
Ajiyar zuciya mai k'arfin gaske momma tayi, had'e da shafar wuyanta da ke ji tamkar an daure mata shi da igiya, yayin da idanuwanta sun kad'a sun yi jajir.
Afusace Jarumi ya cigaba da cewa duk wurin malamin da na je magana d'aya ce, tabbas sai Aliyu ya yi aure don haka ba mu da za6i illa mu kashe yarinyar bayan aure.
Sai abu na gaba muddin kina so hakkar mu ta cima ruwa, dole sai kin hana Aliyu kusantar yarinyanan malam ya gayamin muddin suka yi tarayya, komai na mu ya rushe duk wani wahala na tsawon shekaru 28 ya rushe.
Hannunshi yasaka a pocket d'in rigar shaddar da ke jikinshi, ya ciro wasu bak'ak'en layu ko kallonsu ka yi sai gabanka ya fad'i ya mik'awa Momma, ki binne su dai-dai wurin da ki ka san Aliyu zai taka.
Hannunta na rawa ta kar6a ta shiga jujjuya su.
Sake dauko wata batta ya yi wacce aka lullu6e da fatar damisa, wannan kuma ki turare shi idan ki ka san Aliyu zai shak'i k'amshinsa karki sake wani ya ji k'amshinsa fa ce Aliyu, kinji ko?"
Gyad'a kai ta yi kafin ta gyara zama muryarta bata fita wtsosai saboda shak'ar da ya yi mata, ta ce ba ka yi min gamsasshe bayani magani na menene?"
"Shiru ya yi kamar ba zai yi magana ba daga bisani ya zauna kusa da ita, ya dafa kafad'arta ya yi kasa da murya tamkar mai rad'a ya ce amfanin wannan magani shine mazakuta Aliyu zai mutum mutusss, koda tsirara ya ga mace ba zai ji sha'awarta ba.
Karki manta sihiri da ke jikinsa na tsanar aure ne da tsanar mata ba na sha'awarsu ba, ki sani kasancewar Aliyu da wannan yarinya a waje d'aya dole wata rana zai ji sha'awarta, idan har ya had'a shinfid'a da ita daga ni har ke kashinmu ya bushe don haka ki kiyayye.
"Shikenan idan wannan ne Jarumi bakada matsala.
Da kyau 'yar gari sai ki tashi ki tafi, na gama magana Sai dai idan wani emergency ya taso zai nemi ki.
Mik'ewa tayi tasaka rigarta da black shade d'inta, ta kuma zuba guzirin shed'an d'in da yabata a handbag.
***---****----****


Da misali k'arfe 5 na yammaci Aliyu yana zaune a office d'inshi, ya duk'ufa akan system dinshi aiki yake sosai.
Aka yi knocking k'ofa yes!
Yafad'a batare da ya kalli me shigowa ba,
Sakatariyarshi ce Ester.
Cikin girmamawa ta ce Sir Jamal ne ya zo kasan da zuwanshi a shigo da shi.
"Sai a lokaci ya d'ago darara idanuwanshi, masu masifar tafiya da imani 'ya mace ya ce ki shigo da shi mana.
Okay sir!
Tafad'a had'e da juyawa.
Bata jima da fita ba Jamal ya shigo hannu ya mik'awa Aliyu suka yi musabaha kafin ya ja kujera ya zauna, ya ake ciki abokina tun jiya yakamata mu tatttauna zance barrister sai dai rashin wadattace lokaci ya hana mu?"
"K'ayattace murmushi Aliyu ya yi ya mayarda laptop dinshi gefe, ya kalli Jamal a natse ya ce gaskiya ba laifi Barrister tana da kyau sosai kuma da alamu tana da kyau hali, sai dai banji sonta ko k'ank'ani ya shiga zuciyata ba, kawai dai yanayin shigarta da yadda take magana ya burge ni, matuk'a.
Amma a haka zan daure na aureta tunda an riga an mak'alk'alamin ita bani da za6i.
"Jamal ya yi murmushi tare da jinjina zance abokin nashi, ya gyara zamanshi yana duban Aliyu cikin sanyaya murya ya ce ina gani tunda har ka amince wannan ba abin damuwa bane duba da biyayya ce za ka yi ma mahaifinka,
"Inaso ka dauki zance da muhimmanci kada kayi halin ko oho da lamarin barrister, ba mamaki ita ma biyayya ce za ta yiwa nata iyayyen ina rok'o ka abokina da kayi abinda ya kamata.
"Ta6e baki Aliyu ya yi yana yatsine fuska "to ni miye nawa aciki?"
Daddy ya ce in shirya naje naga yarinyar na kuma je, bayan nadawo na shaida mishi ta yi sai dai gaskiya ban nuna mishi bana sonta ba, yanzu dai lokaci biki kawai nake jira.
"Ba damuwa abokina idan da rai da lafiya two months kamar gnbe ne, ya.zu yaushe za mu sake komawa waJenta?'
"Banaso a semi matsala daga gareka.
Cewa2 Jamal yana duban Almyu.
"Gaskiya yanzu bani da lokaci akwai d'inbin ayyuka agabana, kuma ma miye amfanin zarya gun yar)nyar da banida ra'ayinta, ina ce sai in kana son mace ka ke d'oki da rawar jiki son ganinta?"
"Gaskiya hakan bai dace ba abokina kadai duba, koda zuwa end of this month ne mu kai mata ziYara wallahi yarinyar tana da kirki matwk'a.
"Shikelan Jamal zan dtba nagani amma a halin da ake ciki yanzu bani la |okaci, sai mu jira zuwa k'arshen wannan watan.
Ba damuwa abokina kadai k'ok'arta.
Dariya Aliyu ya yi a ta{aice$ya ce naga alama kai da barrister ta ku!ta zo d'a}a.
Dariya Jamal 9a yi yana mai mik'a masa hannu suka kashe.
***----***---****
*YOLA*

Barrister Amina tare da Barrister Zarah suka jero suna fitowa daga magistrate couru 3.
Barrister Zarah ta dubi barrister Amina ta ce bebs ya had'uwarku da(Aliyu ta kasance hope guy ya yi miki?"
"Murmushi Barrister Amina tayi tace Ba laifi ya amsa sunanshi namiji yana da kyau sosai da cikar kwarjini, ya had'u irin had'uwar da kowace 'ya mace take buk'ata.
Ya yi miki kenan?"
Ba laifi gaskiya karo na farko a rayuwata da naci karo da namijin da naji farat d'aya ya kwanta min a rai.
Ta k'asara magana tana tunowa da fuskar Aliyu.
masha Allah!
Haka nakeso ji daga gareki bebs fatana Allah ya had'a kawunanku ya kade duk wata fitina da ke ciki.
Amin! Bebs.
****----****-----****
A kwana atashi asarar mai rai yau gashi saura sati uku bikin Aliyu da barrister Amina, zuwa wannan lokaci abubuwa da dama sun faru daga ciki akwai masu dad'i akwai akasin hakan.
"Kud'ad'e masu kauri gaske Daddy ware ya ba k'anwarshi Salma ta je Dubai ta had'owa Aliyu kayan lefe na gani na fad'a taci mutuncin naira ba kad'an ba.
Daddy bai saka momma cikin hidimomin bikin ba, asalima ma bata san da zance lefe ba, sakamakon yadda ya ga tana nuna adawarta akan aure a fili, tun abin yana bashi mamaki har yadawo bashi tsoro lokaci da ya sanarda Salma zance ita ce ta bashi shawarar ya dinga 6oye Mata duk wani abinda ya yashafi zance auren na Aliyu, har zuwa lokaci da za'a yi biki saboda basu san miye manufarta ba.
nan take Daddy ya yi na'am da shawarar Salma saboda shi kanshi lamarin na masifar daure mishi kai.
"Akwati goma sha biyu Salma ta had'a har da tsaddadiyar mota akai kirar cadillac, lokaci da aka kai lefen gidan Barkido ya yi fad'a sosai a cewarshi bayason bidi'a da kyar dangi suka shawo kanshi ya amince aka kar6i kayan.
"Barrister Amina kwance akan gadonta ta yi zurfi a tunanin Aliyu abu d'aya ya ke daura mata kai, ya kuma jefa zuciyarta cikin tunani shi ne tunda Aliyu ya zo sau d'aya bata k'ara jin d'uriyarshi ba.
Sai kayan lefe aka kawo gidansu shin me hakan yake nufi?"
Anya kuwa Aliyu yana sonta?"
Wad'annan su ne tambayoyin da tarasa wanda zai bata amsar su.
"Mtsss....!
Ta ja tsaki ta dauki pillow ta matse gam a k'irjinta, ta d'an girgiza kanta cike da haushin kanta ta tuna da halin da ta tsince kanta, game da Aliyu domin tun daga ranar da idanuwanta suka ganshi, sai tunaninta ya canza zuciyarta ta bijiro mata da wani al'amari mai wuyar fassarawa.
Tsundun ta tsunduma begen Aliyu al'hali shi d'in bai san tana yi ba.
Ba ko shakka tasan ta kamu da soyayyarshi mai zafin gaske, duk da tana da labarin bai cika zama wurin d'aya ba, shi mutum ne mai yawan tafiye-tafiye ak'alla ace yana kiranta a waya ko gaisawa su yi koda bai mata firar soyayya ba.
Yaushe ma ya ga numbernki da zai kira ki.
Wani bangare na zuciyata ya ce da ita.
Yanzu ahaka za su yi aure al'hali bai da lokacinta, kenan hakan za su yi zaman aure?"
A karo na biyu tasake jan tsaki mtsss!
Cike da takaici zuciyarta sai rad'ad'i take mata, sosai take ji zafin kanta yadda ta shiga damuwa akan mutume da bai ma san tana yi ba, asanyaye ta mik'e tashiga bathroom sakamako kiran sallar magarib da aka fara.
***----****----*****
*LAGOS*


Aliyu na zaune a office dinshi da ke Lagos ayyuka sun masa yawa ba kad'an ba, duk da yau ya sami sassaucin aiki, a matukar gajiye ya jingina bayanshi ga jikin kujera da yake zaune akai a hankali ya zare sun shade glass din da ke manne a kwayar idonshi, tare da lumsashe idanuwanshi wayarshi tayi ringing har ta tsinke bai d'aga ba, a karo na biyu tasake ringing sai da ta kusan tsinkewa ya mik'a hannu ya dauka batare ya bud'e idanuwanshi ba ya yi picking ya kara a kunnenshi.
"He...llo!
Yafad'a chan k'asan mak'oshi.
ka ci gidanku Sultan.
Ba shiri Aliyu ya ware idanuwanshi ya kuma gyara zamanshi, sakamakon muryar Daddy da taki dodon kunnenshi.
"Dad ina wuni?"
Ban san inda yake ba.
Cikin shagwa6a Aliyu ya turo baki yana cewa Daddy....am sorry!
Duk da ban san laifi da nayi ba.
Fad'a sosai Daddy ya shiga yi mishi ta hanyar cewa karka maidani mutume banza Gadanga, sau nawa ka je Yola wurin Amina bayan zuwanka na farko?"
"Tsuke fuska ya yi kamar Daddy yana ganinshi, ya ce Daddy am too busy ban samu zuwa ba ayyuka ne suka yi min yawa.






Jeeddah Aliyu
[7/26, 11:50 PM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE IDAN KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619


DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA


*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```


*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```


*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``


*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYYATUDEEN


*SLIMZY*:- IZZATA


*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO




*GIDAN RINA*


*10*


Amma duk lokaci da na samu sassaucin aiki zan shirya in je, amma kuma Daddy sai nake gani ko ban je ba zan iya aika P.A na kamal amadadi na, sai ta yi mishi list na abunda take buk'ata ko nawa ne zan ba t.....
"To hell with you ka da kud'in naka Gadanga.
Daddy ya katse cikin fushi Daddy ya cigaba da cewa an gayamaka komai ne kud'i suke iya siye, in fact yarinyarnan ba 'yar matsiyata ba ce ita kanta mai kud'i ce balle aje ga iyayyenta.
Yadda ka ke tink'aho ubanka mai arziki ne ita ma nata uba mai arziki ne, inaso ka jingine zance kud'i a gefen ka natsu kasan me ka ke yi, saboda kai ba k'aramin yaro bane.
"Aliyu kamar zai fashe da kuka yake shafa sumar kanshi kafin ya ce kayi hak'uri Daddy I don't mean to hurt you am just try to tell you how busy I'm but am so sorry, zan yi k'ok'ari gobe na biyo morning flight nayi weekend a Yola.
"That's my favourite boy haka nakeso ji Gadangana.
kafin Daddy yasake magana ya katse kiran had'e da jefa wayar bisa file d'in da ke gabanshi,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login