Showing 75001 words to 78000 words out of 80263 words

Chapter 26 - Gidan Rina Book Complete Jidda Aliyu.txt

31 Jan 2025

9434

da ke hannun maryama, wanda Aliyu shi ma yana da shi duk da kun cire nashi tun yana jinjiri saboda kada a gano d'an maryama ne amma ta6o hannunshi ne ya toni asirinku nagano shi d'in d'an Maryama ne ba Zaituna ba.












Jeeddah Aliyu
[7/27, 12:30 AM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE IDAN KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619


DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA


*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```


*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```


*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``


*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN


*SLIMZY*:- IZZATA


*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO




_LAST PAGE_


*Ban yi editing ba ku yi hak'uri da errors d'in da za ku ci karo da su*


*40*




*NNAMDI AZIKIWE INTERNATIONAL AIRPORT ABUJA*




Flight d'in da Aliyu ya shigo ya yi landing a Nnamdi azikiwe international airport abuja, batare da ya kira direban shi ba ya bi taxi zuwa hospital d'in da aka kwantar da Daddy.
Koda ya iso Daddy ya farfad'o rana d'aya duk ya zabge ya yi wata bak'ar ya rama, kaman wanda ya shekara yana jinya abin gwanin ban tausayi.
"Cikin yana yi na kariyar zuciya Aliyu ya isa gareshi ya rungume shi tare da fashewa da kuka kaman k'aramin yaro, gani hakan yasa su Zee-zee suka shiga taya shi.
Cikin muryar kuka Zee-zee ta ce "Ya Sultan momma ta gudu an neme ta sama da k'asa a hospital d'inan an rasa.
A fusace Daddy ya katseta ta hanyar cewa "Zainab ba nace kar ku sake yi min zancenta anan wuri ba.
Kayi hak'uri Daddy insha Allahu.....ba za'a sake ba Zainab ki bashi hak'uri.
Cewar Aliyu yana kallon Zee-zee.
Kusa da shi Zee-zee ta matso tare da rik'o d'ayan hannunshi tayi k'asa da murya tare da fad'in ka yi hak'uri Daddy ba zan sake ba.
Kafin Aliyu ya sake yin magana Abban Barrister A Alhaji Abdallah Barkido ya ban ko k'ofa ya shigo yana muzurai, kaman wani tsohon Soja.
Ummi da twins suna biye da shi kowane su daga ni yaci kuka har ya godewa Allah, Cikin sauri Aliyu ya ta shi daga jikin Daddy yana share hawayenshi ya ce "Sannu da zuwa Abba...?
Wani mugun kallo Abba ya watsa masa cikin kakkausar murya da hargowa ya ce "kai.....ina 'ya ta.....?"
Aliyu cikin kad'uwa yake kallon Daddy zuciyarshi na bugawa da k'arfin gaske, ya furta Abba wacce 'ya....?
"Wacce 'ya kake tambayata Aliyu to a ubanka nace ta ubanka. Aliyu....billahilazi idan ba'a ku fito min da 'yata za'a yi babban tashin hankali, da yafi wanda kuke ciki gayyar tsiya masu abin kunya saboda wannan abin kunyar naku yasa kidnappers suka yi garkuwa da 'ya ta.
Sosai Aliyu ya tsorata da jin abin da Abba yake fad'a.
Daddy ne ya yunk'ura ya tashi tsaye da kyar ya nufi Abba yana cewa "don Allah Alhaji Abdallah ka zauna ka yi mana bayani a natse.
Aliyu ma da kake gani yanzu-yanzu nan ya iso daga Lagos, ga dukkan alamu bai da masaniya akan abinda kake tuhumar mu da shi.
Mtssss.....Abba ya ja tsaki tare da buge hannun Daddy da ya rik'o shi, ya ce "Wallahi ba zan zauna ba M Ardo har sai kun fad'a min inda 'yata take.
Khalid ne ya dauko kujera ya kama Abba ya zaunar da shi, ya durk'usa gabanshi ya yi k'asa da murya ya ce "ka dubi girman Allah Abba ka kwantar da hankalinka duba da yana yin da mutane nan suke ciki ya isa ya zama sheda basu da labari akan Kidnapped d'in Ya Minal.
Saura kirisss.....numfashin Aliyu ya fita daga gangar jikinsa, wani irin duhu ya maye ganinsa, da kyar ya iya d'aga k'afafunsa ya isa wajen da Ummi da Khalil suke tsaye zugun!
Ya ce Ummi me ya sami Amina ni dai nasan nayi waya da ita safe bata gayamin ko nan da k'ofar gida zata fita ba to....ya akayi kidnapped d'inta?"
Shin kidnappers d'in sun kira Abba nawa suka buk'ace abasu...?
Ajiyar zuciya Ummi tasauke mai k'arfin gaske tare da ba shi labari kamar yanda Abba ya sanar da ita, hankalin Aliyu ya yi mugun tashi duk ya bi ya rud'e.
Gani haka yasa Abba ya d'an sauk'o da kanshi ya sake basu labarin yanda al'amari ya faru, Teema ta d'ago kanta da ke duk'e a k'asa ta kalle su tare da fad'in nasan inda take.
Cike da zallan firgici suka zuba mata idanuwa, Aliyu kam tashe ta tsaye ya yi, ya ce "tana ina Fateema fad'a min matata tana ina....?
Teema ta ce tana inda ta 6oye umma Maryama gidan Ya Jamal.
Daga nan ta shiga ba su labari abin da tasani.
jikin Aliyu yana rawa ya kira wayar Jamal saidai kashhh....a rufe take, nan da nan hankalinsa ya k'ara tashi.
Don haka gaba d'ayan su suka had'u suka dunguma zuwa gidan Jamal hatta Daddy ba'a barshi ba.


*JAMAL*


Jamal da matarsa suna baro Nimzamia hospital, Suka nufi gidan yayar shi aunty Sakina da ke zone six.
A falonta suka isko ta cikin tashin hankali ya bata labari abinda ke faru saboda lokaci da Uncle suraj da boys dinshi suke dukan shi, ya gane Uncle shiyasa ya zo ga Aunty sakina ya da ta taimaka musu, kasancewarta k'awar Nafisa matar uncle Suraj ta tuntube ta taji ko tana da masaniya akan abin da mijinta yake shirin aikatawa.
"Sakina tana kiranta batare da gardama ba gayamusu ta ta6a dauk'ar wayar Jarumi da momma ta kira alokaci yana wanka anan ta ji ta'asa da suke k'ulawa, tun daga lokacin take bibiyarsa a 6oye yanzu haka tana cikin abuja su had'u a bakin Emmaculete hotel, anan tayi masauki zata musu jagora zuwa madallah village inda take da tabbaci Suraj ya 6oye su maryama a poultry house d'in shi.


*MOMMA*


Dijama da momma suna zaune a bedroom, Dijama ta kalle momma ta ce kin bani mamaki Zaituna ya aka yi kika bari shed'an da son zuciya suka d'ebe ki kika aikata wannan mummunan aiki..?
Yanzu duk karuwanci da muka yi abaya bai isheki ba sai da kika aikita zina da aurenki, to...gashi nan abinda son zuciyarki ya jawo miki wannan kayan kunya har ina.
Ta k'arashe magana tana kya6e baki.
Cike da takaicinta momma ta ja tsaki mtsss....ta nemi gefen gado ta kwanta tare da lumshe idanuwanta. Dijama ta kad'a kai kana ta nufi bathroom ta bud'e ta shiga momma nagani haka ta dauke key d'in motar Dijama ta fice da gudu-gudu, kaitsaye gida ta nufa cikin yana yi na tashin hankali ta danna horn Daniel ya bud'e mata gate, ta shigo.
"Agaugauce ta shiga sasshen ta dauki ATM d'inta tasake ficewa saida ta fara tsayawa a bank tayi withdrawing d'in mak'ud'an kud'i, sannan ta dauki hanyar madallah village cike da mugun nufi
Uncle Suraj ya saki k'ayatattace murmushi tare da fad'in tun da kin ri ga da kinsan dukan sirrina, bai kamata na cigaba da 6ata ma kaina lokaci ina ba ki labarai ba.
Saboda haka zan fito miki da manufa ta ina da buk'atar ki dauko min documents d'in dukiyar M Ardo gaba d'aya saboda mallaki na ce.
Ki sani dauko documents d'in yana nufi fansar ran mutanen ki da nayi garkuwa da su, rashin amincewa da buk'ata ta yana nufi gaba d'ayan ku za ku rasa ranku.
Jikin barrister A ya dauki rawa ta had'iye wasu yawu masu masifar d'aci, da kyar ta iya furta documents d'in su na ina....?
Uncle ya yi murmushin samu nassara fuskar shi cike da tsintsa farin ciki ya ce "su na cikin closet d'in da ke bedroom d'in Aliyu, idan kika bud'e closet za ki tarar da Safe a cikinta documents d'in suke, ban san codes d'in safe d'in ba, aikinki ne ki nemo code d'in.
Ni dai muradina ki kawo min documents d'in dukiya ta.
"Cikin fuskar tausayi da karaya barrister A ta ce "Uncle naso ka bani dama zan warware wannan matsala, nayi maka alk'awali zan tsaya maka har sai Daddy ya dawo maka da dukiyar ka da ya kar6e.
Na rok'e ka Uncle ka bani wannan dama.
Uncle Suraj ya girgiza kanshi tare da fad'in komai ya ri ga da ya zo k'arshe barrister, ahalin yanzu babu wani taimako da za ki iya yi min ki bi umarni na kawai domin tsaratar da rayuwar mutanen ki.
Shikenan Uncle zan yi yanda kake so, amma ka sani wannan ba zai ta6a dawo maka da abubuwa da ka rasa abaya ba.
Uncle mu 'yan Adam mu kan tafka manya-manya kurakura a rayuwar mu, amma kuma idan mu ka rok'i ubangiji sai ya gafarta mana domin shi mai gafara ne.
To.....me yasa mu 'yan uwan mu suka yi mana kuskure ba za mu iya yafewa ba...?
Uncle ko a yanzu za kana da wadatattace lokaci da za ka fuskanci d'an uwanka ku gyara abin da ku ka 6ata, domin shima a yanzu idan za ka bincke shi tabbas....ya yi nadamar abin da ya yi maka that's why people have second chance ka yi hak'uri uncle ka ba wa d'an uwan ka second chance.
Jikin Uncle ya yi sanyi saboda har gobe yana tuna maganar shi ta k'arshe da Dada, wacce ta kasance nasiha ta k'arshe a duniya.
"Suraj kai yaron kirki ne ban so ka bi mummunan tafarki da Muhammad ya bi, duk abin da ya yi maka ka yi hak'uri ka bishi da addu'a shiriya wata rana koda bana duniya zai yi nadama abin da ya aikata maka.
Kar ka k'ullace d'an uwan ka Suraj banaso ka bi son zuciyar ka kaman yanda shi ya bi, kada ka biyewa rud'in zuciya zata iya rusa maka kyawawan halayyen ka Suraj......
Wata irin nadama ce ta lullu6e Uncle fuskar shi ta jik'e sharkaf.....da gumi ya yi shiru yana kallon barrister A ya kasa furta koda kalma d'aya ne.
**----**-**-----**--** Aliyu da su Daddy tun kafin su k'arasa layin gidan Jamal, suka ci karo da motar barrister A a gefen hanya duk gilasan ta a farfashe.
"Suka k'ara shiga tashin hankali fiyye da farko suna cikin wannan halin, sai ga Jamal ya kira Aliyu nan da nan ya bashi labari iya abin da ya sani.
Sosai hankali Aliyu ya k'ara tashi da ji cewa uncle Suraj da momma ke da sa hannu ga dukan matsalolin da suke ciki.
Cikin wani irin yana yi Aliyu ya ce "kar ka yi yunk'uri tun k'arasu ku jira mu a bakin hotel d'in za mu zo da police saboda is very risk zuwan mu batare da jam'ian tsaro ba.
Jamal ya ce Shikenan ku yi sauri Aliyu saboda bamu da wadattacen lokaci komai zai iya faru.
Kaitsaye su Aliyu suka wuce police headquarter batare da 6ata lokaci ba DPO da kanshi ya had'a team suka dauki hanyar Emmaculete hotel in da suka had'u da Su Jamal motar Nafisat matar uncle Suraj tana gaba su na biye da ita tare da Jami'an tsaro.
"Bangare su barrister Z da ke daure a upstairs cikin taimakon Allah Sa'eed ya yi dabarar kwancewa, jikinsa yana rawa shiga kwance su barrister Z bayan ya kwance su, malam ya ce ku taimaka ku danne Maryama nayi gaggawa yi mata ruk'iya ban mu sani ba ko za mu fita wurinan a raye ba.
Ina fatan ta dawo hankalinta kafin mugaye mutane nan su gama yanke hukunci abin da za su yi mana.
barrister Za ta ce haka ne malam ya kamata maryama tasan abin da ya faru da ita.
Babu 6ata lokaci malam ya shiga yi mata ruk'iya Baaba laraba ya tasaka d'an kwalinta ta toshe mata baki, kada ajiyo ihun ta a k'asa.
"Uncle ya d'ago jajjaye idanuwanshi masu cike da zallan nadama ya bud'i baki da zai yi magana, momma ta bankad'o k'ofa ta shigo hannunta rik'e da 'yar k'aramar bindiga.
Yayin da yaran Uncle Suraj suke biye da ita saboda ta ri ga da ta siye su da kud'ad'en da ta zo da su.
Daga Uncle Suraj har Barrister A suka mik'e tsaye cikin kad'uwa, kafin Uncle ya dauki pistol d'inshi da ke ajiye akan kujera har Momma ta k'araso kusa da shi, cikin fushi ta dauke shi da rikitattace mari a kumatun shi na hagu yana d'agowa tasake dauke shi da wani a kumatun shi na dama.
Uncle Suraj ,ya d'ago dafe da kumatu yana kallonta baki bud'e,
Tsawon lokaci ya dauka yana kallon nata kafin ya ce "Ni za ki mara Zaituna??
Cikin tsananin fushi har tana had'awa da huci ta ce "Ba wai iya marin ka kawai nayi ba Suraj har rayuwarka sai na raba ka da ita, ba ka za6i ka tozarta ni a idon duniya ba, ni kuma zan tabbatar da na tura ka k'iyama.
Da sauri Barrister A ta nufe momma muryar ta tana rawa ta ce "kar ki yi haka momma Uncle ya yi nadama abin da ya aikata, kuma ki sani daga ke har shi masu laifi n.....
Bata k'arashe magana ba momma ta dauke ta da bahagon mari, tasa bindigar hannunta ta daketa a goshi tsananin zafi ya ratsa tun daga tafin k'afarta har zuwa tsakiyar kanta, take ta sulele k'asa goshin ta yana zubar da jini.
Duk da haka Momma bata bar ta ba bin ta yi tana duka had'e da saka k'afarta tana surin ta.
Gani haka yasa Uncle ya zabura zai kai ma barrister A dauki, kafin ya k'araso wajen su Momma ta saita shi da bindigar hannunta batare da tunanin komai ba ta sake masa harsashe a gefen cikin shi, k'arar bindiga tare da sautin ihun Uncle Suraj suka karad'e ciki da waje falon.
A matuk'ar rud'e barrister A ta yunk'ura ta tashi da kyar, tare da kiran sunan Uncle ta nufi wajen da yake kwance cikin jini, kafin ta kai hannunta ta ta6a shi, ita ma momma ta hal6e ta a kafad'arta ta dama harsashen ya ratsa fatar jikinta tare da huda k'ashin ta, cikin k'araji da kururuwa ta fad'i kusa da Uncle Suraj wanda yake fitar da numfashi sama-sama.
Cikin rashin Imani balle tausayi Momma ta kalle Oska ta ce "Osaka je ka zo min da Maryama, yanda na rasa M Ardo ita ma ba zan barta ta rayu da shi ba.
Yi maza ka zo min da ita so nake naga su uku suna daukar rai sannan ne zuciya ta za ta lafa da tuk'uk'i da take min.
An gama Hajiya yanzu nan zan cika aiki, amma key yana wajen oga Suraj.
Zo ka caje shi maybe key d'in yana cikin ajihun shi, da kyar Uncle ya bud'e bakin shi ya ce "Zaituna don Allah ki kyale su kar ki cutar da su ni ne nayi miki laifi, ki yi duk yanda kika dama da ni amma su ki kyale su.
Oska ya kwashe da dariya had'e da dauke Uncle da mugun suri sai da kanshi ya bugi kujera, ya duk'a ya ciro key gaban aljihun rigar sa.
yana magana dariya mugunta ya haura sama jin takon tafiya an nufo d'akin yasa Sa'eed ya dauki kujera ya la6e bayan k'ofa, Oska yana bud'e k'ofar Sa'eed na sauke masa kujera aka yayin da Malam ya buga masa wani kofin silver da ya tarar a d'akin, Oska ya kwalla k'ara ya fad'i igiya suka saka suka daure shi.
"Sa'eed ya dauki bindigarsa ya wuce gaba malam yana binsa a baya yayin da barrister Z take bin bayan malam, abayanta kuma Baaba ce da Maryama wacce ta warke sumul....ta dawo hankalinta.
"Kafin su sauka k'asa suka jiyo jiniya motar police sai kawai suka tsaye cakk.....su na jiran su ga abin da zai faru.
Momma wacce jin k'arar jiniya police ta gigita ta duk tabi ta rud'e, ta Kalle d'aya daga cikin yaran ta ta ce "na shiga uku kaman police ne suka zo?"
Ba kama ba ce Hajiya su d'in ne don haka kowa ya yi ta kanshi saboda ba mu da wadattace bullets da za mu yi fad'a da su, kowa ya kare kansa da bullets d'in ya rage mishi.
Wani irin gumi ya karyowa momma duk ta bi ta tsorace tana kallon yaran ta, suka nufi window suka lek'a gani yawan police d'in da ke kewaye da su yasa suka, karaye gudun kada su afko musu su kashe a banza yasa d'aya daga cikinsu ya kalli sauran 'yan uwan shi ya ce duk mai so ya cigaba da numfasawa, ya yi surrender saboda babu hanyar fita anan wuri.
Yayin da a can waje DPO yake sanar musu da su mik'a kansu ta ruwan sanyi saboda suna kewaye da police babu hanyar fita su yi surrender kawai.
"Babu 6ata lokaci suka nufi k'ofar fita kowane su hannunshi sama, da gudu police d'in suka k'araso wajensu suka buga musu handcuffs tare da zuba su cikin motarsu duk abin da yake faruwa su Aliyu su na tsaye a wajen gate saboda police sun hana su k'arasowa ciki.
"Momma ta Kalle Uncle Suraj ta fashe da kuka cikin muryar kuka ta ce "Ka cuce ni Suraj ga shi ta sanadin ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login