Showing 24001 words to 27000 words out of 80263 words

Chapter 9 - Gidan Rina Book Complete Jidda Aliyu.txt

31 Jan 2025

9449

Wasu yawu masu masifar d'aci ta hadiye tashiga kame-kame uhm....uhm.....lafiya qalau kawai sanyi wuri ne bai wadace ni ba.
Ta6e baki Dijama ta yi had'e da yatsine fuska kafin ta furta kedai ba kya rabuwa da zance wofi, ko munafuki ba zai ce wurinan da zafi ba.
"Batare da momma ta kula ta ba gaba d'aya hankalinta ya raja'a da kallon Aliyu da barrister A, da ke ta faman zabga murmushi suna gaisawa da jama'a bata ankara ba har suka iso gunta, zazzak'ar muryar barrister A mai shegen dad'i ta dawo da ita hankalinta da kyar momma ta iya controlled kanta, ta amsa gaisuwar da Barrister A take mata.
"Tsabar kwarewa da bariki yasa momma ta mik'e ta had'e su duka ta rungume, sai faman zuba musu albarka take sosai Barrister A ta ji dad'i a tunaninta uwar mijinta na sonta, har suka nufi high table suka zauna momma ta na cikin tashin hankali saboda har ga Allah ba ta dauki za ta ga barrister A haka ba. kyawo da wayewar yarinya suna neman zuzuta tunaninta.
Lokaci da mc ya umarce ango da amarya su fito filin domin su taka rawa, gudun abin fad'a yasa momma ta fito tana yi musu lik'i ita ma Ummi ba'a barta a baya ba.
"Kud'in da Abban barrister A ya zuba fad'arsu ma k'auyanci, ne gudan aure shalele shi dole naira ta koka.
Kasancewar events d'in yau ya kera na jiya yasa sai around 1:30am aka tashi, yau ma sai da Aliyu ya raka barrister A a wajen mota sannan suka yi sallama.
A washe gari misalin k'arfe 2:30pm ana gama sallar juma'a aka daura auren Aliyu da barrister A akan sadaki naira dubu 100, daurin aure da ya tara duban jama'a.
Misalin k'arfe 5:00pm Ummi ta shirya walima ta musanmman a gidanta, wanda mata manya suka halarci wurin anyi wa'azi mai shiga jiki akan zamantakewar aure daga bisani aka ci abinci serve yourself duk abin da ranka yake so za ka ci idan za ka wuce abaka jakka mai dauke da pic d'in ango da amarya, acikin jakka har da atamfa ak'allan kud'inta za su kai 6k.
*9:45pm*
k'anwar Abba ta fito da barrister A lullu6e cikin farar lafayya ko fuskarta ba'a gani, ga wani k'amshi na musanmman da take yi direct setting room d'in Abba aka wuce da ita sosai Abba ya yi mata nasiha, daga bisani ita ma Ummi tayi mata.
"Abin mamaki Ummi nagama mata nasiha Abba ya rik'o hannunta ya kalli k'anwarshi mai suna Maimuna ya ce mu je Maimuna ki rakani na kai, 'yata d'akinta.
Jin furucinshi yasa mamaki ya rufesu sanin halinshi da suka yi yasa ba su tambaya ba, dole Maimuna ta mik'e tana rik'e da barrister A wacce ke ta faman shasshak'ar kuka, Abba da kanshi ya yi driving da suka iso gidan, har cikin bedroom d'inta ya kaita sannan ya yi mata sallama ya fito, sai daga baya k'awayeta suka iso wanda sosai abin da Abba ya yi yai matuk'ar burgesu.






Jeeddah Aliyu
[7/26, 11:59 PM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619


DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA


*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```


*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```


*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``


*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN


*SLIMZY*:- IZZATA


*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO




*GIDAN RINA*


*17*


Misali k'arfe 10:30 na dare ango Aliyu ya iso tare da tawagar abokanshi, bayan anyi wasa da dariya kowa ya kama gabanshi, Aliyu yana dawowa daga raka su ya rufe k'ofar main parlour ko kallon d'akinta bai yi ba, ya nufi master bedroom d'inshi da ke upstairs.
"Gyagyad'i tafara daga zaune hakan yasa ta tashi da kyar saboda tsananin gajiya ga Kuma bacci da ya cika idanuwanta.


Ta cire kayan jikinta ta maye gur6insu da wata pitch colour nightgown wacce ta tsaya iya gwiwarta, ta tufke gashinta wurin d'aya tabi lafiyar gado bata matsantawa kanta da dogon tunani ba, shiyasa barci ya yi sauri dauketa.
"Washe gari sai misali k'arfe 11:00 na safe ta falka inda Allah ya taimaketa tayi sallar asuba, agurguje ta gyara bedsheet ta kunna burner ta zuba turaren wuta d'akin ya dauki sanyayye k'amshi sannan tanufi bathroom tayi wanka.
Simple makeup tayi fuskarta sai glowing take yi.
Tasaka wani tsadadde lace jikinshi marrow colour anyi mishi Zane flowers baby pink da sky blue style d'in doguwar riga sosai kayan suka k'awata kyakyawar surar jikinta, tasaka half cover baby pink in colour bata daura d'an kwali ba sai tayi using d'an siriri veil ta yane dogon bak'in gashinta.
Jikinta na fitarda k'amshi na musanman, ta dauki wayoyinta had'e da burner ta nufi parlounta nan ma ta k'amsashi, daga bisani ta sauko downstairs parlour komai na parlour White colour ne.
Tayi tsaye tana kallon tsari parlour ta gyad'a kanta a zuciyata tana yaba yadda Aliyu yake matuk'ar so White colour.
Burner ta jona ta sake zuba turare ta shiga arranging throw pillows d'in da ke kan kujeri.
"Daga bisani ta nufi kitchen tasaki murmushi hatta da kitchen cabinet fari ne tass....ta lek'a store cike yake taf da foodstuffs iri dabam-dabam.
Ta dawo parlour ta zauna akan one sitter ta dauki phone d'inta ta bud'e data, ta shiga handle d'inta na Instagram tana karanta comments d'in well-wishers, hanci da dodon kunnenta suka ji footsteps da k'amshi desingner perfumes d'inshi gabanta ya shiga dukan tara-tara.
"Kasa d'agowa tayi har ya k'araso cikin parlour ya sha ado da dakakkiyar shadda fara sai walk'iya da daukar ido take.
K'afarshi sanye da fari sandal kanshi ba hula amma ya gyara sumar kanshi ta kwanta luf-luf gwanin ban sha'awa.
Hannayenshi zube ciki aljihun wandonshi ya nemi sofa da ke facing d'inta ya zauna ya yi crossing legs d'inshi, sai wani shan k'amshi yake.
"Sai lokaci ta d'ago ta d'an zame daga kan kujera, cikin muryarta mai d'and'ano gaske ta ce ina kwana?"


"Saida ya k'are mata kallo ta k'asan ido a zuciyarshi yana yaba tsananin kyau da tayi, cikin k'asaita ya amsa da lafiya qalau kintashi lafiya?"
"Lafiya qalau Alhamdulillah!
Ta amsa mishi, komawa tayi ta zauna daga haka ba Wanda yasake cewa da d'an uwanshi ci kanka.
Ita tana operating phone d'inta shi Kuma yana girgiza k'afarshi a hankali, knocking d'in k'ofa akayi ya yi kamar bai ji ba, cigaba da knocking akayi da d'an k'arfi still ko motsawa bai yi ba balle tasa ran zai tashi, kallonshi tayi a tsanake, taga tabbas ba shida niyar tashi gani yadda ya kwanta akan kujera hadda su lumsashe idanuwa.


"Ta6e baki tayi kafin tace Yalla6ai ana knocking.


Shiru bai amsa ba sake mai-maitawa tayi cikin d'aga murya Yalla6ai ana knocking.
"Bud'e idanuwanshi ya yi ya zuba su akan fuskarta ya d'age girar ido, kasa jure kallon eye's ball d'inshi tayi ta kauda fuska, ya yatsine fuska yace wai waye da wannan sanyi safiya zai nemi ya takurawa mutane?"
Nifa Allah banaso damuwa mtsss....yak'arasa magana da jan tsaki.
"Saida ya gama jan ajinshi kamar mace sannan ya mik'e ya nufi k'ofar yayin da barrister A ta rakashi da idanu, Kai wannan guy akwai yanga kalli yadda yake tafiya tafad'a a k'asan zuciyarta.
"Yana bud'e k'ofa yaci karo da Isah direba tsaye dauke da basket da warmer a hannu, barka da asuba maigida"
Cewar Isah direba yana murmushi.


Harara ya zuba mishi maimakon amsa gaisuwar tashi, cikin shan k'amshi ya ce Isah banaso tsohon iskanci, gidan bak'onka ne da za ka tsaya kana min knocking?"
"Allah ya huce zuciyar maigida gani nayi bai kamata na shigo gaba gad'i, a gidan ma'aurata ba izzini amma tuba nake yi ayi min afuwa.
"Shiru ya yi yana kallon Isah kafin ya ta6e baki ya ce dallah malam wuce ciki banaso iyayi tsiya.
Ya wuce gaba Isah yana biye da shi ina kwana amarya?"
Cewar Isah yana washe hak'ora.
Cikin fara'a ta amsa da lafiya qalau ta mik'e ta kar6i warmer d'in hannunshi, ta nufi dining area yayin da Isah ya bita rik'e da basket.
Ta ajiye warmer akan dinning table ta kar6i basket d'in had'e da furta sannu da k'ok'ari an gode.
Yauwa amarya!
Isah ya fad'a had'e da juyawa ya koma parlour, cikin girmamawa ya ce maigida ko kana da buk'atar wani abu na tsaya?"
"Girgiza Kai ya yi na barka lafiya Isah ya fad'a had'e da nufar k'ofar fita.
Saida ta dauko plate da mugs had'e da spoons a kitchen, sannan ta shiga bud'e warmers d'in ta farko wainar shinkafa ce tayi laushi har ta gaji ta bud'e ta biyu miyar taushe ce taji tantakwashi, k'amshi ya buge hancinta, sai guda d'aya mai dauke da chips da fry plantain sai sauce d'in Koda da hanta ya ji karas da cabbage, sai flakes mai dauke da kunu gyad'a yaji Madara fari kal....da shi ga Kuma farfesu kayan ciki da na cow tail ta gyad'a kai ciki da yabawa, dole ta koma parlour domin ta Kira d'an iko nata ya zo ya yi breakfast.
"Yalla6ai nayi arranging table ka zo kayi breakfast.


"Saida ya yi mata kallo na nashi na d'age girar ido kafin ya gyad'a kai, tsaye tayi tana jira ya tashi Saida ya gama jan ajinshi sannan ya mik'e tabi bayanshi, da sauri ta jawo mishi kujera ya kalleta ya yatsine fuska da sauri ta kauda nata fuska, ya zauna ta dauki plate batare da ta kalle shi ba ta ce akwai waina da chips wane za'a zuba maka?"
"Bana cin abinci mai nauyi.
Ya fad'a batare da kalleta ba.
Na zuba ma chips kenan?"
Ya gyad'a kai.
Ta zuba ta ajiye a gabanshi.
Ki je store ki dauko kayan tea ki had'o da nessacoffe.
"Yana gama magana ya koma jikin kujera ya lafe, ya Kuma yi folding hannayenshi a kirji.
Mamaki ne ya lullu6eta gani yadda ya yi mata magana cikin izza da gadara, bata ce komai ba ta tafi store ta dauko abinda ya buk'ata tea za'a had'a maka?"
"Coffee!
Ya fad'a a takaice.
Ta shiga had'awa za ta zuba sugar ya ce bana shan sugar, honey za ki zuba.


"Shiru tayi na seconds kafin ta ce ina zuma yake?"


"Ki je store ki duba.


"Dole ta koma store da kyar ta gano idan Zuma yake ta dauko, ta zuba tea spoon uku ta juya ta ajiye mishi.

Na waye?"
Ya furta can k'asan mak'oshi.


Me kenan?"
Tafad'a tana kallonshi.
Coffee!
Ta hadiye yawu kafin ta ce naka ne.
Humm.... barrister bana Shan zak'i sosai Zuma da ki ka zuba ya yi over.
Yanzu kam sosai taji ranta ya6aci ya fara kaita bango da reni wayonshi, da kyar tayi control temper ta ta ce Yalla6ai miyasa tun farko da nake had'awa ba ka fad'amin adadin Zuma da zan zuba ba?
Ya d'ago idanuwanshi Yana kallonta gira d'age yayin da ta kauda fuska.
Ya ce had'a coffee yana miki wuya ne?"
Girgiza Kai tayi.
To sake had'a min wani banaso musu.
Batare da ta ce komai ta dauki wani mug ta sake had'awa, ta kalle shi ta ce spoon nawa zan zuba na honey?"
Yatsanshi guda ya d'aga ta6e baki tayi ta d'an juya coffee ya rage zafi ta ajiye mishi, sannan tayi serving kanta waina ta zuba ta ci ya rigata tashi duk da ta lura bai wani ci abinci kirki ba.
Tana kammalawa ta kwashe plates d'in suka yi using ta nufi kitchen ta wanke, sannan tadawo parlour Koda ta shigo Yana waya Yana gama waya ya mik'e ya dubeta ya ce ni zan fita.
Muryarta asanyaye ta ce adawo lafiya.
Har ya juya ta ce Yalla6ai karka manta ajima around 9:00 o'clock za mu tafi dinner da abokan aikina suka shirya mana.
"Ya juyo ya k'ura mata idanu kamar mai nazari, ta sunkuyar da Kai k'asa.
Wai ke har yanzu bidi'o'i naki ba su gadi k'arewa bane?"
Yalla6ai ba wani bidi'a abinci ne kawai za'a ci a wuri, don Allah ka taimaka min mu je idan ba mu muje ba zasu ga kamar na musu wulak'anci.
Ta k'arasa magana kamar za tayi kuka.


Batare da ya ce da ita zai je ko ba zai je ba yai tafiyarshi, ranta ya sosu ba kad'an ba saidai batada yadda zata yi ta zuba tagume ta afka tunanin irin zaman da za suyi domin tun tafiya bata yi nisa ba tafara gajiya da halaye Aliyu.








Jeeddah Aliyu
[7/26, 11:59 PM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619


DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA


*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```


*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```


*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``


*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN


*SLIMZY*:- IZZATA


*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO


*Haske writers association*


*GIDAN RINA*


_this page is for you Rahinerth alk'aluma shidda suna jin dad'in comments d'inki keep its up dear!_


*18*


Zuwan barrister Z gidan ya rage mata tunanin Aliyu, nan take ta bata labarin yadda tayi da shi.
Karki damu bebs ko wancan karon haka ya yi mana kamar ba zai je ba, sai gashi duk events d'in da akayi ya yi attending.
"Ki saki ranki inshallah ko wannan zai je, Aliyu bahagon mutum ne ba kasafai ake gane idan ya dosa ba.
Yakamata ki jajirce zama da irinshi sai an shirya.
"Talla6e kumatu tayi tana kallon barrister Z kafin ta ce ni zan gayamiki bebs yau da safe wurin breakfast kawai saida ya haddasa min headache, labari abinda yafaru ta shiga gayawa Zarah.
Dariya sosai barrister Z taci tabbas bebs Aliyu ne dai-dai ke kina tak'ama miskilanci sai gashi kin had'u da Wanda yafi ki.
Bari kawai bebs na had'u da gamo na.
Gaskiya kam bebs kin had'u da gamonki sai hak'uri.
Dariya suka yi daga bisani suka mik'e suna zagaya gidan, yayin da Barrister Z sai yaba kyau da tsarin gidan take.


*****""'***""******
Tun misali k'arfe 7:00pm wacce za ta yi wa barrister A makeup d'in zuwa dinner ta zo, kuma har zuwa lokaci Aliyu bai dawo gida ba.
Saida ta sallaci sallar isha'i aka fara tsantsara mata makeover, black gown tasaka aka nada mata bride turban White colour, tayi kyau na ban mamaki saidai duk zuciyarta a chakud'e take sakamakon rashin sani manufar angon nata.
Sai k'arfafa mata gwiwa Barrister Z take duk da haka hankalinta bai kwanta ba.


Lokaci sai ta tafiya yake dole tafito, barrister Z na biye da ita har suka iso parking lot, da sauri Isah direba ya bud'e mata mota kirar jeep Volkswagen farar tass....da ita tana danna kanta ta gashi zaune ya yi relaxing sai faman operating wayarshi yake, k'amshi perfume d'inshi ya cika motar.
Batasan lokaci da tasaki ajiyar zuciya ba.
"Batare da ya kalleta ba ya ce barrister ga ki da son bidi'a amma bakida kama jiki, almost 20 minutes ina zaman jiranki har nafara tunani ko kin fasa zuwa dinner ne, na kama gabana.
Saida ta zauna kusa da shi ta kuma k'are masa kallo, sannan ta ce lamarinka sai kai Yalla6ai tunani bai bani za ka je dinner ba.
Sai gashi har zaman jiranki nayi.


Ya karasa magana yana ta6e baki tare da cewa wai Isah me kake jira ne da ba za ka ja mota mu tafi ba?"
Umarninka nake jira maigida.
"To na ba ka umarni sai ka ja motar mu tafi, kana k'ara 6ata mana lokaci.
A tunaninta idan ya gama magana da Isah zai kulata sai taga sa6ani hakan.


Don haka ita ma taja bakinta ta tsuke Bata k'ara cewa uffan ba har sanda suka iso hall d'in, suna fitowa ya rik'o hannunta suka k'arasa ciki hall, dinner ta k'ayatarda Aliyu matuk'a a cewar shi duk events d'in suka yi ba wanda ya burge shi irin dinner d'in, saboda ba hayaniya sai slow music ke tashi anci ansha anyi couples dance sai kusan 1:00am aka tashi kowa ya kama gabanshi.


"Tun a mota tafara bacci har suka iso gida bata saniba, tasheta Aliyu ya yi ta hanyar cewa barrister ki tashi mun iso gida.
ko motsawa bata yi ba ji ya yi zai iya tafiya yabarta anan, har ya bud'e mota ya fita ko me ya tuna sai dawo gefen da take, ya shiga bubbuga hannunta da k'arfi bugu d'aya zuwa na biyu ta bud'e idanunta masu cike da bacci.
"Fahimta abinda ke faruwa tayi shiyasa bata furta uffan ba tafito tana rangaji tana had'a hanya ta nufi cikin gida, dai-dai k'ofar shiga main parlour ta kusa fad'uwa da sauri ya tarota ya rik'o shoulder ta, ya d'an rungume rabin jikinta yayin da ya sak'ala d'ayan hannunshi akan waist d'inta.
"Wani irin kunya taji ya lullu6eta sakamakon yadda ya rungume waist d'inta nan take ta wartsake daga baccinta, a haka suka cigaba da tafiya har zuwa bedroom d'inta.
A gefen gado ya zaunar da ita ya kalleta ta k'asan ido ya ga yadda take lumshe ido alamar bacci bai gama sakinta ba, ya ce kiyi k'ok'ari ki rage kayan jikinki za ki fi jin dad'i kwanciya.
Daga haka ya juya har ya murde handle ya d'an juyo cikin wani irin murya ya furta "Good night!
Murmushi tayi kafin ahankali ta ce "Good night!
Haka kawai ta tsince kanta cikin nishad'i marar misaltuwa, umarninshi tabi ta hanyar sauya kaya zuwa sleeping dress.
****""***"""'*****
Washe gari!


Kasancewar gajiya tayi musu yawa hakan ya basu damar yin bacci, Kuma da yake daga gidan Daddy ake kawo musu abinci.
"A kwana na shidda da bikinsu tana zaune a falonta tana tunani fara girki a yau, saidai batasan miye favorite d'inshi ba.

Gani za ta wahalada kanta a banza yasa ta mik'e ta nufi falonshi da ke upstairs, ta tura k'ofar ta shiga da sallama zaune ta sameshi yana aiki a system.
Jin motsi bud'e k'ofa da kuma k'amshi fitinane turareta ya bugi hancinshi, yasa d'ago da kansa ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login