Showing 69001 words to 72000 words out of 80263 words

Chapter 24 - Gidan Rina Book Complete Jidda Aliyu.txt

31 Jan 2025

9436

sameta ba.
har ya shiga jirgi bai fasa tunani da zance zuci ba yana cikin tunane-tunane jirginsu ya d'aga.
***----**----***----**
Jarumi uncle Suraj yana hakince akan royal chair wacce ta k'awata masa falonsa, da ke poultry house d'inshi ya yi crossing legs dinshi jikinshi sanye da farar shadda hannunshi na dama rik'e da pistol yaranshi suka shigo d'aya sabe da barrister A a kafad'arsa, ya direta gaban Jarumi tare da furta "mai girma Jarumi mun cika aiki.
Da pistol d'in hannunshi ya yi masa ishara da ya ja baya, ya tsare barrister A da shegu idanuwansa kafin ya saki wani shegiyar murmushi ta gefen baki.
Ya kalli d'aya daga cikin yaransa ya yi masa alama da ya cire mata salatif d'in bakinta, nan take ya cika aiki tana jin an bud'e mata bakinta ta dagargaje iya k'arfinta ta kurma ihu wayyyo........don Allah ataimake ni wasu la'ananun Allah sun satoni wayyo Allah....ataimakeni.
"Jarumi ya mik'e daga mazauninsa ya nufi wurinta ya shiga zagayata, jikinta ya bata akwai mutum a kusa da ita ta juya da k'arfi ta shiga ja da baya tana kuma kici-kici kwance igiyar da suka daure mata hannaye, tuntube tayi da center table tayi baya za ta fad'a kanshi cikin sauri Jarumi ya rik'o hannunta ya daura bakinsa dai-dai k'ofar kunnenta ya ce "welcome to my palace sarauniyata.
"Un.....cle....sur..raj!
Tafad'a cikin rawar murya. "Yesss.....sweetheart ashe ina da matsayi a wurinki har haka bansani ba duk da kin kasance, a cikin wannan hali kika iya sheda muryata ina godiya rabin raina kai....oska zo maza ka kwance ma sarauniyata hannayenta, za mu fi jin dad'in gaisawa da sauri wanda ya kira da Oska ya zo ya kwance mata hannaye.
Ita ma ciki sauri ta cire blindfold d'in idanuwanta ta yada ganinta cikin parlor, tana kallon gumaka yaran Jarumi saboda yadda suka yi tsaye k'ame sun fi kama da gumaka har ta gangaro kan Jarumi wanda ke tsaye gefe yana zabga murmushin mugunta.
Wani mugun kallo ta watsa masa shi kuma ya washe mata hak'ora tare da nufar mazuninsa na tun farko ya zauna ya yi crossing legs dinshi, ya d'aga pistol d'in hannunshi yana sosa gefen fuskarsa a fusace barrister ta nufi wurinsa ta nuna shi da yatsa tare da fad'in "kai.....uncle kayi hauka ne me yake damun kanka, ka ne shin kuwa ka san hukunci kidnapping a kund'in shari'a?"
Uhm..uhm....Ya za'a yi nasani my beautiful daughter in law wannan sai ku manyan lawyers.
Ta girgiza kanta cike da takaici take kallonshi saboda ta fahimci yana so ya raina mata hankali, cikin fushi ta ce "to.....uban me zan maka da kasa aka yi kidnapping d'ina zuwa nan...?"
Ta6e baki ya yi kafin ya ce ki natsu barrister muyi magana cikin mutunci da lumana.
"Harara ta zabga masa tare da fad'in babu zance natsuwa ko mutunci atsakaninmu uncle, idan har kana so mutunci da lumana ka sa banzaye gumaka yaranka su maidani inda suka satoni, ni kuma zan rufa maka asiri na dauke wannan al'amari a matsayin sharrin zuciya.
"Idan kuma nak'i fa my beautiful daughter in law?
Za kayi nadama mafi muni a rayuwarka, ni kwata-kwata kaina ya daure nasa gane menene manufarka na satoni?"
To....ta ya za'a yi ki sani baya baki bani damar da zan sanar da ke ba.
ya k'arashe magana yana murmushi abinsa.
Ya cigaba da cewa Ki nemi kujera ki zauna ki bud'e kunnenki da kyau ki saurare manufofin da suka sa na tura gumaka yarana suka yi kidnapping d'inki, saboda haka ki nemi wuri ki zauna tun kafin ki kaini bango nasa a zaunar da ke dole.
"Rau-rau tayi da idanuwa tare da furta amma kasan hakan bai dace ba, ko?"










Jeeddah Aliyu
[7/27, 12:28 AM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619


DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA


*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```


*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```


*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``


*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN


*SLIMZY*:- IZZATA


*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO


_SECOND TO THE LAST PAGE_


*39*




*NATIONAL HOSPITAL ABUJA*






Daddy kwance akan gadon asibiti anyi masa fixing d'in drip a hannunshi na dama, sai sharar bacci yake yi Zee-zee wacce ta gama waya da Aliyu ta mik'e daga kan kujerar da ta ke zaune, ta nufi wajen gadon Daddy ta zauna kusa da shi.
"Ahankali ta rik'o hannunshi na dama cikin tsananin tausayi take kallon fuskar mahaifin nata, yayin da bangare zuciyarta guda take ji tsanar mahaifiyarta tana huda sasssa jikinta.
Ta lumshe idanuwanta hawaye masu zafin gaske suka zubo mata, bata damu da ta goge su ba ta ce "Daddy sam ba kayi dace da mata tagari ba, ba ka samar mana da uwa tagari ba.
Daddy a yau ina nadamar kasancewar 'yar da Zaituna ta haifa momma ta cucemu Daddy ta zubar mana da daraja da k'ima a idon duniya.
Ahalin yanzu ba wanda zai auremu saboda mu kasance 'ya'ya matar da ta aikata Zina da igiyoyin aureta. "Shikenan yanzu ba mu da damar shiga Jama'a sai an goranta mana.
ta k'arashe magana had'e da rushewa da kuka mai tsananin gaske ta kifa kanta akan k'irjin Daddy, tana cigaba da kukanta.
Teema ta Kalle Meena wacce idanuwanta suka yi luhu-luhu saboda tsabar kuka, ta ce " Ya Meena na rok'e ki da ki daina kukan nan ni fa ya dace nayi ta rusa kuka ba ku ba, saboda ko ba komai ku ta hanyar ha.....
Da sauri momma ta zabura daga bacci k'arya da take yi, ta dannawa Teema ashar tare da fad'in "Teema wane sharri ne aljanunki suke shirin k'ula min?
Da ba zasu bar ni naji da wanda aka riga aka doura min ba.
"Meena ta taso da sauri ta nufi wajenta gabanta na fad'uwa ta ce "momma kina nufi abinda ake yad'awa a kafaffen labarai akanki sharri ne ba gaskiya bane?"
"Kuka momma ta fashe da shi tana girgiza kanta kaman k'adangarwa "sharri ne da gadar zare da magauta suka shirya min Meena, saboda an ga mahaifinku zai fito takarar kujerar Governor.
"Meena ta share siriran hawaye da suka zubu mata da bayan hannu, ta ce "to.....amma momma me ya ki ka je yi a hotel kuma ba kaya a jikinki sai wani d'an munafukin bathrobe ne sanye ga jikinki...?
Gaba d'aya momma ta didice da ji wannan tambayar ta Meena, nan da nan tayi tunani k'aryar da zata yanka mata sai kawai ta karkace bakinta ta ce "na fito daga gida da zumar zan je gidan k'awata Hajiya Dijama, har na kusa isa gidan wata bak'ar mota tasha gaban motata wasu katti majiya k'arfi nagani sun nufo motata kafin ki ce kwabo sun fesa min wani abu ga fuska shikenan ban sake sani idan kaina yake ba sai falkawa nayi nagani akan gadon hotel tsinane yaronan da ban san uwar da ta haife shi kwance kusa da ni, na yunk'ura da k'arfi na nufi k'ofa ina bud'ewa sai kawai naci karo da Daddynku a tsaye kafin nayi wani yunk'uri kare kaina sai kawai wad'annan la'antattu 'yan jarida suka kewaye mu.
Cike da fushi Meena ta ce "tabbas....ko waye ya shirya miki wannan abu momma sai Allah yasaka mana ya bi mana hakki 6ata mana suna.....
Mtssss......Dogon tsaki Teema ta ja tare da fad'in kaichonki.......momma wai kam har sai yaushe za ki daina daukawa kanki zunubai?"
Shin ke bakisan hukunci k'arya bane a addinance?"
Kiji tsoron mahalincinki momma ki tuna komai dare dadd'ewa za ki mutu kuma tilasss.....za ki riske abinda kika shuka yana jiranki a kabarinki.
Momma ki sani duniya k'ararriya ce lahira kuma a can za mu dauwama......iya aikinka nagari shine zai ceceka, tun tashe ni nayi wayo momma banta6a gani kin yi aiki nagari ba shin ke ba ki tsoron azabar Allah ne?"
Teema ta k'arashe magana tana mai tsare momma da firgitattu idanuwanta.
"Momma ta rushe da kuka tare da fad'in Teema me nayi ma aljannunki ne me na tsare musu ne da akoda yaushe suke bi na da mugun alkaba'i?"
"Har Teema ta bud'e baki zai tayi magana Meena ta dakatar da ita ta hanyar rik'o mata hannu tashi mu tafi d'akin Daddy mu bar momma tana buk'atar hutu.
Batare da Teema ta furta uffan ba ta mik'e yayin da Meena da tana janye da hannunta, saida suka kai bakin k'ofar fita Teema ta juyo ta kalli momma cikin sa'a idanuwan momma su na kansu, tasaki mata mushirinki murmushi had'e da karkad'a mata babban yatsanta ta nota shi k'asa alamar you're finished.
Da sauri momma ta sadda kanta k'asa tana jin wani masifaffen zafi da turiri a k'asan zuciyarta, ta kuma sha alwashi ko ta wane hali sai ta dauki fansar abinda Jarumi ya yi mata.
Ba zai yu ba ita kadai sunanta ya 6aci a duniya dole su biyu ne zasu sha tsinuwa daga bakin mutane duniya ba wai ita kadai ba.
Sannan wannan tozarci da ya yi mata iya saninta ba su shirya shi cikin tsarin plans d'insu ba, wato nufinshi ita tun anan ya gama amfanin da ita shiyasa ya fallasata a idon duniya, hawayen takaici suka zubu mata bata damu da ta goge su ba saboda wuta ce take ci a zuciyarta ba kuma zata daina ruruwa ba har sai ta cimma burinta na gani bayan Jarumi da Barrister A domin ita ce mutum ta farko da tafara challenges d'inta.
"Idanuwanta ne suka hasko mata wayar Meena da ta bari a gefen drawer gado, hannunta har rawa yake yi ta dauki wayar, idan Allah ya taimake ta Meena bata saka security code a wayarta, abu na farko da tafara yi shine calling d'in number Jarumi abin takaici wayar tashi a kashe take.
K'awarta Dijama ta lalabo ringing biyu zuwa uku tayi picking muryarta adak'ile ta ce ''Hello.....
Hello....Dijama!
Wa ke magana...?
Cewar Dijama duk da tagane muryar momma.
Ban so tsohon iskanci Dijama atsawon zaman da nayi da ke ko sautin tusa ta kika ji yaci ace kin sheda ta balle muryarta.
"Allah ya ba ki hak'uri Zaituna ni sai yanzu na sheda ki, da farko naji muryarki tayi dususu shiyasa ban gane ki ba.
Zaituna wani mugun abu naga yana kara kaini gidan rediyo da gidan television ke har ma da kafaffen sada zumunta, shin ke ce da kanki kika aikata wannan mugun aikin ko kuma ussaina ki ce....?
Mtssss.....momma ta bata amsa da dogon tsaki tare da cewa uwata ce ta aikata ba ussaina ta ba, look.....Dijama ban kira ki ba don tambaya da bada amsa ba na kiraki ne don ki taimaka min ki zo ki fitarda ni daga asibiti nan, tun kafin ciwo na gaskiya ya kamani.
Uhmm.....cewar Dijama har tana ta6e baki kina wane asibiti ne....?
"National Hospital a room 9 ki zo min da kaya nasaka saboda ni da wanda yake tsirara duk d'aya.
"To.......shikenan gani nan zuwa ki zama ready kada gari taimako ni ma a zuba ni a Median.
Mtsss.....momma ta ja tsaki tare da hanging up.


*FEW MINUTES AGO*


Dijama ta parker motarta a parking space d'in asibiti, ta fito cikin sauri ta nufi cikin reception d'in asibiti ta bi corridor da zai sada ta da room d'in da momma take kwance, ta tura k'ofa ta shiga momma tana ganinta tayi zubur ta mik'e zaune tun kafin Dijama ta zauna ta ce "Bani kayan na saka banso yara nan su shigo su ganki.
"A yatsine ta bud'e handbag d'inta ta ciro brown jallabiya ta mik'a mata, tasaka jikinta har rawa yake yi ta yanne kusan rabin fuskarta da mayafin rigar.
"Har suka fice daga d'akin zuwa parking space ba su ci karo da idon sani ba.
***----***---*****----**
*MADALLAH VILLAGE*


Barrister A ta gallawa Uncle Suraj harara tare da fad'in wallahi da sannu Allah zai toni asirinka uncle, sai ka girbi abinda ka shukka da hannunka mugu bak'in azzalumi.
"Ko kad'an fuskar uncle bata nuna ya ji zafin kalamanta ba, sai ma wani shegen murmushin da ya yi ya d'aga pistol d'in hannunshi ya yi pointing d'inta cikin kakkausar murya ya ce "Za ki zauna ko sai na har6e ki ne...?
Sai da tasake zuzzuba masa harara kafin ta zauna tayi bala'in daure fuskarta ta ce "Na zauna sai ka yi gaggawar fad'amin uban me zan maka da ka satoni mugu kawai mai fuska biyu...?
"Numfasawa ya yi tare da gyara ya zamanshi ya ce "ina fatan kina da labari halin da in laws dinki suke ciki....?
Dama ka satoni ne don ka sanar da ni halin da suke ciki...?
Cewar barrister tana aika masa da wani mugun kallo.
Cikin kwanciyar hankali ya ce "ah'a......ba ko d'aya.
To kayi gaggawa sanar da ni dalilinka saboda banida lokacin 6atawa tare da kai.
"Barrister kenan ki bi ni ahankali saboda duka mutanen ki suna k'ark'ashin ikona, ba ki da zabi sai abinda na za6a miki.
"Zaro idanuwanta tayi cikin kad'uwa ta ce "me kake nufi da wannan kurman zance naka....??
Murmusawa ya yi tare da mik'ewa tsaye ya nufo wajenta, yana mai cigaba da murmushi da sauri ta tashi tsaye muryarta tana rawa ta ce "kar ka sake ka matso ku sa da ni.
Dariya ya kwashe da ita tare da fad'in ki biyo ni domin ki sami amsar tambayar da kika yi min saboda ni ma banida lokaci 6atawa wajen amsa miki tambayoyin ki.
Mtsss.....ta ja tsaki ta bi shi abaya kaman kazar da kwai ya fashewa a ciki.
Upstairs ya nufa haka ta dinga bin shi har zuwa k'ofar wani d'aki da ke rufe, ya yi using d'aya daga keys d'in hannunshi ya bud'e k'ofa.
Da fuskar barrister Z tafara cin karo da ya ke tana facing k'ofa tana d'addaure, da igiyar akan robber chair. "Cikin firgici da tashin hankali barrister A ta bangaje uncle Suraj tak'arasa wajen Barrister Z ta durk'usa tare da cire mata salatif da aka rufe mata baki da shi.
Kafin tayi magana ta hango malam shima adaure kama barrister Z, sai kawai ta mik'e tsaye ta bi d'akin da kallo maryama da Baaba laraba idanuwanta suka hasko mata su adaure, yayin da Sa'eed yake daure duk fuskarshi ta kumbura jini ya bushe a gefen bakinshi da alama ya daku ba kad'an ba.
Gaba d'aya jikin barrister A ya dauki rawa kaman mazari, a fusace ta nufi Uncle Suraj da ke tsaye ajikin k'ofa yana zabga mata murmushi sai kace wanda ya aikata abin k'irki.
"Kai mahaukaci ina ne uncle?"
Me wad'annan bayin Allah suka yi ma da za ka kawo su nan??"
Bebs.....uncle Suraj yana yi ma momma aiki ne.
muryar barrister Z ce ta d'aki kunnen barrister A wacce ta Juyo da sauri cike da zallan mamaki tacce momma kuma??"
Kwarai kuwa tare suke.
Uncle ya girgiza kanshi tare da fad'in point of correction Barrister Zarah....Zaituna tana min aiki ne ba ni ne nake mata aiki ba yaushe tsohuwar kilaki kamar Zaituna take da matsayin saka Jarumi kamata aiki.
Harararshi barrister A tayi tare da fad'in dallah malam ka rufe min bakinka....ka bar ni nayi magana da k'awata.
Mak'e kafad'a ya yi tare da ta6e baki.
barrister Z ta ce
lokaci da jirgin mu ya yi landing dama nace miki zan kira ki da zaran mu iso, kafin na kira ki sai kawai ga Uncle Suraj ya ce "ke kin ka aiko shi ya yi picking dinmu, kasancewar nasan matsayinshi a gidan da kirkin shi da kike fad'a yasa ban 6ata lokaci wajen dogon nazari ba na umarce malam muka shiga motarshi daga nan ba mu sake sani idan kanmu yake ba, sai daga baya muka dawo hayyacinmu muka tsince kanmu anan a d'addaure kuma anan muka tararar da Maryama da Baaba har ma da Sa'eed.
"Uncle ya shafi gajeren gemunsa ya tanko zuwa gaban barrister Z ya duk'a ya dauki salatif d'in da barrister A ta cire mata, yana fad'in to fad'i ba'a tambayeki ba labarin ya isa haka.
Na fahimci idan na zuba miki ido sai ki cinye min lokaci da labarai.
Ya nufi wajen barrister A ya tank'e hannunta ya jata zuwa waje, ya yi wulgi da ita ta fad'i k'asa cikin rashin imani ya murzawa k'ofa key ya rufe.
Barrister A ta mik'e da sauri ta rik'o gefen rigarshi tana rok'onshi don Allah Uncle Suraj kayi hak'uri ka saki bayin Allah nan.
Me suka yi maka ne?
Batare da ya tanka mata ya nufi steps yana takawa ahankali, arud'e ta bishi har tana had'awa da tuntube uncle.....please ka zo ka bud'e su musanmman malam a haife ya haifeka.
Ya k'arasa sauka k'asa ya nufi kuejarar da yake zaune ya zauna, sai wani karkad'a k'afafu yake yi da gudu tak'araso ta zube gabanshi tana mai cigaba da rok'onshi, gani ko matsowa bai yi ba balle tasa ran zai kar6i buk'atarta.
"Gani yanda ya yi banza da ita yasa ta mik'e tasoma zazzaga masa kwadon bala'i da masifa nan ma kamar ba da shi take ba.
"Gani yak'i tanka mata yasa ta sassauta murya ta ce "zUncle laifi me muka yi maka ne da ka kawo mu wannan wuri...?
Ya gyara zamancshi tare da yi mata shegen murmushin nan nashi, ya ce "yanzu kika yi tambaya mai amsa sai ki nemi waje ki zauna domin ba zan ba ki amsa kiyi min tsaye aka ba.
"Batare da gardama ba ta zauna k'asa akan tiles tana kallonshi.
Na sato ki ne saboda kina so ki taimakawa Maryama, nayi kidnapping d'in barrister Z da kakan ta saboda suna so su taimaka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login