Showing 72001 words to 75000 words out of 80263 words

Chapter 25 - Gidan Rina Book Complete Jidda Aliyu.txt

31 Jan 2025

9419

miki Maryama ta dawo hankalinta na sato Sa'eed ne domin inaso ya sanar da ni duk wani shirinki akan Maryama.
"Me Maryama tayi maka ne da ba ka so samuwa lafiyarta?"
Saboda ta chanchaci ta dauwama a haukace, shine hukunci azzuluma mayaudariya irinta.
Maryama ita da mijinta mugaye ne duk abinda na zama a yau su ne sila.
Barrister A ta galla masa harara tare da fad'in uncle banso wasa da hankali idan za ka yi magana Just go straight forward ka ce ba momma kake yi ma aiki ba, ita ce take maka aiki kenan da hannunka a haukan maryama...?
Murmushi ya yi tare da fad'in kwarai kuwa hatta abinda ya faru da Zaituna a yau ni ne na shirya shi.
"Saboda me Uncle an maka wani laifi ne da ka za6i ka tarwatsa farin ciki iyali guda....?
Kafin na tartsawa musu farin cikin su ne suka fara tarwatsa min nawa, duk abinda na aika a yanzu daukar fansa ne akan d'an uwana M Ardo.
Nayi amfani da Zaituna ne kawai don na taka ta domin cimma burina.


*LABARIN JARUMI UNCLE SURAJ ARDO*


Uncle Suraj ya gyara zamanshi tare da fad'in "Sai ki karkad'e kunnenki da kyau ki sha labari, kuma duk abinda zan fad'a miki na rantse da ubangiji da ya busa min numfashi babu k'arya acikinsa.
Karo na farko da barrister A ta ji wata 'yar natsuwa ta saukar mata, saboda ta k'agu ta ji laifi da M Ardo da Maryama suka aikata masa da har ya za6i ya jefa rayukansu cikin mummunan hali, ga kuma wasu bayin Allah da ba su ji ba ba su gani ba. kaman ita da su barrister Z yana so ya shafe su.
"Nan da nan annurin kan fuskar Uncle Suraj ya dauke chakk.....kamar an yi ruwan sama an dauke, saida ya dauki tsawon lokaci kafin ya ce
kaman yanda kika
sami labari ni maraya ne, mahaifiyata ta rasu kuma ni kadai ta haifa.
A yanda na samu labari da ga bakin Dada ta ce ko ganina bata yi ba Allah ya kar6i ranta.
Dada wacce ta maye min gur6in mahaifiyata ta shayar da ni tare da d'anta M Ardo alokaci bai wuce shekara d'aya ba.
Tun kafin na fara wayo nake shan gori da hantara daga d'an uwana M Ardo, a koda yaushe yana kirana da marar sa'a a rayuwa wanda tsabar rashin sa'ar sa ko nono mahaifiyarshi bai sha ba.
sai na kishiyar uwa ya sha ya kan ce da ni ba don shi ba da tuni na bi uwata k'iyima.
Lokaci da na fara wayo na fahimci idan maganganu shi suka dosa, duk lokaci da ya ce da ni haka sai na fashe da kuka naje wurin Dada na sanar mata.
ta rarrashe ni da kalamai masu dad'i, shi kuma tayi masa dukan tsiya.
Dada tana matuk'ar k'aunata zan iya cewa fiyye da 'ya'yan cikinta, kuma duk cikin 'ya'yanta idan kika cire M Ardo kowane su yana so da k'aunta.
M Ardo ya tsane ni tsana mai tsananin gaske wacce har takai yana hassadan cigaba na, ban tabbatar da hakan ba sai lokaci da na had'u da Maryama.
"Barrister A ta katse shi da sauri ta hanyar cewa wacce Maryama....?
kaitsaye ya ce Maryama mahaukaciya uwargidan M Ardo.
Barrister A ta girgiza kanta cike da d'ibin mamaki ta ce "cigaba ina saurare ka.
"Na had'u da maryama a Ahmadu Bello university Zaria[ABU ZARIA] shekarar 1972 kusan kusan shekara 48 kenan.
Alokaci ina karatun degree na ina shekarar k'arshe ita kuma tana shekarar farko, department d'inmu d'aya kasancewar mu mun fito gari d'aya wato Yola yasa muka fara zumunci daga karshe alak'ar mu ta tashi daga zumunci zuwa zazzafar soyayya mai k'arfin gaske ina matuk'ar k'aunar Maryama Kaman numfashina haka ita ma take sona.
Ban ta6a tsanmani akwai wani mahaluk'i da zai iya raba Maryama da soyayyata ba koda mahaifanta ne, ashe gajeren tunanina ne ya bani hakan.
Na kammala karatu na cike da nasara ba al'afahari ba duk yawan 'ya'ya Ardo ba wanda ya kai basira ta, Allah ya albarkace da ni kwakwalwa mai sauri rik'e abu komai girmansa ko kuma k'ank'ata shi zan iya cewa wannan baiwar ita ce tak'ara jayo min zazzafar kiyayya daga d'an uwana M Ardo, saboda ina kammala karatu mahaifinmu Allah ya jik'ansa.
Amin summa Amin!
Cewar Barrister A tana mai talla6e kumatunta.
Yayin da Uncle Suraj ya cigaba da cewa duk wani kasuwanci na mahaifinmu a wancce lokaci da ni ake tafiyar da shi, duk wani sirri na dukiyar mahaifinmu ba wanda ban saniba.
M Ardo hassada da bakin cikina kaman zasu kashe shi saboda haka ya kudurta anniya duk wani farin cikina, sai ya yi awon gaba da shi.
Sai ya fara bin bokaye da malaman tsinbu duk don a shiga tsakanina da mahaifina ya cire ni daga cikin kasuwancin sa, tsafi gaskiya mai shi sai gashi na wayi gari duk abinda na ta6a sai ya lalace, sannu-sannu na fara janyowa mahaifina asara wacce yana daff....da afkawa kariyar arziki da
mahaifina ya fahimci abin daga gareni ne sai, ya fara daure min fuska baya so ganina ya tsane ni daga k'arshe sai cewa ya yi na daina zuwa kasuwa har sai ya nemi ni, abin mamaki yana cire ni daga dukiyarsa sai gata dawo tana hab6aka fiyye da farko, ban gama jinyar kora da mahaifina ya yi min ba sai ga wani sabon al'amari maryama za ta aure d'an uwana M Ardo ba ni ba.
Ranar nayi kuka kamar raina zai fita
Dada ce kadai mai rarrashi na, ba k'aramin fushi Dada tayi da M Ardo a dalilin ta ce ya hak'ura da auren Maryama saboda ni ne nafara neman aureta, amma sai ya k'ekyashe k'asa ya ce Allah ya kashe shi babu wanda ya isa ya raba shi da maryama.
inaji ina gani M Ardo ya aure Maryama, kuma ba wanda ya nuna masa kuskure sa saboda malamin shi ya riga ya rufe masa bakin mutane ba wanda zai iya tanka masa.
Washe gari da aurensa da maryama ya zo ya same ni a d'akina da ke soro gidanmu, cike da izzgilanci yake kallona kafin ya ce "Suraj dama na gayamaka bakada sa'a a rayuwa amma ba ka yarda ba, sai gashi ka fara ganin zahiri da kanka.
"Yanzu duk abinda ka mallaka ya dawo nawa, hatta maryama da kake hauka akanta, yanzu tawa ce kad'an ka fara gani daga cikin k'iyayyar da nake maka.
Tsabar takaici da wuta tsanar sa da ke ruruwa a zuciyata ya hanani tanka masa, har ya gama tsoki burutsun sa ya fita, kawai dai ina ta sharar hawaye barrister A kiyayyar 'yan uba bala'i ce da kukana nasame Dada na kwashe duk abinda yafaru na sanar mata, ita kuka ni kuka daga k'arshe dai ita ce ta lallashe ni ta kama shanunta da ke k'iwo ta sayar ta bani kud'i na ja jari, na fara kasuwanci saidai kashhh....ban maida watani uku ba duk yawan kudin suka lalace, kasuwancin ya rushe.
"Ina cikin wannan halin muka waye gari mahaifin mu ya rasu, bayan an raba gado an ba wa kowane mu hakkinsa a dare da ba zan ta6a mantawa ba sai ga M Ardo ya zo min shi da abokinsa Kabir, cike da izza da zallan izzgilanci ya umarce ni da na mallaka mishi nawa gado ba
musu balle gardama na tsince kaina da dauko masa takardun dukiyata na ba shi, ya kalle ni yana dariyar mugunta ya ce "Suraj!
na ce na'am Yaya!
Ya ce inaso ka shiga duniya kayi nesa da nan karka dawo har abada, nan ma sai na tsince kaina da cewa to.....Yaya.
washe gari ko sallar asuba ban yi ba na had'a kayana ban yadda zango a ko ina ba sai k'asar Cameroon, anan na share shekaru masu
yawan gaske ko sunan k'asata Nigeria ban so ji.
"A haka na cigaba da rayuwa ko zance aure bana yi, wannan shine dalilin da yasa ban yi aure da wuri ba.
Cikin ikon ubangiji da k'udirarsa na waye gari ba abinda nakeso irin naganni a k'asata ta haihuwa, haka na had'a 'yan kayana na baro, Cameroon dama bai tara komai ba illa tarin wahala da k'uncin rayuwa.
"Lokaci da na iso gidanmu 'yan uwana kowa ya yi farin cikin dawowa ta, saidai ban tarar da Dada ba Allah ya yi mata rasuwa shekaru bakwai da suka wuce.
Nayi kukan mutuwarta sosai saboda ita ce nake kallo a matsayin mahaifiya ta.
Anan na samu labari M Ardo yadawo daga k'asar waje ya yi kud'i na ban mamaki, yana d'aya daga cikin masu kud'in Nigeria.
Alokaci da ake bani wannan labari jin nake yi tamkar zan had'e zuciya na mutu daga nan nasha alwashi sai na dauki fansar abinda ya yi min.
"A wani yammaci ina zaune a k'ofar gida abin duniya ya taro ya yi min yawa sai ga wani matashin saurayi ya zo mini, wai in zo mahaifinsa naso magana da ni ban yi gardama ba na bi saurayin zuwa gidansu duk ban sanshi ba, muna zuwa ya yi min iso d'akin da mahaifin nasa inda yake kwance yana jinya "Amina kinsan waye mahaifin wannan saurayi....??
Barrister A ta girgiza kanta.
Suraj ya share hawaye da suka zubo masa da tafin hannunshi, tare da fad'in Kabir ne abokin Yaya M Ardo wanda tare da tallafinsa ne d'an uwana ya lalata min rayuwa, yana kuka yana bani labari yanda aka yi suka yi min asiri.
"Alokaci da yake bani wannan labari sai kawai na tsince kaina da jin rashin imani na ratsa zuciyata, ba abinda nake buri irin na bi hanyar da d'an uwana ya bi domin na dauki fansar abinda ya yi min.
Duk rok'on gafara da Kabir yake min ban ko kalle shi ba kawai na tsince kaina da ficewa daga d'akin, da taimakon abokina Hamza na samu wani shaharare boka ya yi min asirin da M Ardo da kansa ya zo har Yola ya dank'a min kula da kamfaninsa da ke Yola.
Sannu-sannu bata hana zuwa saidai adad'e ba'a kai ba, kaman yadda naji malam bahaushe yana cewa....sai gashi cikin lokaci k'ank'ani M Ardo ya yarda da ni ya zumduma ni cikin dukiyarsa tsumdu.
"Gani yanda ya bani amana sai jikina yafara sanyi, ga kuma Maryama da ke jin kunya a duk lokaci da muka had'u.
Ana ciki haka Allah ya had'ani da Zaituna wacce kyawo ta ne ya rud'ani zance gaskiya ina matuk'ar son mace mai kyau duk da nasan a baya tayi sana'ar karuwanci a yanzu ta tuba, ba wani aibu idan na aureta.
Na gabatarda da Zaituna a wurin M Ardo a matsayin wacce zan aura, kinsan me ya ce Amina....??"
Nan ma girgiza kai barrister tayi ta zama speechless, saboda jin labari take yi kaman tatsuniya.
Cike da takaici uncle Suraj ya dauki handle cups da bottle d'in champagne da ke ajiye akan center table d'in da ke gabansa, ya tsiyaya a two cups ya mik'awa barrister A guda bata yi gardama ba ta kar6a saboda tana tsananin buk'atar abinda zata jik'a makoshinta da shi.
"Bayan kowane su ya jik'a nasa mak'oshi Uncle Suraj yana jujjuya cup d'in hannunsa tare da kallon cup d'in kamar a cikinsa ne zai lalla6o labarin nasa da zai ya cigaba da ba ma barrister A.
Saida ya yi shiru few minutes kafin ya cigaba da cewa da "bud'ar bakinsa sai kecewa da dariya ya yi cikin izza da izzgilancin nasa da ya saba yi min tun muna yara ya ce "dama nasan sai hakan tafaru da kai Suraj, ba ka nace sai ka aure mace mai kyau ba wannan dai tsohuwar karuwa ce kai da 'ya'ya nagari saidai ka gani a garemu.
Ya k'arashe magana yana mai kwashewa da dariya, daga ni har Zaituna a sanyayye muka fito daga office d'in shi har nayi nisa da office d'in ina jiyo sautin dariyar tasa, daren rana ban runtsa ba. washe gari na had'u da Zaituna na gabatar mata da burina naso ta aure M Ardo mu kwashe dukiyarsa saboda ita ce take saka shi izzgilanci da girman kai.
"Da yake ita ma wata shasssha ce batare da wani dogon nazari ba ta amince, daga nan muka wuce wajen wani boka a wani kauye da ke minna ta jahar Niger state shine ya yi mana asirin da M Ardo ya aure Zaituna.
Lokaci da muka gano Maryama tana da juna biyu mun je wajen boka da zumar ya lalata cikin, ya ce ba makawa sai ta haife shi.
Sai muka buk'ace ya yi mata asiri ta haukace.
Lokaci da Zaituna ta haihu 'ya mace saidai bata zo da rai ba sai muka taki sa'a M Ardo yana Lagos, abin mamaki sai ga maryama ta haihu duk da cikinta alokaci yana da watani takwas.
Ashe twins ne a cikin nata kuma duk maza shiyasa ta haihu a watani 8 saidai ita ma d'aya bai zo da rai ba.
"Na cewa Zaituna ta dauke d'an Maryama ta mayar nata ta dauki gawar 'yarta mace ta ce ita ce maryama ta haifa, tasa a binne d'an Maryama wanda bai zo da rai ba.
"Hikima ta tayin hakan shine ban so M Ardo ya ta6a alfahari da cewa maryama ta ta6a haifa masa d'a namiji, dama burinsa Maryama ta haifa masa magaji.
mune muka yi ma Aliyu asiri da yasa ya tsani aure da mata, a dalilin boka ya gayamana muddin mu kayi sake Aliyu ya yi aure ba za mu cimma burinmu na mallaka dukiyar M Ardo ba.
Labari ya canza daga lokaci da M Ardo ya nemo masa aurenki, mu je wa boka da buk'atar ya wargaza aure kaman yanda ya saba yi mana a baya sai cewa ya yi tabbas sai Aliyu ya aureki domin ya ga rabon 'ya'ya atsakaninku saidai kada mu sake Aliyu ya kusance ki, daga lokaci da ya kusance ki komai namu zai tabarbare sai gashi hakan tana shirin faru
Ni da Zaituna mun kasance muna aikata Zina yanzu haka ina da 'ya a tare da ita.
"Barrister A ta katse masa hanzari ta hanyar cewa "Ai nasani ko ba Teema mai aljannu k'arya kake nufi ba, tuni nagano 'yarka ce uncle Suraj.
Cikin kad'uwa uncle Suraj yake kallon barrister A, ita kuma sai murmushi take zabga masa.
Nasan kana so kasan ta wacce hanya na bi nagano Teema 'yarka ce....?
Amsar ita ce ta cikin baccin Teema.
Bacci kuma....?
Uncle Suraj ya maimaita cike da mamaki.
Kwarai kuwa ta baccinta wanda ko ita kanta Teema batasan na sani ba, ranar da Aliyu ya yi tafiya zuw Lagos ina jin tsoro kwana ni kadai sai na nemi Zee-zee da Meena su zo su tayani kwana amma sai momma ta hana su.
Sai kawai na gayyato 'yan aikina da su zo mu kwana tare har na rufe k'ofa sai naji knocking koda na bud'e k'ofa sai naga Teema, kamar yadda tasaba yi pretending d'in iskokanta hakan tayi min ta wuce ni batare da ta ce da ni uffan ba, ina kallonta ta haura upstairs na bi ta da sauri tana zuwa ta bud'e bedroom d'ina ta shiga ta kwanta kan gadona, sai lokaci ta ce da ni matar yaya na zo na tayaki kwana ne.
Nayi mata murmushi tare da cewa nagode Teema.
Bata dauki dogon lokaci ba tafara bacci ni kuma na dauko laptop dina domin nayi wani aiki, Teema tana cikin mutane da ke bayyanar da damuwarsu ta cikin baccin da suke yi. Can tsakiyar dare baccinta yafara nisa sai tafara kuka ta na fad'in momma kin cuceni Me nayi muku ke da uncle Suraj za ku samar da ni ta k'azamar hanya Allah ya isa tsakanina da ku ba zan ta6a yafe muku ba.
Alokaci na firgita had'e da gigicewa ba kad'an ba da farko na dauko ko iya shegen ta ne, na iskoka sai na isa daff.....da ita na aza hannuna a k'ofufin hancinta sai naji saukar numfashinta tabbas bacci ne take yi kuma ya yi nisa sosai.
"Ka ji ta yanda aka yi nasan Teema 'yarka ce.
Uncle Suraj ya saki murmushi ya ce gaskiya you're very smart barrister A kwakwalwar ki tana ja sosai.
Dariya tayi tare da ajiye cup d'in hannunta ta ce "Uncle kenan ai ba banza ba Abba na yana ce saida ya ga na zama cikkakiyar lawyer
Abban ki ya ci a bashi award domin gashi ta sanadin mayarda ke lawyer kina bankad'o sirrika mutane.
"Dariya barrister A tayi tare da fad'in gaskiya ya chanchanci abashi abinda ya fi award saboda, ga shi a sanadinsa zai cuto rayuka da yawa daga halak'a daga ciki kuwa har da kai Uncle.
Uncle Suraj ya girgiza kanshi tare da fad'in karki yi gaggawa Barrister A ki d'an takata kad'an.
Saboda mijinki Aliyu da kike gani ba d'an Zaituna bane Maryama ce ta haife shi kinga ya kamata ki san irin hatsarin da uwar mijinki ta ke ciki.
Ga mamakinsa sai ya ga tayi murmushi tasake kur6a champagne d'inta, ta ce "kwarai kuwa nasan da hakan nagano hakan ne kusan kwanaki biyu da suka wuce a dalilin cindo[6th finger]

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login