Showing 18001 words to 21000 words out of 80263 words
gida.
Jeeddah Aliyu
[7/26, 11:52 PM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619
DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA
*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```
*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```
*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``
*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- RUYUWATA
*SLIMZY*:- IZZATA
*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO
*GIDAN RINA*
*12*
Washe gari bai samu damar biyawa wajenta kafin ya wuce Abuja ba, ya dai kirata a waya suka yi sallama duk wannan abin yana yi ne don kawai ya farantawa Daddynshi rai ba wai don ya ji yana sonta ko kuma ra'ayin aure ba.
***----***---****
*ABUJA*
Da yake jirgin safe Aliyu ya shigo yana isowa direbanshi Isah ya yi picking d'inshi daga Airport, lokaci da ya iso Ardo mansion ba nemi kowa ba ya wuce flat dinshi dama wannan yana d'aya daga cikin d'abi'unshi, za ka san tafiyarshi amma ba lalle bane kasan dawowarshi.
"Freshen up ya yi gani lokaci sallar azhar ya yi yasa yasaka farar jallabiya mai gajeren hannu, ya nufi masjid da ke gidan ya yi sallah yana dawowa ya cire jallabiyar ya jefa akan sofa ya nufi master bedroom dinshi ya haye tangameme gadonshi, ya k'ara gudu Air con ya lumshe shanyayun idanuwanshi masu cike da bacci bai dauki dogon lokaci ba bacci ya yi awon gaba da shi.
sai misali k'arfe 5:17pm ya farka a gurguje ya yi wanka saboda jikinshi ya sake bayan ya yi sallah la'asar ya canza jallabiya jikinshi zuwa fari three quieter da white colour hoodie armless, wacce ta fito da muscles d'inshi farare slippers masu taushin gaske yasaka, ya kwashi wayoyinshi ya nufi flat d'in momma.
A falo ya tararda ita da girls d'inta sai faman zazzagawa Tima fad'a take akan tak'i shan maganinta.
Ya yi sallama can k'asan mak'oshi Minat ta amsa mishi sannan ta gaidashi, ya amsa mata kamar yadda ya yi sallama.
"Zee-zee ma ta gaidashi ya yi banza da ita, Tima da ke shasshek'ar kuka ya dakawa tsawa ke!
A firgice ta d'ago ta dubi shi rufewa mutane baki tun kafin na take miki wuya, me akayi miki da za ki tsirawa mutane kuka duk kin cika min kunne?"
sadda kanta k'asa tayi tana sharar hawaye, ke Zainab me take yi ma kuka?"
Magani ne momma ta bata tak'i sha shine momma take mata fad'a.
"Yatsine fuska ya yi ya ce momma please....ki dinga hak'uri da yarinyar nan mana, tunda ta ce bataso magani ba sai ki kyalleta ba in fact wannan magani mai wari tsiya ko waye dole ya yi kuka shan shi, ni narasa ina ki ka samo shi.
"Kafira harara momma ta zanga masa kafin ta ce gidan ubanka na samo shi, wallahi Sultan ka shiga taitayinka da ni.
Dama ina cike da kai zaman jiran zuwanka nake.
"Kallo da yakewa su Zee-zee yasa suka gano me yake nufi da sauri suka mik'e Minat ta kamo hannun Tima suka nufi upstairs parlor.
"Ya tsare momma da idanuwanshi da suka nuna zallan 6acin rai, duk duniya ba abinda ya tsana irin fad'a tun yana yaro da ka yi mishi fad'a gara ka rufe shi da duka.
Gani yadda ya tsareta da idanu yasa tagano ya hasala, dama haka takeso saboda duk lokaci da ya harzuk'a tafi sauri aiwatarda shirinta akanshi.
"Don haka ta cigaba da cewa wai har da kai sultan za'a had'a kai a munafuce ni, wato shine za'a kai kayan lefen aurenka Yola ina matsayin mahaifiyarka ba d'an banza da ya gayamin sai da naji a bakin shannu talla, hakan da ku ka yi kai da mahaifinka kun kyauta?"
Tak'arasa magana tana share hawayen kissa.
Ta gefen ido take satar kallonshi.
Sosai jikinshi ya yi Sanyi gani yadda take kuka kuma duk a dalilinshi, ya sausauta muryarshi cikin tattausan lafazi yafara magana ki yi hak'uri momma bansan cewa Daddy bai gayamiki zance lefen ba, ni kaina ba sanarda ni ya yi ba sai ana gobe za'a kai kayan Aunty Salma ta kirani a waya take sanarda ni.
Kada wannan abin ya dameki momma Daddy ya yi haka ne duba da banaso aure, ya kuma san duk abinda banaso ba lalle bane ki so shi, ki kwatarda hankalinki momma aure ma ba sonshi nake ba balle wacce aka kai ma kayan lefe.
"Gyara zama momma tayi ranta fari tasss.......ta ce ni na dauka ko had'uwarka da yarinyar kafara sonta, musanmman da naji ance kyakyawa ce ajin farko.
"Uhm....yafada had'e da dafe goshi ya ce kema momma kina da wani zance sai kace kin manta da waye Aliyu, ko kayan sawa nace banaso to ta tabbata banaso su kuma har abada ba zan so su ba, balle mace wacce kiyayyata darsu azuciyata.
"Hamdallah momma tayi ta cika fuskarta taff da murmushi, ta ce ka bi hankali sultan kada Daddynka ya yi sauri hal6o jirginka ka ko san ba za ku kwasheta da kyau ba.
"Insha Allah bama zai gane ba saboda ko cikin kuskure banta6a fad'a mishi bana sonta ba.
Madallah d'an albarka bari nasa Laure ta kawo ma abinci.
Da sauri ya ce no am okay"
Sama-sama suka cigaba da fira yawanci firar tasu duk tambayoyi ne momma take mishi, akan barrister wani ya bata amsa wani kuma ya ta6e baki ko ya yi shiru.
***----****----****
*™YOLA*
Tafiya Abba ya shiryawa ummi da Barrister Amina zuwa Dubai, siyayyar kayan aurenta milliyoyin kudi ya basu ita kanta Ummi sai da ta zare kud'ad'e masu dibin yawa a account d'inta da za tayi tafiyar da su Barrister A ita ce 'yarsu ta fari kuma 'ya mace daga kanta za suyi shekaru kafin su aurarda Rahma don haka duk wani tanadinsu akanta suke yi.
Ana sauran kwana biyu tafiyar Barrister ta zauna tayi nazarin irin makud'an kud'in da take da a account d'inta tarawa kawai take batare da tana amfani da su ba, don haka yanzu amfaninsu yazo, zarar abinta tayi za tayi tafiyar da su.
"Kwanansu tara a Dubai suka juyo Nigeria duk tsawon lokaci nan Aliyu bai nemi ta ba, kamar yadda ita ma bata nemi shi ba duk da koda yaushe cikin tunaninshi take, amma ba za ta iya karya bulleta ba ta nemi shi.
****''''****'''''***
*ABUJA*
Aliyu zaune a sitting room d'in Daddy suna tattauna nasarar da ya yi a business trip d'in da yadawo, Daddy ya gyara zamanshi ya dubi Aliyu da kyau kafin yace wane irin shiri ka ke yi dangane da aurenka?"
Yatsine fuska ya yi ya ce babu.
meaning?"
cewar Daddy a fusace.
Daddy babu duka fa jiya-jiyanan nadawo ko hutawa banyi ba, yanzu haka gajiya bata gama sakeni ba.
"Sosai ran Daddy ya 6acin sai kallon Aliyu yake kamar ya rufe shi da duka.
Ya ce wannan zance banza ne yau duka saura kwanaki tara a daurama aure, amma ba ka shirya komai ba.
Kai kenan duk lokaci da akayi maka magana akan aurenan sai kasan yadda za ka kare kanka, ka sani sultan ina nema maka alkhairi ne ba sharri ba domin duk uba nagari yana fatan d'anshi ko 'yarshi suyi dace da abokanan rayuwa masu nagarta da mutunci.
Abinda nake so ka gane Sultan shi ne wannan auren umarnina ne, ba wai ina shawartaka ba don haka ka kasance a shirye ka kuma yi abinda kowane ango yake yi yayin aurenshi, saboda ba abinda za'a fasa sai in dai mutuwa ce ta dauke ni kafin lokaci, shi ne ka ke da damar fatali da umarnina, shiyasa da na fahimci mahaifiyarka tana min zagon k'asa a zance aurenka na tsigeta a tafiyar domin banaso abinda za kawo min tangard'a saboda haka ka kiyayye.
Sosai jikin Aliyu ya yi sanyi ya kalli inda Daddy yake zaune, ya ce Daddy kayi hak'uri wallahi abubuwa ne sukayi min yawa har narasa ina zan sa kaina.
"Takaici ne yak'ara kama Daddy batare da yace da shi komai ba, ya mik'e ya shiga bedroom bai dauki dogon lokaci ba yadawo hannunshi dauke da led'a fara ya jefawa Aliyu gashinan abinda ka kasa yi ne nayi invitation ne na dauri aure in ka ga dama ka ba wa friends da business partners d'inka, tashi ka bani wuri.
Salun-alun Aliyu ya mik'e ya fice zuciyarshi ba dad'i.
Jeeddah Aliyu[7/26, 11:54 PM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619
DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA
*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```
*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```
*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``
*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYYATUDEEN
*SLIMZY*:- IZZATA
*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO
*GIDAN RINA*
*13*
B'acin rai ya bayyana k'arara akan fuskarshi hakan yasa idanuwanshi ma'abota kyau da kwarjini, suka canza launi daga farare zuwa ja.
picking lot yanufa da gudu direbanshi isah ya taso ya jawo mota ya bude masa k'ofa ya shiga.
Sai da suka dauki hanya kafin yace gidan Jamal za ka kaini kira shi a waya ka ji ko yana gida.
Okay....boss"
Cewar Isah direba yana ciro wayarshi daga gaban aljihu farar shirt da ke jikinshi, ya yi dialling numbern Jamal.
Boss ya ce yana River plate park ka sami shi acan.
Omg! Uban me Jamal yake tsinta a park sai ya lura mutane na cikin damuwa yake tsira yawo marar amfani "mtssss....ya ja tsaki cike da takaici ya umarce Isah ya kai shi can.
Suna isowa Isa ya bude masa k'ofa yafito ya kai hannu ya kar6i ledar da ke hannunshi, sai lokaci Aliyu ya tuna da ledar.
"Please.....Isah sake kiranshi ka ji yana dai-dai ina.
kafin ya kai da kirar nashi suka hango shi, yana k'arasowa ya mik'awa Aliyu hannu suka gaisa jerawa suka yi yayin da Isah ke bin bayansu.
Cikin wasu bukkoki da ke dauke da kujeri kamar na kaba had'e da table a tsakiyarsu, suka nufa Jamal ne yafara jan d'aya daga cikin kujeri ya zauna, da sauri Isah yajawa Aliyu kujerar ya zauna cike da damuwa ya dafe goshinshi waiter ne ya kawo musu menu ko da akwai abinda suke buk'ata Jamal ne ya yi musu order.
"A natse yake kallon abokin nashi kafin ya ce ya akayi ne king naga kamar da damuwa akan fuskarka?"
Ajiyar zuciya ya sauke mai k'arfin gaske ya ce ba kama bane Jamal, damuwa ce takeso yi min yawa.
Subhnalillah......meke faruwa ne?"
Hannun ya mik'awa Isah batare da ya yi magana ba, ledar da ke hannunnshi ya mik'o mishi shi kuma ya mikawa Jamal.
"Invited card ne na dauri aure koda na dawo daga Zurich har Daddy ya bugu su.
Ya k'arasa magana kamar zai yi kuka.
"Fito da cards din Jamal ya yi yana kallo yana murmushi saboda tsananin kyau da tsadarsu, ya ce lalle Aliyu kai d'an hutu ne sam baka san wahala ba, gaba d'aya rayuwarka cikin gatanci ka ke yi ta hatta aure ma baka san wahalar nemanshi ba, yi maka akayi.
"ka tsinci zankad'edd'iyar mace kyakyawa ajin farko a gidanka wallahi ka ji dad'inka.
"Yalwattace murmushi ya yi sannan ya jan tsaki mtsss.....ya ce ina gatanci ga aure da ba soyayya a cikinshi, wasu lukuta inda na zauna ina nazari har misalta yadda zamana da Barrister zai kasance, saboda ita kanta ba son nawa take yi ba dole ne akayi mata kamar yadda akayi min.
Yanzu dai mu aje zance kana so ko baka so, tana so ko bataso muyi wanda ke gabanmu.
Ya raba card's d'in biyu ya mik'awa Aliyu kashe d'aya ka ba wa business partners dinka, wannan zan ba wa friends d'inmu, sai abu na gaba ka shirya muje Yola domin muji nata bangare me take shiryawa ka san dole ba za'a rasa events d'in da za suyi ba irin su dinner, cocktail party.
"Dallah ya isa ana zaune qalau za ka daukowa mutane bidi'a, ba da ni za'a yi wannan iskanci ba.
yakarasa magana yana hura hanci.
Dariya Jamal ya yi ya ce ka ji da shi wai ciwon ajali a d'an yatsa aure ne dai ba fashi sai ayi.
"Sai kuyi tayi amma dai ba wanda isa ya sani zuwa party da ban yi niyya ba.
Ba wannan ba yanzu yaushe za mu tafi Yola?"
Mu bari koda zuwa ranar labara ne, duk da ranar ina da aiyyuka da yawa a gabana.
"Koma menene agogo sarki aiki jingine shi za kayi, har sai muje mun dawo, ka godewa Allah abokina da yabaka zuk'ekk'iyar mace irin Barrister Amina wallahi kayi dace da mata.
Yarinya natstsiya mai kunya uwa-uba wayewa da gogewa na tsantsa ilimin zamani, kuma ga dukan alamu har na addini tana da shi.
"Aliyu ya yi murmushi sannan ya ta6e baki ya ce nima ai tayi dacen miji santalele, business tycoon irina wanda mata suke haukar so amma sai gashi ita tasamu a arha.....
"Jamal yaja tsaki....mtsss had'e da cewa kai dai anyi tsoho d'an iska wallahi, wato kana sane da haukar da mata suke yi akanka, basarwa kawai ka ke yi.
"Ba gashi hakan ya yi wa barrister rana ba zata kwashi gara6asa.
Duka Jamal yakai mashi yana cewa ka shiga uku king ka dai anyi 6aud'add'e mutum, a lokaci d'aya sukayi dariya har suna tafawa.
"Ka shirya kawai gobe muje sai mu dawo a ranar, ka ga ba za mu koma ba sai an sakata a lalle alokaci ta dau k'amshi sai ka shinshshina kayanka a tsanake.
"Sosai maganar ta Jamal ta bashi dariya don haka ya shiga kyakyatawa abinshi, wanda hakan ya janyo hankali Isah direba ya kura mishi idanu, a zuciyarshi ya ce lalle yau za'a yi ruwan sama boss yana dariya.
"Shikenan ka shirya mu bi jirgi safe kamar yadda mu kayi a wancan lokacin.
****----*****---****
*YOLA*
*10:44am*
Barrister Amina tana zaune akan dining table ta sanya abinci agaba, tana kallo ta kasa ci gaba d'aya tunanin Aliyu ya cakud'e mata zuciya, wani lokaci sai tayi yunkuri kirar numbernshi sai zuciyarta ta haneta saboda aganinta kiranshi zai zama ta zubarda ajinta ne.
"muryar Barrister Z taji tana gaisawa da Ummi, hakan yasa ta saki nannauyar ajiyar zuciya ta yi wulgi da folk d'in hannunta sannan ta mik'e tsaye dai-dai Barrister Z na isowa, amaryaaaa....
Cewar Barrister Z tana mai rungume Barr A murmushi Barr A tayi had'e da dan gajere tsaki, ke zo muje room d'ina akwai abubuwa da yawa da za mu tattauna.
Gefen gadon d'akin sauka zauna barr Z ta ce ya dai bebs naganki wani irin ko dai har kin fara shiga cikin fargaba aure ne?"
"Da yake muddin zakayi aure sai kayi ta faman da zullumi barin gidanku, amma karki damu bebs na d'an lokaci ne za ki saba mu ma can takalminmu ya tsinke sai gashi yanzu mun manta da gida sai dai mu kai ziyara.
"Barr A ta dalla mata harara tana mai jan dogon tsaki mtssss......
Barni da wannan zance bebs ni ai na jima da shiga wannan fargabar tun kafin zuwan lokaci gaba d'aya komai ya cakud'e min, babban tashin hankalina bai wuce irin zaman aure da zanyi ba.
"Tak'arasa magana kamar za tayi kuka.
"Dafa ta Barri Z tayi cikin tausassa harshe ta ce miye dalilinki na fad'i haka bebs?"
"Dalilina bai wuce har zuwa yanzu da ya rage sauran 'yan kwanaki k'alilan azarga min igiyoyin aurenshi akaina, amma babu wata kyakyawar fahimtar juna atsakaninmu bana tunanin Aliyu Ardo yana jin burbushin sona azuciyarshi, ni kuma gashi soyayyarshi ta mini mummunan kamu shiyasa natsuwa da kwanciyar hankalina suka kaura.
Damuwa tayi min katutu har cin abinci naso gagarata, ni narasa yadda zanyi da rayuwarta.
"Ba wata kulawa da nake samu daga gareshi, bai damu da ni ko kad'an ba ya yi halin ko oho da al'amurina babban takaicina Ummi sai faman shirye-shirye take ba abinda ya dameta, na tabbata da Abba yana da masaniyar da rashin fahimtar da ke tsakaninmu da tuni zai yi fatali da zance aurenan, to abinda ni kaina bana fatan faruwarshi duba da yadda na tsunduma
kogin soyayarshi.
_Just to manage_
Jeeddah Aliyu
[7/26, 11:54 PM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619
DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA
*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```
*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```
*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``
*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYYATUDEEN
*SLIMZY*:- IZZATA
*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO
*GIDAN RINA*
*14*
murmusawa Barrister Z tayi tare da girgiza kanta sannan kuma ta, gyara zamanta ta fuskanci Barrister A ta ce don ya nuna halin ko oho akanki, baya nufi bashida ra'ayinki,
Benbs kiyi la'akari da yanayin aikinshi ba na zama wuri d'aya bane.
ke da kanki kin sani don ya gayamiki, kuma duk da rashin kulawarshi ba'a fasa gudanarda komai ba.
Don haka "don Allah ki kwatarda hankalinki kada ki haifarwa da kanki da wata matsala.
"Amma bebs ai yana da number wayana miyasa bai kirani ba?"
Kema ai kina da numbernshi miyasa ba kira shi ba?"
Saida ta galla mata harara kafin tace haka kawai zan kira shi salon ya daukeni marar aji.
Oh! Haka ne ashe ba shi kadai bane mai laifi, kema kina da naki saboda haka ki jingine wannan k'orafin naki bai samu kar6uwa ba.
Muyi magana da ke gabanmu.
Dole barrister A ta share zance duk da yana nuk'urk'usar zuciyata ta dauki invited cards suka fice wurin rabawa 'yan uwa da abokan arziki.
A washe gari mai gyara jiki ta musanmman da Ummi ta kira daga Sudan ta iso, tun daga ranar ta shiga gyara Barrister A.
***---***---***---****
*ABUJA*
*10:37am*
Aliyu yafito cikin shirin shi na farar shadda daga flat d'inshi yanufo na iyayyenshi, a sitting room ya tararda Daddy da momma zaune.
Tun kafin ya k'arasa yake jin tashin muryoyinsu, tsinta kanshi ya yi da jin 6acin rai saboda yasan duk saboda zance aurenshi ne yake saka su hayaniya.
Jikinshi asanyayye
ya nemi kujera can gefe ya zauna ya talla6e ha66arshi yana kallonsu, batare da ya tanka musu ba.
Daddy ne ya yi k'arfin halin cewa Sultan ina zuwa da sanyi safiyanan?"
uhmm....saida ya yi ajiyar zuciya kafin ya