Showing 21001 words to 24000 words out of 80263 words
ce Yola...
Daddy ya fad'adda murmushinshi ya ce da kyau my fav boy, shigowar nan taka maganarka ce muke yi ni da mahaifiyarka, bisa wani tunani da nayi na yanke hukunci a gidanka da ke Yola za ka fara zama kai da matarka, na wani d'an lokaci kafin ta tare anan Abuja duk wani abu da gidan yake buk'ata an zuba maka.
Idan akwai abinda bai maka ba in ka je sai kayi min magana kaji ko?"
Dafe goshi Aliyu ya yi ya shiga nazarin maganar Daddy tsawon some minutes kafin yad'ago wearing a killer smile on his face "ya ce thank you Daddy Allah yak'ara lafiya da nisan kwana ni zan wuce.
Yak'arasa magana had'e da mik'ewa Allah shi yi maka albarka Gadangan Daddy Allah ya tsare min kai, yakare ka daga sharri mutum da na aljan, yadda ka ke min biyayya kaima Allah yabaka masu yi maka.
Cak...Aliyu ya tsaya saboda sosai addu'ar Daddy ta ratsa k'ashi da 6argon jikinshi, saida ya juyo sannan ya amsa da Amin summa Amin Daddy.
Momma ta tur6une fuska ta ce zo nan Sultan nima a matsyina na wacce ta haifeka ina da magana.
Har Aliyu ya juyo Daddy ya ce je ka abinka Gadanga za ta 6ata maka lokaci ne a banza, shiru Aliyu ya yi shi bai tafi ba kuma shi bai dawo ya zauna ba.
Sosai ran momma ya 6aci tasaki tsaki ta kuma shan alwashin sai ta raba Barrister A da numfashinta, gashi tun kafin ta shigo ta fara raba mata kan iyali.
Ta cije le66enta na k'asa ta yi kyaci ta mik'e fuuuu...tafice daga sitting room.
Daddy ya dubeshi yana murmushi cikin sigar kwantarda hankali ya ce yi tafiyarka Allah ya kiyayye hanya barni da ita zan rarrashe ta.
Cike da gansuwa Aliyu ya gyad'a kai ya fice.
***--****----*****
Daga Airport Aliyu ya wuce gidanshi shi kanshi gidan ya burge shi sosai, bai kuma ci karo da wani abinda bai mishi ba saida suka huta shi da Jamal kafin su nufo gidansu Barrister A lokaci da sak'o ya riske Barrister A Aliyu ya iso ana mata gyara jiki tsakanin jiya da yau fatar jikinta tak'ara glowing, sai fitarda k'amshi mai jan hankali take.
Scrub d'in da ke jikinta ta nufi bathroom a gurguje ta wanke tafito daure da towel, ta dube k'awarta Fadila wacce cousin d'inta ce 'yar wurin Aunty Khadija ce.
Tq ce Fadila please ki je wurinsu kafin na shirya, saida Fadila ta tsokaneta kafin ta fice tanufi falon bak'i.
Cikin abinda bai wuce 10-12 minutes ba Barrister A ta shirya ciki atamfar exclusive d'inki riga da skirt ya zauna dass....a jikinta d'an siriri veil kalar atamfarta ta yane kanta da shi, ita kanta lokaci da tayi arba da dressing mirror saida tasaki k'ayatattace murmushi, sakamakon kyau da tayi ta fice daga d'akin cikin yanayin tafiyarta mai matukar daukar hankali.
"Tun kafin ta k'arasa shiga falon iska ya kai musu fitinanne k'amshinta, ta tura k'ofa bakinta dauke da sallama ta shigo.
Jamal da Fadila suka amsa mata sa6ani gogan naku da lips dinshi ne kawai suka motsa, saida ta zauna kafin ta gaida su a lokaci d'aya dukansu suka kalle ta, sosai kyawota ya rud'asu da sauri Aliyu ya dauke fuska.
Jamal ya yi murmushi yana mai cigaba da kallonta ya ce amarya da fatan za'a yi mana afuwa, kasancewar kin ganmu kwatsan ba sanarwa, muyi ta neman layinki baya shiga kinsan dai yadda lamari network yake.
Sadda kanta k'asa tayi tana wasa da yatsun hannunta, tasan duk abinda Jamal ya fad'a ba gaskiya bane yana dai neman ya kare abokinshi ne.
"Da kyar ta d'ago tayi murumushi, batare da tace komai ba Jamal ya dubi Fadila ya ce malama Fadila zubamin lemo muje daga waje, naji shirye-shiryenku kafin ango da amaryar nan su gama zantawa dariya Fadila tayi tana mai cewa lalle kam gara mu basu wurin naga sai fik'i-fik'i da idanuwa suke yi.
"Murmushi Aliyu ya yi cikin husky voice d'inshi ya d'ago yana lumshe lulu eyes dinshi, ya ce Fadila daina biyewa Jamal kinsan nace ke ce ta hannun dama na.
Dariya Fadila da Jamal suka yi yayin da Fadila ta tsiyayawa Jamal juice a handle cup, sannan ta kalli Aliyu ta ce na daina ranka ya dade Jamal ne yakeso ya had'amu, ba kuma zai yi nasara ba.
"Karka dai manta da alk'awalinmu.
Tafad'a had'e da nufar k'ofar fita Jamal ya biyo bayanta yana cewa ai bai isa ya manta da wannan alk'awalin ba.
Bayan fitar Jamal da fadila suka yi shiru na some minutes shine ya fara d'agowa cike da isa da tak'ama ya kalle ta ya ce Barrister ya gida ya kuma shirye-shirye biki?"
Ita ma ta d'ago da murmushi akan fuskarta wacce sai glowing take, ta ce Alhmdulilah!
Yalla6ai ina neman alfarma wurinka da, ka kirani da ainihim sunana Amina ko ka ce Minal.
"D'an gajere murmushi ya yi kafin ya ce nima sunana Aliyu ko ki ce Sultan ba yalla6ai ba, don haka sai kindaina kirana da Yalla6ai zan daina kiranki da barrister.
Turo d'an k'aramin bakinta tayi mai kama da gidan tsuntsu, tana gunguni k'asa-k'asa.
"mekika ce ne?"
Ni ba da kai nake ba.
Tafad'a cikin sigar shagwa6a.
Ta6e baki ya yi ya dauke fuskarshi da barin kallonta.
Shiru suka sake yi na tsawon lokaci daga bisani Aliyu ya ce taimaka kiyi min text din account numbernki.
Tayi rau da idanu ta ce me za kayi da shi?"
Cikin daure fuska ya ce ina ruwanki da abinda zan yi ke dai ki turomin kawai, batare da ta furta uffan ba tayi mishi sending.
yana jin shigowar text a wayarshi ya duba ya ga ita ce, sannan ya d'ago ya sake cewa dame-dame za ku yi na shagalin biki?"
Ta d'an kad'an idanunta ta ce za muyi Fulani night sai mother night sai kuma dinner da abokan aikina suka had'a mana.
Jeeddah Aliyu
[7/26, 11:55 PM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619
DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA
*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```
*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```
*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``
*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYYATUDEEN
*SLIMZY*:- IZZATA
*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO
*GIDAN RINA*
*15*
Ya d'an yi rolling lulu eyes d'inshi ya ce kai duk ku kadai, lalle barrister kina so bidi'a.
Ta d'ago ta zuba mishi idanu tsananin kyau da kwarjininshi suka cika mata idanu.
Ta kasa dauke idanuwanta daga kanshi, gani yadda tai mishi kurrr.....da idanu yasa ya dafe goshi "Omg barrister daina yi min kallon tuhuma ai gaskiya na fad'a ya k'arasa magana yana d'age girarshi.
Sosai hakan ya k'ara mishi kyau.
lumshe idanu tayi eyelashes d'inta suka kwanta kamar ta k'ara da na katti, daga bisani ta bud'e idanun nata ta ce idan ba kada ra'ayi events d'in zan yi magana sai a fasa Yalla6ai.
Ta k'arasa magana tana kallon shi.
"Ya d'an shafo gashin kansa yana ta6e baki ya ce uhm....a'a kuyi kayanku dama ku mata ba'a rabaku da bidi'a.
Tayi murmushi kawai ta rausayarda kanta gefe, kafin tadawo da ganinta akanshi ta ce hope za kayi k'ok'ari kayi attending events din ko?"
Yalwatattacen murmushi mai narkarda zuciya yasaki, yana kallon kwayar idonta wani yarrr.....taji yayin da sanyi ya ziyarce sassan jikinta batasan sanda ta lumsashe idanunta ba.
Cikin sanyi murya ya furta ya na iya dole na zo, kada nasake wani laifi saboda na fahimci kallon mai laifi ki ke min.
A hankali tayi 'yar siriryar dariya mai ban sha'awa.
"Ya d'an gyara zamanshi yana kallon cikin idanuwanta ya ce kin ji sabon canji da aka samu yanzu anan za ki fara zama kafin ki tare a Abuja.
Yalwatattace murmushi tayi kafin ta ce ni wallahi hakan ba k'aramin dad'i ya yi min ba.
Ta k'arasa magana tana sunne fuska.
Uhm....ya fa'da had'e da kallon tsakiyar idanunta ya ce dole ya yi miki dad'i saboda ba ki gaji da cinyewa Abba tuwo ba.
Sosai maganar tashi tabata dariya ai kuwa ta dara har kana ji sautin fitar dariyar ta, ta.
Yadda take dariya ba k'aramin burgeshi ta yi ba har baisan lokaci da ya shagala da kallonta ba, jikinta ya bata ana kallonta hakan yasa ta mayarda ganinta akanshi.
"Gani ta fahimci yana kallonta yasa ya waiyace ya mik'e da sauri yana kallon wrist watch da ke daure a tsintsiyar hannunshi, yana mai cewa za mu wuce saboda yau zamu koma Abuja sai ranar da za ku fara programs d'inku zan iso.
"Mik'ewa tayi fuskarta cike da murmushi ta ce Allah ya kaimu, ya Kuma kai ku lafiya ka gaidamin da su mommy.
"Sai da ya nufi k'ofar fita sannan ya ce Amin!
Bayanshi tabi parking lot ta hango Jamal da Fadila, suna fira abinsu yadda yake tafiyarshi ta k'assaita yasa har ta ci mishi suna tafiya side by side sosai suka dace da juna.
Suna shiri tafiya motar Barrister Z ta danno kai, cikin sanyi murya mai d'and'ano gaske, Barrister A ta ce yalla6ai d'an tsaya ku gaisa da best friend d'ina Barrister Zarah.
Cak.....ya tsaya har Zarah ta k'araso wacce tun kafin ta iso take zuba murmushi, ta ce sannunku!
Jamal ne ya amsa mata da yauwa Barrister ya hak'uri da Jama'a.
"Alhamdulillah!
Ashe na taki sa'a yau dai gani ga angon namu mai tsada ai na dauka sai na rubuta requested letter zan samu ganinka.
"Sosa keyarshi ya yi yana murmushi kafin ya ce laifin k'awarki ne da bata dauke ni ta kaini gidanki na kwashi gaisuwa ba.
Lokaci d'aya dukkaninsu suka yi dariya sannan suka gaisa fira suka d'an ta6a, daga bisani suka yi sallama.
Bayan sun wuce s d'akin barrister A suka yi direct, nan suka bud'e sabuwar fira duk dai akan Aliyu ne, Barrister Z da Fadila sai shawara suke bata, yadda za ta sami matsugunni a zuciyarshi sosai tayi na'am da shawarar tasu.
***---****---****---***
*ABUJA*
Momma wacce abin duniya ya taro ya yi mata yawa, tarasa inda zata tsoma ranta taji sauki ta kira Jarumi ko da wata mafita daga gareshi, sai ma lullu6eta da fad'anshi na raini wayo da ya yi har yana had'awa da yi mata barazana mai firgitarwa, shiyasa tak'ara tsundumawa damuwa fiye da ta farko ga kuma Daddy ya ce su had'a kayansu ita da yara gobe zasu wuce Yola.
"Dole bata da za6i ta shiga had'a abubuwan da za tayi amfani da su, ita kanta tasan ba abu mai yuwa bane ayi shagulgulan bikinan ba uwar ango, dole ta rarrashi zuciyarta ta danne abinda takeji tashiga jama'a ayi da ita muddin bataso jama'ar duniya su saka alamar tambaya akanta.
Washe gari jirgin safe suka biyo zuwa Yola.
"Girls d'inta sai murna da annashawa suke, bros d'insu zai yi aure zai kawo musu sister in law, afakace momma take danna musu harara.
"Daga Airports gidansu suka wuce wanda uncle suraj ne ya yi picking d'insu.
Ta 6angare gidansu Barrister A shirye-shirye suke ba kama hannun yaro tuni 'yan uwa da abokan arziki na nesa da na kusa sun fara cika gida, gani yadda gidan yafara haltsunewa yasa barrister A da k'awayenta komawa gidan Barrister Z a can suke nasu shirye-shirye.
***---****---****
_RANA BATA K'ARYA_
musu iya magana suka ce saidai uwar d'iya taji kunya, daren yau da misali k'arfe 9:00pm za'a yi Fulani night tun wayewar gari ake yi wa barrister A gyaran jiki daga ciki har da k'umshi na zane lalle baki da ja, abinka da farar fata lalle ya yi dass....a fatar hannunta da k'afafunta duk wannan shirye-shirye da suke hankalin barrister A atashe yake, sakamakon rashin jin d'uriyar ango tun daga ranar da ya zo ko a waya bai kirata ba.
Sai ma ita ce ta kirashi sakamakon alert na mak'udan kudad'e da ta gani daga gareshi, kiran nata ma k'in d'agawa ya yi sai d'an guntun text da ya turo mata I'm busy I'll call you later, bai kuma kirata ba hakan ba k'aramin kada mata anta jikinta ya yi ba, har yamma lis bata ji daga Aliyu ba zai zo ko ba zai zo ba, sosai tasha jinin jikinta.
Kasa hak'uri tayi taja Barrister Z agefen ta kora mata bayanin damuwarta, shiru Barrister Z tayi kafin ta ce ko za mu kirashi ne da sauri Barrister A ta girgiza kai, ba za mu kirashi ba saboda zai dauka kamar na damu da shi ne.
Ya zo ko kar zo duk uwarsu d'aya ubansu d'aya awurina duk irin zaman da ya tanada mana shi za muyi, koda sonshi zai yi ajalina ba zan ta6a zubarda ajina na bishi ba.
Karki ce haka Minal komai na duniya a hankali ake binshi sai ka ga ka ci ribar abin.
Cewar barrister Z.
"Ba za ki gane ba Zarah duk aure da aka gina shi ba soyyayya dama hakan zai faru.
murmushi barrister Z tayi ta kuma rik'o hannun barrister A, karki matsantawa kanki da yawa bebs Allah ya na tare da mu, insha Allah komai zai tafi yadda mu ka tsara.
Nodding head kawai barrister A ta yi.
Misali k'arfe 8:30pm amarya ta sha makeover cikin kayan Fulani na sak'i royal blue in colour, ba k'aramin kyau kayan suka yi mata ba musanmman yadda wuyanta ya sha sark'a tsakiya na duwatsu masu launi dabam-dabam sosai ta fito bafullatana.
Yayin da k'awayeta su ma sun had'e cikin kayan Fulani saidai nasu farare ne.
Tuni motoci suka fara daukar mutane zuwa hall d'in da za'a yi events d'in.
Har zuwa lokaci barrister A bata ji daga Aliyu ba, sai k'ok'arin danne abin take a ranta saboda bata so mutane su farga su gano halin da take ciki.
_Fans ba yawa Just to manage_
Jeeddah Aliyu
[7/26, 11:55 PM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619
DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA
*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```
*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```
*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``
*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN
*SLIMZY*:- IZZATA
*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO
*GIDAN RINA*
*16*
Daga ita sai fadila ne a cikin mota har suka iso hotel d'in zuciyarta a cakud'e, direba nayi parking k'awayeta suka lullu6e motar.
lokaci da take k'ok'arin fitowa daga mota barrister Z ta kutso ta matsa daf da ita ta rad'a mata, Aliyu yafi almost 10 minutes a mota yana jiran zuwanki.
"Ajiyar zuciya ta sauke wani irin dad'i ya ziyarceta, tana gama fitowa Aliyu ya fito daga nashi mota sanye cikin tsadaddiyar shadda fara tass....kanshi sanye da hula zanna bukar, lokaci da suka had'a idanu ba k'aramin kyau ya yi mata ba.
Yayin da shi ma yake yaba tsan-tsa kyau da ta yi.
"D'an siriri murmushi ya saki mata, ta mayar mishi da martani har da k'arin lumshe idanu.
Saboda murmushi nashi ba k'aramin awon gaba da ruhinta ya yi ba.
Ga mamakinta ya na k'arasowa kusa da ita ya rik'on palm d'inta cikin nashi, sai kuma ta kawarda mamakin nata sakamako tunawa da ta yi Aliyu wayayye ne ya kuma wadatu da ilmin zamani, don ya rik'o tafin hannunta baya nufi komai a wurinshi.
"Suna shiga hall Siblings sisters d'inshi suka mik'e suka nufo su, sosai Barrister A ta burge su musanmman Meena da ta k'asa 6oyewa saida ta furta ta hanyar cewa wow....tubarakallah masha Allah you're so beautiful sister in law.
Kalamanta ya sa barrister A ta gano sister din Aliyu ce ta yi mata murmushi had'e da furta thanks!
You're highly welcome.
Cewar Meena.
Wurin da aka tanada domin su suka zauna aka soma gabartada da programs d'in, anyi rawa an kuma zuba naira ba kad'an ba sai around 12:30am aka tashi kamar yadda suka shiga hall rik'e da hannu juna haka suka fito har mota ya rakata, duk wanda ya ga yadda yake bata kulawa zai dauka akwai soyayya mai k'arfin gaske atsakaninsu.
Da kanshi ya bud'e mata k'ofar mota tana murmushi ta zauna ta dube shi cike da kulawa ta ce "Good night!
Saida ya haskata da tsadadde murmushinsa sannan ya amsa da "Good night nd have a nice dream.
Yatsunta ta guda biyu ta d'aga mishi had'e da furta bye da haka direba ja mota suka tafi, ya kalli Jamal da ke tsaye a gefe yana kallonshi ya ce mu tafi ko?"
Suna tafiya Jamal ya ce gaskiya abokina ka yi dace da mata kyakyawar gaske ba ko shakka za ku haifa mana kyawawan yara.
Aliyu ya yi dariya marar sauti ya ce ni fa har yanzu ban ji son barrister a zuciyata ba, ga kuwa zai yi matuk'ar wahala ku sami yara.
"Jamal ya ja tsaki mtsss.....kafin ya ce wai kai wane irin tintirin d'an iska ne me zuciyar dutse?"
Ba zaka gane ba Jamal shi so ba mutum yake dasa shi a zuciya ba, Allah ne yake jarabta d'an Adam da shi.
Murmushi Jamal ya yi ya ce zancenka haka yake, amma akwai sakawa rai idan har ka sakawa ranka soyayyar barrister ba za'a dauki dogon lokaci za ka afka a sonta, ko don kyau halinta.
"Girgiza kai kawai Aliyu ya yi sakamakon yadda ya fahimci duk abin da zai fad'a ba lalle bane abokin nashi ya fahimce shi ba shiyasa ya ja bakinshi ya tsuke.
***---****---****
*WASHE GARI*
Akayi mother night wanda har iyayyensu sun je, sai lokaci momma ta ga barrister A duk da girls d'inta sun ba ta labarin kyawonta har da nuna mata pics d'inta, tsabar takaici ya hanata kallon pics d'in.
Sosai momma ta firgita lokaci da ta yi arba da barrister A cikin wedding gown golden in colour, kanta dauke da bridal turban Royal blue colour, yayin da Aliyu ke sanye da farar shadda as usual sai dai ta yau babbar riga ce kamar yadda ya rik'o hannunta a events d'in jiya haka ma yau suka shigo, ba k'aramin kad'awa hanta cikin momma ta yi ba.
Ba abin da take sai zufa K'awarta Dijama ce, tadawo da ita natsuwarta ta hanyar cewa lafiya Zaituna duk sanyi Ac da ke wurinan naga ke sai had'a gumi ki ke?"