Showing 63001 words to 66000 words out of 80263 words
"Don Allah Hajiya kiyi hak'uri wallahi na zata ita kike nufi, saboda ita kadai ce muke da a gidanan mai irin wannan lalura amma kiyi hak'uri ki gafarce ni tuntun6en harshe ne.
"Tuntun6en harshe uwarka ko na ubanka yau sai kabar gidanan, tunda bakada kunya har za ka iya duba tsabar idona duk kwarjini nan nawa ka kira 'yata mahaukaciya wallahi sai kabar gidanan bak'in munafuki.
"Afakace Sa'eed yake harararta yana yatsina a zuciyarshi kuma sai rama zaginshi yake ya ce ka ji ja'ira wai kwarjininta da wannan shegiyar fuska kaman dudduge kuturu, sai shegen fari fuuu...kaman jan kosai ga ki nan babbar munafuka da wasu shegun d'uwawu kaman na masu rawan makosa.
Kai...!
Don ubanka mikake fad'a ne?
Na ga sai musu-musu kake da baki, ko zagina kake yi?"
"Zagi kuma..?
ya maimaita yana wani zare idanuwa, tare da fad'in Allah dai ya kauda 6aci rana Hajiya.
Rashin sani ma'anar maganar ta sa yasa taja tsaki mtsss....tanufi bakin gate tana cigaba da zaginshi hade tak'ara jaddada masa sai yabar gidanan.
"Duk yawan masifar da ta dinga zazzagawa Daniel bai sa yafad'a mata ba sai cewa ya yi bai ganta ba.
Bayan ita da Aliyu ba wanda ya fita daga gidan.
A fusace tanufi flat d'inta yayin da Sa'eed ya bita da murmushin mugunta har da yi mata gwalo.
***----*****----****
Ta bangare barrister kuma ta kira barrister z ta bata labarin abinda ya faru, yayin da barrister z tak'ara tabbatar mata da cewa gobe zata zo da malam tana gama waya da ita Aliyu ya kirata video call, wani shegen dad'i mai kama da ice cream ya ziyarceta tana kallo har kiran ya tsinke bata yi receiving ba, wai ita adole aji take ja...lol.
"Wani kira na sake shigowa da ya yi kusan tsinkewa sannan tayi picking. kyakyawar fuskarshi ma'abociyar kwarjini ta bayana a screen d'in wayar yana zaune akan resting chair da ke gidan Daddy na lagos.
"Hey.....my lazy lawyer how you're feeling now?"
Sanyayye murmushi tayi tare da fad'in I'm feeling better Yalla6aina ya gajiya flight hope ka ci abinci ba ka zauna da yunwa ba?"
"Gajiya flight na wartsake ta a conference hall tun zuwana muke meeting ban wuce one hour da fitowa ba, shiyasa sai yanzu na samu damar kiranki.
"Allah sarki my hubby da ina kusa da kai da nayi maka massage.
Ta k'arashe magana tana masa dariya.
Murmushi ya yi tare da shafa sumar kanshi ya ce
Aminaa....!"
Na'am!
Ta amsa masa anatse
"I miss you so much yau kadai duk naji wani iri ji nake kamar na bud'e idanuwana naganni kusa da ke, I miss you & how close we used to be I miss how much you used to care about me, I miss the time we spend together bakina ba zai iya fad'ar yanda nayi kewarki ba saidai kawai ya misalta I miss you a lot I wish to open my eyes to see you standing beside me.
"Lumsashe idanuwanta tayi sosai kalamanshi suka ratsa jinin jikinta, ta fad'ad'a murmushin kan fuskarta tare da fad'in I miss you so badly Yalla6aina nima ji nake kamar nayi tsuntsuwa nagani kusa da kai ba abinda yake fad'ar min da gaba a duk lokaci da na tuna cewa ni kadai yau zan kwana a gidanan.
Ta karashe magana tana share hawayen shagwa6a mai cike da zallan kissa.
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce "I'm sorry wifey wallahi the trip is very important to me da nadawo gobe amma don't worry, it won't take long its just one week, I would be back so stop crying kin ji Babyna..?
Ta share 'yan budaren hawayenta tana dariya, knocking d'in da taji anayi da yasa ta ce hubby I have a visitors bara na bincika za mu yi waya anjima saboda bangaji da kallon wannan kyakyawar fuskar taka ba.
"Nima haka Babyna.
Yafad'a tare da katse kiran.
Tana bud'e k'ofa suka had'a idanu da uncle Suraj sai da taji mummunan fad'uwar gaba, ta k'irk'iro murmushin dole ta ce Barka da zuwa uncle Suraj!
"Yauwa the best lawyer in the world!
Cewar uncle Suraj yana mata wani shegen murmushi mai wuyar fassarawa.
Ita ma murmusawa tayi batare da ta tanka mishi ba.
"May I...?
Yafad'a yana nuna hanyar da tare da hannunshi.
Yes of course ta karashe magana tana mai juyawa cikin falo, ya biyota a baya.
ruwa da Juice mai sanyi ta kawo mishi ta nemi kujera da ke nesa da shi kad'an ta zauna.
"Ya gyara zamanshi kafin ya ce ya gida barrister ya akaji da bankad'o sirrinka Jama'a...?
Ai barrister kuna k'ok'ari ba kad'an ba, samun masu yi aikin Allah irinku sai an tona sannu da hidintawa Jama'a my beautiful daughter in law!
Dariya tayi sam bata kawo komai aranta ba saboda ya saba da yi mata irin wannan wasa, sai kawai ta ce uhm....uncle kadai baka rabuwa da abin dariya ni fushi ma nake yi da kai.
Ta karashe magana tana 'yar k'aramar dariya
"Shiru ya yi yana kallonta wanda sai mai hankali zai gano idan kallon nasa ya dosa, ya saki k'ayattace murmushi ina neman afuwa tun kafi nasan laifi da nayi amma fad'amin laifi da nayi my beautiful daughter in law na k'ara bada hak'uri?"
"Dariya barrister A tayi ta ce wato uncle shine ka turamin miji Lagos kai kuma ka dawo Abuja, wannan ai rashin adalci ne.
"Zaro idanuwa uncle ya yi tare da rufe bakinshi da tafin hannunshi yana dariya, ya ce kai my beautiful daughter in law na fahimce kina daff...da sussuta min yaro to karki damu bari na kira Yaya M Ardo na fad'a masa kince ya dawo miki da mijinki kina k'ewarsa.
"Sosai take dariya yayin da dariyarta ta tayi wufff.....da imani uncle ya shagala iya shagaltuwa da kallonta, tana maida ganinta akanshi ya yi sauri kauda fuska yana shafar munafuki gemunshi mai kama da na balagagge bunsuru had'e da wani ja'irin murmushi.
Ta ce rufamin asiri uncle da wasa nake.
"Ya mik'e tsaye tare da cewa ni zan tafi dama Zaituna ce ta kirani wai tanemi maryama sama da k'asa bata gannta ba shine nakeso nasamu bayanai daga gareta, ta yanda akayi har tayi sakaci maryama tafita daga gidanan saboda inaso nakai report wa 'yan sanda kinsan 6atan mutum ba k'aramin abu bane, musanmman ita maryama da ke dauke da lalura ta ta6in hankali.
"Shiru barrister A tayi gabanta na fad'uwa duk tayi wani iri fuskarta ya nuna rashin gaskiyarta a fili, har tayi niyyar ta fad'awa uncle ita ce ta dauke maryama sai kuma taga rashin dacewar hakan gara ta jira zuwa gobe idan malam ya zo, maybe adace maryama ta dawo cikin hankalinta sai tafad'a masa yayin da uncle Suraj ya kafeta da idanuwa yana karantar yana yinta anatse.
"Gani yadda yake kallonta yasa tattaro natsuwarta wurin d'aya ta ce wai Uncle wacece maryama nan?
Sunanta kawai nakeji ga bakunan jama'a har yau banta6a ganinta ba.
"Uncle ya yi bazawarin murmushi na gefen baki ya d'age girar ido ya ce ba kisanta ba ko?"
Ta gyad'a kanta tana mai cigaba da murmushi yak'e.
karki damu my beautiful daughter in law za ki santa very soon saboda ina ji a jikina bata yi nisa da mu ba kawai kiyi fatan aganta.
Bari na wuce akwai musu jirana a office gashi kuma inaso na biya police station.
Shikenan uncle Allah yasa aganta sai anjima a gaida gida.
Batare da ya amsa mata ba ya nufi k'ofar fita da sauri.
"Sa'eed yana fitowa daga band'aki Daniel na budewa uncle gate yafita.
"Ya bi gate d'in da kallo cike da takaicin rashin sanarda uncle abinda yafaru na nemansa da suka yi a d'azu.
Jeeddah Aliyu.
[7/27, 12:23 AM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619
DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA
*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```
*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```
*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``
*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN
*SLIMZY*:- IZZATA
*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO
_Assalamu Alaikum masoya masu bibiyar novel dina wasu daga cikinku sun kirani wasu kuma sun turomin message sun yi min nuna damuwarsu na rashin gani new update, wanda suka yi min texts ban yi reply ba su yi hak'uri abin ne da yawa nagode kwarai da gaske da KULAWARKU_
*37*
*AM ARDO CONTRACTUAL & BUILDING MATERIALS NIGERIA LIMITED*
_*LAGOS NIGERIA*_
*Time:-1:30pm*
Daddy da Aliyu suna gabatarda meeting da employers d'in kamfaninsu, a conference hall da ke cikin company. text ya shigo wayar Daddy bai duba wayar ba saida suka fito daga meeting.
Ya bud'e text d'in abinda ya gani ya yi matuk'ar girgiza hanta cikinshi, da sauri yafito daga office dinshi ya nufi na Aliyu agaugauce ya sanarda shi zai wuce Abuja Maryama ta6ata.
Yatsine fuska Aliyu ya yi tare da fad'in haba Daddy ya za'a yi ka tafi a yanzu bayan kasan irin mahimmanci da project d'inan yake da garemu, da irin mak'udan kud'i da zamu samu please Daddy ka bar zance tafiya nan koda zuwa jibi ne, uncle suraj yana Abuja na tabbata zai yi handling komai kamar kana nan.
A fusace Daddy ya ce rufemin baki Sultan tun kafin na kwashe ka da mari project d'in banza project d'in wofi, saboda neman duniya sai na kasa tafiya nasan halin da matata take ciki ka shiga taitayinka da ni banso ka k'ara kwatata yi min irin wannan zance idan har kai ba zaka iya handled komai sai tare da ni sai ka bari babu dole mtsss....ya k'arashe magana da jan dogon tsaki bai ko saurare abinda Aliyu zai ce ba ya bude k'ofa ya fita ko gida bai koma ba ya wuce kaitsaye airport.
***---****---*****---***
*Abuja*
*Time:-10:00am*
Barrister A tana tsaye a kitchen tana ba ma 'yan aikinta umarni abinda zasu girka mata a matsayin breakfast, suka jiyo wani shegen heavy knock ta Kalle Bintu ta ce "Bintu je ki gani wanene ke min knocking da sassafe nan.
Bintu tana bud'e k'ofa taga momma a tsaye jikinta sanye da sleeping dress, sai d'an wani siriri scarf da ta yane kanta da shi ta ce "ina kwana momma?"
Wulak'antattace kallo ta watsawa mata tare da sa hannayenta ta tureta gefe, ta shigo cikin falon ranta a 6ace ta shiga kwalawa barrister A kira "ke Amina!
Amina!"
Kina ina fito ki fad'amin ubanda ya baki izzini dauke maryama daga gidanan?"
Jikin barrister ya dauki rawa ta zazzaro idanuwa cabdijam....wane munafuki ne ya fad'a mata ni na dauke Maryama.
A fusace momma ta shigo kitchen d'in tashiga k'arewa Barrister A kallo mai cike da tsana, yayin da barrister A ta tsareta da nata idanuwa ba alamar tsoro babu yabo ba fallasa ta ce "ina kwana momma?"
"Ke saurara bak'ar munafuka alguguma har ni za ki nemi ki tonawa asiri, wallahi kiyi kad'an fad'amin menene hujjarki na dauke maryama daga gidanan?"
Rolling idanuwa Barrister tayi hankalinta kwance ta ce "wai saboda kawai ki sami hujja momma kika shigo min a hargitse.
ni wallahi na dauka ma gobara kika yi, Kalle kayan jikinki momma wannan sam bai dace tsohuwa kamanki tana yawo da sleeping dress a farfajiyar gida ga katti bila adadin kiyi ma kanki fad'a mana.
Ba ma wannan ba wane munafuki ne ya gayamiki ni ce na dauke maryama?"
Sororo da baki sake momma take kallon barrister A kafin tayi kwafa ta ce "kiyi katon kuskure Amina kuma tabbas sai kiyi nadama mafi muni a rayuwarki, ki rasa wanda za ki k'aluballanta sai ni tanuna k'irjinta da yatsa ta girgiza kai ba ki san wacece ni ba.
Shiyasa kika yi min kutse don tsabar iskanci kina tambayata wanda ya gayamin ke kika dauki maryama to a Cctv camera naga lokaci da kika fita da ita ke da Teema da bak'in munafuki nan Sa'eed.
"mtsss.....Barrister taja tsaki tare da fad'in wacece ke momma? Face bak'ar azzuluma muguwa, kina matsayi mace kuma uwa amma bakida imani balle tausayi ko kad'an a zuciyarki.
kuma Cctv ki ya gayamiki k'arya ni ban dauki maryama, saboda haka don Allah ki fita ki bani wuri banso haukar tsofa.
Nunata da yatsa momma tayi ta ce "Ni za ki gayawa maganar banza Amina?
"Ke uwata ce da ba zan gayamiki maganar banza ba, kisani momma Ubangiji yana ara mana lokaci mu yi amfani da shi mu nemi duniyarmu da lahirarmu, amma wasu dolaye masu 6attaciyar dabara irinki, sai su yi amfani da lokacinsu su ci karensu babu babbaka.
momma ki sani ubangiji ya ara miki lokaci har na tsawon shekaru 28 kina shagalinki batare da wani ko wata ya ce da ke uffan ba, a yanzu kuma lokacin naki ya k'are don haka bakida sauran dabara kiyi amfani da d'an gajere lokaci da ya rage miki, ki tubawa ubangiji ki rok'e gafararsa da wanda kika zalunta. Ki gyara abinda kika 6ata tun kafin lokaci ya k'ure miki.
Matsowa momma tayi daff...da ita tadafa kafad'arta ta ce "karki damu da ni ki damu da kanki domin komai zai iya faru da ke, na rantse da Allah idan har ba ki fad'amin inda kika 6oye maryama ba sai na salwantar da rayuwarki.
"Ture mata hannu Barrister tayi tare da kauda fuskarta tamkar abinda tafad'a bai firgitata ba, ta matsa jikin kitchen cabinet ta jingina jikinta had'e da rungume hannayenta a k'irji cike da natsuwa ta maida ganinta akan fuskar momma ta ce "Ikon Allah!
Wanda yafi gaban mamaki momma me na tare miki, da za ki zo min flat da sassafe ko breakfast ban yi ba kina min barazana da mutuwa?"
Ni abinda yake bani mamaki ke nan da kike ashe za ki iya kashe mutu, to.....fad'amin mutum nawa kika kashe sannan kuma mutum nawa kike da burin kashewa nan gaba?"
ta k'arasa magana had'e da takowa ta iso daff....da momma ta cigaba da cewa nasan ina d'aya daga cikin mutane da kike da burin kashewa saboda ko yanzu kin fad'a sai kuma maryama, to....amma ni abinda ban gane ba surukata shin har da mijinki m Ardo yana ciki jadawalin mutane da za ki kashe....!
Hannu momma ta d'aga da zumar ta wanka mata bahaggon mari, cikin zafin nama tayi karaf....ta rik'e mata hannu cikin fushi da tafarfasar zuciya ta zuba mata manyan idanuwanta da suka fara canza colour ta ce "Don't ever try to raise your dirty hand on me or else are will break your bones zan manta da cewa ke kika haifi Aliyu understood?"
Ta k'arasa magana had'e da wulgi da hannun momma.
Cikin tsananin 6aci rai irin wanda momma ta jima rabon da tayi irinsa, take kallon barrister A kafin ta ce "Don't you dare to talk to me like thats Amina.
Shegen murmushi barrister tayi tare da fad'in oh....haka ne surukata to ya kike so nayi miki magana?"
Baya nasan ke azzuluma ce, zaluncinki ba wai iya kan kishiyarki ya tsaya ba har da 'ya'ya da kika haifa da cikinki.
kaicho ki momma kin ji haushi kuma inaso ki sa aranki yanzu na fara bankad'o ma'adanai sirrikanki.
"Daga haka ta ra6a ta gefen momma ta wuce tana karkad'a mata mazauna ta haura upstairs tashige bedroom d'inta.
Wani irin zufa ne ya karyowa momma tun daga tsakiyar gadon bayanta har zuwa dudduge k'afarta, gashi night gown d'in jikinta silk ce nan take ta shar6e da zufa kaman an watsa mata ruwa cikin tashin hankali marar misaltuwa ta baro flat d'in tanufi nata, a falo ta tararda Teema zaune tana ganinta ta tintsire da dariya ta taso daga mazauninta ta nufo wajenta, ta shiga girgiza kanta gashin kanta na wargajewa cikin wata irin rikitattaciyar murya ta ce "ki daina wahalarda kanki momma na riga da na 6ata komai, bari na fad'a miki kad'an daga cikin abinda na aikata ni ce nan na lalata asiri da kika yi ma Ya sultan kada ya kusance matarsa.
Ba iya wannan kadai ba ni ce na nunawa matar yaya inda kika binne layoyin da kika yi ma Daddy asiri ya manta da maryama, ba iya wannan ba momma nice na fad'awa matar yaya za ki kashe maryama.
Amma duk wannan abu da nayi momma, bai rage min jin rad'ad'in abinda ke kika aikata min ba. momma kin 6ata min rayuwa kin cuceni me nayi miki da kika samarda ni ta k'azamar hanya me nayi miki momma?
Da aurenki momma kika aikata zina kuma don tsabar rashin jin tsoro Allah, kika kawoni cikin 'ya'yan halak momma me zai faru da rayuwata idan har Ya sultan yasan cewa ni da shi ba ubanmu d'aya ba, wane hali zee-zee da meena zasu shiga idan suka gano mahaifiyarsu ta aikata zina har tasamar musu da k'anwa 'yar zina shin da wane ido za ki kalle Daddy ki fad'a masa kin aikata zina da k'aninshi Suraj me kike tsanmani zai faru idan na sanarda wani ko wata a cikin iyalan abind......
Teeema......da mugun sauri momma ta rufe mata baki had'e da kiran sunanta, don girman Allah Teema ki rufamin asiri kada ki fad'i wannan magana nasan ban kyauta miki ba amma ya na iya da k'addara.
Teema wacce ke gunji kuka kamar ranta zai fita ta gantsarawa momma cizo ga hannu babu shiri momma tasaki mata baki.
Teema ta durk'ushe k'asa tasaki wani irin kuka mai ciwo cikin murya kuka ta ce Allah ya isa tsakanina da ke momma Allah sai yasaka min wallahi ba zan ta6a yafe miki ba.
Ta k'arasa magana had'e da mik'ewa tanufi wata flower vessel na glass ta jefata jikin plasma, ta