Showing 36001 words to 39000 words out of 80263 words
restuarent, plates da spoons had'e glass cup ta dauko ta wanke, ta juye abinci ta kuma doura kajin sama plate ta nufi falon ta tararda ya haura sama, tasan wanka zai yi ta koma kitchen ta dauko drinks da ruwa.
'Bata jima da zama ba ya fito sanye da wandon pajama as usual ba riga, ya zauna a tsakiyar rugs carpet, ya mik'e kafafuwanshi hannunshi ya kai ya dauke remote control ya canza channel.
"Ta kalleshi tana yaba fad'i da girman k'irjinshi a zuciyarta cikin wani shegen voice mai dad'i ta ce "Yalla6ai ga abinci yanzu za ka ci ko sai zuwa anjima?"
"Ya Kalleta atsanake ya mayarda ganinshi akan Tv ya ce "Tunda na fita banci komai ba sai coffee kawai, ko ke bakya ji yunwa ne?"
Murmushi tayi ta ce "inaji mana saidai ba sosai ba kaman kai.
Naso nayi girki kafin ka dawo koda na duba store ba foodstuffs"
Murmushi ya yi tare da girgiza kanshi yana cewa "barrister kenan ya za'ayi ki samu foodstuffs anan saidai a apartment d'in momma.
Idan nayi wanka na fita tun safe sai dare nake dawowa, kuma ba kowane lokaci nakeci abincin gidanan ba, saboda ina da k'yak'yami k'azantar chef Emma nake ji.
"Dariya tayi tana jinjina zance nashi tare da kallonshi ta ce "Gaskiya Yalla6ai kai hukuma ne.
uhmmm......koh?"
Girar idonta ta d'age alamar eh!
Ya yi murmushi kawai had'e da fara cin abincinshi, yana cikin ci ya d'ago ya dubeta ya ce yadai naga ke bakyaci abinci sai faman kallona ki ke yi, ko kallon fuskar tawa ya k'ossar da ke?"
Sai da tayi dariya mai ban sha'awa kafin ta ce Yalla6ai kenan ina abun kallo a fuskarka wanda har zai iya k'ossar da ni?"
Auu......kina nufi ba abun kallo afuskana?"
"Uhm.....ni dai ban ganshi ba.
Ashe ba iya snoring da kicking d'in d'uwawun mutane ba har da ciwo makata yana damunki.
Yak'arasa magana yana kallon cikin idanunta yana murmushi.
"Ta kauda fuskarta da sauri da barin kallonshi, tana ya motsa fuska had'e da turo baki.
Gaskiya Yalla6ai you kill me at all.....ni ce nake snoring?"
Ai ni ki ka kashe barrister can you imagine in my own room you kick me in the middle of the night.
"Yadda ya k'arasa magana yana wani gesture ya yi masifar bata dariya, sosai da ke dariya har tana dafe cikinta.
Ya k'ura mata idanuwanshi yana kallon yadda take dariya ba k'aramin burgeshi tayi ba, musanmman yadda pink lips d'inta suke motsawa tsintar kanshi ya yi da kai hannunshi akan upper lips d'inta ya rik'e shi yadda ba za ta ji zafi sosai ba, ya ce lalle.....yarinya nan kin reni wato ma dariya ki ke mun?"
Ai kuwa sai na cire miki lips in yaso naga da wanda za ki sake yi min dariya.
Soft hands d'inta ta doura akan nashi ta shiga kici-kici ture hannun nashi cikin sigar shagwa6a ta ce auuch....Yalla6ai da zafi fa.
Da zafi ko?"
Yafad'a yana kallon tsakiyar idanunta.
Turo baki tayi had'e da furta ni ka sakeni ko na cije maka hannu.
"Dungure mata kai ya yi yana fad'ar kura kawai.
Ita ma tayi dariya tana cewa na dai ji.
Ta mik'e tsaye ta koma gefe ta zauna yaja plate d'in nama gabanshi, ya ci sosai ya kora da ruwan juice yana gamawa ya tura plate yana cewa gashinan ki ci raguwana ko za ki sami tabarakina kidaina snoring, yana gama magana ya mik'e ya haura upstairs.
Ta bishi da kallo cike da nishad'i ashe Aliyu yana da sauki kai sai in ka zauna da shi za ka fahimci haka.
"Ita dai komai nashi burgeta yake yi ta tabbatarwa da kanta shi d'in cikkake namiji ne mai kwarjini.
Tsarin zubinshi yayi mata kullum kwanan duniya soyayyarshi na dad'a shiga zuciyarta, alhali shi kuma ba burbushin sonta a tashi zuciyar, ta d'an girgiza kanta cikin rashin jin dad'i sannan taja naman gabanta taci har ta k'oshi ta sanya ragowa cikin fridge, ta dawo taci gaba da kallon channel d'in girke-girke.
Ta dauki dogon lokaci sosai ganin dare yayi sai ta mik'e ta had'a mashi coffee ta hau sama ta tura k'ofar ahankali tunaninta yana cikin falon, sai taga ba kowa.
"Kaitsaye ta shiga master room d'inshi ta hango shi kwance akan tangameme gadonshi, yana bacci sam bata yi mamaki ba tasan yana cikin gajiya.
Ta doura coffee akan d'an k'aramin center table, idanunta suka hango wasu documents zube a k'asa ta shiga tattara mishi, tana waigowa ta ganshi zaune ta kalleshi tana fad'in "Allah yasa ba motsi na bane ya tasheka ba?"
"Ya girgiza kanshi ya ce "Ah'ah dama baccin nawa bai yi nisa sosai ba.
Ta yi murmushi kafin ta ce akwai abinda ka ke buk'ata bayan coffee nima nafara jin bacci.
"Ki je ki kwanta sai da safe.
Allah ya tashe mu lafiya.
Amin yafad'a can k'asan mak'oshi.
***"""****"""****
Washe gari da wuri ta tashi duk tasan basuda foodstuffs ta shiga gyaran gida, tana cikin mopping d'in downstairs falo Aliyu ya shigo ta runsuna har k'asa ta gaidashi ya amsa da murmushi akan fuskarshi.
"Ki shiga daga ciki tare da nake da maza zasu shigo da kayan abinci store.
Toh.....
Tafada had'e da daukar mopping bucket ta fice daga falo, dama already tagama mopping d'in tana dai d'an k'ara goge wuri ne.
"Tana zaune a falonta ya tura k'ofa ya shigo, batare da ya bari sun had'a ido ba ya ce ki tashi ga foodstuffs an shigo da su ki had'a mana breakfast.
Saidai karki yi amfani da gas yanzu nan aka jona cylinder d'in, ki yi amfani da stove akwai kerosene aciki.
"Bai jira jin ta bakinta ba ya yi tafiyarshi, ta bishi da kallo cike da sonshi.
Murmushi tayi a k'asan zuciyarta ta ce Aliyu hukuma zama da kai sai mai dogon hak'uri, dubeshi don Allah kamar ba shi bane daren jiya muke nishad'i tare ba.
Koda misalin k'arfe 10:00am tayi har ta kammala girki ta yi arranging table, agurguje tashiga wanka tafito bataso ya yi latti saboda lokaci da tana kitchen yana downstairs falo taji yana waya yana da meeting around 11 o'clock.
"Simple makeup tayi tasaka material d'inki doguwar riga, ta yane kanta da veil ta bi lungu da sak'o na jikinta da perfumes jikinta da d'akin suka dauki k'amshi ta kalli mirror ta d'an saki murmushi, ita dai atsarinta tana masifar son turare shiyasa bata rabuwa da shi hakan yasa take cikin dadd'add'e k'amshi mai tsawa a rai.
Flip flops slippers tasaka a k'afafunta ta sauko k'asa, tana tsaye a dining area taji footsteps d'inshi ta maida ganinta akanshi yasha farare suit hannunshi rik'e da briefcase, tana kallonshi har ya k'araso cikin falon ya ajiye briefcase d'in akan center table sannan ya nufo wurinta taja mishi kujera ya zauna tayi serving dinshi.
Suna kammala breakfast ya dubeta ya ce mu je ki gaida Daddy jiya da dare ya dawo daga Lagos.
"Yana gaba tana binshi a baya suna zuwa compound idanuwanta suka sauka a apartment d'in Maryam, kamar yadda tayi jiya hakan ne yafaru tayi tsaye tana kallon wurin.
Sosai taji tsigar jikinta ya tashi, ta tsince kanta da son sani miyasa duk cika da girman gidan iya apartment d'in ne kawai keda k'ura da k'azanta.
"Mu je mana!
Sautin muryarshi ya dawo da ita duniyar tunani.
Jeeddah Aliyu
[7/27, 12:02 AM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619
DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA
*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```
*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```
*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``
*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN
*SLIMZY*:- IZZATA
*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO
*GIDAN RINA*
*24*
A dining area suka iske ahalin gidan suna breakfast.
Daddy yana ganinsu fuskarshi ta cika da farin ciki, wanda ya kasa 6oyewa sai zabga murmushi yake yana fad'i barka ku da zuwa yaran albarka.
"Barrister A ta durk'usa har k'asa ta gaida daddy da momma yayin da su Zee-zee suka gaidata ita da Aliyu.
Ku zauna ku yi breakfast tashi Zaituna ki yi musu serving.
Cewar Daddy yana washe baki yana kallon momma.
Sosai ran momma ya 6aci da jin furuncinshi duk da haka sai tashiga murmushi yak'e wanda yafi kuka ciwo.
Kafin tayi magana Aliyu ya rigata ta hanyar cewa Daddy a k'oshi muke.
Daddy ya ce shikenan mu je sitting room dina zan yi magana da ku.
Har momma ta mik'e tsaye ya ce A'ha'h!.....Zaituna koma ki zauna da yarana kadi nakeso magana mu je sultan.
momma tana kallo suka haura steps suka barta tsaye da baki galala, me Daddy yake nufi da yaranshi kawai yake so magana?"
Tabbas.....akwai abinda yake nufi tasanshi farin sani bai cika fad'ar magana marar manufa ba.
Jikinta ya yi sanyi tashiga wasi-wasi shin ko yafara hal6o 6oyayye sirrita ne?"
Idan haka ta kasance kashinta ya boshe awurin Jarumi ba ko shakka sai ya yi gunduwa-gunduwa da naman jikinta.
Wani shegen fitsari taji yana k'ok'arin kuce mata, da sauri-sauri gudu-gudu take haura steps.
"Duk magana da girls d'inta suke babu wacce taji, tana shiga bedroom kaitsaye ta zarce bathroom, tsabar rud'ewa ko bathroom slippers bata saka ba.
"Ta ware k'afafunta a tsakiyar tiles ta tattare doguwar rigar leshi da ke jikinta, tasaki fitsari daga tsaye ji ka ke sharrrrrr.......saida ta gama fitsarin ta ankara da inda tasake shi, ruwa ta debo ta tsaftace jikinta da wuri sannan tafito ta zauna gefen gado ta rafka tagumi, sai kuma ta mik'e zubur....ta dauki wayarta tayi dialling contacts d'in Jarumi, rufi asirinta ta kira shi tun kafin zarginta ya tabbata.
Yana dauka ko gaisawa bata bari suka yi ba muryarta na rawa ta shiga fad'ar Ja.....ru.....mi.....akwai matsaloli domin ba guda d'aya bace suna da yawa ta farko dai sultan ya sadu da matarshi, na biyu kuma kaman Alhaji yafara gano plans d'inmu don Allah duk abinda ka ke yi ka ajiye ka zo Abuja mu had'u.
"Kittt.....taji an datse layin duk da haka ta cigaba da fad'ar hello....hello...Jarumi kana ji na?"
Sororo tayi rik'e da waya a hannu tasake afkawa sabon tunani me kuma wannan d'an iskan Jarumi yake nufi da ita....?"
"Ta zube akan gado kamar kayan wanki yayin da wani mashahuri tsoro ya k'ara shigarta.
****"""****""""****
A sitting room d'in Daddy kuma suna zama daddy ya kallesu ya ce dama dangane da aikin matarka ne, akwai wani team na independence lawyers shugabansu childhood friend dina ne na yi magana da shi next coming Monday za ta fara aiki da su sai ki zama ready.
"Nagode Daddy Allah yak'ara girma da nisan kwana.
Amin!
Daddy Yafad'a yana k'ara fad'add'a murmushinshi.
"Shima Aliyu godiya ya yi mishi had'e da sallama tare suka dawo apartment d'insu, ya dauki briefcase da sauri ta kar6a tayi mishi rakiya har zuwa parking lot.
"Tana dawowa ta shiga tattara plates d'in da suka yi amfani da shi ta wanke.
Bata jima da zama a falo ba, su Zee-zee suka shigo cikin shirin tafiya school da yake kowacce su lectures d'in safe take da, Teema ce kawai bata zuwa makaranta saboda lalurarta.
"Fira suka ta6a sama-sama barrister A ta dubensu ta ce har kun fito?"?
Meena ce ta bata amsa eh....matar yaya yau lectures d'in safe mu ke da, Teema muka rako ta tayaki fira.
"Ita bata da lectures d'in ne?"
Murmushi Meena tayi kafin ta ce, bata zuwa school saboda yanayi na rashin lafiyarta, secondary school d'in adaddafe aka samu tagama.
"Shiru barrister A tayi tana kallon fuskar Teema wacce bata ma san me suke yi ba, saboda ta shagaltu da wasa da yatsun hannunta.
"Ajiyar zuciya barrister A tayi kafin ta ce Ayya......Allah ya bata lafiya.
Amin!
Suka had'a baki sai mun dawo matar yaya.
Allah yatsare sai kun dawo.
kayan kallo ta kunna suka fara kallo ita da Teema, suna cikin kallo bacci ya dauke Teema akan kujerar da take kwance.
Innocent face d'inta barrister A take kallo, can ita ma tafara hamma pillow kujera ta dauko ta kwanta akan rugs carpet a haka bacci ya dauketa.
"Can cikin bacci taji kamar inuwar mutum tsaye akanta, kasancewar baccin nata bai yi nisa ba.
Ta falka atsorace tana mik'ewa zaune taga Teema, tsaye gashin kanta ya wargaje ya rufe mata fuska wanda koda tayi bacci yana gyare tsaf.......sa6ani yanzu da ya yi wani cirko-cirko.
"Inna lillahi wa'inna illahim raji'um!
Barrister A tafad'a cikin sark'ewar lafazi.
"Sosai ta tsorata da ganin Teema a cikin wannan yana yi, ta had'iye yawun tsoro ta ce Tee...ma...menene haka?"
"Ba Teema bace ki tashi ki je ki ceto rayuka mutane guda uku daga ciki har da mijinki, kada ki bari su cutar da shi kamar yadda suka cutarda mutane guda biyu.
Ba mu da k'arfi taimakonsu saboda su fi mu k'arfi amma ke kina da k'arfi ceto rayuwarsu tsawon shekaru 28 muna jiran zuwanki.....domin ki bankad'o ma'adanan sirrika da ke 6oye Amina......kada ki kyalle su ki daukar mana fansar abinda suka yi ma godiyarmu.
"Teema na gama magana ta koma kan kujerar da tashi ta kwanta, ta cigaba da bacci abinta.
Cabdijam!
Barrister A tafad'a tana squeezing fuskarta, tabbas tashiga sark'akk'iya.
Shin meke faruwa da Aliyu, shin wani irin sirri ne da zata bankad'o wanda a tsawon shekaru 28 aka rasa wanda zai bankad'o shi sai ita?"
"Rashin sani wanda zai bata amsoshi tambayoyinta masu matuk'ar rud'a d'an Adam su hartsuna masa tunani.
"Yasa tayi K'ok'ari yakice tsoro da ya lullu6eta ta waiga ta kalli Teema wacce har yanzu take sharar bacci.
Kujera ta nema ta zauna, tsawon 20 minutes Teema ta dauka tana bacci kafin ta falka, sosai hanta cikin barrister A ta motsa sakamakon falkawarta daga bacci.
"Abin mamaki Teema ta mik'e ta nufo ta, zubur.....barrister A ta mik'e ta shiga ja da baya anufinta da tayi tazara kad'an da ita, ta 6alla da gudu ta haura upstairs tayi locking k'ofa.
"Karaf......Teema ta rik'o hannunta batare da tace ita komai ba tashiga jan ta duk da barrister A ta tsorata matuk'a haka ta cigaba da bin ta.
Ta backyard suka bi har izuwa garden sannan tasake mata hannu tayi mata ishara da hannunta cike da wani sabon tsoro barrister A tabi hannunta da kallo, a jikin bishiyar mangwaro taga wani tulin k'asa kamar gidan tururuwa.
"Dawo da ganinta akan Teema tayi cikin wani irin tsoro mai barazanar tafiya da numfashinta, ta ce k'asa ce Teema mai zan yi da ita?"
"Teema wacce ke wasa da yatsunta kamar yadda take yi a koda yaushe, bata ce komai ba sai cigaba da wasanta take yi.
"D'an gajere tunani tayi cikin sauri ta nufi wurin ta zube gwiwayoyinta duka biyu a k'asa tasaka hannayeta tashiga tonu wuri, gani zata wahala abanza hannayenta ba za su iya hak'o wurin ba.
"Ta mik'e da sauri tashiga dube-dube can idanunta ya kyallo mata k'arfen rodi, da gudu ta dauko ta shiga hak'o wurin sai da tayi gina mai zurfi gaske kafin ta ciro wasu 'yan uban layoyi birjik....masu ban tsoro da firgici.
Babu shiri tayi cilli da su ta mik'e tsaye jikinta yana rawa kamar mazari, ta zaro manyan idanunta tana kallo layoyin kafin tadawo da ganinta akan Teema wacce har yanzu tana cigaba da wasa da yatsunta.
"Na shiga uku!
wad'annan layoyi na menene Teema ki ka sani na hakk'o?"
Batare da Teema ta bata amsa ba ta kwashe layoyi, sannan ta dubeta sai lokaci tayi magana yi hak'uri matar yaya yanzu ba lokaci tambaya da amsa bane, mu hanzarta bari wurinan tun kafin wani ido ya ganmu.
Ta ko ina jikin barrister Amina rawa ya keyi, tsawon rayuwarta bata6a gani irin wannan al'amarin ba.
"Suna shigowa main parlour ta ruga kitchen ta dauko ruwan masu sanyi gaske tasha, sai lokaci tasami 'yar natsuwa.
Koda ta dawo falo Teema bata nan sai 'yan uban layoyi da ta zube mata akan center table, cikin kad'uwa ta d'ebesu ta nufi upstairs bedroom.
"Ta kasa zama ta kasa tsaye takai gwaro takai mari, shin ya za ta yi wad'annan kayan tsinbace-tsinbace?"
Oh!......ya rabbi ka kawo min mafita.
Cikin sauri ta ciro wayarta daga charging mutum na farko da ya fara zuwa mata arai ta kira ko za ta samu mafita.
Agaugauce take dialling digit d'in Barrister Zarah, wayar har tayi ringing ta tsinke Zarah bata yi picking ba.
"Ta yada ganinta akan wall o'clock ta tabbata a irin wannan lokaci barrister Z tana cikin courtroom, dole wayarta zai kasance a silent.
"Zarah ce kadai take iya tunkara da wannan murd'add'en labari, rashin samunta a waya ba k'aramin cikasss......ya kawo mata ba.
"Ta koma gefen gado ta zauna talla6e da kumatu, sai sak'a da warwara take yi.
Gani lokaci na ta tafiya bata tsinana komai ba, sai d'an banzan tunani da fargaba da suka taru suka hanata shakattt.
"Cikin wani yana yi mai wuyar fassarawa ta tashi saida tafara adana layoyi, kafin ta sauko k'asa ta nufi kitchen domin daura launch.
****"""****""""*****
Tana kammala girki ta juye a warmers ta shirya table, sannan ta nufi bedroom da nufi yin wanka tana shigowa wayarta na ringing da azama tayi picking.
Hannunta har rawa yake yi musanmman da taga Barrister Z ce, batare da ta bari suka yi doguwar gaisuwa ba ta shiga bata labarin abinda yafaru da kuma neman mafita.
"Ita kanta Barrister Z ta kad'u da jin wannan labari.
Amma don ta k'arfafawa k'awarta k'arfin gwiwa duk tasan cewa tashiga *GIDAN RINA* mai cetonta sai Allah.
"Da farko shawarar da zan ba ki, ki fara bincike akan Teema shin da gaske ne tana da lalura ta shafar aljanu?"
Sai abu na gaba dole sai kin cire tsoro kiyi fitsari ki zubawa layoyin kowane irin sihiri ne zai karye, ki kuma tsananta bincike ki gano waye ya yi wannan asiri,