Showing 66001 words to 69000 words out of 80263 words
tararatse ta bi duk abinda ya kai hannunta tana kuka tana farfasawa, da gudu bala'i Zee-zee da Meena suka fito daga bedroom dinsu cikin tashin hankali suka yi kan Teema had'e da rirrik'eta.
Sai cewa take ku barni na lahanta kaina ko zai rage min ciwo da nake ji a zuciyata.
"Haba Teema.....haba wannan wane irin tashin hankali ne, har sai yaushe za ki daina d'aga mana hankali a gidanan...?
Cewar Zee-zee tana girgiza kafand'u Teema.
Cikin muryar kuka Teema ta ce har sai lokaci da momma ta bud'e bakinta tafad'awa duniya wacece ni, da kuma irin rayuwar da ta za6a min anan gaba.
Ta k'arashe magana had'e da ture su ta 6alla da gudu ta shige d'aki ta rufo k'ofa har da su murza key.
"Cirko-cirko suka yi tare da kallon-kallon atsakaninsu, su Kalle momma ta Kallesu Meena ce ta kawo k'arshen shiru nasu ta hanyar cewa momma me kuma kika sake yi ma Teema?"
"Saida momma tayi ajiyar zuciya kafin ta ce "Ba abinda nayi mata matsiyata iskokanta ne suka motsa, amma ni me zan mata.
"Wannan karo Zee-zee ce tayi magana kwata-kwata ban yarda da wannan al'amarin naki ba momma, a koda yaushe iskokan Teema suka tashi duk yawan mutane gidanan ba su tsinewa kowa sai ke, yau kuma da kunnena naji Teema tana miki Allah ya isa kai.....ina momma wannan lamarin naki akwai lauje cikin nad'i Zee-zee ta k'arashe magana tana girgiza kanta.
"Momma batasan abinda zata ce da su ba, gaba d'aya noti kanta ya kwance shiyasa ta bi ta gefensu ta shige bedroom d'inta
***---***---****----**
Jirgin da Daddy ya biyo daga Lagos zuwa Abuja ya yi landing a Nnamdi Azikiwe international airport Abuja, Daddy yana fitowa daga jirgi ya kira direbanshi ya zo ya yi picking d'inshi suna cikin tafiya bisa hanyar zuwa gida message ya shigo wayarshi sai kawai ya tsince kanshi da fad'uwar gaba, ya bud'e sak'on yayin da gabanshi ke cigaba da fad'uwa *_idan har kanaso kasan wacece matarka Zaituna Ka yi gaggawa ka zo western dreams hotel room 126_*
Rass....rasss....! Sautin da ke fita daga k'irjin Daddy zuciyarshi sai halbawa take da k'arfin gaske, ya bud'e baki da kyar ya ce da direbanshi ya wuce da shi western dreams hotel.
Jeeddah Aliyu.
[7/27, 12:25 AM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619
DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA
*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```
*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```
*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``
*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN
*SLIMZY*:- IZZATA
*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO
*38*
Barrister A tayi wanka ta shirya ta nemi wuri ta zauna tana jiran barrister z ta kirata, ta ce sun iso tazo tayi picking d'insu har k'arfe 12 noon ya yi bata ji daga gareta ba.
Ta kira wayarta yafi a kirga sai kawai taji matar nan mai zazzak'ar murya tana fad'in wayar a kashe take.
"Da sauri ta mik'e tsaye tafito compound ta yafito Daniel da hannu ta tambayeshi ina Sa'eed ya ce mata tun jiya yalla6ai Aliyu ya aike shi poultry house d'inshi da ke suleja ya kai ma manager sak'o, jiya bai samu zuwa ba shiyasa yau ya tafi tun da sassafe amma shima ya yi mamaki abinda ya hanashi dawowa har yanzu.
Sai kawai ta tsince kanta da fad'uwar gaba mai tsanani, da sauri ta juya flat d'inta babban takaicinta bai wuce contact d'in Jamal da bata da shi ba.
Gani zata 6atawa kanta lokaci da fargaba yasa ta haura sama ta dauko handbag da makullin mota, har tayi reverse ta fita daga gidan tana jin fad'uwar gaba kaitsaye gidan Jamal ta nufa.
***---****----****--***
Direban Daddy yana danno mota a western dreams hotel.
Daddy ya jin fad'uwar gabanshi ya k'aru fiyye da farko, direban ya yi parking ya fito ya bud'ewa Daddy k'ofa yayin da Daddy bai ma san sun iso hotel d'in balle yasan direban nashi yana bude masa k'ofa.
Gani shiru nashi ya yi yawa yasa direban ya d'an sunkuya had'e da tura kanshi cikin motar kana ya ce "Alhaji mun iso!
Firgigit......! Daddy ya yi kaman wanda aka tadda daga bacci ta hanyar watsa masa ruwa musu masifar sanyi.
Cikin mutuwar jiki Daddy ya zuro k'afafunshi k'asa kafin ya yunk'ura ya fito da gangar jikinshi waje.
"Batare da Daddy ya kalle direbanshi ba ya ce "Ka zauna a mota ka jirani ina zuwa.
Yanda yake tafiya kawai zai tabbatar maka da baya cikin natsuwarsa, yana zuwa bak'in k'ofar d'akin ya taka birki almost 3 minutes yana tsaye shi bai yi knocking bai kuma juya inda yafito ba.
Can ya ga wankin hula zai kaishi dare ya yi kasada ya daura hannunshi, a jikin k'ofar ya shiga knocking ahankali.
Jarumi da ke haye da ruwan cikin momma ya dakata da abinda yake yi, ya tsurawa k'ofar idanu, yayin da Daddy bai fasa knocking d'in ba.
"Cikin tsanani gajiya Jarumi ya mirgina gefe ya kwanta yana sauke numfashi, batare da ya kalle gefen da momma take ba ya ce "Zaituna ina gani room service ne ya kawo abincin ki tashi ki kar6o.
Batare da ta furta uffan ba ta mik'e da kyar saboda ta gurzu a wurinsa ba k'adan tsirara haihuwar uwarta ta mik'e, ta dauki bathrobe tasaka ta nufi k'ofa wacce har zuwa lokaci Daddy yana cigaba da knocking d'in hankalinta a kwance tayi unlock d'in k'ofar saboda sam bata kawo tunani yau ce ranar da zata kasance ranar tonuwar asirinta ba, tana bud'e k'ofa idanuwanta suka sark'e da na Daddy wanda ke tsaye sai faman tattara babbar rigarsa yake, ga kuma matsananci fad'uwa gaba da yasaka shi agaba, saura kirisss.....numfashin Momma ya fita daga gangar jikinta yayin da duhu ya mamaye gani Daddy kwakwalwarsa ta daina aiki ta tsaya cak.....tsananin rud'ewa da tashin hankali marar misaltuwa ya sanya momma ja da baya, muryarta na rawa da kyar ta had'a ruguwar jarumta da ya rage mata ta shiga had'a kalma da kalma tasha bak'ar wahala kafin tasamu ta had'a. kalmar Al....ha..ji...!
Jarumi da ke kwance daga shi sai boxer saboda bayan tanufi k'ofa yasaka boxer d'in, dalili kuwa yasan dole room service d'in ya shigo don haka bai kamata ya ganshi naked ba.
"Cikin wani irin yana yi Daddy ya bi bayanta yayin da idanuwanshi suka sauka akan Jarumi, cikin tashin hankali yake kallonshi gani haka yasa Jarumi ya mik'e zubur.....da zumar ya ture Daddy ya gudu, cikin zafin nama Daddy ya cafke dantse hannunshi ya kuma fizgo shi da k'arfi har ya yi nasarar tureshi bisa gado, Momma wacce ke gefe tsaye ta kurma mashahuri ihu sakamako yanda taga Daddy yana dambe cirewa Jarumi masks, kururuwa take yi da dukan k'arfinta shiru nata ya tsaya ne cak....adai-dai lokaci da Daddy ya yi nasarar yaye face masks d'in, fad'uwar gabanta ya k'aru a dalilin fuskar da take kallo wacce tsawon rayuwarta bata ta6a koda mafalkinta ba, kafin tayi yunk'uri tambayarshi waye shi ya akayi ya rikid'e ya zama Jarumi?"
Shin ko Jarumi yana canza launi ne ko kuma yana da sihiri da yake canza kamanu, idan kuwa haka ne tabbas ya cuceta me zata cewa Daddy ta tabbata koda zata mutu tasake dawowa duniya ta cewa Daddy abokin fasik'ancinta d'an uwanshi ne Suraj Ardo ba zai ta6a yarda ba.
Daddy yana cire masa face masks ya koma gefe yana kallonsa da idanuwanshi da sukai jajir, yayin da numfashinsa ya shiga daukewa yana dawowa ya misalta shekarun abokin fasik'ancin momma wanda ko d'anta Aliyu ya girmeshi nesa ba kusa ba, saidai ya zo tsaran Meena ba ma Zee-zee ba.
"Cikin mugun tashin hankali momma ta nufi wajen duplicate d'in Jarumi, kafin ta aika masa tambayar da ke nuk'urk'usar zuciya da kwakwalwarta kafin tayi wani yunk'uri 'yan Median suka bankad'o k'ofa suka cika d'akin kowane su yana k'ok'arin daukar abinda zai watsawa duniya.
"Gani haka yasa Daddy ya k'ara firgita, numfashinsa ya tsaya cak....ya sulele k'asa ya some.
Momma tafasa ihu tayi kanshi tana jijjiga shi yayin da press sai ya k'ara cika d'akin suke, kamar turo su ake yi yayin da wasu nan take suka watsa akan social Median, asirin uwargida M Ardo ya tonu an kamata tana fasik'anci da d'an cikinta, wasu maganganu ba dad'i ji.
Yanda momma taga flash d'in camera yana shawagi ta ko ina akanta, yasa tayi suman k'arya.
Ma'aikatan hotel d'in ne suka kira ambulance aka turo Daddy da momma akan gadon daukar marar lafiya, sai lokaci direban Daddy yaga abinda ke faruwa.
Alokaci da ake k'ok'arin fitowa da Daddy da momma duplicate d'in Jarumi ya sami hanyar guduwa.
Kaitsaye national hospital akai nufa da su har a can....basu tsira daga Median ba saboda biye suke da su har lokaci da aka shigarda su d'akin taimakon gaggawa.
"Bayan kowa ya kama gabansa manager hotel d'in ya tsinto kayan momma ya rufe d'akin.
Jin kad'an da fitarshi Jarumi uncle suraj ya fito daga ma6oyarsa bathroom, ya dinga kwasa dariya kaman wani motsatsi.
Saida ya yi mai isarsa ya nufi k'ofar fita ya ciro key daga aljihunshi ya bud'e y k'ofa, ya lek'a ya ga babu kowa a corridor ya fito abinsa zuciyarshi fara tass....yau burinsa na daukar fansa akan d'an uwansa M Ardo ya cika dama burinsa ya 6ata masa reputation shi da iyalinsa.
"Lokaci da barrister A ta iso k'ofar gidan Jamal tayi horn batare da mai gadi ya bud'e gate ba, ya fito gefen goshinsa sanye da plaster ya gaidata tare da sanar da ita mutane gidan duka suna asibiti.
"Sosai tasake shiga firgici cikin tsoro da fargaba ta ce "waye ba lafiya a gidan?"
Mai gidan da iyalinsa jiya daddare armed robbers suka shigo mana gida kalli goshina, dukan bindiga ne suka yi wa maigida dukan tsiya suka yi awon gaba da bak'in da suka zo jiya gidanan.
Barrister A ta dafe saitin zuciyarta da ke hal6awa da k'arfi kana ta shiga furta
"Innalillahi wa'inna illaihim raji'um.....!
Da kyar ta iya tambayarsa wane asibiti Jamal yake, sannan an sanar da Jami'an tsaro.
Ehh.....an sanar da su ko d'azu sun zo sun sake bincike da yi min tambayoyi shi kuma maigidan yana Nimzamia hospital.
"Cikin mugun tashin hankali ta tashi motarta, da zumar zuwa asibitin da Jamal yake kiran Abbata ya shigo wayarta kaman ba zata dauka ba, sai kuma tayi tunani tana buk'atar wanda zata yi magana da shi.
Tana picking ko gaisuwarta Abba bai tsaya amsawa ba ya ce "Minal wai meke faruwa ne a family mijinki?"
saura kad'an tasaki steering mota, muryarta tana rawa ta ce "Abba wani ya sanar da kai wani abu ya faru ne?"
Ba wanda ya sanarda ni gashinan yana yawo a kafaffen yad'a labarai da kafaffen sada zumunta, abin ba kyau gani.
"Abba ni bansan komai ba wallahi.
Cike da takaici Abba ya ce "mother in law d'inki mijinta M Ardo ya kamata a waster dream hotel she's having an affair abin takaici da k'aramin yaro, kuma wani kayan haushi Median ta shigo cikin al'amari
sai yad'awa suke yi.
Kiyi gaggawa ki had'a kayanki ki zo Yola banaso press su yi wani rubutu akanki matsayinki na daughter in law a gidan zai iya shafar career ki.
Idan babu flight ki nisanta daga gidan ki 6oye kanki zuwa gobe ki biyo jirgin safe.
Girgiza kai tayi har ta bud'e baki za tayi magana sai ta laura ga mirror mota da wani black van tun daga fitowarta gidan Jamal yake biye da ita, tunaninta ya bata watakila hanya d'aya zasu bi kuma gashi ta tare musu hanya saboda sannu-sannu take driving, gani haka sai ta d'an k'ara gudu sai kawai mai motar ya dinga yi mata wani mahukacin horn.
Kawai tayi decided ta gangara gefen hanya tayi parking saboda zata fi samun natsuwa ta fahimtarda Abba ya fahimci ita ma a yanzu tana d'aya daga cikin alhalin duk abinda ya shafe su, ya shafata ko ta gudu ko ta tsaya ba abinda zai canza hakan.
Tana gama parking sai kawai van d'in ta zo da matsiyacin gudu, tasha gaban motarta cikin tsananin tsoro ta ce "Abba ga wata black van tasha gaban mo.....
Kafin tak'arasa wasu mutane guda biyu suka fito daga van d'in d'aya daga cikinsu ya d'aki glass d'in motarta ya tarwatsi da sauri ta duk'e gudu kada glass d'in yayi mata rauni a fuska, da k'arfi ya fincikota daga cikin mota ya fito da ita waje sai ihu take, ta wayarta da tafad'i Abba yake jiyo ihunta tana neman taimako, d'ayan ya duk'a ya dauki wayarta ta ya yi switch off d'inta tare da jefawa aljihun black lather jacket d'in jikinsa, tana ji tana gani suka jefata cikin motar tare da saka mata blindfold suka kuma rufe mata baki da salatif, ba ka ji komai sai gurnaninta doguwar tafiya suka yi saida suka fita garin Abuja k'auyen madallah suka nufa sai da suka yi tafiya mai nisa kafin su nufi wani poultry house suka yi horn mai gadi ya bud'e musu gate, bayan su yi parking d'ayan daga cikinsu ya sa6o barrister A a kafad'arsa suka shiga da ita wani flat.
*****---****-----*****
Jamal da ke kwance akan gadon asibiti saboda yaran, Jarumi sun yi masa shegen duka har da rauni aka matarsa Zulaiha ta shiga shafinta na Facebook sai kawai taci karo da sabon labari, cikin mugun tsoro ta mik'awa Jamal wayarta. sosai shima ya firgita da ganin labarin jikinsa yana rawa ya mik'e daga kan gado ya cire rigar asibiti Zulaiha ta taimaka masa ya saka jallabiya, hannunta ya riko had'e da daukar handbag d'inta wacce yake da tabbacin makullin motarta yana ciki, parking space suka nufa ya mik'a mata handbag d'inta tare da cewa Zulaiha yi sauri ki ja mota mu tafi.
Ina za muje Jamal kai da baka lafiya?"
Nace ki ja mota mu tafi banso silly questions.
Yanda ya k'arashe magana cikin tsawa yasa babu gardama ta ja mota suka fice daga Nimzamia hospital.
***--*----***-----*---***
*LAGOS NIGERIA*
Tun safe Aliyu yake conference hall yana meeting saboda wani contract na gina manya-manya tituna da hanyoyin ruwa da kamfaninsu na contractual & building material company wanda kowane kamfani irin nasu yake sa ran ya samu project d'in, daga k'arshe kamfanin su Aliyu ne ya yi nasarar samun contract d'in.
"Saboda haka cike da farin ciki Aliyu ya fito daga conference hall direbanshi ya bud'e masa mota ya shiga, sai lokaci ya yi switch on d'in phones dinshi da zumar ya gira rabin ransa.
Da safe kafin ya shiga meeting da suka yi waya bai sake waya da ita ba gashi yanzu har 1:27pm, ya yi dialling digit d'inta saidai wayarta ta a kashe kafin ya yi yunk'urin kiran d'ayan layinta call d'in k'anwarsa Zee-zee ya shigo wayarsa, ya yi picking tare da kara wayar a kunnenshi cikin matsanancin kuka Zee-zee ta ce "Don Allah Ya Sultan duk inda kake duk abinda kake yi ka jinginar ka zo Abj muna cikin tashin hankali wanda ba za mu iya jure shi mu kadai ba, muna buk'atar taimakonka.
Ya lumshe idanuwanshi tare da fad'uwar gaba mai tsanani ya ce Zainab waye ya rasu?"
Ya Sultan ba wanda ya rasu amma wallahi gara ace rasuwa ce aka yi da wannan iftila'i da ya fad'awa zuri'armu. Yaya Daddy ne ya kama momma a hotel tare da k'aramin yaro wanda a shekaru ba zai wuce age mate din Meena ba they're having an affair kuma gaba d'aya duniya ta dauka bansan ya aka yi median tasan abinda yake faruwa a hotel din ba yanzu haka sai yad'awa ake yi musanmman a social median saboda Abba Yusuf, ya biya wasu daga gidanje rediyo da talevision da su daina yad'awa shiyasa abin ya yi sauk'i a kaffafen yad'a labarai
ta k'arashe magana tare da rushewa da wani sabon kuka har tana shed'ewa.
Innalillahi wa'inna illaihim raji'um!
Aliyu ya shiga maimaitawa har wani duhu-duhu yake gani da yana da d'abi'ar saurin kuka da yau ba abinda zai hana shi rushewa da kuka, cikin wani yana yi na k'onar zuci ya ce "Zainab ki daina kuka saboda ba abinda zai canza faruwar wannan al'amari, ba'a fata sai ma ya haifar miki da wata matsala muyi hak'uri mu kuma doshe kunneyenmu mu dauki wannan al'amari a matsayin k'addararmu, ke ce babba ki rarrashi k'anneki kafin na zo kinji?"
"To Yaya tafad'a tare da share hawaye.
Ina Amina in tana kusa da ke ki bata waya nayi magana da ita.
Yaya batanan tun lokaci da al'amari ya faru na shiga apartment d'inta, masu aikinta suka ce tafita kuma har yanzu bata dawo ba, duk da muna hospital na bar ma Daniel sak'o idan tadawo ya sanar da ita muna asibiti.
"Shikenan Zainab ki kula da Daddy kafin na zo ki kuma kira uncle Suraj ki sanar da shi abinda ya faru, ya sameki a hospital ba za ki iya hidimar asibiti ke kadai ba.
"Yaya na kira shi yafi a kirga wayarshi switch off.
Aliyu ya dafe goshinsa damuwarsa ta k'ara k'aruwa.
"Ba damuwa ki cigaba da zama wajen Daddy ita kuma Meena da Fateema su zauna wajen momma kafin in iso.
To....Yaya ta k'arashe magana had'e da hanging up.
Aliyu ya kira number wani friend dinshi da ke aiki a Airport ya ji ko akwai jirgin da zai tafi Abj da rana, cikin sa'a ya ce akwai 2:30pm zai tashi ya ce ya siya mishi ticket gashinan zuwa a cikin Airport din ya samu ya yi sallar azhar, yana gama sallah saida ya sake gwada kiran number barrister still tana rufe hakan ya k'ara jefa shi a damuwa saboda yasan bata da hearing a court, da kanta ta sanar da shi lokaci da ya kira ta da safe ta ce yau tana gida ba zata fita ba.
"Oh.....ya rabbi ka taimake ni kasa ita ma ba wani mummunan abu ne ya