Showing 60001 words to 63000 words out of 80263 words

Chapter 21 - Gidan Rina Book Complete Jidda Aliyu.txt

31 Jan 2025

9426

dining area, ta zauna kusa da barrister ta sunkuya dai-dai kunnenta ta rad'a mata momma tafita zata had'u da Jarumi ta kar6o poison da zata kashe maryama da Baaba laraba, saboda nace sai na tona mata asiri shine ta rufeni a d'aki.
Kiyi sauri ki fita da Maryama daga gidanan idan kika bari ta dawo tabbas maryama zata mutu.
Gaban barrister A yayi mummunar fad'uwa ta zazzaro idanuwanta, cikin kad'uwa take kallon fuskar Teema mai kama da ta momma Murmushi Teema tasaki mata tare da fad'in ki tashi matar yaya kada lokaci ya k'ure miki.
Gaba d'aya ta zama speechless sai kawai ta tattaro raguwar natsuwarta tayi amfani da ita ta hanyar mik'ewa tsaye, da gudu ta haura sama ta canza kayan jikinta ta dauko makullin mota.
Ta tarik'e hannun Teema gudu-gudu suka isa flat d'in maryama wani heavy knocking tashiga yi, har tana had'awa da kiran sunan Baaba.
Ta window baaba ta lek'o wacce fuskarta ta kumbure saboda maruka da tasha, hannun momma ta bud'e kumburaren bakinta ta ce 'yar nan daina wahalar da kanki da bugun k'ofa tun jiya Zaituna ta kar6e makullin hannuna.
"Barrister A ta zaro idanuwa ta ce Baaba ki kwantar da hankalinki, yanzu nan zan nemo hanyar da zan fito da ku.
Girgiza kai Baaba tayi tana fad'in babu wata hanya 'yar nan dama nasan zuwanki sasshe nan sai ya haifar mana da gagarumar matsala.
"Batare da barrister ta tanka mata ba tanufi backyard Teema ta bita a baya, windows d'in wuri tashiga dubawa taga babu yanda za'a yi mutum ya iya fita ta cikinsu.
"Iya tunaninta ta rasa lala6o mafita, juyawa da zata yi tayi ma Teema magana sai taga wayam...bata wajen da sauri ta dawo gaban barandar flat d'in tana kallon k'ofar.
"ji tayi an dafa kafad'arta ta waigo atsorace Teema tagani tana mik'a mata wasu tulin keys, matar yaya ki gwada wad'annan kila adace ki samu key da zai bude k'ofar.
Jikin barrister yana rawa ta kar6i keys d'in daga hannun Teema, tashiga gwadawa duk wanda tasaka bashi bane, sai wani shegen sweating take yi kaman wacce aka watsawa ruwa.
"Daga can gate Sa'eed ya hangota ya nufo wajenta, sam bata lura da ya iso wajen ba sai kawai taji sautin muryarshi yana cewa ma'am ko zan iya taimaka miki...?
Da mugun tsoro ta waigo suka had'a idanu muryarta na rawa ta ce Sa'eed wallahi ka tsorota ni banga lokaci da ka iso wurinan ba.
"Murmushi ya yi tare da fad'ar ai kin shagala da gwada keys ne shiyasa baki lura da ni ba. Kawo na taimaka miki ta mik'a masa keys d'in ta koma gefen teema tayi tsaye zugun.....






Jeeddah Aliyu
[7/27, 12:21 AM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619


DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA


*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```


*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```


*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``


*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN


*SLIMZY*:- IZZATA


*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO


_ina ma'abotan so k'amshin ga dama tasame ku idan kina son ki kasance cikin k'amshin a koda yaushe tamkar barrister A, ki tuntube ni ina siyarda Arabian perfumes masu k'amshin gaske da saurin siye zuciyar maigida k'amshi shine mace duk mace da ta bari mijinta yaji odour a jikinta taci baya saboda haka ki garzayu ki kwashi gara6asa ina siyarda Arzaan, Armani, Burhan, Al-maleka, mufaddal, Dima, Asarar Alhub perfumes da dai sauransu Bangare body spray akwai Nada, Bushra, thaljee kuma akwai Air freshener domin k'amsasa d'akin uwargida da na maigida ina da turaren garwashi mai shegen k'amshi akwai hand&body lotion skin dinki ya yi smooth ki dinga glowing, palm dinki ya yi soft kaman auduga ga mai ra'ayi siya sai a tuntubeni a wannan number 07032566172 don Allah serious buyers only_








*GIDAN RINA*






*35*






Momma tana zaune gefen gado a hotel d'in suka saba had'uwa da Jarumi gaba d'aya shirinsu na daff...da lalacewa tun jiya da ta dawo daga unguwa kamar ace ta shiga flat d'in maryama ashe zata yi karo ne da sabon tashin hankali, tun daga shigarta Falon ta cin karo da abinda bata ta6a tunani faruwarshi ba.
Maryama na zaune a falo cikin tufafinta masu kyau, ga jikinta ba datti tsaf-tsaf da ita kaman ba mai ta6in hankali ba.
"Saura kirisss.....zuciyar momma ta buga tunda take a rayuwarta bata ta6a riskar tashin hankali irin wannan ba, shiyasa tun farko ta shawarce Jarumi su kawarda Maryama kada zuwa gaba ta zame musu matsala tsabar taurin kanshi yasa yak'i amincewa da shawararta to ai ga irinta nan.
"A fusace ta fizgo wuyan Baaba ta shek'eta sosai kamar zata rabata da ranta, sam bata yi la'akari da tsofanta ba ta shiga dukanta ba ji ba gani saida ta gaji tasake ta ta koma kan Maryama ita ma duka taci, ta farfasa mata baki daga bisani taja ta kaman kayan wanki ta watsata d'aki ta rufe ta kuma kar6e keys d'in hannun Baaba, shine tana fitowa ta kira Jarumi a waya ta sanarda shi halin da ake ciki da yake yana cikin abuja ya ce da ita gobe da safe zai zo ya kawo mata poison ta zubawa maryama da Baaba a abinci su duka biyu su mutu, alokaci da take waya da shi ashe Teema tana la6e momma na gama waya Teema tafito daga ma6oyarta tana kyakyatar dariya tare da fad'in sai na fad'awa Daddyna. shine momma ta rufeta a d'aki saboda toshewar kwakwalwa da gajin hak'uri irin nata ta fita tabar Teema a gida.
Jarumi kuwa sai kai da kawo yake tsakanin wannan bango zuwa wannan bango, gaba d'aya jijjiyoyin kanshi sun tashi sun yi radau-radau idanuwanshi sun yi jajir kallo d'aya za ka yi mishi ka gano irin 6acin ran da yake ciki, sai huci tare da k'yarma yake yi.
sai da ya furzar da zazzafan iska daga bakinshi kafin ya ce Har yanzu ina mamakin Zaituna ta yanda k'aramar yarinya irin barrister Amina tafi ki wayo in banda kina dabba ko a ciki dabbobi Zaituna ke jaka ce, uban me yakika zo yi anan shin ba ni nace da ke zan zo har gida na kawo miki poison d'in ba...?
Ko don kutumar b***ubanka gidan bak'o na ne?
Banza jahila mai kwakwalwar dabbobi.
ya k'arashe magana yana zabga mata uwar harara.
Momma ta gyad'a kanta a tsorace sai zarar idanuwa take.
Ya sake watsa mata harara a karo na biyu ya ce shine don kina sha'awar mahaukaciya 'yarki ta fallasa min sirri kika barta gida ita kadai, kika fito?" idan har haka ta kasance ki fara kirga sauran kwanakinku a duniya don wallahi sai na kashe ku.
"Cikin kad'uwa Momma ta zaro idanuwa, jikinta yana rawa ta bud'e bakinta da kyar ta ce ban yi tsanmani rashin imaninka Jarumi ya kai har da za ka iya kashe 'yarka jinin jikinka ba.
idan har ni ba ka had'a alak'ar komai da ni Kaman yanda ka ke a koda ayaushe, to....karka manta da fateema 'yarka ce..
Shut up Zaituna nagaji da saurare maganganu ki marasa amfani, don fateema tana 'yarta ce miki nayi ina buk'atarta ban k'ula alak'a da ke ba face sai da na hango zan samu biyan buk'atar raina a duk lokaci da na cima burina, yada kwallon mangwaro na huta da kuda ba zai zame min wahala ba.
"Hanta cikin momma ta murd'a saboda duk lokaci da Jarumi ya ce zai kasheta ta kan dauki zancen nashi a matsayin barazana, sa6ani yau da ta hango zahirin hakan a cikin idanuwanshi sakamakon ya cire face mask d'in fuskarshi.
Kafin tadawo daga duniyar tunani ya fizgota da k'arfi yana fad'in fita ki bani wuri ba wani poison da zan ba ki, ki je ki baje basirarki kada numfashin maryama ya kai gobe inaso sak'on mutuwar maryama ya riskeni idan har hakan bata kasance ba, ki sani sai na dinga yanka naman jikinki har sai kin mutu.
Ya karashe magana had'e da hankad'ata waje ya rufo k'ofa.
****-----*****---****
Luckily Sa'eed na gwada d'aya daga cikin keys d'in k'ofar ta bud'e, Baaba na tsaye sai wuk'i-wuk'i take da idanuwa da taimakon Sa'eed barrister A tafito da Maryama suka sakata a mota, kasancewar da sanyi safiya ne sauran ma'aikatan gidan suna cikin d'akunansu ba su fito ba, gateman ne kawai a tsaye yana kallonsu.
Barrister ta mik'awa Sa'eed key mota ta ce kayi driving dinmu Sa'eed ni ba zan iya ba.
"Har suka fito daga gidan batasan ina suka nufa ba, har saida Sa'eed ya tambayeta.
Ma'am ina muka nufa naga sai tafiya muke ba ki fad'amin in da za muje ba?
Ban saniba Sa'eed amma kai kana gani ina zan samu safe place da zan kai su, kafin zuwa gobe?
Abinda ban fahimta ba ma'am meyasa kika fito da su...?
Ajiyar zuciya barrister tayi tare da fad'in saboda ana farautar rayukansu
iya abinda zan iya sanarda kai ahalin yanzu saboda haka sa'eed ka nemo muna mafita kawai, saboda kai ma yanzu ta shafe ka kuma kaga daga Daddy har Aliyu sun yi tafiya dole muna buk'atar taimakon wani kafin nasamu hujja da zan dogara da ita na kama momma da laifi dumu-dumu, saboda yanzu banida wani kwakwaran evidence a hannu.
"Gaskiya ne ma'am amma me zai hana mu nemi taimakon Uncle Suraj shi kadai nake saka ran zai iya basu kariya....?"
Uncle suraj?
Ta maimaita sunan.
Ehh....ma'am shi kadai nake gani zai iya wani abu akai saboda wannan matsala ce da ta shafi iyali bai kamata mu dauko bare mu saka a ciki ba.
"Idan kuma ba ki amince da wannan shawara ba ki kira M Ardo kawai ki fad'a mishi abinda ke faruwa ko kuma ki fad'awa Yalla6ai Aliyu.
"Barrister A ta girgiza kanta tare da fad'in ba zaka gane ba Sa'eed duk laifi da akace babu evidence akanshi k'irk'iraren labari ne, dole sai da hujjar da zata tabbatarda momma mai laifi ce.
Kira uncle suraj d'in in kana da contact dinshi mu ji ko yana gari.
Sa'eed ya ciro wayarshi daga gaban aljihun shirt d'in jikinshi, ya yi dialling number uncle suraj sai dai kashhh...wayarshi a rufe take.
Ma'am wayarshi arufe take ko na kira oga Jamal shima zai iya taimakawa.
"Cikin sauri baerister ta ce Kwarai kuwa kira Jamal zuciyata tafi kwantawa da shi.
"Ringing d'aya zuwa biyu Jamal yayi picking Sa'eed ya mik'o mata wayar agurguje tayi mishi bayani, yace su iske shi gidanshi da ke zone two Sa'eed yasan gidan.
Abinda bai wuce mintuna biyar ba suka iso gidan koda suka shigo compound Jamal yana tsaye yana jiran isowarsu ya yi musu iso a guests room d'in gidan. barrister A tayi ma Baaba sallama da zumar zata dawo gobe.
Parking lot ta tararda Jamal yana jiranta, anatse ta fayyace masa abinda yake faruwa sosai ya kad'u ya kuma shiga firgici daga bisani ya yi k'arfaffiyar ajiyar zuciya tare da fad'in gaskiya barrister A bai kamata kiyi sauri aminta da abinda Teema ta fad'a ba, karki manta tana da uziri.
"Murmushi barrister A tayi ta kai dubanta wajen da Teema ta ke tsaye nesa da su ta shagala da wasa da yatsunta, kamar yanda take yi a koda yaushe.
ta girgiza kanta ta ce kaine kake gani haka amma ni jikina yabani duk abinda Teema take yi da saninta take yin sa.
"Jamal ya zaro idanuwa kaman kwaryar idanuwashi zasu fad'o k'asa, cikin sark'ewa harshe ya ce mekike nufi barrister A nifa sam ban fahimce ki ba...?
Ahalin yanzu duk bayani da zan maka ba lalle bane ka fahimta ba, amma lokaci ne zai fahimtarda kai ka jira har zuwan lokaci ni nan zan fayyace maka komai.
Jamal ya sauke tagwaye numfashi ya ce ki dai zauna kiyi nazari barrister banaso abinda zai haifarda matsala tsakaninki da Aliyu, musanmman ahalin yanzu da ya baki amanar zuciyarshi sanin kanki ne ba abinda yafi ciwo a wurin masoyi irin cin amana, da za ki bi shawarata barrister da kin hak'ura da taimakon maryama ki mayarda ita inda kika daukota, idan taimakonta kike so yi ki bi wata hanya amma ba wannan ba, wallahi ina jin tsoro abinda zai karyawa Aliyu zuciya saboda ya kamu da soyayyarki ba kad'an ba.
"D'an dakata....Jamal!
Barrister A ta katse mishi hanzari, zuciyarta na bugawa very fast ta ce Aliyu ne ya gayamaka ya kamu da soyayyata ko kuma hasasshenka ne ya hasasso maka haka...?"
"Sai da ya murmusa kafin ya ce bangane ba shi king bai ta6a bayyana miki yana sonki bane?
Ta hadiye yawu tare da girgiza kanta, saboda zallan mamaki lalle Aliyu ya cika shu'umi.
'Yar siriryar dariya Jamal yayi tare da fad'in yanzu dai mu ajiye wannan zance a gefe muyi wanda yake gabanmu, kina gani idan bamu sanarda king da wuri ba hakan ba zai haifarda matsala ba?"
Ta girgiza kanta kafin ta ce aganina sanarda shi a yanzu batare da wata hujja ba shine zai zama matsala saboda zai dauka ina zargin mahaifiyarshi ne, batare da wata hujja ba.
Jamal kada mu yi gaggawa mu jira har nayi katari da hujja da za mu dogara da ita.
"Shikenan duk yanda kika ce haka za'ayi.
Suka yi sallama ta rik'o hannun Teema suka shiga mota a wannan karon barrister A ke driving tun a farkon layin shigowa unguwar ta aje Sa'eed, wannan duk yana cikin part of plans d'inta.
Daniel ya bud'e mata gate ta nufi parking lot tayi parking motarta tafito tare da Teema, saida ta kashewa Daniel gargad'i kada koda kuskure ya fad'awa momma ita tafita da maryama.
Koda ta shiga falonta k'arfe 12:40pm gaba d'aya kwakwalwarta ta toshe tana buk'atar ta ware lokaci na musanmman da zatayi tunanin mafita.
"Kitchen ta nufa ta dauko ruwan roba masu sanyi, bata ko nemi cup ba ta balle murfin robar ta kafa bakinta saida ta kusan shanye fiyye da rabin ruwan sannan ta ciro robar daga bakinta ta direta akan fridge, tasaki ajiyar zuciya koda tafito daga kitchen bata ga Teema ba murmushi tayi tana girgiza kanta, abayyane ta ce Teema kenan ke da iskokanki kuna buga wasanku mai kyau da tsari yanzu ni kuma yanzu ne zan fara nawa wasan




_Readers ku zuba ruwan comments ni kuma gobe na zuba muku long typing_








Jeeddah Aliyu
[7/27, 12:23 AM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619


DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA


*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```


*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```


*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``


*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN


*SLIMZY*:- IZZATA


*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO




*GIDAN RINA*








*36*




Da k'arfi momma take danna horn kamar gaba d'aya za tashi unguwa, da gudu Daniel yafito daga band'aki ya bud'e mata gate.
Tsabar tashin hankali da take ciki yasa ta kasa k'arasawa parking lot sai daf da barandar shiga flat d'in maryama tayi parking, tafito daga cikin mota da wani mugun sauri tanufi k'ofar da zai sadda ta da main parlor maryama manya-manya d'uwawunta sai wani 6al...6al...6al suke yi da yake gown d'in shadda ne a jikinta, gaba d'aya d'uwawun nata sun kwashe rabin rigar shiyasa ta tsangale sai kace Rukayya Dakaratu ta shiga gaba tana biye...lol..
Garin sauri ta hau barandar ta taka wrong steps da yake sai ka taka kusan five steps kafin ka hau barandar.
Saura kad'an tafad'i duk da haka, ita sam bata damu ba murad'inta tayi four eyes da maryama, jikinta yana rawa ta ciro key daga handbag d'inta sau biyu key d'in yana sa6ulewa daga hannunta yana fad'uwa.
Da kyar tayi nasarar tattara natsuwarta waje d'aya ta bud'e k'ofar, tun da ta jefa k'afafunta cikin falon bataci karo da Baaba ba tasan akwai matsala tak'ara mulmula manyan mazaunanta masu barazana yaga rigar jikinta, ta nufi d'akin da maryama take ciki k'ofar da tagani a bud'e ya haifar mata da mummunan fad'uwa gaba, duhu ya maye ganinta miyau bakinta ya kafe batasan lokaci da tayi fad'uwa 'yan bori ba da6asss......su kansu d'uwawunta da zasu yi magana da sai sun yi mata Allah ya isa saboda ta azabtarda su ba kad'an ba.
"Da rerrafe ta k'arasa shiga d'akin duk da tasan a rufe ta barshi hakan bai hanata duba bathroom ba, ko Allah zai sa kwakwalwarsu ta toshe kaman nata sun 6oya a bathroom nan ma taga wayam....da gudun bala'in tafito compound ta hango Sa'eed yana wankewa barrister A motarta, nan ko rahoto yake dauka.
"Ta shiga kwalla masa kira kai Sa'eed!
Sa'eed!
"Banza ya yi da ita kamar bai ji ba sai wak'e-wak'ensa yake, gani haka yasa ta nufi wajensa yana ganinta ya cire earpice d'in kunnenshi ya durk'usa hannunshi rik'e da brush d'in da ake wanke tayoyin mota da shi.
"Wata kafira harara tafara wulga masa tana fad'in kai wane irin bagidaje ne sa'eed?
Tun d'azu nake kwalla maka kira amma kai hankalinka yana ga wankewa k'anwar uwarka mota, sai kace ubanta ke biyanka salary ko ubanta kake ma aiki ban saniba?"
Sa'eed ya girgiza kanshi ya ce Allah ya huci zuciyarki Hajiya, kunnayena suna doshe da earpice shiyasa ban ji kiran naki ba don Allah kiyi min afuwa.
"Mtssss....taja dogon tsaki tare da fad'in dama tambayarka zan yi ko kaga lokaci da wani ko wata yafita da mahaukaciyar gidanan?"
"Sa'eed ya yi shiru na 'yan dak'ik'u kafin ya ce auuu....Hajiya kina nufi Teema gaskiya banga fitarta ba s....
Shut up.....!
Jahilar tsawa da momma ta daka masa yasa shi saurin had'iye sauran kalamansa, ya ja da baya yana kallonta a tsorace saboda shi da kanshi yasan ya ta6o _*GIDAN RINA*_
"Sa'eed yanzu don bakada mutunci 'yar tawa ce za ka kira da mahaukaciya...? Ba shakka duk yanda akayi da jaki sai yaci kara.
kana gidan ubanta a k'ark'ashin inuwarsa, kana ci kana sha da gumin ubanta shine don b**ubanka za ka kira 'yarshi da mahaukaciya.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login