Showing 3001 words to 6000 words out of 80263 words
Barkido ta yi wanda yak'arawa kyakyawar fuskarta ma'abociyyar kwarjini kyau, ta ce Barkido ne ya yi min miji.
"What's?
Barkido kuma oh my god!
That's old man ba zai bar mutane su huta ba.
"Mak'e kafad'a Barrister Barkido ta yi alamar ni ma shi nagani.
Abin takaici bansan waye mijin ba kuma aure ba zai wuce 2 months ba.
"Cabdijam!
Lalle this time Barkido ya zo mana da Babban al'amari, amma Bebs miye mafita?"
"I don't know bebs ki nemo mafita before Zuciyata ta buga, kinsan kuma idan zuciya ta buga bebs mutuwa ake yi.
Tak'arasa magana cikin kalar tausayi.
"Dariya Barrister Ladan ta yi ta ce kwantarda hankalinki k'awata kamar kin yi bako ya mutu.
"Mtcwww!
ta ja d'an siriri tsaki
Da ace bako zai mutu da sai na fi kowa murna da farin ciki, kinga abin ya zo min da sauki.
"Wane bako Ki kewa fatan mutuwa?"
Wanda zai zo neman aurena mana.
Sosai Barrister Ladan ta ke dariya saida ta yi mai isarta kafin ta ce, Bebs please mu koma zance mu na farko karki fasamin ciki da dariya.
"Shiru suka yi na d'an lokaci kafin Barrister Ladan ta ce ba za mu yi sauri yanke hukunci ba, k'awata har sai mun had'u da shi idan ya yi miki falillahi hamdu.
"Idan kuma bai yi min ba?"
Barrister Barkido tafad'a tana mai kafeta da ido.
Alokaci za mu nemo mafita sai mu koreshi cikin sauki, kamar yadda mu ka yi wa na baya.
"Ba za ki gane ba Zarah a wannan karon har rantsuwa Barkido ya yi akan lalle sai na kar6i mutume amatsayin mijina.
Kinga kenan zance mu koreshi ma bai taso ba.
"Inna lillahi wa'ina illahim raji'un....ban zace abin ya kai haka ba, yanzu dai mafita guda d'aya ta rage mana dole ne mu duk'ufa addu'a da sadaka Allah ya yi mana kyakkyawan za6i, domin shi kadai yasan abinda yafi dacewa da bawansa.
"Haka ne Bebs amma mazanan suna bani tsoro ko zance aure banaso anayi min, sai gashi kwantsa lokaci da ban yi zato ba ya riskeni.
"Ki daina jin tsoro minal saboda ba duka gaba d'aya maza suka taru suka lalace ba har gobe akwai nagari akwai bata gari.
"Uhm! Bari kawai Zarah ko iyayyenmu kina kallo yadda suke gwagwarmaya da halin d'iya maza, balle mu da mu ke tasowa wallahi da iyayyena za su kyalleni da zan iya rik'e kaina batare da aure ba.
"Allah ya kiyayye bebs ba ma fata ki k'are rayuwarki batare da kin aurarda jikokinki ba.
Barrister Barkido batasan lokaci da dariya ta subuce mata ba, ta ce kai Zarah ba ma 'ya'yana ba.
Eh! mana.
Ita ma tafad'a tana tayata dariya.
Nan take Barrister Barkido ta ji hankalinta ya kwanta damuwar da ta ke ciki ta ragu, shiyasa batada k'awa da ta wuce Zarah saboda duk lokaci da shiga matsala ita kadai take tunk'ara.
"Haka suka cigaba da tattauna zance har Barrister Zarah ta iso k'ofar gidanta, nan suka yi sallama Barrister Barkido ta ja motarta ta nufi gida zuciyarta wasai babu saura damuwa.
****----*****-----***
*WAIWAYE ADON TAFIYA*
*WANENE ALIYU?*
Aliyu Muhammad Ardo shine cikkakke sunanshi, fari ne tass!
Mai matsakanci tsawo yana dogon hancinshi, akan zagayayyar fuskarshi ma'a6ociyya kwarjini.
"Aliyu miskili ne na bugawa a Jarida daily trust shiru-shiru yake bayaso yi doguwar magana yana da zafin zuciya matuka ga sauri fushi da kamar kububuwa.
Aliyu sunan Kakanshi na waje uba yaci shiyasa ake kiranshi da sultan.
"Mahaifinshi Alhaji Muhammad Ardo haifaffen gari Yola ne ya yi ilmin addini da na boko, saidai boko ya fi k'arfi sosai shiyasa ya dusashe na addini.
"Alhaji Muhammad Ardo mahaifinshi Aliyu Ardo a wanchan lokaci mai arziki ne, sosai, ya yi suna har a kudanci Nejiriya k'arin abin ga kuma sarautar da yake da.
"Yana da matan aure har guda hudu da sad'aka guda uku, shiyasa yake da tarin 'ya'ya har talatin da biyu.
Muhammad Ardo mahaifiyarshi Fatima ita ce mata ta biyu, tana da 'ya'ya bakwai ahalin yanzu uku su mutu saura hudu sai d'an kishiyarta Suraj wanda take riko, mahaifiyar Suraj ta rasu tun daga haihuwarshi alokaci Fatima tana goyon Muhammad sai ta kar6i suraj ta cigaba da shayarda shi, idan ba fad'a maka aka yi ba ba za ka ta6a sani ba ita ta haife shi ba.
Muhammad shine d'anta na uku.
"Alhaji Aliyu ya mutu kusan shekaru ashirin da biyar kenan da rasuwarsa.
Matanshi da sadakunshi, da wasu daga cikin 'ya'yanshi sun rasu.
Mahaifiyyar Muhammad tana d'aya daga cikin matan Ardo da suka rasu.
"Duk da haka da yake akwai tarin jikoki shiyasa har yanzu Family din yake da yawa.
Alhaji Muhammad Ardo ya yi karatu boko sosai wanda har ya kaishi da zama Ambassador a England a lokaci matarshi d'aya Maryam tsawon shakaru goma sha biyar da aurensu, Allah bai bata haihuwa ba.
"Da suka dawo Najeriya ya shiga business har ya yi nassarar bud'e kamfanuni da dama arewaci da kudanci Najeriya.
Yana d'aya daga cikin manyan masu kud'in Najeriya.
Yana da gidajen man fetur billa adadin da manya-manya malls a Abuja da Lagos, Alhaji Muhammad Ardo mutum ne mai kafirin neman kudi.
Shiyasa d'ansa tilo Aliyu ya gadesa ba abinda yasani illah neman duniya.
"Lokaci da Alhaji Muhammad Ardo yadawo da England ya had'u da Zaituna Wanda k'aninshi Suraj ya had'a shi da ita.
[7/26, 11:35 PM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619
DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA
*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```
*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```
*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``
*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- RUYUWATA
*SLIMZY*:- IZZATA
*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO
*GIDAN RINA*
*FREE PAGE*
*3*
Zaituna cikkakiyar 'yar duniya ce Mai lasisi a hannu, asalinta 'yar k'asar nijar ce iyayyenta sun mutu tun tana da karanci shekaru.
"Hannu k'anwar mahaifinta Adama ta taso ba k'aramar azaba k'anwar mahaifin nata take gana mata ba, Adama muguwa ce ta k'arshe lokaci da Zaituna ta kai shekara goma sha biyar, ta aurarda ita ga wani tsoho mai mata uku ita ce cikon ta hudu.
''Tun daga lokaci rayuwarta tak'ara shiga garari saboda mijin nata Rudda ya fi Adama mugunta nesa ba kusa ba.
Dukan mata yake kamar ba zai barsu da rai ba, yana d'aya daga cikin dalillai da yasa Adama ta bashi aurenta don tasan azaba za ta sha ba kadan ba.
"Ga kuma matsalar kishiyoyinta kasancewar sun fi ta shekaru, sai su dinga had'e mata kai.
kullum sai sun kulla mata makircin da Rudda zai daketa saida tadawo tamkar ta6arya kir6a sakwara saboda duka.
"Ana cikin haka tasamu ciki duk da cikin da take dauke da shi, bai fasa lakada mata duka ba.
"Cikinta yana da wata bakwai ya daketa kamar yadda yasaba hakan ne yasa ta haifi bakwani, d'a namiji yaro yana da wata d'aya kachal a duniya.
Atsakiyar dare, Rudda ya nemeta tak'i yarda ya rufe ta da duka sai dukanta yake tana ihu, duk yawan matan gida da gayya 'ya'yansu ba wanda yakawo mata dauki.
"Da Rudda ya gaji da dukanta sai kawai ya shak'e mata wuya sai kakarin mutuwa take, gani zai kasheta abanza yasa tashiga lallu6e abinda za ta kwace kanta da shi, cikin sa'a ta ci karo da wuk'a daure a k'ugunsa cikin zafin nama ta zaro ta cikin kube, ba tare da dogon tunani ba ta da6a masa a ciki.
"Yafad'i k'asa yana kugi gani yadda jini ke malala yasa ta buga ihu tafice da gudu tanufi dakuna kishiyoyinta, tana neman taimakonsu.
"Gani halin da mijinsu yake ciki suka fara ihu yayin da 'ya'yansu suka rufe Zaituna da dukan mutuwa.
"Allah ya taimaketa ta kwace daga hannunsu ta 6alla da gudu bala'i ta yanki daji, ba ta ko bi takan bakwani yaronta ba wannan shine sanadin zuwanta Nigeria da farko Lagos tafara yadda zango ana ta hadu da k'awarta Dijama suna aikin wanke-wanke wurin wata bayarba mai siyarda abinci.
"Gani yadda Zaituna take da kyau da diri yasa maza suka fara nemanta da lalata, da farko ta k'i amincewa saida Dijama tai mata huduba sannan ta amince.
"Sannu-sannu idanunsu yana bud'ewa suna k'ara wayewa, da tafiya tai nisa sai suka koma gidan karuwai suka kama d'aki.
"Cikin lokaci k'alilan Zaituna ta zama k'ursugumar karuwa.
Shekaru sun tafi customers suka fara yi musu wuya, sai suka yi kaura zuwa garin kaduna anan ta hadu da Alhaji sambo ya nuna yana sonta da aure nan take ta amince.
"Dijama ta nemo wani malami ya zama waliyin Zaituna aka daure musu aure ta tare gidan mijinta Alhaji sambo, anata gajere tunani tun da tafi uwargida Alhaji kyau nesa ba kusa ba dole ita ce mowar gida.
Da yake Uwargidan Alhaji Sambo ita ma ba kanwa lasa bace, ta tsare gaba ta tsare baya shi kanshi Alhaji tsoronta yake saboda bata bar shi a banza ba.
"Zama yak'i dad'i tsakani Zaituna da kishiyarta, ita da kanta tanemi Alhaji Sambo yasaketa saida suka kai ruwa rana kafin ya amince yasaketa d'in.
Bayan ta kashe aureta da Alhaji Sambo ta ji ba za ta iya komawa, k'azamar sana'arta ta karuwanci ba ta ja jari da kud'in da take tarawa a asusunta na banki.
Ta shiga safarar tufafi na mata da na zama daga Dubai, gani haka yasa k'awarta Dijama ta watsarda karuwanci ta aure wani Alhaji Yusuf da ke zaune a garin Abuja, wannan shine dalilin Zaituna na sake kaura zuwa babban birnin tarayya Abuja tanemi gida a unguwar Garki ta kama hayya.
"Yayin da mijin Dijama ya bata jari mai kauri ta zuba a kasuwancin Zaituna, cikin d'an lokaci kad'an suka bud'e manya shaguna har guda biyu.
Lokaci ya mik'a sosai har Dijama ta kai ga haihuwa, wannan ne ya sakawa Zaituna tunanin sake yin aure kwatsan Allah ya had'ata da Suraj Ardo, da farko ya nuna zai aure ta ko ya akayi auren ya juye kan d'an uwanshi Muhammad, Alhaji Muhammad Ardo aminine awurin mijin Dijama.
"Batare da dogon bincike ba ido rufe da zugar Suraj Alhaji Muhammad ya aure Zaituna, irin aurenan na bariki.
Da yake uwargidansa Maryam mace ce mai hak'uri gaske da kauda kai sai zaman nasu ya yi dad'i.
"Wata Zaituna biyu a gidan tasami ciki, ashe ita ma Maryam tana da shi 6oyewa ne kawai ta yi batare da tafad'awa kowa ba.
'Sa6ani Zaituna da gaba d'aya dangin mijinta ba wanda baisan tana da ciki ba, farin ciki awurin Alhaji Muhammad ba kama hannun yaro.
"Cikin maryam yana da wata hudu ya bayyana saboda tsananin girmansa, sai lokaci Muhammad yasan tana da ciki ranar kamar zai yi hauka saboda murna da farin ciki.
"Gaba d'aya kulawarsa da tattalinsa suka koma kan Maryam, hakan ba k'aramin bak'antawa Zaituna ya yi ba.
"Cikin Maryam na da watani shidda ta had'u da lalura ta6in hankali, duk wani asibiti na masu ta6in hankali, Muhammad yakaita abin yaci turo dama ciwo ke shiga farat d'aya sauki kuma ya na zuwa ahankali.
"Rayuwar Maryam gwanin ban tausayi ga ciki ga hauka, ko yaushe k'ok'arin take ta gudu, ba yadda dangin Muhammad ba su yi da shi ba akan yakai Maryam Mental asylum amma yak'i amincewar da shawararsu.
Aganinshi Maryam bata chanchanci hakan daga gareshi ba, ya tabbata da shine ya had'u da lalura irinta ta ba za ta gujeshi ba.
Za ta zauna da shi har k'arshen rayuwarta saboda haka ya za6i zai cigaba da zama da ita har zuwa lokaci da Allah zai bata lafiya.
''Gani halin da Maryam ta tsince kanta aciki yasa Zaituna ta yi laushi, tagano rayuwar d'an adam ba'a baki komai take ba.
Tadawo tana bata kulawa ta musanmman duk da kowace daga cikinsu cikinta ya tsufa, wani ikon Allah rana d'aya suka haihu Zaituna ta haihu da safe d'a namiji kyakyawan gaske.
"Yayin da dare na zagayowa Maryam ta haifi 'ya mace saidai bata zo da rai ba, ranar Muhammad har kuka sai da ya yi ranar sunna d'a Zaituna ya zagayo aka saka masa Aliyu.
Daga lokaci haihuwa ta budewa Zaituna ta haifi Zainab, shekarar Zainab biyu kachal ta haifi Amina sai auta Fatima.
"Fatima tana fama da lalura ta shafar jinni tun tana yarinya take fama da ciwon wanda har zuwa yanzu ana nema mata magani duk tsawon wannan lokaci Zaituna ba ta waiwayin K'asarsu Nijar ba.
******------*****-----
Family Alhaji Usman Barkido family ne mai girman gaske, wanda girmansa yasa duk wanda yake cikin garin Adamawa yasan da wannan family kasancewarsu jinin sarauta.
"Alhaji Usman Barkido yana da 'ya'ya da tarin jikoki, saidai duk yawan 'ya'yanshi bai yarda sun yi aure ba daga daga tsatso shi ba, don haka tun daga kan 'ya'yanshi mata har zuwa maza aure had'i yake musu.
"Wannan al'ada ta shi hatta jikokinshi ba su tsira ba, namiji ko mace da kai isa aure zai nemo maka partner kuma, kuma cikin amincewa Allah sai ka ga sun zauna lafiya.
"Barrister Amina Abdallah Barkido tana d'aya daga cikin jikokinsh 'ya ce ga d'ansa Abdallah Barkido.
Abdallah Barkido mutum ne mai tsautsura ra'ayi mafad'aci gaske mutum ne mai zafin rai, matarshi ta aure d'aya Hindu shi da Hindu anyi musu aure had'i batare da su na son juna ba.
"Abdallah baya son Hindu ko kad'an duk da kasancewarta kyakyawa aji farko, kuma 'yar uwarshi ta jini hakan bai sa ya so ta ba.
"Hindu mace ce mai hak'uri gaske duk wulak'anci da Abdallah yake mata shanyewa take, bata kai k'ararsa ba Allah yabata cikinta na fari ta haifi Amina wacce suna mahaifiyar Abdallah ta ci shiyasa suke kiranta da Minal.
"Zuwan Minal duniya ya chanza Abdallah har yafara nunawa Hindu k'auna.
Abdallah yana matuk'ar son Minal bai had'ata da komai ba, lokaci da tana yarinya idan tana rashin lafiya har kuka yake yi.
Muddin kanaso ka ga 6acin ransa kata6a Minal.
"Shekarar Minal biyu a duniya Hindu tasake haihuwa 'yan biyu duka maza, Khalil da Khalid sai Ahmad sai kuma auta Rahma wacce bata wuce 9yrs ba.
"Minal lawyer ce mai zaman kanta sau biyu Barkido yana za6a mata miji tana rejected, tare da goyon bayan mahaifinta Abdallah wanda yasha al'washi ba zai ta6a bari ayiwa 'yarshi auren dole ba.
"Wata rana Alhaji Muhammad Ardo yakawo ziyara a yola, ya je gaida Barkido kasancewar Barkido abokin margayi Aliyu Ardo ne.
Anan yake tambayarshi Aliyu yaranshi nawa, sai ya ce har yanzu bai yi aure ba, sosai Barkido yarufe Muhammad da fad'a daga k'arshe ya ce ya turoshi ya zo ya ga Amina su dai-daita.
*wannan kenan*
[7/26, 11:38 PM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE IDAN KANA SO SAI KA TUNTUBEN WANNAN NUMBER*
0813943903
*GIDAN RINA*
*Haske writers association*
Na Jeeddah Aliyu
*4*
*CIGABAN LABARI*
Barrister Amina tana tafiya tana tunanin maganganun da Barrister Zarah, ta gaya mata wanda suka zama sanadin rage mata damuwa.
"Agajiye ta iso gida a parlour ta tararda mahaifiyarta Hindu wacce suke kira da Ummi suna zaune da Rahma, da ke kallon cartoons.
Da sallama dauke da bakinta tashigo.
Sannu da zuwa Ya Minal.
Rahma tafad'a tana mai mik'ewa tsaye ta kar6i handbag din Minal
Yauwa Rahma kallo ake yi?"
Eh! Cewar Rahma tana mai nufar dak'in Minal takai mata bag d'in.
"Washhh! Barrister A tafad'a had'e da zama akan hannun kujerar da Ummi ta ke zaune.
"Sannu da gida ummi?"
''Yauwa Minal sannu da zuwa ya aiki da fatar anyi nasara?"
Alhamdulillah!
cikin yarda ubangiji mu yi winning case d'in.
masha Allah!
Ummi tafad'a cike da farin ciki nasara 'yarta ta.
Mik'ewa ta yi had'e da furta Ummi bara na watsa ruwa ko na d'an ji k'arfin jikina.
Toh! Afito lafiya
ummi tafad'a da murmushi akan fuskarta.
Da isar ta d'akinta ta cire kayan jikinta ta daura towel, ta fad'a bathroom ta sakewa kanta shower bata dauki dogon lokaci ba tafito, ta zauna gaban mirror ta shiga shafe lallausar fatar jikinta da lotion mai k'amshi gaske.
"Ta gyara fuskarta ta hanyar simple makeup, ta bud'e closet tafito da gown na atamfar Holland tasaka had'e da fesa Arabia perfume ta jikinta dauki k'amshi.
"Rahma ta turo k'ofa dauke da sallama.
Ya akayi ne auta?"
Ummi ta ce in gaya miki in kin kammalla abinda ki ke tana son ganinki.
"Ta kalli k'anwarta ta anatse ta ce ki ce da ita gani nan zuwa.
Toh!
Rahma tafad'a tana ficewa daga d'akin.
Barrister A ta cigaba da daura d'an kwalinta tana kammalawa tafice rik'e da wayoyinta.
Tana isa parlour ta tararda ummi tana waya, ta samu wuri ta zauna, tana karantar yanayinta koda wata damuwa sai taga sa6anin haka, sai ma fara'a takeyi.
"Ummi ta k'are wayar ta juyo ta kalli Barrister A fara'a tak'ara yalwanta akan fuskarta, ta ce dama zan yi miki magana akan mutane da za su zo neman aurenki.
"Ummi ta yi shiru na wasu 'yan dak'ik'u kafin ta ce shine naga yadace mu yi magana.
Toh.....ummi ina saurarenki.
Cewar Barrister A tana mai gyara zamanta.
Yayin da Ummi ta cigaba da cewa Minal lokaci yana tafiya a kullum k'ara girma ki ke, shekaru ki suna tafiya ak'allan yanzu kina da shekara 25 a duniya zuwa wannan lokaci ya kamata ace kina d'akin mijinki.
"Amma a dalilin taurin kanki da na mahaifiki gashi har yanzu kina gida, Minal ki yi wa kanki fad'a kada ki biyewa