Showing 15001 words to 18000 words out of 80263 words

Chapter 6 - Gidan Rina Book Complete Jidda Aliyu.txt

31 Jan 2025

9442

ya tsurawa wayar ido yana girgiza k'afarshi, zazzafar ajiyar zuciya ya yi had'e da jin haushin Daddy ganin da k'arfi da yaji yana so ya mak'alk'ala masa auren yarinyar da baya jin sonta a zuciyarshi.
"Zuwa wannan lokaci yaci ace Daddy ya jinjina masa da namijin k'ok'arin da ya yi na amincewa da auren, yaci ace ya yaba masa ya kyale shi yaji da k'unci da rad'ad'in da zuciyarshi take mishi, ya Daddy yakeso ya yi da rayuwarshi ne?
"Shi mutum ne da bayaso damuwa ko kad'an sai gashi stress yana so ya yi mishi yawa.
ya jima shiru yana nazarin abinda ya kamata ya yi, yasan tabbas bashi da mafita dole yaje Yola, musanmman yadda ya daure kanshi har da wani cewa zai yi weekend a can, ya zame mishi wajibi dole ya je ko baya so in dai yana so zaman lafiya tsakaninshi da Daddy.
Ya d'ago kan ya dubi wrist watch d'in hannunshi sannan ya mik'e tsaye ya dauki wayoyinshi ya bar office duk da yana da tarin ayyuka masu matukar muhimmanci.
****----****----****
*ABUJA*


Momma tafito daga apartment d'inta jikinta sanya da buba ta material black & golden colour, kaitsaye apartment d'in eMaryam ta nufa dai-dai k'ofar shiga main parlor ta tararda wata 'yar kyarmusasshiyar mata tana jiranta, barka da fitowa Hajiya!
Yauwa Ruky!
Shigo daga ciki ki ganta kwananan jikinta ya fara sauki sosai, momma tafad'a tana wucewa gaba Ruky na biye da ita tun daga main parlor za ka fara ji gurnaninta, tsaki momma ta ja mtsss!
wata k'ofa ta nufa ta sanya key ta bud'e wani irin masifafe wari ya bugi hancinta babu shiri ta doshe hanci da tafin hannunta, cikin fushi ta shiga kwalawa inna Laraba kira inna laraba.....inna laraba fa!
Da gudu tafito daga bedroom d'inta d'an kwalinta a hannu, cikin yanayi na tsoro ta k'araso gani Hajiya.
Wannan wane irin wari ne ke fitowa daga d'akinan?"
Jikin inna laraba yana rawa ta shiga d'akin, Maryam na takure a jikin bango sai fizgar gashin kanta take tana wani irin gurnani bakinta na fitarda miyau mai yauk'i, k'afafunta da hannayenta daure da sark'a abin gwanin ban tausayi.
Cikin rashin tsoro Inna laraba tanufi wajenta, tashiga dubata tagano kashi ne tayi d'agata tayi tanufi bathroom da ita ta tsaftattace mata jiki had'e da sauya mata kaya ta fito da ita bisa gado ta zaunarda ita, ta dauki tissue ta goge inda kashin ya6ata tayi mopping ta kuma fesa air freshner sannan fa momma da Ruky suka shigo duk da haka sai wani yayatsine fuska momma take.
"Cikin daure fuska momma ta dubi inna Laraba ta ce inna ba mu wuri likita za ta duba ta.
To!
Cewar inna Laraba tana mai ficewa daga d'akin.
Daf da Maryam momma ta tsaya ta d'ago ha6arta cikin zallan rashin imani ta dauke ta da mari, sai da ta kai kwace, sai kawai ta rufeta da duka tana yi tana zurfa mata zagi shegiya tsinaniya muddin ina raye kin dinga gani bala'i da masifa har karshen rayuwarki.
Ba dai kin k'i mutu ba tsawon shekara ashiri da takwas ina azabtarda ke, da yake ran kare ne da ke kin k'i mutu ki hutarda kanki nima in huta, to tunda kin kafe mu zuba ni da ke d'a halak ka fasa, shegiya mai taurin ran tsiya.
Ta k'arasa magana tana huci.
Dafa kafad'arta Ruky tayi cikin sigar rarrashi ta ce don't worry Hajiya komai yana da lokaci tunda ki ka iya jure zama da ita na tsawo shekaru 28 kisanta ba zai miki wahala ba.
"Bana so na kasheta ne da kaina Ruky na fi so wahala ta kashe, ta kinga ba wanda zai zargeni.
"Haka ne Hajiya you're too smart.
Dariya momma tayi cike da jin dad'i an ya6e ta.
Yi maza Ruky ki yi mata allurar haka kawai 'yan kwanaki nan da aka daina yi mata allura tafara acting like normal mutane, kin ko ga ba abu mai sauki bane na barta ta wark'e don haka daga yau kin dinga yi mata allura kenan.
"Murmushin mugunta Ruky tayi ta bud'e handbag tafito da wani Vaccination, saida ta cika sirinji ta kama hannu Maryam wacce tun lokaci da momma ta jingeta take kwance lamo kamar mai bacci, ga jijiyar hannu Ruky tai mata allura ko motsawa bata yi ba cikin abinda bai wuce 30 seconds ba tayi bacci.
"Wani mushirikin murmushi momma tayi tana k'arewa Maryam kallo, sannan ta juyo ta nufi k'ofar fita yayin da Ruky ta mara mata baya flat d'inta suka nufa.
"A main parlor suka tarar da Tima zaune tana wasa da yatsun hannunta, kamar mai lissafi momma ta dube ta ta ce Tima me ki ke yi anan?
Ba na hanaki zama a falonan ke kadai ba, ina zee-zee da Minat da suka barki ke kadai?"
Har momma ta gama zuba mata tambayoyi bata kalleta ba, sai wasanta take da yatsunta.
"Tima.....magana nake da ke fa.
Wani irin d'agowa tayi idanuwanta sun yi jajir sai kace abinda aka zubawa Barkono, ta mik'e zubur ta nufi wajen momma da sauri momma ta ja da baya cikin wata rikitattaciyar murya ta ce "za ta zo tabbas tana gam da zuwa ita ce za ta tone rijiya mai dauke da macizai da kunamu ta fito da jar jakka mai dauke da kundin sirri.
Tana gama magana ta juya ta nufi d'akinta tai barking k'ofar da k'arfi gaske.
momma da Ruky suka bi ta da kallo, girgiza kai momma tayi cikin rashin daukar Maganar Tima da muhimmanci ta nufi sofa ta zauna wacce ke kallonta ta nunawa Ruky ta zauna.
Hajiya ina tausayi Tima wallahi, har nake gani kamar zunubin da ki ka aikata ne yake bibiyarta.
Murtuk'e fuska momma ta yi kamar bata ta6a dariya ba, hakan yasa Ruky ta sha jini jikinta.
"Duk haka sai da momma ta nuna mata k'ofar fita da d'an yatsanta, tashi maza Ruky ki fice min daga gida aiki ki ke min kuma ina biyanki mak'udan kudi bana wasa ba, daga yau sai yau ina gargadinki kar ki sake yi min kutse a cikin al'amurana duk duniya bani da babban mak'iyi irin mai fad'amin gaskiya.
"Allah ya ba ki hak'uri Hajiya na tu.......
Ya isa dallah kin riga da kin batan rai ki fita kawai sai gobe in kin zo.
Mik'ewa Ruky tayi sahunta a likkafa ta fice cike da takaici irin wulak'ancin da momma tayi mata.
****---****----****
*YOLA*
Misali k'arfe goma sha biyu na rana jirgin da Aliyu ya shigo ya yi landing, direbansu na yola ya kira ya dauko shi daga Airport gidansu da ke nan Yola ya sauka ya yi wanka ya shirya masjid ya fara wucewa ya yi sallar Juma'a daga masallaci, ya wuce gidan uncle suraj anan ya ci abinci suka shiga tattauna zance business duk lokaci da uncle Suraj ya dauko zance aurenshi sai ya shasshata zance.
Anan ya yi sallar la'asar, kafin ya yi sallama da uncle ya nufo gidansu Barrister Amina.
"Barrister Amina ta kammalla shirinta tsaf cikin Arabian gown ash colour tayi rolling da d'an siriri veil orange colour, ta fito sak'ale da handbag d'inta ita ma kalar orange tayi masifar kyau da yake Ummi ta fita shiyasa ta lek'a d'akin mai aikinsu Asabe ta ce koda Ummi ta rigani dawowa ki fad'a mata na fita saloon gyara gashi, gudu-gudu ta fito saboda daga wurin saloon tana so ta biya gidan Barrister Zarah Ladan tun kafin ta k'arasa parking lot tai using remote k'ofufin motarta suka bude ta shiga tayi ma motar key tayi reverse, ta nufi gate sai gate d'in a bude wata dalleliyar mota kirar Jeep Volkswagen, ta shigo dole tai reverse ta koma baya ta bata wuri ta wuce a tunaninta ko d'aya daga cikin guest d'in Abba ne, wani abin takaici ba kowa a gida dole ta tsaya tai entertained d'insu, ta kashe motar had'e da jan tsaki mtssss!
Ta bude k'ofa ta fito yayin da bak'in suka yi parking, direba ne yafara fitowa ya bud'ewa Aliyu k'ofa ya fito tai tsaye turuss....tabbas ta shaida fuskar Aliyu cikin salon tafiyarta mai daukar hankali ta isa wurinshi, fuskarta dauke da sanyayye murmushi sannu da zuwa!
Ta fad'a kamar mai koyon magana.
Cikin husky voice dinshi ya ce Yauwa mun same ku lafiya?"
Lafiya qalau ya su mommy?"
Lafiya qalau suke.
masha Allah!
juyawa tayi wajen gate man ta yafuto shi da hannu, cikin azama ya iso ta ce ka shiga da bak'o falon bak'i ina zuwa tak'arasa magana had'e da nufar cikin gida.






Jeeddah Aliyu
[7/26, 11:52 PM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619


DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA


*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```


*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```


*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``


*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYYATUDEEN


*SLIMZY*:- IZZATA


*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO




*GIDAN RINA*


*11*




Ta kwalawa Asabe kira ta tayata had'a mishi abinci da drinks, ta dubi Asabe ta ce dauki ki kai masa Asabe ki ce mishi ina zuwa.
"Bayan Asabe ta kai mishi abinci ta dawo ta lek'a d'akinta ta ce ta kai mishi saida iya juice ya sha ya ce ya k'oshi da abinci, shikenan Asabe ki mayarda abincin kitchen.
Ta mik'e ta isa gaba dressing mirror ta gyara fuskarta, ta fesa Asrar alhub perfume sannan ta fice cikin sanyayar muryarta tayi sallama ya amsa can k'asan mak'oshi, sai da ta zauna a sofa da ke facing nashi sannan tasake gaidashi ya amsa a tsanake, shiru ya biyo baya kowanesu da abinda yake sakawa a ranshi wayarshi tayi ringing hakan yasa ta d'ago ta sace kallonshi ya yi receiving call d'in cikin tsadadd'en turancinshi yake magana, da business partner dinshi tsawo 30 minutes ya dauka yana waya kafin ya katse kiran ya d'an sace kallonta dai-dai ita ma ta d'ago ta kalleshi karaf idanuwansu suka sark'e, wani irin kwarjini na musanmman kwayar idanunshi tayi mata fiyye da farkon ganinta da shi, kamar daga sama taga yasake mata k'ayatattace murmushi wani irin sanyi ya ratsa tun daga tsakiyar brain d'inta har zuwa tafin k'afarta.
"Ita kanta batasan lokaci da ta mayar masa da martani murmushin na shi ba.


"Cikin salon maganarshi mai cike da yanga da aji ya ce Barrister da fatan za'ayi min afuwa kasancewar kin gani daga sama ba sanarwa, wannan ya faru ne a dalilin rashin sanin phone number dinki kiyi hak'uri da rashin ganina ayyuka ne suka sha min kai, yanzu dai bani digit dinki gudu kar a koma 'yar gidan jiya.
Yakarasa magana yana shafar geminshi.
Ta sadda kanta K'asa fuskarta dauke da yalwattace murmushi, ta shiga karanto masa numbers dinta duka guda biyu da ta ke using da su.


"Ya shigar da digit din a wayarshi ya yi saving da Barrister 1 da kuma barrister 2 ya kira numbers da wayoyinshi a lokaci d'aya phones d'inta guda biyu babban da k'arama suka yi ringing ta kai dubanta ga wayoyi ni ne kiyi saving numbers d'in yafada kamar mai koyo magana.
"murmushi kawai tayi batare da tayi magana ba, haka Kuma bata kalleshi ba.
Shiru ya biyo baya na tsawo wasu dak'ik'u, gani za su 6ata lokaci a banza shi kuma ba abinda yafi ba muhimmanci irin lokacinshi saboda kowace dak'ik'a tana da matukar amfani a wurinshi, a cewarshi idan lokaci yawuce shikenan ba zai ta6a dawowa ba shiyasa yake matuk'ar mutunta lokaci.
"Don haka ya gyara zama duk da shi d'in ba gwani surutu bane, amma kuma ya zama dole ya yi shi a gaban barrister sakamakon fahimtar da ya yi ita ma gwanace a fagge miskilanci, sosai yake mamaki yadda zamansu zai kayya shi da ita.

Ya yi gyaran murya kamar mai shirin kiran salla, ya ce Barrister maganarki tsada ne da ita ko ya ke ki ke presented case a court oho!"
Yadda ya k'arasa magana yana rik'e habbarshi yai masifar bata dariya, har batasan lokaci da tasaki dariya mai k'aramin sauti ba har tana had'awa da rufe fuska da tafin hannunta.


"Shi din ma murmushi ya yi ya cigaba da cewa kodai har yanzu fushi ake da rashin zuwa na.
"Girgiza kanta tayi ta kalle shi da raguwar murmushi a fuskarta ta ce "A'a Allah ni ba fushi nake ba duk abinda ka fad'a ina saurare kuma na fahimci bayaninka.
"To amma ai ba ki ce da ni komai ba duk da hak'uri da na bayar anyya kuwa barrister kin hak'ura kodai na nemo paper da biro na rubuta miki I'm sorry ma'am sau dubu?"
"Zaro golden eye's d'inta ta yi had'e da furta rufa min asiri yalla6ai, ni asuwa da zan ba ka wannan danye aiki.
Ke barrister mana masu murd'e gaskiya ta koma k'arya ku murd'e k'arya ta koma gaskiya.
"Turo baki tayi cikin shagwa6a da ita kanta batasan tayi ba, abinka da sangartattaciya ta ce ni gaskiya ba haka nake ba ka je ka bincika sosai za'a gayamaka bana d'aya daga cikin masu aikata wannan aiki saidai in kuma akasi aka samu, wannan kam ba zan maka musu ba saboda d'an adam azaji ne.
"D'an ta6e baki ya yi ya d'age girar ido yana kallonta wanda hakan ba k'aramin masifar k'ara masa kyau ya yi ba, ya ce gashinan yanzu ina ba ki hak'uri kin k'i hak'ura.
"Ta d'ago ta dube shi da yalwatattacen murmushinta har sai da dimple d'inta duka biyu suka lotsa, hakan yasa kyawun fuskarta ya k'aru cikin sanyinta had'e da tattausan lafazi ta ce "Don Allah yalla6ai ka rufa min asiri kuma ai zance bani hak'uri bai ma taso ba saboda ba wani laifi da aka yi min ba.
"Murmushi ya yi ya ce shikenan tunda kin ce haka.
Daga haka ya yi shiru dama can ya gaji da surutu saboda har kanshi fara ciwo, shi kanshi yana mamaki yadda ya barke baki yana zuba a gabanta.

"Gani yadda ya yi shiru ta gano fuel dinshi ya k'are saboda haka ta gyara zamanta, tana wasa da bangles d'in hannunta ta ce yau ina ka baro Jamal?"
"Saida ya dauki lokaci kafin ya ce "lafiya qalau yake munyi waya da shi kafin na iso nan da yake daga Lagos nake kaitsaye daga can nayo nan, shiyasa ba ki gan mu tare ba.
"Ayya!
Ta fad'a tana murmushi.
Sai kinyi hak'uri da ni Barrister saboda yana yin aikina ban cika zama ba sosai yanzu haka on Monday zan tafi business trip a Zurich sai satin bikinmu zan dawo don haka duk abinda ki ke buk'ata Jamal ko kamal P.A na za su kawo miki, amma zaki rik'a jin wayata duk lokaci da na samu sarari.
"Ba dawuwa Allah ya taimaka!


"Amin ya fad'a yana mik'ewa tsaye zan wuce sai gobe in na shigo, ki gaida mommy in sun dawo.
"Ita ma mik'ewa tayi had'e da cewa zasu ji an gode kwarai Allah ya tsare.
Ya gyad'a kai had'e da ficewa da sauri shiyasa bata sami damar raka sa ba ta koma cikin gida, ko zama bata yi ba maigadi ya dinga shigowa da manya-manya shopping bags yana ajiye had'e da wasu manyan kwalaye.
Ya kuma mik'a mata envelope mai dauke da kud'ad'e masu yawan gaske, ita kanta sai da ta jinjina yawan kud'in.
"Ta zuge zip d'in handbag d'inta ta jefa envelope d'in ta kira Asabe ta shigarda kayan store.
Ta dauke jakkarta ta sake fitowa ta ja motarta ta nufi wajen saloon.
****"""*****"""****
*WASHE GARI*


Barrister A da kanta ta shiga kitchen ta had'a mishi had'add'u dishes, sai misali k'arfe 4:20pm ya iso lokaci da sak'on isowarshi ya riske ta tana zaune ta shirya cikin red colour din straight rubber gown mai adon stones a jiki tai masifar fitowa da shape d'inta, ta yane kanta da scarf multi colour jikinta na fitarda k'amshi Dima da Asrar ahub perfumes.
"Ta dauki phones d'inta tafito kaitsaye ta nufi falon bak'i tayi sallama, ya amsa ciki zazzak'ar muryarshi saida ta zauna sannan ta gaida shi, ya amsa fuskarshi sake.
"Sai lokaci ta kalli kayan da ke jikinshi farin material ne na maza transperent, saboda har ana iya hango white vest dinshi sosai kayan suka k'ara fitowa da kyawunshi, ita kam tsawo rayuwarta bata ta6a gani farar fata da farin kaya yake masa kyau irin Aliyu.
"Ba laifi yau ya ci abincin da aka kawo mishi saidai kad'an yaci, yau d'in ma ya yi k'ok'ari ba kad'an ba wurin yi mata fira bai wuce 1 hour da zuwa ba ya ce zai wuce ta rako shi had'e da yi mishi godiyar kayan jiya.
"Yana batun shiga mota direban Abba yadano kai dole ya jira fitowar Abba suka gaisa, saidai babu wata walwala akan fuskar Abba ya tank'e fuska kamar maigadin mak'abarta sai ma wajen 'yarshi ya juya yana washe mata hak'ora, ta shige jikinshi tana cewa whats a pleasant surprise Abba!
"I'm sorry my princess I come without informing.
Yafad'a yana ciro ta daga jikinshi.
It's okay Abba...saidai gaskiya ba ka kyautawa Ummi ba duk dai ba wannnan ne first time da ka fara yin haka ba.
Ta k'arasa magana kamar da fushi akan fuskarta.

Yayin da Aliyu ya zama d'an kallo sai sata kallonsu yake, saboda sun yi masifar burge shi da alama akwai shak'uwa mai k'arfi atsakaninsu, kamar shi da nashi mahaifi ba san time d'in da ya yi murmushi ba da ya tuna da yadda wani lokaci suke daro shi da Daddynshi.
"Abba ya ce ki je sallame bak'onki ki dawo naji laifina naga fuskar my cute princess ta nuna fushi.
Murmushi tayi wanda bai wuce le6enta ba ta ce uhum!
Abba ya nufi cikin gida ta juyo wajen Aliyu tana murmushi ta ce sai anjima yalla6ai amma gobe kafin ka wuce za ka biyo muyi sallama ko?"
"Insha Allah Abba's girl!
'Yar dariya tayi had'e da cewa ka ganka ko...
Batare da yasake cewa komai ba ya bude mota ya shiga direbanshi yaja suka fice daga gidan, sannan ta juya zuwa cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login