Showing 1 words to 3000 words out of 59977 words
Chapter 1 - BABANA DA MIJINA BOOK COMPLETE Fertymerh Zarah --.pdf
Unknown
22 Mar 2025
4473
Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen2⃣)
WHATSAPP NO:
+2347039625239
BABANA DA MIJINA
©Fertymerh Xarah
1
Agogon alarm dake manne a bangon falon ya buga qarfe ďaya dai dai na dare,
Ta ďauke kanta daga kallon agogon ta maida jikin TV tana kallon aljaxeera....
Xaune take akan sofa tana sanye cikin rigar barci mai tsantsi fara sol,
Ba wata muguwar kyakkyawa bace can, tana da kyau dai dai nata sai dai kuma mace ce Mai aji
na qarshe,
Akan tsinin hancinta tawwadar Allah ce da aka haifeta da Ita tayi mata kyau kasancewarta farar
mace
daga nan xaune taji tsayuwar motar mahaifinta, idan da sabo ta saba da wannan hali na
mahaifinta da mijinta na fitar dare ko dawowar dare, gwanda mahaifinta ďan siyasa ne shine
mataimakin gwamnan birnin kebbi, sukanyi meeting ďin dare akai akai wataran ma a gidan
sukan taru suyi tana jiyo hayaniyar su daga nata gidan,
Bai jima da tsayuwa ba taji ya shige sashensa, tayi hamma haďe da yin miqa cikin wani irin
yanayi na barci dai dai lokacin daya shigo falon da qatuwar kwallo a hannunsa,
Ko kaďan bai raxana da ganin matar tasa a Wannan lokacin tana xaman jiransa ba Co's ta
saba,
ta xuba masa idanuwa tana kallonsa cikin wani irin yanayi fuskarta ba walwala, ya cillar da
Kwallon dake hannunsa haďe da xare socks ďin qafarsa duk Idanunsa akan ta
har ya gama cirewa yayi sassanyar ajiyar xuciya, duk hankalinsa da attention ďin sa yana
kanta, ya sami kansa da ruďewa, akwai wani sassanyan kallo cikin kwayar idonta Wanda ba
duk mata Allah ya mallakawa ba, ya nufeta cikin wata irin tafiya ta izza cike da taqama ya
xauna a kusa da ita haďe da ďora hannunsa akan nata hannu,
Kiyi haquri Iman kamar yanda kike a kullum wasan kwallo wani abu ne d.... yayi shiru
sakamakon wani kallo da tayi masa,
A iya sanina wasan kwallo anayinsa ne da rana ko da safe amma ku bansan wane irin Wasa ne
naku da sai dare kukeyinsa ba,
Ya tsura mata ido,
Iman baki yarda dani bane, ko kina xargina?
Ba xargi a nan illah gsky nake son ka gayamin, bayan albashinka na banki kana nufin duk
wannan dukiyar daka tara duk akan kwallo ne ? Ya gyada kansa
Kwarai Kuwa, kije ki tambaya kiji duk ďan kwallo na asali Mai fita waje yana ball ba qaramin
kuďi suke samu ba, ki yarda dani Mai sunan mamana bani da wani mugun hali Wanda xai cutar
dake, tayi shiru kawai idanunta sun kawo kwalla ta kasa yarda da mijinta da mahaifinta,
tsakanin *babana da mijina* baxan ce ga Wanda yafi wani so na da kula dani ba, ga kuďi har
batason ganin su kasancewar tana xargin masu su, ta goge hawayen fuskarta, yana kallonta
cike da so da tausayinta yana jinta har cikin ransa shi kansa baisan wane irin so yake wa
Fatima ba, ya riqo tafin fuskarta haďe da sanya yatsansa yana share hawayen fuskarta,
Babban tashin hankalina shine naganki cikin damuwa, har sai yaushe xaki yarda dani Iman,
idan baki yarda dani ba Waye xai yarda dani, wallahi ni ďan kwallo ne kidaina xargina,
taja numfashi haďe da Sakin malalacin murmushi tana kallonsa
na yarda da kai mijina, amma Ina so ka kiyaye kayi a hankali da duniya ka Kuma ji tsoron Allah,
jikinsa yayi sanyi
Yace Insha Allah Iman, ya riqa hannunta suka tashi da kansa yaje ya kashe tv da komai, tana
tsaye sarqe da hannayenta a qirjinta tana kallonsa cikin so da qauna, ya juyo yana kallonta
'let's go... ta juya yabi bayanta, har suka hau step ba mai mgn a cikinsu kowa da saqe saqen
xuciyarsa,
ďakin qanwarta Fauxiya ta nufa ta buďe dakin a hankali ta shiga, ta same ta tayi barci sosai
ďakin ya ďauki sanyin a.c ta qudundune guri ďaya da alama tana jin sanyi sosai,ta juya tana
kallon sa,
'you see Fauxiya bata jin magana duk ynda nayi da ita akan shan sanyinnan bataji,
Ahmed yaje ya kashe a.c ďin kana ya ďauki blanket ya lulluba mata bayan ya gyara mata
kwanciya, ta matsa ta gefenta ta xauna, addua tayi mata kafin su bar ďakin,
Kai tsaye toilet ya nufa yayi wanka, yana shirin barci ta shigo da coffee a hannunta, ya karba
yana kallonta da murmushi,
'thank you wify ,tayi murmushi ta xauna bakin gado tana kallonsa,
Yana gama shan coffee ďin ya juyo ya sumbaceta a goshi yana fadin gudnyt, kafin tayi mgn har
ya faďa Kan gado ya kwanta, ta bisa da ido cikin tausayin kanta hawaye suka xubo mata,
Wannan wace irin rayuwace, wane irin aure ne wannan, am a doctor, mijina yana aikin banki,
idan ya fita tun da safe baxan qara sa shi a ido ba sai 6pm da yayi wanka yaci abinci ya fice sai
1 ko 2am wataran ma sai da safe take ganinsa ya dawo wai yaje training ďin kwallo,
Yau satinta biyu rabonta dashi tana buqatar mijinta tana da haqqi akansa bai damu ba saboda
ita tana da buqata sosai ba Kamar shi ba ko xasuyi wata a hakan baxai damu ba,
A matsayina na matarshi abokiyar rayuwar sa bashi da lokacin da xai xauna dani and sai dai
kullum idan nayi masa Mgnr fitar dare yace bana yi masa uxuri da yawan ayyukan dake
gabansa a banki, da dare Kuwa xaije training na kwallo,
Ban rasa ci ba ban rasa sha da sutura ba amma na rasa kulawa da soyayyar mijina abin
tambaya anan shi wannan shine ginshiqin auren, am not satisfied with my husband, bama
Wannan ba rashin xamansa gida...
Babana ďan siyasa ne shi ba mai xama bane idan baya gari yau gobe yana wata qasa, idan
yana gari shima baxaka ganshi ba sai cikin dare yake dawowa, idan taje mashi da complain na
fitar mijinta sai dai yace
'haquri xakiyi tunda koni mahaifinki kina ganin ba maxauna bane, muna meeting sosai Mai
muhimmancin acikin dare, tunda ya gayamiki wasan kwallo suke xuwa kiyi haquri ki barshi
komai lokacine, ta share hawayen ta cike da mamakin kalaman mahaifinta,
shekara biyu da rasuwar mamana, banda kowa a duniyar nan bayan *babana da mijina* sai
qanwata fauxiya, bansan wa xan kaiwa kukana ba ya share min shiyasa ko aiki naje banda
tunani sai na *babana da mijina* babu wanda baya fuskantar challenge(qalubale) a rayuwa, and
is up to us to accept such challenges mu bita da duk fuskar da rayuwa ta xo mana....
Jin shiru bata kwanta ba ya juyo yana kallonta,
'lafiya Iman, me kike tunani, ta tashi da sauri tana fadin ba komai ta nufi toilet, ta saki ruwa tana
kuka sosai yanda baxai jiyo ta ba......
*Dedicated dis buk to*
*Rabi'atu Sk Mhs*
*Sadiya Lawal bala*
*Aysher Gambo*
BABANA DA MIJINA
©Fertymerh Xarah
2
Asalin labarin......
Ahmed mutumin jihar Birnin kebbi,
Daga kallo na farko mawuyacin haline ka gane qabilar da ya fito Hausa ko Fulani, wani mutum
ma'abocin cikar zati da kamala da duk wani nau'in daidaito na rayuwa,
Mahaifinsa malam Abubakar buba malamin islamiya ne mutum ne mai ilimin addini, haka
mutanen unguwa suna tsananin girmamashi,
Sai mahaifiyar Inna, shika dai ne ďa a gunsu, bayan rasuwar mahaifinsa suka shiga wani hali
na rashin babu, gashi qarami a lokacin primary 6,
Ba Mai taimaka masu wani sa'in ma Inna ke xuwa wankau ta sami kudin da xata ciyar dashi, shi
Kuma Ahmed a rayuwarsa yana son karatu shiyasa yake dagewa akan karatun, he is gifted tun
yana qaraminsa malamai sun San dashi,
Ahmed yayi karatunsa da taimakon mahaifiyarsa dake siyarda qarfinta dan ganin farin cikinsa,
lokacin da ya shiga babbar makaranta I mean higher institution duk qaddararta sai da ta saida
ganin ta cika masa burinsa,
Alhamdulillah ya kammala degree ďin sa lfy duk aikin dayaje nema na gwamnati bai samu ba,
duk inda yaje nema baxai samu ba, abokan karatunsa Waďanda iyayensu suke da kuďi sun
fara aikin banki saboda suna da ďaurin gindi a gwamnati wasu ma sun fita waje neman wani
ilimin, shikam degree ne iya qarfinsa yana so ya sami aiki dashi ko yayane dan ya tallafi
mahaifiyarsa....
Kwanci tashi asarar mai rai yau gashi an kwantar da Inna asibiti babu kudin magani Babu
babban tashin hankalinsa kamar ciwonta ulcer da kuma hypertension, duk inda ya buga bai
sami kudin ba, abokansa dake bashi aro sun daina saboda baya biya,
Ya qara komawa asibiti kai tsaye ya nufi inda likitan ya roqesa ya taimaka ya duba mahaifiyarsa
fisabilillah saboda bashi da kuďi, fafur likitan yaqi har kuka yayi wani mutumi dake xaune office
ďin shima yaxo likita ya dubashi ya dubi likitan,
Nawa ne kudin maganin,
Dubu biyar ne fa bawani yawa, kamarsa baxai iya biyawa mahaifiyarsa kudin magani ba,
baxaije ya nemi aiki ba, muma karatu mukayi muka sami aikin,
Ahmed ya dubesa, ko xaka daukeni aiki ne, ko wane irine inaso indai xaka biyani na kula da
mahaifiyata
Likitan yace bama daukar mutum aiki sai mai ilimi kai kuma baka dashi,
Ahmed yace inadashi nayi karatuna na kammala na nemi aiki ban samu ba yaciro takardunsa
ya nuna masa, likitan ya duba sosai Ahmed ya cancanci a daukesa aiki saboda matakin
karatunsa Kuma result ďin sa mai kyau ne...
Xan iya samama aiki da wannan result amma sai idan xaka iya biyan dubu hamsin, kasan aikin
gwamnati ynda yake Kuma a banxa baxaka sami aiki ba sai ka kashe kuďi....
Ruwan cikinsa na soma qugi Wanda bai sami dubu biyar na magani ba Ina xai sami dubu
hamsin a ynxu, ya karbi takardunsa ya juya ya fice yana hawaye,
dakin da aka kwantar da mahaifiyarsa ya nufa har lokacin bata farfado ba barci takeyi,
qarqashin pillow ďinta ya cusa takardun xaije ya nemo kuďi da qarfin jikinsa ya juya ya fice....
Ya fito harabar asibitin ya haďu da wannan mutumin na ďaxu ya kirasa yaje,
Sannu saurayi,
Ahmed ya qara gaida mutumin,
Na ganka kana da hankali sosai Kuma da ganinka xakayi jarumta xan baka kuďi ka taimaki
mahaifiyar ka kakuma sami na aiki indai xaka iya min aiki,
Wane aiki ne xan iya....ya faďa muryarsa na rawa
Mutumin yace ka taba riqa bindiga? Ahmed ya girgixa kansa yana kallonsa cike da mamaki,
Xaka sami kuďi sosai indai xaka iya shiga cikinmu, ni babban ďan ta'adda ne nayi irin Wannan
rayuwar taka ta talauci da haka hr na rasa iyayena, saboda rashin kuďi gurin haihuwa matata ta
rasa ranta, bansan wace irin rayuwa muke ciki a ynxu ba da masu kuďi basa taimako dan Allah,
Mai kuďi daga shi sai xuri'arsa, ďan siyasa ma haka, neman aiki ynxu baxaka samu ba sai dai
su bawa yan uwansu, shugabannin mu na Yanxu basa aiki kamar na da, shin miye laifin talaka?
da haka na nemawa kaina aiki nakewa masu kuďi fashi, inada yara biyar duk aka sami kuďi
kowa Ina bashi kason sa da haka nake gayyatar ka kashigo cikin xaka sami kuďi Kuma xakaji
daďi....
da'ace mutumin ya lura da yaga xufar dake ambaliya a fuska da jikin Ahmed, yayin da gudun jini
ya Katse a jikinsa, hanjin cikinsa ya dunqule guri ďaya
ďan fashi kenan xai xama, barawo Mai daukar haqqin mutane haqqin da ba nasa ba, duk
wahalar nan da yayi wajen neman ilimi da kwalinsa sai ya qare a sata.... tor miye amfanin
karatun da yayi? Wata xuciyar tace rayuwar mahaifiyar ka fa, kana nufin karatun yafi tane?
BABANA DA MIJINA
©Fertymerh Xarah
3
Shiru yayi yana kallon mutumin sosai xuciyar sa sai bugawa take yayinda take ingixa sa akan
ya amincewa mutumin ya sami kudin da xai Kula da Inna, tunda yan uwansu ma sun gujesu
basa taimaka masu da komai tunda ba su da,
Baya manta sanda mahaifinsa na da rai yan uwansa kamar xasu haďiye su saboda kulawa
Kuma saboda mahaifinsa mutum ne dayasan haqqin ďan uwa yake biya masu buqatocinsu, yau
gashi babu ran mahaifinsa sun gujesu saboda basu da komai, mahaifiyarsa na kwance ba kuďi
Kuma ba Wanda xai iya xuwa ya xauna da Ita asibitin sai shi.....
Wannan dalilin ne ya Sanya Ahmed amincewa ya karbi tayin oga nas Wanda yayi matuqar jin
daďi da ya amince kai tsaye ya bashi dubu goma da address ďin inda xai same sa....
Bayan ya karbi kudin jikinsa na rawa yaje pharmacy dake nan asibitin ya siyo magani ya nufi
inda mahaifiyarsa take,
Yanda ya sameta hankalinsa yayi matuqar tashi ya juya xaije ya Kira likita ta riqo rigarsa, da
kyar take iya mgn
Baxan tashi ba Ahmed, buri na bai cika ba inganka yau ka xama wani mutum da duniya xata so
kuma tayi alfahari dashi, kayi haquri da duk yanda rayuwa ta xoma, ka nemi halal, ka Kula da
kyau kada kabari ruďin duniya da abinda ke cikinta ya ci galabarka,
Hawaye yake sosai, jikinsa na rawa hankalinsa yayi matuqar tashi da maganganun
mahaifiyarsa,
Baxaki mutu ynxu ba Inna sai nayi maki gata, ya banbare hannunta da kyar ya fita da gudu
neman likita,
Ko kafin su xo rai yayi halinsa, Allah ya gafartawa Inna......
*
Alhaji Abdallah mutumin xuru ne qaramar hukumar Birnin kebbi,
Babban mutum ne mai ji da kansa Wanda duniya ke damawa dashi a siyasa, shine mataimakin
gwamna a Yanxu kafin ya sami matsayin da yake a yanxu sai da yayi fafatukar duniya da shige
shige Wanda Dama a Yanxu idan mutum na neman cimma wani buri nasa yakan manta Allah
ya kauce hanya, a taqaice sai da ya bada jinin ďaya daga cikin yaransa kafin ya sami kujerar da
yake Kai a yanxu,
Ya'yan shi biyar mata biyu maxa uku sai matarsa Mami, mace mai kirki da mutunta ďan Adam..
Naxir shine babban yaron sa, sai fatyma(iman), Musa, Ismail da qaramar su Fauxiya,
Acikin yaran kaf ya fison Fatima da Fauxiya ko kaďan baya son Abinda xai tabasu, soyayyar da
yake nuna masu daban ce da ta sauran yaransa.......
Kuďin sa Kuwa baa magana, yana da dimbin tarin dukiyar da yabayarda ya'yan sa uku duka
maxa,
Mutuwar su tana xowa Mami a baxata, babu ciwo babu komai xaka ga kumfa na fita bakin su
daga nan Kuma rai yayi halinsa, da haka ta fara rasa yaron ta Naxir...
Naxir ba qaramin mutum bane, a shekaru yabawa 26 har an nema masa mata, fatyma Kuwa a
lokacin ba Mgnr aure a gabanta she is 24 karatunta ta sanyawa gaba, she want to achieve the
goal, bata da buri a duniya kamar ta wayi gari yau ta ganta cikakkiyar likitar mata tana jin
haushin yanda mata ke Kai matsalolinsu da sirrin jikinsu ga likita namiji,
Sanda babansu ya fara siyasa a lokacin komai ya soma sauyawa daga rayuwar gidan na rasa
babban ďan gidan, sosai Mami ta shiga damuwa shi kansa Baban ya nuna damuwarsa duk da
shine sila akan komai,
Sai wani lokaci da matsafin nasu ya nemi ya bada ďaya daga cikin ya'yan sa mata, sosai
hankalinsa ya tashi domin a duniya ba abinda yake so kamar Fatima da Fauxiya komai xai iya
akansu,
Ya qara russunawa haďe da gyara hannu jar rigar dake jikinsa ta tsafi,
Kiyi haquri shugabata xan bada yarana biyu maxa a maimakon matan Ina matuqar sonsu
musamman ma Fatima Iman.......
Ta kece da wata dariya mai raxanarwa sai da gurin ya ďauka kafin tace
Sima ta amince yau da dare nake buqatar jinin Ya'ya ka,
An gama ya shugabata ya faďa yana russunawa,
Ta qara wata dariyar kafin ta juya Kan amininsa Wanda shine sanadin kawo sa gurin,
Me xaka bawa Sima gobe tayi Kari dashi labaran? Ya sunkuyar da kai cikin girmamawa...
Babu ya shugabata sai abinda kika yanke min, banda kowa ynxu a duniya duk na bayar
matatace kawai ta rage...
Bana son matar ka, bana son jininta tuntuni na gayama dan haka ka nemomin jinin wani mutum
ko wane irine ka kawo min a gobe,
Shikenan ya shugabata.... ta qara yin wata dariyar bayan ta nuna na kusa dashi,
Kai kuma munada labarin anyi haihuwa a gidanka jinjirin mukeso kafin ayi suna......
Da haka kowa Sima ta gaya mashi Abinda xai kawo ta Kuma cikasu da kuďi iya adadin da suke
so....
Dama hakane idan har xaka shiga wannan har ka xaka wayi gari baka da kowa a duniya duk ka
bayar saboda neman haram da son abin duniya ka sami kuďi, mecece ribar wannan sana'a?
Da dare duka yaran na tare da Mami, sai Kai da komawa yake naganin yanda xai ďauki