Showing 18001 words to 21000 words out of 59977 words

Chapter 7 - BABANA DA MIJINA BOOK COMPLETE Fertymerh Zarah --.pdf

Unknown   

22 Mar 2025

4487

kinyiwa baba laifi, kin xubar da maganinshi shiyasa ya dake ki, don't hate your
father,

Kuka take sosai ba kakkautawa, numfashinta har sarqewa yake, idanunta sunyi jawur sun
kumbura, idan Iman ta kalleta itama sai taji hawaye na xubo mata, fauxie bata taba kasancewa
a irin Wannan yanayi ba, abinda ta jima batayi mata ba dan tayi shiru sai ta ďauketa ta goyata
tana rarrashinta,
Fauxie ta kwantar da kanta a bayanta hannuwanta qanqame da Ita hartayi barci bata daina
sauke ajiyar xuciya da qarfi ba,


A hankali Iman ta kwantar da Ita kan sofa tana kallon yanda fuskar ta kumbura, kanta yayi xafi
sosai dama tasan Wannan Kukan sai ya janyo mata ciwon kai,

Tana son sanin dalilin mahaifinta na dukan fauxie akan magani,

Meyasa ya fifita maganin akanta? Wannan Karon xata tunkaresa da Mgnr sai idan itama xai
daketa,


Ban yarda da cikar imanin mahaifina ba, tabbas akwai wani boyayyen al'amari game da
rayuwarsa shida Deedah, akwai abinda suke boyemin Wanda ya kamata na sanya ido akai na
gano ko menene, tabbas a yau na kasance mai xargin *babana da mijina* ban sani ba ko Allah
xai iya yafemin xargin dana ke masu? Ta soma kuka sosai Mai narkarda xuciya,

Tana cikin ruďani, Tana neman mafita, tana cikin tsoron halin da suke ciki ita da qanwarta,


Sa'eed na xaune yana kallonta xuciyarsa ba daďi shima kamar xaiyi Kukan a yanda yakeji a
xuciyarsa, domin Iman ta xama wani bangare na xuciyarsa duk da tana matar abokinsa yana
jinta a xuciyarsa tare da tsananin tausayinta,

Irin Kukan da take mai raguwar xuciya baxai iya daurewa ba sai ya tayata, _and he don't want
to be among, he dunno why her cry weakness him, he want to turn this sadness to joy...._,


Abinda yasa a ranshi yana son bata farincikin da ta rasa gurin mijinta, yana so yabata kulawa
irin wacce mace ke buqata a gurin mijinta kamar yanda shima bai sami kulawar gurin matarsa
salima ba, _he want to make these tears to smile_.


Amma ta wace hanya?

Babana da mijina.....


©fertymerh Xarah


19


Tashi yayi ya fice daga gidan baki ďaya, cikin mamakin Deedah inda yake xuwa yabar
matarsa a Wannan halin.....



Salima na xaune da qawarta ya shigo, cikin girmamawa qawar ke gaidashi amma banda salima
ta ďauke kanta wani gefe tana taunar cingam,



ďakin sa ya nufa,
Qawar ta dubeta,
'bara na tafi salima mijinki ya dawo sai wani lokaci,

'Haba habbi idan ya dawo me xanyi masa, kiyi xamanki Musha hira, Mai aiki xata Kula da shi,


'Chabďi lallai salima Ashe har ynxu kina nan da halinki, shiyasa naga ya shigo ko sannu da
xuwa baki masa ba, bansan meke damun rayuwarki ba, baki Kula da mijinki bakya kyautata
masa, kina da miji mai kyau da kuďi ďan gayu dashi.....

'kiyi shiru habbi bana son haka, ba ruwanki da kyawun mijina,


'au kishi kike yi, kina sonsa kike masa haka, ai wallahi Sa'eed yafi qarfin ajinki kema kinsani
darajar ya'yan ki kike ci ina gaya miki gsky a matsayina na aminiyarki ki canxa halinki ki rungumi
mijinki,


'Naji sai anjima habbi,
'ki koreni ynxu tunda na gaya miki gasky, ta tashi sabe da jakarta ta fice bako sallama, salima
na bita da kallo,


Duk Mgnr da suke akan kunnuwan Sa'eed, yasan halin salima baxata taba canxawa ba yana
mamakin xuciya irin tata, yasan inda xai kamata,



Yana xaune mai aikin ta shigo da kaya a hannunta ta ajiye a gabansa ta fita, bata jima ba sai
gata ďauke da ruwa da lemu, ta xauna haďe da tankwashe qafafuwanta tana xuba masa abinci
a plate, shiru yayi kawai yana kallon yarinya aikin da take yafi albashin da ake bata, dole xai
qara mata kuďi, ya ďauko Mai aiki saboda wanke wanke, mopping da kula da yara, sai gashi
mai aikin ita ke kula da komai tun daga gidan, yaran har Mai gidan komai itace,


Tana gama xuba masa ta tashi ta fice da sauri batare da ta kallesa ba Kamar yanda matar
gidan ta gargaďeta.


2day~


Tun daga ranar fauxie bata qara xuwa gurin baba ba hassalima muryarshi idan taji guduwa take
ta boye bayanda Iman batayi da Ita ba, ta riga ta sanya tsoronsa a xuciyarta,


Shima baba yana tsananin nadamar Marin da yayi mata dan gashi fatyma tana xarginsa da
wani abu akai, baya manta sanda taxo ta sameshi da Mgnr dan me xai Mari fauxie akan
magani,


'saboda tayi min asara,

'wannan wace irin asara ce da tafi lafiyar fauxie baba?
'banason Mgnr banxa fatyma, Fauxiya ya'ta ce I have the right in mata duk abinda naga dama a
duniyar nan bamai cewa dan mi saboda ni na haifeta,


'Ni xn tambayeka dan mi saboda qanwatace, ita kaďai nake da a duniyarnan, amana ce a
gurina idan na Bari aka cutar da Ita gobe Allah xai iya kamani, Inaso na bata farin cikin da bata
samu a gurin UWA ba, fauxie na min kallon wani bangare na rayuwarta jin daďin ta da komai,


'Ashe baki da tarbiya Iman, ni xaki xauna kina gayawa mgn haka, kina nufin bana baku farin
cikin da mahaifiyarku xata baku idan tana raye ko me? Kije gaki gata indai nine sai naga
bayanku...... Sosai ta buďe ido tana masa kallon mamaki da jin furucinsa shi kansa baisan ya
furta ba sai a ynxu sai yayi Saurin gyara mgnrsa,

'Ina nufin kije gaki ga Fauxiya ki xame mata uwa duk abinda takeso ki mata,ki ďauki duk wani
responsibility nata, na yafe maki ita kome xai same ku daga ke har ita baruwana da lamarinku,


Batare da tayi mgn ba ta fice tana kuka sosai, Kukan maraici da rashin gata a ynxu....


Tun daga lokacin ta daina xuwa gaidasa kamar yanda Yace ba ruwansa dasu haka suma ba
ruwansu dashi, sai dai kallo daga nesa ko idan sun jiyo jiniyar motocinsa,



Tana xaune a falo taga jini na bin qafafunta, ba ciwon mara ba komai jini ya soma fito mata, da
sauri ta nufi toilet ta duba, bleeding takeyi sosai kenan cikin xubewa xaiyi ta faďa a xuciyarta sai
ga hawaye na bin kuncinta ta fito da sauri jikinta har rawa yake, tun daga Sama har qasa duk
inda tabi jini ne, tana kuka ta Kira adama ta gyara gidan xataje asibiti,

Sosai masu aikin sun tausayamata, abinda suka lura da rayuwarta akwai kuďi a tare dasu
amma ba kwanciyar hankali.


Tana fitowa Sa'eed na shigowa, yanda ya ganta ya sanyashi fitowa ba shiri,


Key ďin motar ta ta bashi dan batason ta bata motarsa,

'muje asibiti Sa'eed, bleeding nakeyi ka taimaka ka kaini Kada cikin ya xube Ina matuqar son
sa,

Yakai Idanunsa qafafuwanta sosai ya rikice yace ta shiga tashi motar,

FMC suka nufa suna isowa ko parking bai gama ba ta fita da sauri, sai ynxu takejin ciwon mara
amma bata damu ba, Sa'eed na bayanta shima hankalinsa a tashe suka nufi Gynaec,

Tayi Sa'a Dr Fulani na gurin ita ta dubata ta gaya mata cikin ya lalace ya riga ya xube wata biyu,


Wani irin kuka ta soma yi gwani ban tausayi Fulani na rarrashinta da bata baki sai dai tana
mamakin yanda cikin fatyma ke xubewa akai akai bayan ko ynxu ta dubata batada matsalar
komai a tare da Ita,

A Wannan lokacin sai fatyma ta yanke hukuncin xata soma planning meyiwuwa bata da rabo a
duniya sai ta huta da wannan wahala da take taji da wahalar dake damunta, itama Fulani sai
tabata kwarin gwiwa akan haka,


Sa'eed ya Kira Deedah ya gaya masa halin da ake ciki,

Sanda ya xo sosai xaka ga damuwa a fuskarshi, yana tsananin tausayin matarshi musamman
irin kukan da take mai ratsa xuciya, daga shi har Sa'eed sai suka fice daga ďakin dan baxasu
iya jure jin kukanta ba.



Dariya suke ba kakkautawa, irin dariyar da ko ina ke amsawa idan anayinta, sima da mutanenta
kenan,


Burin ka ya kusa cika Abdallah idan kaci gaba da bamu jinin fatyma muna sha, muna jin daďin
sa kaima kana jin daďin mu, akwai kuďi na can na jiranka a ďakin ka, ya sunkuya


Godiya nake ya shugabata, suka ďauki wata dariya....


Bayan sun dawo asibiti suna xaune a falo har salima matar Sa'eed da ya'yan su Adnan da
Khadija,

Fauxie suna gefe suna Wasa da Adnan abinka da yaro bata damu ba sai dariya take tana
xagaye falon ita da Adnan,


Deedah ya shigo da sallama a bayansa wata kyakyawar budurwace ta shigo,


Kallo ďaya Iman tayi masa xuciyarta na soma bugawa fal fal ko sallamar bata amsa ba ganin
ynda Deedah ke rawar jiki akan yarinyar ita kuma Wacece,


Budurwar ta xauna tana gaidasu duk cikin su salima kawai na amsa, Sa'eed ma kallon mamaki
yake masu, Deedah ya soma mgn



Uhm....uhm... Iman ga saudah ta xo ta gaidaki ta miki ya jiki, mgnr da ta fito bakinta da wadda
yaji fauxie nayi nayi matuqar ruďashi,


'ita wacece, daga ina.... dai dai lokacin da yaji fauxie na cewa,

'Adnan ina bindigar ka muyi wasa?

'yace ni banda bindiga daddy bai siya min ba,


' Qarya kakeyi kana da Ita, wacce kaba yaya ya ajiye ma rannan.... ka tuna? kaje kace yaya
yabaka bindigarka muyi Wasa.



Pherty

Babana da mijina.....


©fertymerh Xarah


20

Da kyar ya iya saita numfashin sa gurin Iman ya kawar da jinsa gurin su fauxie amma
hankalinsa a matuqar tashe,


Ya kasa furta mata ko wace irin kalma, baisan yanda xai bayyanata a cikin mutane cewar
wadda xai aura ce,


Ganin haka Iman ta ďauke idanuwanta akansu ta maida kallonta ga su fauxie dan samawa
xuciyarta sassauci kuka ma xata iya a Wannan lokacin, mijinta ya kawo mata wata mace a gida
shiyasa bai damu da bata haqqintaba saboda yana da wasu matan a waje ta sauke ajiyar
xuciya, salima ta kasa haquri cos Macece Mai xafin kishin tsiya,

'ita Kuma Wannan Wacece Ahmed, dai dai lokacin fauxie ta qaraso tana faďin,

'yaya wai Adnan ka bashi bindigarsa xamuyi wasa,


'Kuje ina tashi xn ďauko masa,


'wace bindiga kuma? Cewar salima tana kallonsu,


'toy gun ce na siyo masa ranar ita take mgn cewar Deedah cikin dakewa?


'Malama ke wacece wai kinxo kin xauna gidan mutane,


Saudah ta dubeta cikin basarwa,
'ki tambayeshi mana shi da yaxo dani,


Sa'eed yace ba ruwanki salima matarsa bata tambayesa ba sai ke,


'wallahi sai na tambaya ai ni aminiyarta ce dole na tambayar mata, kayi mgn Ahmed,


Deedah ya kasa mgn ganin yanda Iman ta ďauke fuska daga gareshi yanayin fuskarta ma kesa
hankalinsa daďa tashi,

Saudah tace tunda kin matsa kiji koni wacece to budurwarsa ce, yace naxo naga matarsa bata
lfy,


Sa'eed na jin haka ya tashi yana kiran su Adnan ya dubi salima tashi muje gida, daga kallon
yanayin sa xaka karanci bacin rai a tare da fuskarsa yasa kai ya fice,


'Amma ke Anyi wawiyar mace inda xaki biyo namiji har gidan aurensa wai kinxo gaida matarsa,
kina budurwa ko kunya bakyaji koda yake ba abin mamaki bane tunda mutuncin ya riga ya xube
a titi, ta dubi Iman dake sauke numfashi da kyar,


Fatyma sai kinyi a hankali fa saboda cutar xamani.... tasa kai tafice tana faďa sosai ranta ya
baci,

Suna ficewa Iman ta tashi taja hannun fauxie sukayi ďakin ta,


Saman gadon fauxie ta xauna ta saki wani irin kuka mai cike da qunar xucci, fauxie tayi shiru
tana kallon yayarta kafin taje ta kwanta a bayanta,


'Anty kiyi haquri, anty kiyi haquri shine kawai abinda take faďa har Deedah na shigo ďakin,
yanayin da ya same su yayi matuqar tausaya masu sai yake nadamar xuwa da saudah amma
bayajin xai iya fasa aurenta a yanda yake son yara ynxu ballantana saudah tace xata bashi
soyayya mai cike da kulawa.....
A wanna lokacin faďa sukayi sosai dashi, borin kunya yakeyi dan me xata wulaqanta
baquwarsa, itama rufe idanuwanta tayi ta Hausa da faďa sosai,



Wannan yana ďaya daga cikin tarihinta rayuwar aurensu basu taba faďa ba sai yau Kuma mai
tsanani, fauxie na daga gefe tana kallonsu ta tsurawa bakin Deedah ido tana ganin ynda
yakewa fatyma faďa sosai sai ta soma jin haushinsa ta qara matsawa jikin yayarta ta kwanta
sosai tana kuka domin a ruďe take da sabon canjin da tagani tsakanin yayarta da yayanta, ita
kuka Iman kuka ba mai rarrashin wani har ya gama fadansa yasa kai ya fice, ta rungume fauxie
sosai a jikinta kamar wani xai kwace mata ita,

Ta karbi wannan jarabawar da Allah ke mata da hannu biyu tasan watarana sai labari amma ta
rasa gane kan mahaifinta da mijinta me suke nufi da ita?


Tun daga lokacin daga ita har Deedah suka ďauki fushi mai tsananin gaske da junansu,

Baxai shigo gidan ba sai gab da asuba, wanka kawai xaiyi ya fice daga gidan, abinci ma ya
daina ci a gidan tunda yanada saudah a ynxu,


Iman ma bata taba nemansa ba qoqarinta a ynxu na ganin ta Kula da rayuwar qanwarta Sau da
ke Dama fauxie kan tambayeta ina yaya.... ina yaya,


Takan xauna ita kaďai tayi tunanin rayuwar da take ciki sai dai tayi mgn a xuciyarta, inada
mahaifi kamar bani dashi Muna rayuwa a gida ďaya amma baxan iya kaimashi kuka na ya
sharemin ba, nasani akwai wani lokaci da xaixo Wanda *babana da mijina* xasu kasance cikin
tsananin nadama kan abinda suka min,

Har tsawon sati uku ba wani canji daga gareshi duk da shima kawar da kaine kawai yakeyi
amma yasan fatyma itace rayuwarsa wannan Faďan da sukayi yafi kowa damuwa,


A yau ta shirya tarbon mijinta, xata sauke duk wani fushi dake kanta ta bashi haquri tunda yace
ta kasance mai laifi a garesa ta wulaqanta budurwarsa, ko ba komai mijintane, mahaďin
rayuwarta kuma aljannarta tana tsananin buqatar mijinta a yau, tana wannan tunanin take haďa
masa abincinsa a dinning tanayi tana share kwalla dan batada tabbacin xaici ko baxai ci ba,

Anashi bangare shima haka, ya gaji da wannan fushin na matarsa, ko yana tare da saudah
bayajin daďi kamar yanda yake tare da Iman, yasan shi mai laifine a gurinta na kawo mata
budurwarsa har cikin gida Sannan ya rufeta da faďa, dole xai ďauke girman kansa yaje ya nemi
yafiyar matarsa,

Da Wannan tunanin ya qaraso cikin falo, tana xaune tayi kyau cikin wata atampha,sai ya tsinci
kansa cikin jin kunya da nauyinta ya kasa qarasawa cikin falon,


Qamshin turarensa ya sanarda ita xuwansa tana juyawa Kuwa ta ganshi tsaye,murmushi ta
sakar masa kamar ba abinda ya taba hadasu ta taso kamar yanda ta saba taryarsa,

Tsananin mamaki da jin daďi suka hana masa motsi daga inda yake tsaye musamman lokacin
da yaji ta rungumesa haďe da sumbatarsa a goshi, sai ya riqota sosai yana sauke numfashi da
sauri da sauri,


Ta jasa suka nufi sama, ruwan wanka ta haďa masa bayan ya fito ta taimaka masa ya shirya
cikin kayan barci kana suka nufi dining da kanta take ciyar dashi bayan sun gama ta soma
bashi haquri yayi Saurin rufe mata bakinta,


'Ni ya kamata na baki haquri Iman, ki yafemin ni nasan Mai laifine agareki a koda yaushe,
murmushi kawai tayi,


Ranar sun jima suna hira fauxie dama tuni ta dade da yin barci,


Bayan wani lokaci suka nufi bedroom ďinsu ga mamakinta Deedah addua kawai yayi ya
kwanta, sai ta kasa haquri ta fara masa qorafin fitar da yakeyi a da ynxu ya maidata ina yake
xuwa kwanakinnan Kuma meyasa baya nemanta?



Ya tashi xaune yana kallonta,

'inaji mun gama solving wannan issue dake tuntuni kan fita ta, aiki nake xuwa Kuma training
nake xuwa and what else did you want to know, idan ban fita na nemo ba so kike na xauna a
gida ina bata lokacina a banxa ko Kinsan yanda na sami aikin, kinsan wahalar danayi kafin na
sami aikin? Ki gayamin menene bana miki tun daga ci, sha sutura da sauransu, dame na rageki
a gidan nan fatyma?


Tsananin tsoro da kaďuwa yasa tana kallonsa da mamakin jin furucinsa, yau Deedah call her
with her real name, meke faruwa kada ya daina son tane a ynxu, nan da nan jikinta na soma
rawa da kyar ta iya buďa baki tayi mgn,


'xaman ka dani shine bata lokaci Deedah? Idan ban rasa ci da sha a gidan ka ba na rasa
soyayya da kulawarka, nima xn iya Kula da kaina da qanwata ta qarfin aikina ko babu kai da
babana Deedah..... ta soma hawaye sosai,

'har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login