Showing 42001 words to 45000 words out of 59977 words

Chapter 15 - BABANA DA MIJINA BOOK COMPLETE Fertymerh Zarah --.pdf

Unknown   

22 Mar 2025

4495

gaba ta riskesa saura qiris fauxie ta faďi hannunsa ai kuwa ta qanqameshi,

'ya mutu fa kace, Inna lillahi wa inna ilaihir raji'un,

Dai dai lokacin da Dr Fulani ta fito ďauke da jinjiri a hannunta sai kuka yake tsalawa, lafiyayyen
yaro dashi sak Deedah, kallo ďaya xakayi masa ka gane yaron Deedah ne ba inda ya barshi ta
ko ina,

Da sauri Sa'eed ya ajiye fauxie a tare shida Dr Deen suka nufi Fulani sai dai Deen ya rigashi
karban yaron,

Kukan da Fulani keyi shike ďaga hankalinsu, suka dubeta kuka take sosai,

'Ina Iman? Sa'eed ya tambaya Idanunsa akan ta,

Iman jikinta yayi tsanani sai suma takeyi tun ďaxu,

Jikinsu na soma karkarwa, fauxie ta qaraso tana kallon jaririn, farin ciki xaka gani bayyane a
fuskarta,

'yaya wannan baby anty ne? ya gyada kai yana kallonta,

Tayi cikin ďakin da sauri, alokacin Iman ta sami barci,

Dr Merah yayi ajiyar xuciya cike da tausayamata yana kallonta, haka shima Dr Bakori halin da
Iman take ciki ko kuka xaka iya yi mata,

Tana ganin Merah taje ta riqa hannunsa,

'uncle anty ta haifi baby, yana can inda yaya, Merah ya juyo yana kallonta fuskarta da yagani sai
da gabansa nayi tsananin bugawa, ya buďe idanu sosai yana kallonta,

'accident ne kome, me yajimiki ciwo haka a fuska? Tayi rau rau da idanu ta qara riqa hannunsa,

'baba ne ya dakeni, xaka ramamin,

'Ya salam lallai ba axxalumi irin Wannan mutumin, dubi fuskarta Bakori wannan yarinya xaiwa
irin wannan duka haka,

'kabari kawai Merah amma yarannan sunga rayuwa bama kamar fatyma dubi ynda ta koma
fisabilillah, basuyi dacen uba ba kam,

Suka fito a tare,
'Iman fa?
'ta sami barci,

Suka nufi emergency harda Sa'eed da fauxie, Fulani Kuwa ta wuce da jaririn a hannunta sai
kuka yaron yake sosai,


Sa'eed yaga gawar baba harda fauxie Kuma bata raxana ba batama gane baba bane tana dai
kallonsa ne kawai,

Dr Bakori ya dubi Merah,
'likita xo kagani kamar Ahmed ďin baya Numfashi,

Sukayi kansa da sauri har Dr Deen sai a lokacin Sa'eed ya lura da Wanda ke kwance,

Deedah, meya sami Deedah ya qarasa da sauri, tabbas shine jikinsa duk jini,

Iya ruďewa Sa'eed ya rude musamman da yaga Merah yaja farin kyalle ya rufe Deedah da shi,

'Deedah is dead Allah ya jiqansa ya gafartamasa shine abinda Merah ke faďi yana sharar
kwallah a fakaice, ya tsorata da mutuwar Deedah yana tuna xamansa dashi sanadiyar Iman

yasan irin alaqar dake tsakaninsa da Iman, yasan irin son da suke ma juna tabbas Iman tayi
babban rashi, ba uba ba miji a irin Wannan lokacin da suke tsananin buqatar taimako tunda
basu da uwa,

Inaji tun da Merah ke asibitin bai taba kuka ba sai wannan lokacin, duk dauriyarsa a yau ya
kasa yaja da baya yana sharar kwalla baxai iyaba jikinsa har rawa yake tunanin halin da Iman
xata kasance yakeyi,

Sa'eed ma baisan sanda kuka ya xo masa ba, abokinsa koma ince amininsa.....

Kukan fauxie da Merah sun tayarda hankalin fauxie ganin manyan maxa irin su na kuka ba
qaramin abu bane, duk da take qarama tana jin wani feeling a jikinta ba daďi, jikinta yayi sanyi
ta matsa kusa da Bakori tana kallonsa dan taji suna ambatar Deedah tasan shine kwance a
wurin taga sun rufeshi da xani, tasan haka akewa duk wanda ya mutu kamar yanda malam ya
sanarda ita,

Xuciyarta na soma bugawa fal fal numfashinta har wani sama yake,

'yaya ya mutu? ya gyada kai yana kallonta,

Shikenan ya tafi ya barsu, shikenan baxai dawo ba, shikenan baxai qara siyamata tedy, biscuits
da chocolate ba, shikenan baxai qara Wasa da ita suje yawo ba, shikenan baxasu qara cin
abinci tare ba, baxata qara ganinsa ba itada anty, ta juya tana kallonsu duk sunyi shiru, ta gigice
ta fita daga ďakin haďe da fashewa da irin Kukan nan Mai qara irin na yara, da ka ganta kasan
a gigice take batasan inda xataje ba,

A tsorace ta farfado daga barcin da take, xuciyarta na tsananta bugawa ta tuna Deedah da
yanda ta barshi, ta sauko daga Saman gadon da sauri haďe da fisge drip ďin da ake sanyamata
a hannu,

Mararta a qule take har lokacin tafiya take a hankali ba takalmi ba mayafi sai kallabi akanta,
kallon xararra ake mata a asibitin ga Waďanda basu Santa ba duk inda tabi sai an kalleta, kai
da kaganta kasan haihuwa tayi saboda xaninta duk jinine,

Nurses ďin da suka Santa suka biyo bayanta da sauri suna kiran sunanta, tanaji ta kyalesu sai
ta qara Saurin qafafunta musamman ynxu da take jiyo Kukan fauxie sai ta qara ruďewa,

Tun daga nesa ta tsinkayo fauxie na kuka a jikin Dr Deen, tana qarasowa ana fitowa da gawar
baba,

Ta tsaya cak tana maida Numfashi da kyar kamar wata zakanya jikinta sai karkarwa yake,
juyowar da xatayi taga anfito da Deedah, Sa'eed na bayansu yana sharar kwalla Idanunsa sunyi
matuqar ja,

Fauxie na ganin an fito dashi ta qara fasa ihu a gigice tana neman kwacewa jikin Deen, iman
Kuwa qarasawa tayi ta riqe gawar,

'meyasa kuka rufesa ai bai mutu ba, ku duba suma ne yayi, Deedah baxai mutu ya barni ba,
wannan lokacin Kukan da take harda majina ta xama wata xautacciya,

Duk qarfin hali irin na mutum idan yaga halin da Iman take ciki a Wannan lokacin sai ya xubar
da kwalla,

'Deedah ka tashi sugani su San cewa Baka mutu ba, Deedah ka tashi kaga yaron da muka
haifa, meyasa xakaje ka barmu a lokacin da muke tsananin buqatar ka,

Taje ta riqe Merah,
'kace su dawo dashi acigaba da kula dashi anan, Deedah bai mutu sai idan kune xaku kashe
shi,

Fulani ta qaraso da jaririn a hannunta har lokacin kuka yake kamar yasan abinda ke faruwa,
tunda ya faďo duniya yake kuka,

Kukan yaron har cikin kanta take jinsa, ga Kukan fauxie dake qara rikita kwakwalwarta, tana
ganin lokacin da suka sanyasu a mota ta tabbata lallai gida xa'a je dasu ayi masu wanka da
sallah akaisu makwancinsu, shikenan Deedah yaje yabarta.....


Cak numfashinta na ďauke, sai ta xube gurin a sume....




My wattpad Phertymerh1

*Babana da mijina*


©Fertymerh Xarah


34


*Masu turo ta'aziyar Deedah, iman na godiya sosai, saqonku ya iso*.

Tana xubewa gurin su Dr Umayma sukayi kanta, fauxie na ganin lokacin da ta faďi ta soma
neman saukowa jikin Deen tana kuka amma ya riqe ta tamau sosai a jikinsa,

Aka sanya gawarsu a motar Sa'eed, shi yaja motar su Merah na bi bayansa da nasu motocin,

Iman Kuwa motar Dr Deen aka sanyata tare da sauran likitocin fauxie na kusa da ita fuskarta ta
qara kumbura tayi jawur ga ciwo ga kuka, kanta har nauyi yake mata ga wani Xaxxabi da take ji
wannan karon baxata sami kulawar Iman ba cos ita kanta bata cikin hayyacinta, mutuwar
mahaifi da miji a lokaci ďaya (it's the greatest loss of all losses),
A Wannan ranar xo kaga jama'a, mutane kamar me, nan da nan gari na ďauka mutuwar Alhaji
Abdallah abinka da ďan siyasa sananne a gari,

Mutuwar taxowa mutane a baxata daga shi har Deedah ba Wanda aka yiwa tsammanin mutuwa
a ynxu,

Abokan Deedah suna cikin ruďani da tsoron Allah, duk Wanda yace shine yau ba shi bane
gobe, mutuwar sa ta girgixa shi idan suka tuna jiyama suna tare dashi a office, ya sami
kyakkyawar Shaida daga garesu,

Ma'aikatan gidan maza da mata tamkar sune akayiwa mutuwar, kuka suke sosai sun san
qarshen barin su gidan yaxo, ba uban gidansu to Waye xai riqa biyansu Waye xai riqa ciyar
dasu, wasu ma da gidan suka dogara,

Sa'eed da kansa yaje part din baba ya rufe ďakunan sa na dukiya, mutanen ynxu basu da
amana wani baxaiji tsoron ana cikin wannan tashin hankali ba suje yiwa marayu sata wannan
ne dalilin dayasa ya rufe,

Anje yiwa gawarwakinsu wanka, a Wannan lokacin fauxie na rakube a bed side kanta a
langabe, barci take daga xaune tana gyangyaďawa kamar xata faďi,

Iman Kuwa tana xaune da jinjirin a hannunta tana bashi mamma, ance kuka ma rahama ne
Wannan Karon kam Kukan yaqi ya xo xuciyarta a bushe take, kallon jaririn take,

Yaxo a MARAYA, yaxo duniya babanshi yabar duniya, kakanshi ma yabar duniyar, duk da haka
yaronta baxai taso cikin maraici da rashin gata ba, xata bashi tarbiya ta kula dashi shida fauxie
tamkar Iyayen su na raye, bata da sauran buri a rayuwarta ynxu na ganin ta Kula da marayun
biyu, ta sauke nauyin dake kanta akansu, aure baxata sanyoshi gaba ba aynxu a tsorace take
da kowane namiji da halayyarsa, xata cigaba da rayuwarta a hakan, Wanda take so ya tafi
yabarta tana roqon Allah ya sa shine mijinta ko a lahira,

Sai a lokacin hawaye na samu xubowa daga idanuwanta ta rumtse idanuwanta suka xubo akan

fuskar jaririn Wanda ke barci tuntuni,

Fulani ta karbi yaron ta goya, sai Iman ta maida kanta jikin cinyoyinta tana kuka sosai,

Sanda aka gama masu wanka aka Kira Iman tayi masu addua, kuma tayi cikin jarumta da
dakewa irin tata, ba Wanda batayiwa addua ba acikinsu, tana gani aka ďauki gawarsu,

Sai ta bisu da ido idanunta taf da hawaye fuskarta ďauke da murmushi,

'I know Deedah must come back to me, ni nasan bai mutu ba, nasan Deedah baxai je yabarni
ba, bayan yace xamuyi rayuwa tare mu raini jaririn mu tare,

Xuciyarta ta cigaba da bugawa lokacin da aka fita dasu, taga yawan jama'ar da suka cika gidan
sai taja jikinta ta koma ta xauna, tana bin mutanen dake falon da ido tana kallonsu suna kuka,

Bataga dalilinsu na kuka ba, Wanda suke wa kuka xai dawo tasan xai dawo, xai dawo..... xai
dawo haka kwakwalwarta ke bata

Sai ta fashe da dariya, duk gurin aka juyo ana kallonta, ko miye abin dariya ga Wanda akayiwa
mutuwa?

'lafiyar ki kuwa? Cewar salima tana kallonta cikin tsananin mamaki,

'tor miye amfanin Kukan da kuke, baba ne kawai ya mutu banda mijina, nasan Deedah yana
raye, ynxu xaku ganshi ya dawo xaiyi wanka yayi shirin xuwa masallaci bara naje na fidda
mashi kayan da xai sanya a yau, ta tashi tayi ďakin sa,

Mutanen falon suka kalli juna cikin tsananin mamaki, Fulani tabi bayanta da sauri,

Ta juyo da kafadunta suna fuskantar juna,
'Kinsan me kikeyi fatyma, me kike son nunawa mutane, baki yarda da qaddara bane keba
musulma bace?

'my husband is alive Dr Fulani, Kune keson kashe sa, jiya fa muna tare, yau ma munyi mgn
dashi, ya roqeni gafara Kuma na yafe masa, shine fa ya suma kuke kiran ya mutu,

'Wanda ya mutu baya dawowa Iman, kada ki ruďar da kanki, ki nutsu dan Allah kada wani abu
ya sami kwakwalwarki, dan Allah fatyma kixo muje falo kicigaba da yi masu addua, kinga ga
yan uwanku ma suna ta xuwa.

Iman tayi shiru Kamar mai naxari sai Kuma ta dubeta,

'tell me Fulani idan Marhoom ne ya mutu me xakiji?

Sai da xuciyarta na buga ta gyara goyonta tana kallonta,

'me ya kawo wannan mgnr Kuma? Idan ma mutuwa yayi haquri xanyi nayi tawakkali ga Allah,
nasan yafini sonsa Kuma nasan yafiye masa duniya daďi,

Iman ta girgixa kanta,
'you are not saying the truth Dr fulani, baxaki iya jurewa ba, bakisan xafin dana keji a xuciyata
ba, bakisan ciwon da Mace take ji idan ta rasa abokin rayuwarta ba, ballantana irin nawa rashi
na *babana da mijina* a lokaci ďaya, ta soma hawaye sosai,

ta juya tana ciro kayan Deedah,
'ni nasan bai mutu ba xaki ganshi sun dawo dashi,

Fulani tayi shiru tana kallonta cikin tausayawa, itama ta tsinci kanta cikin kuka sosai ta fice daga
ďakin da sauri.

Haka Iman ta fito da kayansa, juyowar da xatayi tayi arba da tangamemen hotonsu dake manne
a ďakin, yana rungume da Ita suna yiwa juna murmushi, sai ta saki murmushi tana faďin,

'Haba taya ma xasu ce Deedah na ya mutu, nasan xaka dawo kaxo kabasu mamaki su san
cewa kana raye......


An kaisu makwancinsu an rufesu daga su sai halayyarsu sai abinda suka shuka a duniya, in
hairan hairan in shairan shairan, wani abin tsakaninka ne da mahaliccinka, idan ka kasance mai
tuba agaresa,

Duniya kenan....

Babu dukiya aciki, babu gida mai tsada, babu mota mai tsada, babu abinci mai tsada, babu
lallausar katifa mai taushi da tsada, babu Mulkin da ake taqama dashi,

An kaika inda xaka xamo abinci ga tsutsoci, qasar da kake taki da takalmi yau kaine acikinta
timbir, babu mai ceton ka aciki sai Allah, sai aikin da ka aikata a duniya, ya Allah ka tsare mu da
azabar kabari, kasa muyi kyakkyawan qarshe mucika da imani Amin.

Sa'eed kuka yake sosai Idanunsa sunyi jawur, shikenan Deedah yaje ya barsu, baxasu qara
ganin Deedah ba, yayi rashin aboki, Allah ka gafartawa Deedah ka Kai haske a kabarinsa
kamar yanda goshinsa yayi haske lokacin da suke masa wanka,


Suna dawowa jana'iza suka nufi gidan, tun daga waje suka fara gaisuwa ga mutane birjik an

shimfida Manya Manya tabarma saboda masu gaisuwa, yan uwan su Iman ne a waje da suka
xo,


Kai tsaye su Dr Merah suka nufi falon Iman domin yi mata ta'aziya, tana ganinsu ta tashi da
sauri ta nufesu, sai leqen bayansu take burinta taga Deedah a bayansu amma wayam,

Ta dubi Dr Merah, Dr Deen, Dr Bakori, Sa'eed, sai taga suna hawaye kowane na jin nauyin
haďa ido da ita a yau, bakinsu yayi nauyi ga duk kalmar da xata fito bakinsu,

'Banga Deedah ba likita, ina kuka barshi?

Merah yayi qarfin halin mgn, Idanunsa akan nata,

'Dama Wanda ya mutu yana dawowa ne Iman? Deedah is dead, Deedah has gone and he will
never come back, ya tafi ya barmu dole haquri xamuyi da wannan rashin Allah ya fimu sonsa
mutuwa na kan kowa,

'wace mgn kakeyi likita, Kada kace min da gaske Deedah na ya mutu, ya tafi ya barni nida
qanwata, ya tafi yabar jinjirinsa, dan Allah kace masa ya dawo, yaxo ga kayanshi ya Sanya yaje
jumma'a, ta juya tana neman inda ta ajiye kayan,

Kai da kaganta kasan bata hayyacinta a ruďe take, inbashi ba, mace kamar Iman Mai kunya da
kawaici, Mai haquri da tawakkali, Mai hankali da nutsuwa, yasan da hankalinta baxata tsaya
gabansa tana wannan mgn ba ynda take matuqar girmamashi,


Gabaki ďaya falon suka ďauki kuka, Dr Deen ya fita da sauri shida Sa'eed baxasu jure ganinta a
Wannan halin ba,

'ki nutsu fatyma, Merah ke gabanki, baxan maki qarya dan na cutar dake ba kinsani, Deedah ya
tafi inda baxai dawo ba Kinsan miye mutuwa please pray for your father yana buqatar addua
sosai akan Deedah, Deedah ya tafi cikin kyakkyawan qarshe fuskarsa kaďai xata Shaida hakan
da ynda jikinsa yayi kyau, ki roqa masu gafara ki masu addua, please fatyma ki nutsu,
Nan da nan jikinta na soma rawa sai karkarwa take sai ga hawaye sharrrrr,

Shikenan da gaske Deedah ya tafi,

Bakinta na rawa ta nemi gurin xama da kyar tana faďin,

'Allah ya jiqansu, Allah ya gafarta masu, Allah ya haskaka kabarinsu,

Duk falon aka ďauki Amin, wasu Kuwa suka fashe da kuka......


*Babana da mijina*


©Fertymerh Xarah


36


_Congratulations for the completion of ur book Rabi'atu Sk Mashi, MATATA CE, ko ina xanga
Rabi'atul Adawiya? Nagode da qaunarki,_


_mistake page 35 in babana da mijina, ban sani ba ko tsananin ruďewa ce tasanya Iman
sallah bayan ta haihu, it's a mistake pls._




Da kyar yaja qafafunsa yabar gidan, duk jikinsa a sanyaye yake har ya iso gidansa,

Sai da yaje ya duba mahaifinsa har lokacin barci yake kafin ya koma side ďin sa, kwanciya tayi
haďe da lumshe idanuwansa, fuskarta yake gani, murmushinta wani abu ne mai girma a
xuciyarsa, da alama tana matuqar son yaron ya gani a kwayar idonta don haka yayi alqawarin
Kula da Ita da yaron kamar shi ya haifesa, da Wannan tunanin barci ya ďauke sa,

Sa'eed Kuwa yana xuwa gida ya sameta xaune a falonsa tana jiransa, cikin wasu irin shu'uman
kayan barci, rabonta da sanyasu yana ji tun farkon aurensu, ya ďauke kansa cikin basarwa
kamar bai ganta ba yayi hanyar ďakinsa ta biyosa tana faďin,

'ina kaje da wannan daren Abban Adnan,

Yau kuma har wani Abban Adnan ya samu ya raya hakan a xuciyarsa shi da ake kira da xallar
sunansa Sa'eed,

Bai dubeta ba bai Kuma tankata ba ya hau gadonsa yayi kwanciyarsa fuskarsa ba walwala
hakan yasa take tsoron tunkararsa Kada ya sauke fushin akanta, sai ta soma mgn a hankali,

'Dan Allah ina kaje, Allah yasa ba gurin wata kaje ba dan bansan yanda xnyi da xuciyataba,

A

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login