Showing 6001 words to 9000 words out of 59977 words

Chapter 3 - BABANA DA MIJINA BOOK COMPLETE Fertymerh Zarah --.pdf

Unknown   

22 Mar 2025

4489

ce budurwa bayan nurses da yawa sun girmeta wasu Kuma age
mate ďin tane, tana da maneman aure da yawa but she don't have interest on them, ta kunna
fitilar ďakin tana kallon fauxie,

Abubuwa da yawa take tunawa game da rayuwarta da qanwarta, komai suke so suna samu
kuďi da jin daďi, haka komai yi masu akeyi, tun daga kan girki, wanki, shara, kula da gidan da
komai ma baba ya Sanya masu yi masu, sai dai sun rasa kulawarsa basu samun Isashen lokaci
daga garesa, kullum yana hanyar tafiya baya ďebe masu kewar UWA, hawaye suka sumulyo
mata, ta qanqame qanwarta dole tayi aure kodan farin cikinta da qanwarta, dole tayi aure ko
damuwarta xata ragu ta sami soyayyar miji tunda bata sami ta iyaye ba.......

Washe gari tare da Fauxiya suka nufi asibiti, sai tsalle take tana jin daďi, nurses ďin dana Santa
suka soma murmushi,

Yau Fauxiya a asibiti, Ashe akwai rigima..
Fatyma murmushi kawai take hr suka iso office ďinta, ta ajiye Jakarta juyowar da xatayi ba
Fauxiya ba dalilinta, dama tasan a rina,

Ta xauna tana duba files ďin patient ďin da xata duba na ranar, sosai ta dade akansu kafin ta
gama, shiru ba alamar fauxie, ta tashi tabi bayanta inda take xato nan ta sameta office ďin Dr
Merah tana xaune a gefensa da sweet a hannunta sai surutu take masa yana duba patient
ďinsa, sai kayi xaton yar sa ce ta cikinsa
Bata Bari ta ganta ba ta juya da sauri ta nufi a&e,

Su biyu ne aciki shida abokinsa Sa'eed gurin aikin su ďaya a bank,

Da Sallama ta shiga idanunta sanye cikin farin glass, hannuwanta a aljihun Labcoat ďinta, sosai
tayi kyau,

Suka amsa sallamar suna kallonta, bata yarda sun haďa ido ba, drip ta xubawa idanu tana
tambayar ya Mai jiki,

Sa'eed ya amsa da jiki Alhamdulillah, ta maida hankalinta kan haďa masa magani,

Sa'eed ya tashi yana fadin,
Aboki is olmost tym, by 8 xn dawo, ya gyada Kai yana kallonsa kafin ya fice,

Dr. Save a life.... taji ya faďa daga inda yake kwance, kusan faďuwa ta tashi yi, batasan meke
damun patient ďin ta ba, hr lokacin bata tanka ba sai ma qoqarin yaqi da xuciyarta takeyi, ta
juyo haďe da miqa masa magani ya karba, ta ďauko masa swan ta bashi hr lokacin bata kallesa
ba shikuma Idanunsa akanta, bayan ya gama sha, ta duba file ďin sa yana da sauran allura
uku, ta dafe goshinta da hannunta.....

A duniya idan akwai abinda Deedah ya tsana allura, indai akan allura ne yana da rakin wannan,
bai tsoron bindiga kamar yanda yake tsoronta..

Yana Ganin ta ďauko allura ya tashi xaune, wannan Karon fuskarsa a yamutse,

Ummi bana son allura, na roqeki karki min, ta juyo da mamaki tana kallonsa Abinda ta gani a
idanuwansa ya nuna mata yes he mean it, baya son allura, batayi mamaki ba cos tasha samun
case irin Wannan, tayi far da ido bayan ta cire glass ďin idonta,

Ni Kuma sai nayi ma allura, Iman not Ummi pls.... dai dai lokacin Merah ya shigo tare da
Fauxiya a bayansa,

Ta juya tana kallonsa bayan ta sanardashi abinda ke faruwa, Merah ya karbi allura,

Haka mukayi fama dashi jiya, gashi namiji har namiji amma yana tsoron allura kibari xnyi
masa....

So funny, ta soma dariya sosai ba kakkautawa Wanda rabonta da irin dariyar tun Mami na da
rai, shi kansa Merah ta bashi mamaki bai taba xaton tana dariya haka ba, taja hannun Fauxiya
suka fita,

Daga inda take xaune take jiyo rigimarsu da Ahmed Wanda da kyar da suďin goshi yayi masa
suna xaune Merah ya fito,

Kinyi laifi likita, yiwa patient dariya,
Am sorry bansan yanda xnyi bane.....ya fice ta tashi ta shiga ďakin, suna haďa ido ta ďauki wata
dariya harda sa hannu tana rufe bakinta, Fauxiya bata San komai ba amma sai ta taya yayarta
dariya Wanda ya janyo hankalin Deedah xuwa gareta

Itama farace kamar fatyma sai dai tafi fatyma kyau sosai, ita yarinyar wacece ko yar'ta ce,nooo
ai yaji jiya tace ita da qanwart..... tunaninsa ya Katse lokacin da yaji fauxie na faďin

Anty meyasa kike dariya, tayi shiru tana faďin ba komai,

Please tell me sister.... ta juyo tana kallonta cikin xare ido
Nace babu menene...
Fauxie tayi shiru tana kallonta ta juya tana faďin ki jirani Ina xuwa idan naxo ban same ki ba sai
na dake ki Kuma baxan qara xuwa dake ba,

Tana jin haka ta nemi guri ta xauna,ta juya ta fice, Idanunsa akan su suna haďa ido da ita tayi
Saurin ďauke kanta cikin jin tsoronsa saboda raunin dake goshinsa,

'little girl..... ta juyo tana kallonsa,
'Your name...da kyar ta iya buďa bakinta
'Fauxiya Abdallah... ya gyada kansa,
'xo kiji Fauxiya, kamar baxata je ba ta matsa kaďan a tsorace,
'how old are you? Idanunta suka yi rau kamar xatayi kuka,
'6yrs...
Ya xare ido yana kallonta da mamaki, yanayin ta ya nuna a tsorace take dashi sai ya janyota
xuwa jikinsa ya ďorata akan qafafunsa, da sannu ya riqa janta da Wasa harta saki jiki sosai
dashi tana dariya hrda kwantawa a jikinsa,

'Ya sunanka....
'Kice yayaaa,
'yaya xakaje dani inda mamin ka, ya girgixa kansa
'A'ah
'meyasa ?
'mamina tana duka sosai...
'to ni baxan je ba...
'kina so ki xauna dani, mu riqa wasa tare... ta gyada kai da sauri

'idan ummi taxo Kice ta aureni,
'Wacece ummi, yayi shiru kafin
'yace your sister... ta soma dariya tana kallonsa,
'ita ba Ummi sunan taba kace Anty Iman dai dai lokacin ta shigo,idanunta na sauka akansu, ta
ďaure fuska tana kallon Fauxiya, yanayinta ya sanyata saukowa a jikinsa da sauri tana faďin,

Anty shine ya ďorani, Wai sunansa yaya..
'kisa takalmi kixo muje inba haka ba xn tafi na barki anan, ta sanya takalmin da sauri tana faďin,

'Anty Wai inji yaya ki aure sa, yace ku..... ta katseta cikin tsawa..
'shut up Fauxiya... tayi shiru tana kallonsa kafin ta maida kallonta gareta, da qarfi ta fisgi
hannunta suka fice, tabe bakinsa kawai yayi ya maida Idanunsa ya lumshe...

BABANA DA MIJINA

©Fertymerh Xarah

8

Tun bayan barin ta asibitin bata qara xiyartar ďakin da aka kwantar da shi ba, sai ma ta
damqawa Dr Fulani file ďinsa,

Iya damuwa Ahmed yana ciki, he mean it yana sonta, aurenta yake son yi, duk da baisan ita ko
Wacece ba amma ta kwanta masa a xuciya,

Ranar da aka sallamesa yaje nemanta, Dr Ummi.. Dr Ummi nobody knows her... ba Wanda
yasan sunan Acikin likitoci, hassalima ko a nurse sai dai ummu an kaishi inda take yace ba Ita
ba.....

Real name ďinta ne baxai iya faďi ba saboda nauyin sunan a bakinsa, amma ya kamaninta
yake?

'Yace ita farace, doguwa Mai matsaikaicin jiki, tana da tawwadar Allah a fuska Kuma tana da
qanwa Fauxiya,

Dr Umayma tayi murmushi sanin ko wacece,
'Sunanta fatyma not Ummi,
'I know doctor, sunan ne baxan iya faďa ba yana da matuqar muhimmanci a guna...
'duk da haka Ahmad, idan xaka shekara anan asibitin kana Ummi baxaka taba samun ta ba,
murmushi yayi bayan ya kishingiďa....

Alhaji Abdallah abubuwa sun soma damunsa tun lokacin da matsafarsu ta nemi fatyma tayi
aure suna son jariri daga gareta, sosai ya shiga tashin hankali sanin fatyma bata da wani

tsayayye a ynxu,

Sanda ya tunkareta da Mgnr ya ga damuwa qarara a fuskarta Wanda ya Sanya baiji daďi ba,

'ba dan komai nakeso kiyi aure ba fatyma sai dan ni babban mutum ne ďan siyasa da mutane
suke kallo da daraja, da yawa mutane sun San matata ta mutu bani da aure inada babbar ďiya
kamar ki a gida xa'a soma xargin na hana maki aure,

'bayan Wannan fatyma aure daraja ne dashi, ni kaina xanji daďi idan kikayi aure Inaso nasami
jikoki daga gareki, ballantana ma baxamu rabu ba xamuyi rayuwa a gida ďaya dake, wancan
gidan naki ne halaq malaq aciki xaki xauna da mijinki da yaranki...... ta goge hawayen fuskarta

'na fahimceka babana, abinda kake so Inaso dan na farantama kamar ynda kake min, nayi ma
alqawari xn fitar da miji Acikin kwanankinan, ya faďaďa murmushinsa cikin jin daďi ya soma
sanya mata albarka....

Bayan tafiyarta ya faďa cikin tunani, shikenan rayuwar yar'sa ta shiga cikin hatsari kenan, ita
baxata taba haihuwa ba Kamar ynda sima ta faďa duk tayi ciki xasu ďauke yaron da haka xai
cimma burinsa na xama shugaban qasa, hawaye suka xubo wannan wace irin rayuwace.....

Bayan barinta gurin ya shiga cikin tsananin tashin hankali, batasan wa xata fitar ba tsakanin
manemanta, gwargwado kowa nayi mata soyayyar gsky sai dai batasan meyasa xuciyarta tafi
karkata da Ahmed ba, a kullum sai yaje asibiti ya ganta kafin yaje gun aiki, har nan gida yake
xuwa su dade tare da Fauxiya, akwai abubuwa da yawa data duba Wanda yasa ta xabi Ahmed
a matsayin mijin aurenta,

He is happy too sanda yaji umminsa ta amince xata aure sa,

Cikin qanqanin lokaci soyayyarsu tayi nisa sukayi matuqar shaquwa da juna, baba ya aminta
dashi bayan dogon bincike da akayi akansa wurin aiki, basu gane komai ba kasancewar
abokansa na hulda daban, na gurin aiki daban sai suka bashi shaidar gsky....

Bayan auren su ne abubuwa suka soma yi mata yawa tun daga kan mahaifinta da mijinta,

Mahaifinta baxata Kai Kukan mijinta ya duba mata ba saboda ba maxauna bane, idan ma yana
gari tor baxata ganshi ba sai cikin dare akwai wani ďakinsa da yake shiga Wanda ba Wanda ya
taba shiga acikinsa, idan yana ciki ba Wanda ya isa ya shiga haka ma baxai fito daga ciki ba sai
cikin dare da jajjayen kaya wani sa'in ma da abokansa suke shiga,
Mijinta Kuma idan ya fita aiki tun safe baya dawowa sai marece, daga nan xaisa kai ya fice
baxai dawo ba sai cikin dare Wai yaje training ďin kwallo, can you imagine?

Sau biyu Ina samun ciki yana xubewa Wanda na rasa dalilin haka a matsayina na likita, nayi

bincike iya bincike na kasa samun dalili komai nawa normal, Inaso na sami babana Kan Mgnr
koxai taimakamin da wani abu amma baxai saurareni ba cos he is busy, mijina ma yakan nuna
damuwarsa idan ya xube bayan kwana biyu kuma shikenan xai bar mgnr,ban San waxan kaiwa
kukana ba,waxan gayawa damuwata ya taimakeni da shawara kodan mijina...
Na kasa samun soyayyar mijina, ba kulawa kullum busy busy shine maganarsa a duk lokacin
danayi masa qorafi, na kasa sabawa da wannan hali na *babana da mijina* Kuma ban taba
xarginsu ba ko bincike akansu, duk da Allah s.w.a yace LA TAJASSASU
WALA YAGTABBA ADUKUM BAADAD kada kuyi
bincike kuma kada sashenku yariqa cin wani
sashe ma'ana kada wasu mutane su xauna
gulmar wasu mutane.....

Shine Asalin labarin.........

BABANA DA MIJINA

©Fertymerh Xarah

9

Dawowa daga labari ~~~

Tafito daga toilet bayan ta ďauro arwalla, inda yake ma bata kalla ba ta sanya hijab ďinta ta
fara sallah,

Deedah na daga kwance yana kallonta sai ya sami kansa da saukowa ya shiga toilet yayi
arwalla ya bi ta...

Bayan wani lokaci sun gama ta tashi batare da ta cire hijab ďin ba taje ta kwanta haďe da juya
masa baya, jikinsa a sanyaye ya tashi yayi light off yabi bayanta ya kwanta haďe da juyo da Ita,
she is crying....

'why Iman, meke faruwa? Ko motsi batayi ba illa hawaye dake qara xuba a idanuwanta... Ya
cire mata hijabin haďe da qanqameta,

'I hurt my Iman, kiyi haquri akan Wanda kike,i hurt you and I will change, I promise to change
Iman ya qara matseta jikinsa, har lokacin bata tanka ba illa qoqarin kwace jikinta da take yi,

Ya tashi xaune yana kallonta,
'why ol dis...., me Kuma nayi Yanxu, nayi tunanin mun gama mgn dake tun a falo, ta tashi tana
kallonsa sai Kuma taji ta kasa furta masa komai saboda bacin rai da damuwa, he knows it
yasan damuwarta duk baxai wuce fitar dare da rashin bata haqqinta ba, tor ya xaiyi shi kansa a

ynxu baya so yana nadamar xama barawo bayan ga aikinsa, idan yayi yunqurin barin aikin oga
nas xai ďauki mummunan mataki akansa kamar yanda ya faďa,

Kallonta yake yana observing da ido da xuciya, gaba ďaya yanayinta ya sauya ya nuna wata
mace dake axabtuwa da soyayya da sha'awa Mai yawa,

Amma kawaicinta da kau da kai ya rinjayi komai, tana haquri dashi shi kansa ya Shaida, ba
kowace mace xata xauna da miji haka ba shiyasa yake qara son ta, ya riqo hannunta Idanunsa
cikin nata,

Baxan gaji da baki haquri ba, ki yafemin Iman, xnyi qoqari na rage fitar I promise you.....

*

Washe gari bayan ta tashi daga barci tayi miqa a hankali tare da koro addua,
_Alhamdulillahil lazee ahyana ba'adama amatana wa ilaihir nushour,_ ta miqa hannu side ďin
Ahmed taji sa wayam, ta buďe idanuwanta,
She is late, da sauri ta diro ta faďa toilet inda ta same sa ciki yana wanka,

A tare suka fito kowane ďaure da towel, ita iya cinyoyinta shi Kuma iya qugunsa, jikine dashi na
Manya Kuma qasaitattun maza,

dogo ne sosai Mai kyau sura ta ko'ina, a tare suke shirinsu, qoqarinsu kada suyi lattin fita,

Wardrobe ta buďe ta ďauko mashi baqaqen Spanish suit Mai haďe da farin tie, ta ajiye masa
akan gado kana ta soma shirinta cikin riga da zani na Atampha ta ďora labcoat akai da ďan
qaramin gyale tayi rolling, idanunta sanye da farin glass, lokaci ďaya suka gama shirinsu, yaja
dogon hancinta in appreciation ďin irin kulawar da take mishi,
'kinyi kyau dear Allah ya barmin ke, murmushi tayi haďe da manna mishi kyakkyawar sumba a
qirji ya qara rungumeta,

Yana riqe da hannunta suka sauko step dai dai lokacin da Fauxiya da mai Kula da Ita suka fito
tana ďauke da qatuwar school bag ďin ta, murmushi tayi lokacin da suka haďa ido da Ahmed,

'morning sister...
taje da gudu ta rungumeshi tana fadin
'morning yaya... ya ďauke ta yana murmushi haďe da Jan hancinta,
'morning my baby....

Dijeh ta gaidasu kana tayi waje da jakar Fauxiya,

A tare suka xauna akan dining table, Fauxiya baxata tsaya guri ďaya ba, idan taci na wannan ta

dawo taci na wannan da haka hr suka kammala suka fito su uku a tare,

Driver na jiran Fauxiya kai tsaye ta shiga motar tana ďaga masu hannu suma suna mata bye
bye, suka kalli juna haďe da yin murmushi ta shiga motar ta shima ya shiga tasa,

Tana gaba yana biye da Ita hr suka xo FMC birnin kebbi, sai da yaga shigarta kana ya juya tasa
motar xuwa first bank dama kullum sai ya rakata yaga shigarta asibiti yake tafiyarshi.

BABANA DA MIJINA

©fertymerh Xarah

10

Alhaji Abdallah xaune a qasaitaccen falon sa duk abin duniya ya dame sa ya rasa inda xai
tsoma ransa yaji daďi,

Sau biyu yana ďaukar cikinta yana bayarwa ga matsafarsu Gashi wani bincike ya nuna Iman
tana ďauke da wani cikin Wanda daga ita hr Ahmed basu San dashi ba,

Sima ta nuna tana son cikin, tabbas Wannan ma sai ya xube, shin haka rayuwar yar'sa xata
kasance bata haihuwa da tasami ciki ya xubar? Yayi wa kansa wannan tambayar,

'Nooooooo ya faďa a hankali gudun securities ďinsa su jiyosa, Idanunsa sunyi jawur har jijiyoyin
kansa sun fito goshinsa raďau raďau,

Yana son Fatyma yana tsoron wani abu ya sameta musamman a mahaifarta amma ya xaiyi
mecece mafita?

Yayi shiru Idanunsa suna fitar da kwalla lokacin dayaji muryar sima na faďin,
'cikin mukeso Kuma dole abamu idan ba haka xamu ďauki rayuwarta gaba ki ďaya mu baka
dukiya da Abinda kake so na duniya..... Aka kyalkyace da dariya, yayi firgigit daga tunanin da
yake yana kallon falon dariyarta ce kawai yakeji ta ko ina......,

*

Fitowar ta kenan daga ďakin haihuwa, yau a gajiye take sosai tunda taxo bata xauna ba, ga Jiri
da Xaxxabi da take ji Wanda baida nasaba da yunwa anata tunanin kenan,

Ta sami gu ta xauna inda ta sami Dr Fulani, ta dafe goshinta da hannuwanta biyu,

Successful doctor..... yanda suke kiranta idan suna tsokanarta cos da wuya ta karbi haihuwa da
hannunta yaron ya mutu ko uwar sabanin wasu likitocin da har jima yaro sukeyi gurin haihuwa,

a yanda take a natse haka ma take aikinta a natse shiyasa nurses da yawa suke son aiki da Ita,
ba ďaure fuska ko Wulaqanci kowa faram faram take dashi bama kamar patient ďin,

'ya akayi Dr fatyma...cewar Fulani tana kallonta,

Ta ďan ja guntun tsaki kafin ta janye hannunta a goshinta,
'bansan meke damuna ba yunwa ko gajiya... Fulani tace
'harda damuwa fatyma, tor ya xakiyi da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login