Showing 45001 words to 48000 words out of 59977 words

Chapter 16 - BABANA DA MIJINA BOOK COMPLETE Fertymerh Zarah --.pdf

Unknown   

22 Mar 2025

4480

fakaice ya ďan dubeta cikin mamaki bai bari sun haďa ido ba ya ďauke kansa, tana sonsa ne
bata iya Kula da shi,

Ganin baxai tankata ba ta kwanta a qirjinsa, da sauri ya juya mata baya haďe da Jan dogon
tsaki, Hakan da yayi hankalinta yayi matuqar tashi tasan idan Sa'eed yayi mata haka to yana
fushi da itane,

'kayi haquri ďaxu wasa nake ma xnyima tausa ďin,

'karki kuskura ki tabamin jiki, inba haka ba ranki xai baci... duk wannan mgnr da yake fuskarsa
ba walwala,

Nan da nan ta soma hawaye tayi xaune xuruu tana kallonsa, tana gani ya tashi ya kashe wutar
ďakin Kafin ya dawo ya kwanta batare da ya kalleta ba, hankalinta ya tashi sosai ta tashi tabar
ďakin ta nufi nata, ranar barci a idonta sai dai barawo....

Sa'eed Kuwa barcinsa duk na Iman ne, yana tare da Iman, ya tashi yana adduar Allah ya bashi
Iman su kasance tare cikin farinciki da kula da junansu.


Iman Kuwa tana shiga ďaki ta shimfide yaron, ta gyarawa fauxie kwanciyarta anan taji jikinta
xafi rau, ta manta da taci abinci batasha magani ba, gefen fuskarta ma ya fara ďebe kumburi,
tausayin yarinyar ya kamata,

Taya akayi fauxie ta fita wayo da dabara, Ashe surutunta bana banxa bane, sai komai yake
dawo mata sabo, lallai fauxie ba qaramin namijin qoqari tayi ba dan da baba bai gayamasu
komai kafin ya mutu ba da baxatasan komai ba,

Ashe da gskyr Deedah da yace fauxie ce ajalin baba, sanda yayi furucin taso ta tambayesa
dalili amma ta manta, Ashe Deedah yasan baba matsafine amma bai taba gayamata ba sai
Faďan da sukayi na qarshe dashi inda yake cewa, *gwanda xama da barawo akan xama da
matsafi..*,
Inama Deedah ta xai dawo, xata xauna dashi a matsayinsa na barawo, tana son mijinta fiye da
tunanin mai karatu,

*Babana da mijina* sune jigon rayuwata, yau babu su daga ita sai qanwarta da ďanta... ta soma
waige waige a ďakin kamar xataga Deedah, dama a irin wannan lokacin yake dawowa gida, ta
tashi da sauri tana kallo ta window gani take xataga motar mahaifinta ya dawo, xuciyarta ta
kasa amincewa da mutuwarsu, meyiwuwa xasu dawo Gobe a tunaninta sunyi tafiya ne tadawo
cikin ďakin har lokacin hawaye take,

Magani ta ďauko da ruwa taxo ta tayar da fauxie,

Kuka ta fara, tayi saurin toshe mata baki da hannu gudun kada ta tayarda jaririn,

'yi shiru karki tayarda baby, magani xaki sha sai ki koma barcin,

'anty baxan sha ba.... ta qara kwanciya idanunta a lumshe, Iman ta riqo hannunta haďe da
sunkuyawa dai dai fuskarta,

'please babyn yaya, idan kinsha magani yaya will be happy, kuma xakiji sauqi kafin ki koma
Skul fuskarki xata dawo dai dai, your friends will not laugh at you,

Ta buďe idanunta a hankali tana kallon Iman itama kallonta take, sai ta tashi xaune, Iman ta
bata maganin tasha tana yatsina fuska kamar xatayi kuka bata barta ta kwanta ba sai da ta
tabbatar ya kwanta mata, fauxie taje kusa da yaron ta riqo hannunsa ta riqa da nata,

'Anty shi hannunshi yana da laushi, yaushe xaiyi girma kamar ni muyi wasa,

'kiyi barci ba surutu na tayarda ke kiyiba, fauxie tayi shiru haďe da rufe idanuwanta bata saki
hannun yaron ba, Iman ta kwanta a kusa dasu tana kallonsu, barcinta a ranar sama sama ne
sai ta fara ta tashi a firgice.

*

Washe garin ranar Dr Deen tare da mahaifinsa baffa, nan yake bashi lbrn Iman, sosai ya
tausayamasu sai yaji inama Xahradeen xai aureta ya kula da yaronta da qanwarta sai ya
tuntubesa da Mgnr,

Dr Deen yayi shiru kafin ya dubi baffa,

'xamuyi Mgnr wani lokaci baffa, ya tashi ya fice cikin shirinsa na xuwa asibiti,

Sa'eed ma yana shirin xuwa bank salima ta shigo, ta gaidashi ya amsa fuskarsa ba walwala,

'breakfast ďin fa,
'na qoshi,
'Dan Allah kayi haquri ka yafemin,

Ya ďauki jakarsa yasa kai ya fice batare daya dubeta ba, tabisa da kallo ranta a bace tabbas
idan har wata mace kesa yana mata Wulaqanci a ynxu wallahi ko Wacece sai taga bayanta.....


Tunda sassafe Iman ta shiga wankan ruwan xafi, yaran basu tashi ba harta gama ta fito, sai taji

daďin jikinta sosai, tana shirinta take jiyo hayaniyar mutane tasan baxai wuce yan uwansu bane
da suka xo, ita batason xaman makokin nan da duk yawanci Munapurci ake, sai ayita qananan
maganganu kan mamaci, sun maida gidan kamar gidan biki ba mutuwa ba, sai fita ake da
abinci da juice, jiya kaďai tana lura da yanda yanayin gidan ke tafiya, almubazzarancin yayi
yawa.

Wata dattijuwace tayi Sallama ta shigo ďakin,

Iman ta amsa sallamar tana kallonta bayan sun gaisa,

'Tace Inna ai bai tashi daga barci ba,

'banda abinki fatyma shi jariri ai baya tashi barci karkiyi mamaki ma ynxu har ayi wankan a
gama bai tashi daga barci ba, bani shi nan ki gani, Iman ta ďauki yaron tana kallonsa kafin ta
miqa mata shi,

Tana xaune tana shan kunun kanwa fauxie ta tashi barci lokacin har angama yiwa yaron wanka
ana gasa masa cibiya,

'anty nima ayimin wanka cikin robar baby,

'a'a kije dijeh tayi maki a toilet ke bakisan kin girma ba kinaso Inna taga jikinkine,

Ta make kafada kamar xatayi kuka,

'ni banaso anan nake so,
'yi haquri aje toilet ayi maki kinji, keda akewa a Jacuzzi Ina ruwanki da robar wankan jariri,

Ta soma cire kayanta Iman bata ankaraba sai ganinta tayi cikin robar, Inna ta soma dariya, iman
bata ce komai ba har dijeh taxo ta ďauketa da robar tayi toilet da ita sai daďi takeji,

Angama wankan tafito komai sai na jariri xa'a shafa mata,

Lokaci ďaya Sa'eed da Dr Deen suka xo, ta fita suka gaisa dasu kafin su wuce gurin aikinsu,

Dr Merah ma na qoqari akansu har akayi adduar qarshe, ranar komai ya dawowa Iman sabo da
kyar Merah ya kwantar da hankalinta harta yi shiru,


Ranar suna yaron yaci sunan mahaifin sa Ahmed, Dr Deen, Sa'eed da Dr Merah sosai sunyi
namijin qoqari gurin sunan yaron tamkar Deedah na raye, ba abinda suke nema suka rasa daga
ita har jaririn da qanwarta, ba abinda xata cewa waďannan maza uku sai godiya da fatan
alkhairi a rayuwarsu,

Haka rayuwa ke cigaba da tafiya, Dr Deen da Sa'eed na iya qoqarinsu na ganin sun kula da Ita
tare da nuna mata soyayya,

Ba wannan ne a gabanta ba a ynxu, ba wanda takeji a xuciyarta, ba wanda take ita ba lokacinta
a cikinsu bayan qanwarta da ďanta,

Sai addua Sa'eed da Deen keyi a xukatansu na ganin ta amince da soyayyarsu a shirye suke
da su bata farin cikin da ta rasa a baya,

Xuwa wannan lokacin iman tasan ta rasa Deedah ďinta, ta rasa wanda takeso, farincikinta, a
ynxu da ta jima bata ganshi ba bataji ďumin jikinsaba ta yarda ya mutu ya barta har abada,
xuciyar musulunci ce kawai ke riqe da Ita a yanxu,

Hankici tasa tana ďauke hawayen fuskarta cikin tausayin kanta,

Tunda ta iya ta karbi rashin Deedah, na wanene baxata iya karba ba a ynxu? But it's still
painful.... Yeah so painful!


Bata burin mai kuďi ko wane irin mutum ne shi, tafison talaka xama da Wanda bashi da
meyiwuwa hakan xaisa xuciyarta ta xamo so contacted, kuďi basu amfana ta da komai ba illah
baqin ciki a rayuwa,

Wannan dalilin ne ma yasa ba abinda ke burgeta a duniya balle ya sanyata nishaďi, haka take
xaune ba doguwar magana, babu hope, no future, babu xabi acikin rayuwarta, duk yanda Allah
yayi da rayuwarta dai dai ne.

A yau ta tuno da Deedah kan abubuwa da yawa, baxai barta cikin damuwa ba, hawayenta
kaďai xai gani gigicewa xaiyi da tarairaya concern da emotional pity amma ynxu babu shi,

Ba Wanda xai rarrasheta, ba wanda xai sanyata a jikinsa ya nuna damuwarsa akanta, babu
wannan Deedah dake son farin cikinta Wanda xai iya barin komai na rayuwarsa dan yaga ya
faranta tata rayuwar,

Wasu irin hawaye masu ďumi suka barko daga idanunta, a hankali bakinta ya soma motsi,


_"This life has changed... and we go our separate ways Deedah... but you'll still be in my
heart till my dying days... my world has never meet a person like you..... I love you Deedah."_

My wattpad Phertymerh1
*Babana da Mijina*


©Fertymerh Xarah


38


_dis page is for you Faxyfashion_



Ta ďauke kanta daga kallonsa ta maida hankalinta kacokan Kan abincin da take ci,


Fauxie taxo da gudu ta rungumesa tana dariya,

'Mrng yaya...
'Mrng little angel, bakije Skul ba,
'ina jiran driver bai xo ba,

Ya ďauki little yana yi masa wasa, yaron sai dariya yake daka ganshi kaga Deedah photocopy
sak....

Adama ta shigo da kayan kai tsaye ďakin Iman ta nufa dasu duk da batasan ko menene acikiba
amma bata ďebe tsammani ga kayan Iman ne,

Driver yaxo fauxie ta fice tana yi masu bye bye,

Iman ma Acikin shirin fita aiki take tana gama kalaci ta taso ta karbi little yaqi xuwa ya liqewa
Deen,

Ta rataya Jakarta tana faďin,
'xan barka anan kuwa inda adama tunda yau ni kakewa quya,

Dr Deen ya juya dashi tabi bayansa, motarta ta shiga shima ya shiga tasa tare da little,

Itace ta fara fita da motarta yana bayanta, tafiya suke akan titi hankalinta na gunsu, yanda ya
biyota abaya ya tuna mata da Deedah, Allah ya jiqan Deedah ta faďa a hankali.

Tana isowa kai tsaye office ďinta ta nufa shima bai kulataba yayi nasa office da little....

Haka rayuwarsu ta cigabada tafiya tsawon shekara ďaya kenan Iman ta kasa tsaida xuciyarta
akansu, Dr Merah yayi iya qoqarinsa akanta taqi sai ya xuba mata ido yana kallonta yasan
komai daren daďewa dole xata xabi ďaya acikinsu Sa'eed ko Deen ta aura.


Shaquwa ta musamman ta shiga tsakanin little, fauxie da baffa, akoda yaushe suna can sun
maidashi kakansu shi kansa yana jin daďin kasancewa tare dasu badan komai ba dan shima ba
yara ba jikoki daga shi sai masu yi masa aiki sai Deen Idan yana gidan bai fita aiki ba.

A yanda ta lura yaran a ynxu sunfi son xama da baffa akan ta, bata yaye little ba yana shekara
ďaya da wata biyar idan ka ganshi xakayi tsammanin ya tasamma shekara biyu saboda
girmansa da wayonsa ko ina xuwa yake gashi da rigima sosai, sau tari ba'a gidan suke kwana
ba sai inda baffa, yanda suke sonsa yasanyata qaunar tsohon itama akai akai take xuwa
gaidashi ta daukeshi da girma haka take ganinsa Kamar mahaifinta kamar yanda ya ďauketa
ya',

Idan tayi ba dai dai ba yakan xaunar da Ita yayi mata faďa Kamar yanda xaiyiwa Deen, haka
duk wani abu daya shige mata duhu na rayuwa shike warware mata, sai ta daukesa tabashi
wani matsayi a xuciyarta na UBA, a Yanxu tana samun kulawar da bata samu a baya, ga
yaranta suna jin daďin kasancewa dashi ba abinda xata cewa wannan tsohon bayan yi masa
addua a tsawon rayuwarta.


A nata ganin Sa'eed yafi dacewa da aurenta, yafi kowa sanin halinta da mijinta sannan tasan
halinsa fiye da halin Deen, miskilancin Deen kesa take qinsa komai yana yinsa cikin nuna isa da
gadara, ta tambayi Dr Merah xabi acikinsu ya xaba mata Dr Deen Wanda Sam bata amince da
wannan xabin ba, sai taje ga baffa tana tsammanin xaice ta auri yaronsa Deen ga mamakinta
sai ji tayi yace,

'fatyma ki auri Wanda xuciyarki tafi amince maki dashi, Wanda kike gani yafi kusanci gareki inda
hankalinki xaifi kwanciya kiyi xaman aure, ki kuma kula da yarannan guda biyu da suke amana
agareki,

Sai taji kunyarsa da nauyinsa, akwai kawaici a gareta baxata iya fitowa ta gayamasa Sa'eed
xuciyarta tafi aminta da ta aura ba, sai ta kawar da mgnr ta ďauko wani xancen suka cigaba da
hira kamar ya' da uba....

Akwai wani lokaci da lauyoyin babanta dana Deedah suka xo gareta domin dukiyar mamanta
dake hannunsu suna so su rabu da Ita,

Tayi mamakin dukiyar da Deedah ya bari, bar mgnr Waďanda ke cikin account ďinsa, bata taba
sanin yanada irin waďanna kuďin ba, sai ta boye mamakinta lokacin da taga dukiyar baba,

kusan tsoro da ruďewa tayi a inda take xaune,

Files files dake xube a gabanta na kamfani, gidajensa, filaye da shagunansa bata san iya Karsu
ba, ga makullayen motocin da aka xube mata a qalla xasu kai ashirin inma basu haura hakan
ba, anan gida ma tanajin makullan motarsa dake hannunta sun kai bakwai, na Deedah biyar ne
Kuma tasan suka ďai ne motocinsa a duniya Gashi kuma taga xahiri sai ta qara yarda da mijinta
akan babanta,

Ta dubi Sa'eed kafin ta maida dubanta ga Deen domin sune shaidarta sai lauyoyin, idanunta
sukayi rau bakinta har rawa yake kamar xatayi kuka data tuna Deedah,


'Dukiyar Deedah na yafewa ďan mu Ahmed, ku shaidane ko bayan mutuwata idan ya girma
xaku iya bashi, in kuma ina raye Alhamdulillah,

'sai dukiyar baba a raba biyu dani da qanwata, a ajiye mata nata daban, Acikin nawa xan
sallami yan uwanmu da duka ma'aikatan gidan nan, sauran kuďin xn kaisu gidan marayu da
asibiti saboda masu buqata, xan gina masa makarantar islamiya shida Deedah domin lada ta
kai garesu Allah ya gafarta masu,
'banajin xn iyacin dukiyar baba koda kwandalace a ynxu danasan da jinin mahaifiyata da
yayyuna da qannena aka tara wannan dukiyar, kuka take sosai

'Allah ya gafartawa baba, Allah ka yafewa baba, Allah ka yafe kuskurensa daya aikata,

Suka amsa da Amin suna kallonta cikin tausayawa....ta tsurawa dukiyar ido, xuciyarta ta taushe
ta dacewa,

'duniya ba komai bace tamkar matafiyi ne akan tafarki, baba kaďai ya isheta misali, Waye
baisan baba a Nigeria ba shahararren ďan siyasa mai ji da dukiya, a yau yana ina? ya tafi yabar
kuďin a inda ya samesu, ya tafi inda abinda ka shuka shine jarinka, bai tafi da gidajen ba bai tafi
da motocin ba, bai tafi qasashen da yake xuwa ba, qarqashin qasa ya tafi cikin yadin likkafani
dai dai dana kowa, babu AC babu katifa mai taushi, sauran al'amarin tsakaninsa da ubangijinsa
ne, to haka kowa fa xai mutu yabar wannan dukiyar dayake taqama da Ita, dukiyar nan da ake
tarawa ana hana talakawa da masu buqata, dukiyar da ake kashe bayin Allah saboda ita,
dukiyarda xaka ga yan uwa suna faďa suna gaba saboda ita, duk xa'a mutu abarta Allah ya
gafartamana Amin.

2 months later ~~~


Tana xaune a falo cikin Atampha mai qarshen tsada, kanta babu kallabi ta matse gashinta a
tsakiyar kanta, farin glass dake idanunta ya qara ma fuskarta ilhami da kwarjini tana naxarin

wani littafin ilimin halin ďan adam Wanda a fakaice ba komai bane aciki ba sai applied
Christianity, malaman kimiyar halin ďan adam ke amfani dashi jami'oi matsayin hanyoyin gyara
mu'amalar xamantakewar ďan adam tana tsintar na tsinta tana xubar dana xubarwa, sunan
littafin 'The power of positive thinking'.
Da Sallama ya shiga falon ya bayyana cikin kyakkyawar suit (Japanese) da baqin gilashin
Prada a idanunshi, falon ya gauraye da qamshin Dior addict daka ganshi kaga gogaggen ďan
boko.

Kallo ďaya tayi masa taji xuciyarta ta buga a yau, kamar yau tafara ganinsa, bawai yau ta fara
ganinsa ba sai dai bata fiye yiwa mutum kyakyawan kallo ba, yau ta ganshine sosai a gabanta
yayi mata kyau, shima gabansane ya faďi sakamakon ganin Iman yau a ainihinta ba cikin
mayafi da labcoat ba kamar kullum,
Ta lalubi ďan kwalinta ta ďaura ta xare gilashin idanunta tayi mishi barka da xuwa,

Shiru ya ratsa na wani daqiqai wani chemistry mai ban mamaki na aiki a zuciyoyinsu da
kwayoyin idanunsu yana shiga cikin xukatansu dai dai lokacin fauxie ta shigo da gudu da ball a
hannunta little na biye da Ita yana kuka akan tabashi taqi sai dariya take masa,

Suna ganin Dr Deen duk sukayi kansa suka rungumesa suna dariya,

'ďanki kike hanawa ball fauxie, bakiji kunya ba yana kuka yana biye dake,

Ta soma dariya tana kallonsa kafin ta bawa little ball ďin,

'amma shine ya jefomin ita a goshi ina assignment,

'Kiyi haquri kidaina sashi kuka kinji,

Little ya dubesa yana gauranci da alama ya kawo qarar fauxie ne, daga shi har Iman suka
kwashe da dariya yanda yake Mgnr komai baxaka fahimta aciki ba amma yanayin fuskarsa
xaka gane da faďa yake Mgnr, Deen ya rarrashesa haďe da bashi ball ďin ya fice da gudu,

'yaya yau xakaje damu inda baffa,

'kujirani a waje gani fitowa ynxu sai muje, ta fita da gudu itama,

Deen ya dubeta wannan karon ba walwala a fuskarsa,

'inason nasan matsayina a gunki fatyma,

'Sa'eed na xaba, shi nake ganin yafi kowa sanina da halin dana fuskanta a baya, nasanshi ya

sanni,

Ya dubeta da tsananin mamaki,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login