Showing 3001 words to 6000 words out of 59977 words
Chapter 2 - BABANA DA MIJINA BOOK COMPLETE Fertymerh Zarah --.pdf
Unknown
22 Mar 2025
4472
rayuwar yaran biyu.....
BABANA DA MIJINA
©Fertymerh Xarah
4
Already Fauxiya tayi barci, Fatima Kuwa tana study room ta matsawa kwakwalwarta da
karatu,
Musa ne da Ismail ke tare da Mami, sun jima sosai tare da Ita kafin suyi mata Sallama suka
fice...
Yana xaune a falo suka fito, fridge suka buďa kowane ya ďauki yoghurt Wanda dama al'adar su
ce basa kwanciya sai sun sha,
Baba Xamuje barci kayi mana addua, ya ďago yana kallon yaran bawai bayason yaransa bane
son xuciya da neman duniya suka rufe masa ido, yayi matuqar tausayawa yaran,
Shikenan musa ka Kula da qaninka, Allah ya tashe ku lfy ya raba ku da sharrin mutum....
Suka ce Amin,
Ismail yace baba ni gobe baxan tsaya lesson ba ka gayawa driver yaje ya ďauke ni da sauri,
Meyasa Ismail...
Mami tace xataje dani da Fauxiya unguwa banda musa,
Yace tor shikenan xanyi masa magana, musa yace
Baba baka cika min alqawari na ba, kace xakaje dani waje nayi karatu irin anty Iman
Fatyma ai tagama karatun kaima xakaje ni xan kaika da kaina,
Yaron yayi tsalle ya rungumeshi, thank you father Ina sonka..... Jikin Baban yayi sanyi sosai da
kyar ya iya rungume yaron a jikinsa kafin ya rakasu har dakinsu da kanshi, yana labe yana
kallon sanda suke game suna shan yoghurt Wanda a ciki yayi siddabarun sa, basu jima ba
Kuwa suka xube gurin suna kakaki kumfa na soma Fita bakinsu, yaje da sauri ya ďauke yoghurt
ďin ya musanya shi da Wanda baida komai ya fice, idan xakayi masa kallon natsuwa a Wannan
lokacin xaka fahimci baya cikin hayyacinsa ko kaďan....
Mami ta fito daga ďakinta Kai tsaye study room ta nufa ta sami fatyma da tulin takardu a
gabanta, gefenta kofin coffee ne da take korawa akai akai...
Iman ya kamata ki riqa bawa kanki hutu ki samawa xuciyarki sauqi, wannan karatun yayi yawa
haka ke kullum akan takarda....
ta ďago idanunta da kyar tana kallon mahaifiyarta idanunta sunyi jawur sosai sun nuna kalar
barci,
Mami you won't understand,karatun likita is quite different da sauran karatun, kibari nan da
shekara ďaya na kammala karatuna na xama cikakkiyar likita xn fara maki surgery..
Surgery? ta tambaya da mamaki tana kallonta, surgery akan me?
Tayi far da ido tana kallon ta cikin shigar wasa irin ta ya'da uwa,
Tace Mami har ma sai na gaya miki kibari lokacin yaxo xaki sani...
Mami tayi dariya tana tattara littafan dake gabanta,
Ko Alhuda huda yana samawa xuciyarsa sauqi Iman, ki tashi kije ki kwanta,
Ta tashi tana miqa, a tare suka fito suna tafe suna hira, baba na ďakinsa yana jinsu hr lokacin
da yaji Faty na fadin,
Mami Ina ya'yanki ko sunyi barci bnji hayaniyar game ba,
Me yiwuwa haka ne, amma bara na dubasu, ta nufi ďakin Faty na bayanta, yana daga window
yana kallonsu har suka shiga, basu jima ba ya jiyo qarar fatyma tana kiran baba... ya koma yayi
kwanciyarsa kamar mai barcin gaske,
Iya ruďewa sun ruďe bama kamar Mami da ta xama mutum mutum, batasan meke faruwa akan
ya'yan taba, suna haka baba ya shigo cikin yanayin barci sosai ya nuna damuwarsa hrda kuka
yayi.....
Tun daga lokacin abubuwa sun soma faruwa, walwala da jin daďi sun rageshi a gidan, ga kuďi
kamar me, basu taba xargin sa akan Kuďin da yanda yake kashe dukiya ba saboda sun San
dan siyasa ne,
Iman da Fauxiya ne kaďai suka rage masu a ynxu duniya, yana son su fiye da xaton mai karatu
haka yake ji komai xai iya dan ganin farin cikinsu....
2 years later
Siyasa ta tashi sai faman xabe ake ana campaign, baba yaje wa Sima da buqatar Wannan
Karon yana son matsayinsa na mataimakin gwamna kowane mutum ne yaci gwamna a birnin
kebbi yana so yaxama mataimakinsa, wani xabe mai xuwa yana so ya fito takarar shugaban
qasa....
Sosai sima tayi dariya wadda tayi matuqar raxana su,
Buqatar ka xata biya Abdallah, xakaci siyasa idan har xaka bada jinin matar ka......
Sosai ya raxana da jin kalamanta, bai taba xaton akwai abinda xai rabashi da Mami a ynxu ba
saboda ta xamo ginshiqin rayuwarsa,
Auren soyayya sukayi, tun saurayi da budurwa, yana sonta tana sonsa.....
har ya dawo gida bashida sukuni tunaninsa yanda xai bada jinin Mami, ya kasa barci sai faman
juye juye yake akan gado, duk abinnan da yake akan idonta tana kwance tana kallonsa,
Ta matso a hankali xuwa garesa,
Meke damun ka alhaji, yayi firgigit yana kallonta da mamaki,
Kada dai hr ynxu kana tunanin su musa ne? Ya girgixa kansa hawaye suka xubo masa,
hankalinta yayi matuqar tashi,
Meke faruwa meke damunka? Ya janyota sosai jikinsa ya rungumeta...
Ki yafe min, ki yafe min Amina,
Jikinta ya ďauki rawa,
Ba abinda kayimin a xamana dakai, inma kayi na yafe ma nima ka yafemin,
Ya sauke ajiyar xuciya yana qanqame da ita yana jin sonta har cikin ransa Kuma har lokacin bai
daina hawaye ba,
Ta maida kanta qirjinsa hankalinta ya kasa kwanciya da yanayin mijinta tabbas akwai abinda ke
damunsa yake boye mata, Gobe da safe xata tuntubesa ya gaya mata damuwarsa....
Suna haka hr barci ya ďauke ta, ya sumbaceta sosai kafin ya janyo wani Jan kyalle qarqashin
pillow ďinsa....
BABANA DA MIJINA
©Fertymerh Xarah
5
Rumtse idanuwansa yayi kafin ya ďora mata kyallen a jikinta,
A hankali ta buďe idanuwanta tana kallon sa sakamakon wani raďaďi da taji a xuciyarta,
A hankali bakinta Na soma motsi kafin idanun su rufe dai dai lokacin numfashinta na ďauke,
Cikin wani irin yanayi ya rungumota jikinsa haďe da fashewa da wani irin kuka mai tsuma
xuciya,
Mutuwar Mami sosai ta girgixa mutane, yan uwa da abokan arxiki bama kamar fatyma da
fauxiya,
Shi kansa baba idan ya shiga gidan ya sami Fauxiya jikin fatyma sai hankalinsa ya tashi saboda
tsananin tausayinsu da tausayin kansa, a lokacin Fauxiya is 6yrs, sun xama marayu.....
Ma'aikatan gidan ya qara saboda kula dasu, basu da wani aiki a gidan daga ci sai kallo sai
barci, Fatin ce batada hutu saboda karatu...
Bayan wani lokaci akayi xaben siyasa Kuma yaci, sai ya Gina masu wani qaton gida mai hawan
bene guda biyu kowane da gate ďinsa sai aka xagaye gidajen aka maida shi gate ďaya as 2 in
1,
Cikin ďaya suka tare sai ďayan ya ajiye idan fatyma xatayi aure su tare a gidan saboda bayaso
tayi nesa dashi ko kaďan,
Sosai taji daďin haka ynda takeji a xuciyarta baxata iya barin qanwarta da mahaifinta ba, she is
happy with the house, sai ta rungume mahaifinta cikin farinciki shima sai ya tsinci kansa cikin
nishaďi ganin fatyma taji daďi...
*
Ahmad Deedah bayan rasuwar mahaifiyarsa, ya karbi tayin oga nas suna xuwa wurare da
dama sata, ya kware ya iya bama kamar harbin bindiga, baya kissa kamar sauran abokansa sai
dai ya tsoratar da bindiga, haka Kuma idan police sun masu taurin kai wajen bibiyarsu yakan
harbi mutum a hannu ko qafa,
Cikin lokaci qanqani yayi fice ya xama gwarxo aciki Wanda oga nas ke alfahari dashi, duk suka
fita operation sai sunci nasara wannan shine dalilin dayasa oga nas yabawa Deedah matsayi
babba a cikinsu Kuma yakeji dashi and again yana tsoronsa domin mutum ne kaifi ďaya idan
yace eh ko A'a ba Wanda ya isa ya lankwasa sa,
Bayan wani lokaci ya nemi aikin banki kai tsaye ya samu cos kuďi ke mgn Kuma ya bada,
Ya kanje aiki tunda sassafe baxai dawo ba sai marece, idan yayi wanka yaci abinci xai fice inda
sauran abokansa inhar baxasuje sata ba a Wannan ranar,
Idan ka ganshi Kaga kamillin mutum, qasaitaccen namiji mai ji da kyau da kuďi, bafillatanin
gaske, baya neman mata xina,baya shan giya matsalar ďaya ce DAN FASHI.....
Haďuwar sa da fatyma ya samo asaline a bank, taje verification,
Daga yanayin tafiyarta xaka gane nutsuwarta da kamalarta sai dai kallo ďaya xaka mata ka
fahimci baa hayyacinta take ba, kai tsaye ta shiga bankin hannuwanta duka Acikin Jakarta da
alama abu take nema tana tafe tana dubawa,
dai dai lokacin ya fito daga office ďinsa, sanye da baqaqen suit, hannuwansa da laptop yana
tafe shima yana latsa ta cikin sauri...
Kicibis sukayi karo da juna, daga shi hr ita kayan dake hannuwansu suka xube a qasa, laptop
ďin ta ďauke wuta,
Ya salam... ta furta a hankali bayan ta sunkuya daukar laptop ďin bata damu da nata kayan ba,
ta ďago tana kallonsa yana tsaye Idanunsa sanye da farin glass daga kallo ďaya xaka fahimci
bacin rai sosai kwance a fuskarsa, sai ta tsinci kanta cikin ruďewa Abinda bata tabayi ba,
Am sorry please, ya karbi laptop ďin haďe da Jan dogon tsaki ya fice tabi bayansa da kallo
xuciyarta na bugawa kafin ta maido hankalinta ga kayanta dake xube a qasa, ta sunkuya ta
haďa kayanta ta fice....
Ta jima sosai a bankin kafin ta gama verification ďinta, tana gab da fitowa wayarta ta ďauki
qara, ta ciro ta Jakarta Dr.hadixa, sai a lokacin ta tuna da Kuďin dake Jakarta xata tura mata,
Oh sorry Dr. Ina banki ynxu xn turo maki Kuďin.... ta faďa bayan ta ďauki Wayar,
Ta juya da sauri,inda ta fito ta koma tayi masa bayani, ya nuna mata office ďin, tayi godiya ta
juya ta fice...
Da Sallama ta shiga office ďin, yana xaune Wannan Karon ba glass idanuwansa ya xubawa Mai
gyaran laptop ďin ido, tsoronsa kada taqi tashi saboda muhimman abubuwan dake ciki,
Sallamarta ta janyo hankalinsa gareta,
ita ďin ce, me taxo yi office ďinsa, itama tayi mamakin ganinsa jikinta yayi sanyi ganin ana
gyaran laptop ďin, ta maida kallonta garesa hr lokacin fuskarsa ba walwala,
Dama na xone na baka haquri, it seems like na bata ma rai, ni bnganka ba ban San yanda
akayi Hakan ta faru ba kayi haquri,
Ya sauke ajiyar xuciya,
Is ok ba komai, is not your fault is mine..
Tace A'a laifina ne...
Yace laifina ne..
Tace shikenan Nagode ta juya xata fice ya tsaidata,
Ba Wannan ya kawo ki ba, menene, sai a lokacin ta tuna ta ciro Kuďin Jakarta ta miqa masa,dai
dai lokacin da aka gama gyaran laptop ďin sosai yaji daďi,
Nan ma bata jima ba ta fice da sauri xuwa asibiti...
My wattpad Phertymer
BABANA DA MIJINA
©Fertymerh Xarah
6
2 days....
Ta fito cikin shirinta na xuwa aiki, Fauxy na bayanta sai rigima take mata yau sai taje da Ita
asibiti,
Idan naje dake, skul ďin ki fa, Sannan bakyaji ne baxaki xauna inda xan xaunar dake ba,
xakije...... tayi Saurin katseta,
Anty kije dani dan Allah, I will be a good girl,
Ta sanya Labcoat ďinta ta dubi Dijeh Mai kula da Fauxy,
Tace dijeh ki ďauki uwar rainonki ba inda xanje da Ita kisanya mata uniform ďinta kada tayi
late.... idanun Fauxiya sukayi rau sai ga hawaye
Please Anty kije dani, bana son Skul yau,
Fatyma ta fice da sauri dan bata son ganin hawayenta, Fauxiya Kuwa ta soma Kuka sosai...
Harta xo asibiti Kukan Fauxy ke mata yawo akai, office ďinta ta nufa ta ajiye kayanta kana taje
duba patient ďinta data bari a jiya,
Gynaec suka haďu da Dr. Merah,
Morning Dr.
Morning inlaw (yanda yake kiranta saboda Fauxy da ďansa Sultan) you are late today,
Am sorry, fitinar Fauxiya ce tana so naxo da Ita,
Fauxie uwayen rigima itada sultan, ya miqa mata file dake hannunsa Dead Case ne, Matar ta
mutu after delivering amma yaron da ransa,
Ta Karbi file ďin tana dubawa, a tare suka juya inda ya cigaba da mata bayani jiya cikin dare an
kawo wani patient accident case, ya xubar da jini da yawa, xnje gida shiyasa na damqawa
Bakori case ďinsa, ku kula dashi Pls,
Shikenan ta faďa, ya fice, a hanya suka haďu da Dr Hadixa suna tafe suna hira har suka iso
A&E....
She was shocked to see him, mutumin da suka haďu a banki, garin ya haka ta faru she don't
know, sai ta tsinci kanta cikin tausayinsa, shima kallon mamaki yake mata is she a doctor?
tambayar da yayiwa kansa,
Ya jikin ta faďa tana kallonsa,
Alhamdulillah ya faďa a sanyaye....
A ranar ita ta kula dashi saboda Bakori is busy
Sosai Ahmad yaji daďi,
Oga nas da yaransa sunxo dubiyarsa, idanu fatyma ke binsu dashi cikin shigarsu ta mutunci
baxaka taba gane ko su Waye ba, sosai sun birgeta ynda suke mutunta junansu sai dai abu
ďaya na ďaure mata kai ba Wanda yaxo daga gefen Ahmad uwa ko sister kamar xata
tambayeshi sai tayi shiru wannan ba hurumin ta bane,
2:00pm
Lokacin tashinta aiki yayi ta soma harhaďa kayanta, hrta shiga mota ta tuna da patient ďinta,
taje ta sanardashi she is going....
Ya tsura mata ido hr lokacin baisan sunan taba and he need to know....
Hr ta juya sai Kuma ta kallesa,
Sorry to ask, ba wani naka da xaixo ya xauna da kaine kafin Dr. Umayma taxo ita ke on duty,
Ya girgixa kansa,
Babu, NI MARAYA NE..... ya faďa Idanunsa akanta, bnda kowa bayan abokaina,
Sosai ta tausaya masa ta gyara tsayuwarta,
Ka Kira ďaya daga cikin abokanka ya tsaya da kai, ba amfanin barinka kai kaďai cos nurses
baxasuyi jinyarka ba,
Hakane I will Insha Allah, tnx for your care, ta gyada Kai ta juya yayi Saurin tsaidata,
Your name Pls....
Dr. Fatyma Abdallah,
Sunan Mai daraja da muhimmanci a rayuwata, sunan mahaifiyata nake kiranta da Inna, xn iya
kiranki da Ummi?
Ta girgixa Kai tana kallonsa cikin tausayawa jikinta na soma rawa data tuna Mami, ta share
hawayen idanunta,
Nima na rasa mahaifiyata da yan'uwana, am alone with my sister sai mahaifina, ka kirani da
Iman shine laqamina,
Allah ya gafarta masu, tace Amin ta soma share hawayenta abinda ya faďa ya sanyata juyowa
da sauri tana kallonsa,
Ki aureni Iman.... Tsananin mamaki ya sanyata furta komai Illa idanu data xuba masa shima
kallonta yake, she is not dat beauty tana da nata dai dai ita, haskenta shi ya qara mata kyau
Wanda xakayi tunanin ita wata muguwar kyakkyawa ce, sanyin halinta da nutsuwarta yaji yana
raayinta.....
Batare data tankaba tasa kai tabar ďakin yabita da kallo..
Harta iso gida bata da sukuni muryarsa ke mata yawo akai, ki aureni, ki aure ni....
Da kyar ta fito daga motarta, ta juya tana kallon harabar gidan birjik da securities, ina little sister
ta shiga.. Oh Allah ta tuna ita Mai laifi ce a gareta yau baxata xo yimata oyoyo ba tana fushi da
Ita,
Da sauri ta qarasa cikin gidan tana kiran fauxie, shiru bata amsa ba harta iso qaton falon su ga
mamakinta sai ta sameta xaune akan sofa da skulbag ďinta tana ciro littafanta da alama
assignment xatayi,
Ta ajiye kayanta ta qaraso inda take,
Kinaji Ina kiranki kika min banxa, is not the right thing fauxie,
Ta tunxure bakinta ta maida kanta gefe, ta xauna kusa da ita tace da kika je Skul are you not
happy, kinga friends ďin ki, you play and eat together,
Ni banyi wasa ba,
Tor meyasa? Ta nuna ta da yatsa idanunta sun kawo kwalla, ta rungumeta don't cry, gobe dake
xanje, kinci abinci,
Yes sister, dijeh tayi min wanka,
Yayi kyau, ta buďe littafinta tana duba class work ďinta,
Subhanallah Fauxiya me kikeyi a class har kika faďi haka, 2/5
Tayi shiru tana kallonta, sosai ta ďaure mata fuska,
Xamu bata dake, silly girl, simple questions baxaki iya amsawa ba,
Tace Anty ni ban iya ba ku.... ta katseta cikin fushi,
Shut up, ta tashi a harxuqe itama Fauxiya tabi bayanta,
'Anty kiyi haquri, koda naje nayi kuka shine banyi ba,
Har suka iso ďaki tana roqarta,
Anty kiyi haquri karki gayawa baba, ta juyo tana kallonta
Baba kike tsoro kenan, ai Kuwa xn gaya masa,
Ta soma bubbuga qafafuwanta,
Dan Allah anty baxan qara ba, I promise you.....
Da dare ta kasa barci sai juye juye take, idan ta rumtse idanuwanta kyakkyawar fuskarshi take
gani, maganarsa nayi mata kururuwa a kunne.....
NI MARAYA NE KI AURENI.....
BABANA DA MIJINA
©fertymerh Xarah
7
Ta rumtse idanuwanta,
Yh is true as her age ya kamata ace tana da aure yanxu, baba will be happy duk da baya mata
Mgnr auren tasan yana so ne,
Duk Acikin likitocin ita kaďai