Showing 21001 words to 24000 words out of 59977 words

Chapter 8 - BABANA DA MIJINA BOOK COMPLETE Fertymerh Zarah --.pdf

Unknown   

22 Mar 2025

4485

sai yaushe xaka xauna dani kaji damuwata idan har kai baxaka iya gayamin taka ba, tell me
Deedah kasan matsalata a Yanxu da Abinda ke damuna? You are my life partner idan ban
xauna dakai na gayama damuwata ba dawa kake so na xauna, babana ya gujeni nida qanwata
banda kowa a duniyarnan da xan kalla naji daďi kamar kai, nayi xaton bayan miji da yaya xaka
xame mana uwa uba nida Fauxiya, (kuka take sosai)


'Baka xama damu, haqqina ma baka bani, zina kake so nayi kome? Ko wani namiji kakeso naje
na nema a waje, auren soyayya mukayi bana qiyayya ba har sai yaushe xn sami kulawarka,
kasanya neman kuďi a xuciyarka kana so ka manta ko kai waye, tell me miye amfanin Kuďin da
babu kwanciyar hankali akai, ka kwashe dukiyar ka bana so kulawarka nakeso, I want you to
know am not satisfied with you....... buďar bakinsa sai cewa yayi


'Ashe baki da kunya Iman, ni kike ma tsawa, are you shouting on me or what? to baxan ajiye
aikina saboda ke ba.....


Xatayi mgn kenan kuka yaci qarfinta sai ta juya da sauri tabar ďakin ta nufi ďakin fauxie tana
kuka sosai Kamar ranta.


Pherty

BABANA DA MIJINA.......


©Fertymerh Xarah



21



Kukan ta da hawayenta ba qaramin ďaga masa hankali yayi ba sai ya sauko ya bita shima,


Gab da xata sauka step ďin ya rungumeta sosai Kamar xai tsaga kirjinsa ya sanyata ciki Mai
yiwuwa Sannan ne xai xamo contented, ya juyo da Ita yana fuskantarta,


Did I hurt you Iman? tayi masa shiru sai sheshshekar kukanta,

Shikenan naji xn gyara, xan cnxa xn rage fitar na xauna na kula dake, xn riqa baki haqqinki akai
akai idan su kaďai ne damuwarki amma ni banason Wannan Kukan naki,


tayi shiru batare da ta tanka ba idan da sabo ta saba da jin Wannan Mgnr kullum xn cnxa kullum
xn cnxa har yau bai cnxa ba ta lumshe idanuwanta cikin qunar xucci,


A hankali yakai bakinsa dai dai nata yasanya harshensa akan labbanta yana xagayawa dashi
har ya isa cikin bakinta,


Shikansa yayi missing ďin ta he don't know sai yanxu daya ruďe yana kiciniyar rabata da
kayanta da sauri ta riqe masa hannu tana son janye jikinta daga garesa har ynxu xuciyarta bata
huce akansa ba,

A yanda ta lura idanunsa sunyi jawur ya soma fita hayyacinsa baxai iya kyaletaba, itama a
buqace take sai ta saduda ya ďauketa ya nufi ďaki da Ita....


Washe gari har yaso ya makara koda ya tashi bata ďakin, bata tayarda shi ba saboda har ynxu
bata huce ba, ya lura da hakan tunda asuba da xasuyi sallah, ya tashi a gurguje ya nufi toilet,


Koda ya shirya ya fito daga ita har fauxie ba kowa a gidan, tayi gurin aiki fauxie Kuwa tayi Skul,
ya jinjina kansa lallai abin Iman babbane,


Tun da taje asibiti aikin komai batayi ba, tana daga xaune iyakarta da patient rubuta magani ko
dubasa amma bataje karban haihuwa ba kamar yanda ta saba a kullum,



Bayan wasu awanni likitocin suka dawo duk aka haďu a consultant nan aka fara barkwanci
kamar yanda suka saba ana dariya, Iman na xaune komai batace ba illah idanu da ta xuba
masu tana kallonsu ďaya bayan ďaya,

A tsarin halittar ďan adam personality tana cikin rukunin al'ummar da ake kira introvert da wuya
kaga haqoranta sai idan likitocin sun kaure da rigima tayi murmushi tana kallonsu wani sa'in
kuma tasa baki, she is simple batada hayaniya,

Yanxu ma murmushin take tana kallonsu duk mata ne yan uwanta likitoci, basu damu da rashin
sanya bakinta a ciki ba cos sun santa sunsan halinta,


Tashi tayi tana harhaďa kayanta da alama tafiya xatayi,


Dr Hauwa ta dubeta tana faďin, idan gida xakije Dr fatyma taimaka ki saukeni a hanya,


'ba gida xnje ba, banki nakeson biyawa na fiddo Kuďin Skul fees ďin fauxie,


Tace shikenan Bari Dr Fulani ta saukeni, yau bada Mota na xo ba,


Iman tayi masu Sallama ta fice, bata taba biyawa fauxie Skul fees ba sai wannan karon da
mahaifinsu ya yafe su yamaida responsibility ďin fauxie hannunta Kuma she accept xata Kula
da qanwarta duk abinda take so xata iya mata a rayuwa indai baifi qarfinta ba,



Akan hanyarta ta xuwa take wannan xancen xucci harta iso bankin da Deedah ke aiki,


Sai da ta gama Abinda take tukunna ta nufi office ďinsa, batayi tunanin neman Sa'eed ba,
batare da tunanin komai ba ta shiga office ďin yana xaune da laptop a gabansa sai faman
dannata yakeyi, sallama tayi ta qarasa shiga,


Muryarta kawai yaji ya ďago da sauri yana kallonta,

Ta qaraso ta xauna kujerar dake fuskantarsa fuskarta ba walwala,


'Sannu da aiki yayan fauxie, bai amsa mata ba da alama baiyi farin cikin xuwanta a Wannan
lokacin ba duk da bata taba xuwa office ďin sa ba tun bayan auren su,


'Iman wannan tafiyar ta baxata fa, me kika xo yi? tayi masa wani kallo

'tambayata kake dan naxo naga mijina, ko laifine Deedah? ya girgixa kansa yana murmushin
yaqe


'ba laifi bane kuma naji daďi sosai amma naga baki taba kawomin irin wannan xiyara ba,


'tace hakane, skul fees ďin fauxie na....... bata qarasa ba aka buďe qofar office ďin aka shigo,


'cwty you have been waiting da kyar umma tabarni na fito,


Yayi shiru bai amsa ba hankalinsa inyayi dubu ya tashi, Iman ta juya tana kallon wacce ta Kira
Deedah da cwty, saudah ce rataje da qaramar jakarta cikin doguwar riga ta atampha, bata lura
da Iman xaune a gurin ba ta isa inda yake ta sumbacesa a goshi,


'da sauri ya ture ta cikin borin kunya, me kike yi haka Ashe baki da kunya....


Ta ware idanu tana masa kallon mamaki sai alokacin ta lura da Iman dake xaune tana kallonsu,


'oh no wonder shiyasa xakayi rejecting ďina, kace rival ďita ce a banki, ta juya tana kallon Iman,


'sannu anty ya aiki, Iman ta amsa da


'Alhamdulillah cikin basarwa, saudah ta sami guri ta xauna,


'wannan yanayin yafi komai yimin daďi gani ga uwargidanka, ka gayamata matsayina na
amaryarka,


Deedah ya dubeta, get out of my office saudah, ban taba sanin baki da tarbiya ba sai yau, duk
iskancin ki ya tsaya kaina kada ya kai ga matata,


Dariya tayi ta gyara xamanta, Iman kallonsu kawai take kafin ta tabe bakinta ta tashi da Jakarta
a hannu ta fice,

Tana fitowa sukaci Karo da Sa'eed shima ya fito nasa office, a tare suka sakarwa juna
murmushi bayan sun gaisa sai suka jero tare suka fito farfajiyar bankin xuwa inda tayi parking,
tun basu qarasa ba taga fitowar saudah a fusace, Sa'eed ya dubeta


'yau ina qawar rakiya fauxie bn ganku tare ba,


'fauxie na skul, school fees ďin ta naxo fiddawa gobe nake son naje na biya mata,


Yace hakane, nima Adnan gobe nakeson biya masa,


Tace ko na baka na fauxie ka haďa ka biya masu pls, ta ciro Kuďin daga jakarta ta miqa masa,


'nawa ne Kuďin,
'65,000
'barsu hannunki a Yanxu idan na tashi aiki kafin naje gida xn biya na karba gobe ina biya sai na
kawo maki receipt ďin,


'shikenan Nagode sosai ta maida Kuďin jaka akan idon wasu matasa su kusan shidda da alama
yan fashi ne,


'Nine da godiya, kinga Deedah kuwa? ta yatsina fuskarta


'naganshi, bara na tafi Sa'eed sai kaxo,



Sukayi Sallama ta shiga motarta ya juya cikin banki,



Tun da ta fito daga banki taga alamar kamar wata Mota na bin bayanta, ta glass take tsinkayosu
motar cike take da maxa harda bindiga tana gani, hankalinta yayi matuqar tashi ta qara gudun
motar sosai sai taga suma sun qara gudu,

Gudu take shararawa kan titi kamar xata tashi sama suna biye da Ita, su kansu dake cikin motar
suna mamakin yanda ta iya Mota haka gashi sun kusa shiga gari xasuyi missing Kuďin da suka
gani hannunta,



'world best ko asakarwa motar bullet ne, yarinyar ta kware wurin Mota sosai,


'A'a kada ku harbeta an shigo gari, asirin mu xai iya tonuwa kawai mubita muga gidan anjima
muje mu karbi kason mu,



Tana shigowa layin su ta soma horn sosai tun kafin taxo gate an buďe mata ta shiga,


'kai gidan ďan siyasar nan ne Alhaji Abdallah fa,


'abin yaxo dai dai ai, muyi shiri sosai muxo gidan kasan akwai kuďi fa anan, muyi qoqari muci
nasara dan naga harda yan sanda ke gadin gidan da alama Mai gidan na gari, in sunyi gardama
ayi watsin alburushi kowa ma akashe.....


Sukayi dariya haďe da jan motarsu da sauri suka bar layin,



My Wattpad Phertymerh1

Babana da mijina.......


©fertymerh Xarah


22

Harabar gidan maqil take da maxa da mata yan siyasa haka ya tabbatar mata da cewa
baba yana gari,


Da kyar ta iya samun guri tayi parking kasancewar motocin dake gurin birjik, har lokacin jikinta
bai daina rawa ba,


Taron siyasa suka gama da alama, taga suna watsewa suna shiga motarsu ďaya bayan ďaya,


Ta fito daga cikin tata motar ďauke da jakarta, ta rufe motar tayi hanyar gidanta anan taci Karo
da baba ko ta ďaga fuska ta kallesa ballantana ta gaidasa, fuskarta a ďaure tamau tabi ta
gabansa ta wuce batare da ta kallesa ba,


Kallo yabi ta dashi haďe da cixon labbansa cikin jin xafin halin ko inkula da ta nuna garesa a
gaban mutane,



Tun kafin ta qarasa gidan take jiyo Kukan fauxie, ta duba agogon dake maqale a hannunta
11am baa isa tashi Skul ba to meya maida fauxie gida, ta hanxarta da sauri domin yanda take
jiyo kukanta har cikin kanta Kuma ta tabbata baba ma yanajin Kukan yarinyar amma bai damu
ba,

Tana shiga falon ta ganta jikin adama tana jijjigata sai kuka take tana kiran anty, anty,


Da sauri ta qarasa gurin adama tana tambayar meya sameta,


'hajiya tun ďaxu malamar su ta kawota batada lfy sai kuka take, Iman ta karbeta jikinta xafi sosai
idanunta a lumshe da alama ta jima tana kuka yanda idanun suka kumbura fuskar tayi jawur, ta
kalli adama


'amma shine kin san da haka bakimin waya kin sanarda ni ba, inda bn dawo ynxu bafa, kina
nufin sai kibarta tayi ta kuka,

'kiyi haquri hajiya nagayawa yallabai babanta yace inje kawai nayi xaton xai xo ne shinake jira
tun ďaxu shiru, Mtseww Iman taja tsaki ta xauna rungume da Ita tana kiran sunanta a hankali,


Sai ta buďe ido luuuu sai sukoma su rufe, taji kanta yafi xafi sosai, ta cire mata uniform ďinta
tana faďin,


'ďauko min wata riga na sanya mata adama, ta juya bata jima ba sai gata ďauke da doguwar
riga, Iman ta karba tana faďin, ďauko ruwa da panadol abata duk da nasan da wuya ta karbi
magani,


'ai hajiya bataci abinci, foodflask ďinta komai bata taba,


'haďo mata tea mai xafi da sauri pls,


Ta sanya mata rigar,
'anty baba, kice baba yaxo anty,
'baxai xo ba fauxie kicire ranki da wannan Baban a ynxu, tashi kisha tea kisha magani, cikin
kuka ta soma magana,


'Ni banaso baba nakeso yabani, anty kije dani inda baba, iman tayi shiru tana saurarenta tasan
duk ciwon da fauxie xatayi idan ba baba yabata magani ko abinciba baxata karba ba tun tana
qarama haka take shi yayi mata wannan sabon,


Adama ta dawo da kayan a hannunta duk rarrashinta da fauxie taqi ta karbi tea ďin,


Iman ta tashi ta fita, ta tsinkayosa tsaye tare da wani abokinsa har lokacin da sauran mutane a
gidan ta qarasa batare da fargaba ba ta isa inda yake,


'baba! yaji ta sarai yayi tamkar baiji ba dama yasan sai ta nemesa tunda fauxie ba lfy, abokinsa
yace bakaji fatyma na magana bane, ya juyo yana kallonta fuska a ďaure,

da kyar ta iya buďa baki tayi mgn badan ta so ba,

'baba fauxie ce ba lfy, kasan baxata ci abinci ba idan ba kai kabata ba,dan Allah kaxo ka bata,


Baiyi mgn ba ya juya yana kallon ďaya daga cikin mutanen sa hannu yayi masa yaxo da sauri,
ta kunne yayi masa raďa ga mamakin Iman sai taga mutumin yaxo kusa da ita shikuma baba ya
fice da abokinsa,


'hajiya gashi inji yallabai yace abaki a matsayin taimako ki Kula da qanwarki, ya miqa mata
bandir na dubu ďaya, ta karbi kuďin tana juyasu a hannunta, ba dan uba uba bane da ta jefeshi
da Kuďin ko xuciyarta xatayi sanyi,tana tsoron Allah ya kamata da wannan laifin, sai ta jefa
Kuďin sama suka watse suka xubo qasa har a jikin baba, ya juyo a razane dan a zatonsa Sima
ce ke masa ruwan kuďi kamar yanda ta saba sai yaga tsabanin haka ba shakka Kuďin da ya
baiwa Iman ne tayi watsi dasu, yayi shiru yana kallonta ransa inyayi dubu ya baci a Wannan
Karon irin Wulaqanci da tayi masa agaban mutanensa, kallonta yake kallonsa take duk cikinsu
kowane fuskarsa ba walwala, ma'aikatan gidan masu shara da wankin motoci suka xo da gudu
suna tsintar Kuďin, ta nuna su a yatsa,


'su ya dace kabaiwa Kuďin bani ba, bnxo neman taimako a gurin kaba, kuma badan fauxie ba,
ba abinda xai kawoni gurinka,


Inaso in qara tunatar da kai, Annabi S. A. W yana cewa dukkanku makiyayane Kuma xn
tambayi kowanenku akan yadda yayi kiwon da aka bashi,


'ya kai baba wace irin amsa gamsassa kashirya wadda xaka ba Allah ta'alah idan ya tambayeka
akan wannan gobe qiyama,


'ka tuna samun Ya'ya wata baiwace da Allah yakeba Wanda yaso Kuma ya hana Wanda yaso
daga cikin bayinsa, Sannan Kuma jarabawace daga Allah don yaga wanene xai godewa
ni'imarsa Kuma wanene xai butulce, Ya'ya kiwone da Allah ya baka Kuma yayi alqawarin
tambayarka,ta juya ta fice da sauri yana tsaye yana kallonta abokansa suna kallonsa cikin
rashin fahimta tsakaninsa da yar'sa,

Har lokacin Fauxiya kuka take tana kiran baba,

Iman ta xauna kusa da ita,

'baba bayanan fauxie Kuma baba baxai xo ba, sha tea inkin sha magani inbaki chocolate kinsan
yaya ya kawo maki wasu jiya, ta make kafada tana kallonta da idanu jawur,

'Ni banaso baba nakeso, anty ki kaini inda baba, wannan Karon sai ta daure mata fuska sosai
ba alamar Wasa a tare da Ita, ta janyota ta matseta tsakanin qafafunta ita da adama suka mata
ďure, bata wani sha da yawa ba ta kyaleta duk da acikin xafin ciwo take sai da Iman ta bige ta
dan takaici ta qara rungume Iman ďin tana kuka sosai, jikinta yayi xafi sosai sai amai take yi,
hakan yasa tayi mata allura, ta ďauketa tayi mata wanka ta rungumata a jikinta tana rarrashinta
har tasamu tayi shiru, barci ya ďauketa, ta sauke ajiyar xuciya cike da tunanin halin da suke ciki,



Da dare Sa'eed da Deedah a tare suka shigo, sun tausaya halin da suka sami fauxie bama
kamar Deedah dan har yafi Iman damuwa akan ciwonta,


Sa'eed ya tambayi kuďin skul fees ďin fauxie taje ta dauki anan take bashi lbrn Duk yanda tayi
da mutanen da suka biyota kuma tana da tabbacin sai sunxo tunda taga sun dade suna dubin
gidan,


Sa'eed yayi dariya yana fadin ba inda xasu xo Iman ki kwantar da hankalinki ballantana ma gida
irin Wannan na siyasa ga police a gidan,


'taja guntun tsaki tana faďin na tsorata dasu da kyar nasha,


Sa'eed ya tashi da Kuďin a hannunsa yana faďin dama mata tsorone daku abinda bai xama
babba ba shi kuke maidawa babba,

Iman tayi dariya kawai tana kallon fauxie dake jikin Deedah,


Duk Mgnr da suke akan kunne Deedah Kuma yasan sai sunxo tunda hartace sun tsaya suna
kallon gidan, suma sun sha yin haka dole ne yayi shiri akansu dan baxaa basu ko kwandala ba,


Fauxie taqi yarda ya ajiyeta ballantana yaje ya raka Sa'eed sai yaje da Ita a kafadarsa bayan ya
dawo ya kashe wayoyinsa gabaki ďaya dan bayajin xai fita a yau,


Fauxie ma ďakinsa ya wuce da Ita yasamu da kyar ya kwantar da Ita tunda tayi barci, da sauri
yaje ya janyo bindigarsa bullet ya xuba mata kana ya ďura wasu a aljihunsa ya xauna yana
latsar laptop ďinsa, Iman ta shigo tana tambayarsa wankan fa,

'ba Yanxu ba sai xuwa anjima ina wani abu ne, ta tabe bakinta ta fita,


Har 1:00am Deedah baiyi barci ba yana xaune

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login