Showing 24001 words to 27000 words out of 59977 words
Chapter 9 - BABANA DA MIJINA BOOK COMPLETE Fertymerh Zarah --.pdf
Unknown
22 Mar 2025
4484
kamar yanda tabarshi, Iman Kuwa tuni tayi barci,
yanayi yana kallon window bai ďebe tsammani ga xuwansu ba,
Kamar a mafarki Iman taji Harbin bindiga xumbur ta miqe xaune dai dai lokacin da Deedah ya
sauka daga Saman gadon,
'ina xakaje kanajin harbin bindiga ni Dama nasan sai sunxo,
'ki xauna ki Kula da fauxie ta fita da sauri,
Ta balcony ya tsaya yana kallonsu yana labe a gefe, tun daga Sama ya gane ba nasu bane sai
ya fiddo bindigarsa haďe da gyarata,
Artabu aka shiga yi tsakanin barayin da yan sandan dake gurin, kuma sosai sunci nasara akan
police tunda baxata suka masu, from no where suka ji saukar bullet batare da sunsan inda yake
fitowa ba,
Alhaji Abdallah yanajin abinda ke faruwa ya fito da sauri shima bai sauko ba yana sama, ba'a
ganinsa amma shi yana ganin kowa,
Da barayin suka fahimci inda bullet ke fitowa suka soma maida martani,
Hankalin Iman ya kasa kwanciya da Deedah, yafita bai dawo ba sai qarar bindiga kakeji ta fito
daga ďakin anan taci Karo da duk masu aikin sun fito hankalinsu a tashe, ta duba ba Deedah a
falo, inda take jiyo qarar bindiga can ta nufa,
Kusan mutuwar tsaye tayi qafafunta na neman gagararta jikinta sai rawa yake, Deedah da
bindiga, Deedah ke harbi, ina Deedah ya iya harba bindiga, ina ya samu bindiga miye hadinsa
da bindiga,
Harbi yake cikin kwarewa da gwaninta kai da Kaga yanda yake riqe da Ita kasan ba ďan koyo
bane ya gwane ko yanda yake sarrafata,
Duk harbin da yake ba Wanda ya samesa illah shi da ya kashe masu mutane sosai,
Hankalin Iman a tashe ya rabu Kashi biyu, ďaya gurin Deedah ďaya gurin mahaifinta batasan a
wane hali yake ciki ynxu ba(ďa da mahaifi) batasan baba yana xaune yana kallon kowa da duk
abinda ke faruwa ba,
Kamar ance ya waiwaya yaga Iman tsaye tana kallonsa, ba tsoron ganin sa da bindiga yaji ba
tsoronsa kada a harbeta, cikin tsawa ya soma mata mgn,
'ki tafi Iman, haka take jinta kamar mutum mutumi, Karo na biyu ya sake daka mata tsawar dana
firgita ta ganin bata da niyar tafiya,
'Nace ki tafi.......
ta juya da sauri tayi cikin gida, wayarta ta nema ta Kira DPO sosai tasanshi gurin mahaifinta, ta
sanardasu halin da ake ci,
Deedah Kuwa cnxa akalar bindigarsa yayi ya fito daga inda yake boye ya cnxa gurin boyo suka
shiga artabun bullet sosai....
Pherty
[04/03, 6:55 p.m.] Pherty:
*Babana da mijina........*
©Fertymerh Xarah
23
World best yakamata mu haqura mubar gurin nan tun asirin mu bai tonu ba,
Baxamu bar gurinnan ba har sai mun cimma burin mu, ko bamu samu kuďi ba muyi qoqari mu
kashe wancan gaye.....bai qarasa rufe bakinsa ba Deedah ya sakar masa bullet a hannu dai dai
da qarasowar motocin yan sanda, duk Unguwar ta hargitse saboda tsoro da raxana,
Deedah na ganinsu ya cilla bindigarsa qasa kana yayi shigewarsa da sauri cikin falo, duk glass
ďin gidan an farfasa sa,
Iman na xaune da fauxie a hannunta sai faman xufa take ga yan aikinta xagaye da ita, ko
kallonsu baiyiba ya nufi ďakinsa dai dai window ya tsaya yana kallon Abinda ke faruwa,
Sauran da basu mutum ba ana sanyasu a mota, wadanda na mutu Kuwa yaga ana
investigating ďinsu,
Juyowar da xaiyi Idanunsa na sarqe da nata, ya saki wata wawiyar ajiyar xuciya kafin xufa
yafara ratso masa a goshi
'karki tambayeni komai I don't have time for your question, yayi hanyar toilet da sauri yabarta a
gurin,
Ya jima sosai aciki yana watsa ruwa kafin ya fito ďaure da towel iya qugunsa tana nan tsaye
inda ya barta, baiyi mamaki ba yasan xarginsa take inba ya wanke kansa gareta ba yasan
baxata taba yarda dashi ba, ya ďauke kansa daga kallonta ya qarasa tsakiyar ďakin, taja ta
tsaya a gabansa,
'you must answer my question Deedah, meya haďa ka da bindiga,
'da ban riqe bindigar ba kina tunanin da ynxu nida ke bamu dade da mutuwa bane, abinda kike
xargi bashi bane, niba ďan fashi bane kuma ba ďan ta'adda ba, what else did you want to
know?
'ka sauya Deedah, kamaida qarya abincinka yayin da ka boye gskyrka,akwai abinda kake boye
min kagayamin ni matarkace nice yakamata nasan sirrinka tun kafin wani yaxo yagayamin, ni
nafi kowa kusanci dakai, idan kai baxaka xauna ka saurareni ba, ni xn xauna na saurareka tell
me Deedah ina kasami bindiga ka dubi girman Allah ka gayamin gsky...
Gabansa ya faďi jikinsa na soma rawa,
'kifito ki faďi abinda ke xuciyarki Iman, xargi na kikeyi..... tayi saurin katsesa,
'saboda me xn xargeka, kunnena yaji Kuma naga xahiri a yau, menene xargi anan,
Hankalinsa yayi qololuwar tashi saura kaďan towel ďin dake jikinsa ya subulce ya faďi,
'me kika ji me Kuma kika gani,
Fauxie ta gayamin ta ganka da bindiga kuma yau naga xahiri da idanuna ka gayamin kai waye
Deedah?
'toy gun ce fa dana siya inbaiwa Adnan na manta Sanda na siyawa fauxie tedy,
'ina bindigar? yaje da sauri inda ya boye ta dama ya riga ya siye tun lokacin dayaji fauxie na
maganar da Adnan, ya ďauko ya bata ta karba tana juyata a hannunta kafin ta ďago tana
kallonsa,
'wacce nagani yau a hannunka a Ina ka sama?
Yace Sanda naji kina gayawa Sa'eed lbrn barayin dana biyoki nayi xargin nima xasu xo, bayan
na raka Sa'eed sai na tsaya gurin yan sanda dake waje acan na karba shine ya nuna min yanda
xnyi amfani da ita, bayan Wannan ma ina gani a films ynda ake riqonta da yanda ake harbi, ni
kaina nayi mamakin yanda na iya harbin bindiga kuma kinga sun kashe yan sanda gabaki ďaya
nima dan na fake wani guri ne da tuni sun dade da kasheni shiyasa danaga police sun xo na
jefa masu bindigar kada a ganni da Ita a xargeni da ďaukar bindigar yan sanda, believe me
gsky nake gayamiki apart from this bnsan komai ba,
tayi ajiyar xuciya batare da tayi mgn ba ta juya ta fice, Ahmed yabita da kallo yana sauke
numfashi da kyar,
Tana fitowa falon DPO na shigowa, tayi Saurin gaidashi,
'da fatan ba wanda akajiwa rauni fatyma,
Ta girgixa kanta tana faďin babu,
Amma sunce akwai wani nan sama dake harbinsu Waye shi, sai da cikinta nayi wani qugi ta
xaro idanu tana kallonsa,
'ai sun kashe shi, ďan Sanda ne ya tsaya mana yana sauka suka harbesa shiyasa nayi
gaggawar kiranka,
'Allah ya kyauta gaba fatyma,
Tace Amin ya juya ya fice da bindiga a hannunsa, ta dubi masu aikinta,
Ya kamata Kuje ku kwanta tunda mun samu kanmu Allah ya taimakemu,
Suka tashi suna mata sai da safe, taje ta ďauki fauxie har lokacin jikinta xafi rau, a yanda ta lura
wuyanta ma baya tsayi guri ďaya,ko hannunta bata iya ďagawa , akwai matsala dole gobe ta
tafi da Ita asibitin dan sai anyi admitting nata,
Tana shiga ďakin ta sami Deedah na waya da Sa'eed, taji yana yi masa bayanin komai kafin
suyi Sallama ya tsinke Wayar, kallonta yayi bayan ya gama shirinsa na barci lokacin tana
gyarawa fauxie kwanciyarta akan gadon, ya taba jikin fauxie shima yajisa xafi rau,
'Wai meke damunta ne,
'shiyasa nake son xuwa da Ita asibiti ayi mata test agani, ni kaina na rasa gane kan ciwon, Allah
yasa itama baxata mutu ta barni ba, ta soma hawaye sosai....
[05/03, 8:07 a.m.] Pherty: 'Haba ai ciwo ba mutuwa bane, kidaina wannan mgnr, ya ďauki
pillow da blanket ya kwanta a qasa ya bar masu gadon, addua tayi ta shafawa fauxie kana ta
kwanta,
Alhaji Abdallah bai damu da Abinda ya faru ba wannan abin yafi komai yi masa daďi a ynxu sai
dai akwai alamar tambaya tsakaninsa da Deedah koda yake ma Ina ruwansa dashi a ynxu, su
suka sani dama an kashe su ya huta, sima ta sha jininsu.
Washe gari sosai fauxie ke amai, duk hankalin Iman dana Deedah ya tashi a gaggauce suka yi
shirinsu, yayi banki tayi asibiti da fauxie,
Paediatric ta nufa da Ita inda Dr Bakori, bata same sa ba sai ta sami Dr Lawal shi ya karbi
fauxie hannunta yana duba,
Dr fatyma, fauxie ba lafia ne, tun yaushe,
'tun jiya ne,
'oh Allah shine ta koma haka, meke damunta ne,
Iman ta share guntuwar kwalla hannunta har rawa yake kamar yanda muryarta ke rawa fatanta
fauxie ta rayuwa,
'Ni ma nakasa gane ko menene ke damunta, kana ganin hannunta ďaya ma bata iya ďagashi,
wuyanta baya tsayi guri ďaya abinci tun na jiya da safe ne,
'Bari muje lab ayi mata test mugani, yana gaba tana bayansa, binni binni take sharar kwalla,
jikinta duk yayi sanyi da wannan ciwo na fauxie, a hanya suka haďu da Merah da mutanensa
suna shigowa, yau da alama sarauta yake ji ganin kayan sarautane a jikinsa, ga kuma kujerar
xamansa ana biye dashi duk inda xaije,
Sosai ya nuna damuwa tare da tausayawa halin da inlaw ďinsa take ciki, akwai Wanda xaima
operation da safennan shine dalilin fitowarsa yau da wuri,
A lab duk iya bincikensu an kasa gano matsalar, wasu result ďin ma ba'a kawo ba, sai akayi
admitting ďin ta, aka sanya mata drip da akaxo allura ne taqi yarda sai da Merah ya karba yayi
mata da kansa, kuka take tana sai ta dakesu idan ta tashi, dariya suke sosai Wanda ya qara
sanyata fashewa da kuka tana kallon Iman dake murmushi,
'anty kema sai na dakeki tunda kike min dariya,
'na bari fauxie,
Dr Lawal ďa Merah suka fice aka barta da Iman,
'Anty kinga baba ya bani biscuit jiya naci,
'biscuit Kuma, yaushe?
'da xnje Skul da safe,
'ke kuma sarkin Kwaďayi, duk biscuit ďin da kike dashi gida Wanda yaya ke siya maki bai maki
ba sai kin karbi nashi, mutumin da baya sonki,
'Anty ai a islamiya akace duk wanda baya sonka idan yabaka abu kayi bismillah ka karba, kuma
harda qul'huwallahu nayi, Iman ta soma dariya tana kallonta,
'sai kace wani mugun abu fauxie, wannan ciwon ya rikitaki da yawa tunda har sambatu kikeyi,
'Anty kicewa baba ban yafe masa ba, Iman ta dube ta da mamaki,
'ba'a cewa babba ba'a yafe masa ba, me yayi maki,
'baya sona, kuma baya sonki,
'ba abin damuwa bane fauxie, kiyi addua kisami sauqi kinji,
'Anty idan na tashi sai na kashe baba,
Kusan faďuwa Iman ta tashi yi, gabanta yayi wani irin faďuwa,
'kiyi shiru haka fauxie, meya hadaki da kissa Allah ya tsare ki, rufe ido kiyi barci,
'Anty jiya nayi mafarki baba yace sai ya kasheni Kuma kema sai ya kasheki Sannan ya kashe
yaya, anty harda dariya yakeyi nima sai na kashe shi,
'Subhanallah, ai mafarki ba gsky bane fauxie, mutum baya mutuwa sai lokacinsa yayi,
Ganin abin na fauxie bana sauqi bane sai ta Kira Deedah a waya akan yaxo, yace yana hanya
saboda surutanta suna tayar da hankalinta dan ma ita kaďai ce a ďakin ba mutane,
Tana xaune taga gadon fauxie na rawa, ga mamakinta sai taga fauxie na qoqarin tashi ta sauko
yayin da take nuna mata qofar shigowa,
'anty kinga baba sai na kashe shi, anty ki riqe min shi in kashe shi,
Iman ta juya bata ga komai ba sai ta taso da sauri ta riqe fauxie, sai ta soma fisge fisge tana
sai ta kashe shi, hankalin Iman yayi matuqar tashi dan da alama Wannan Karon bata ima fauxie
wani qarfi tajita dashi, suna haka sai ga Deedah da Merah sun shigo da sauri suka qarasa suka
riqeta su biyu, sai fisge fisge take tana sai ta kashe shi,
Sosai al'amarin fauxie ya bawa Iman mamaki a yau, bata taba ciwo irin Wannan ba ko aljannu
ke ruďata, sai ta koma gefe ta xauna qasa dirshan tana wani irin kuka sosai
My wattpad Phertymerh1
*Babana da mijina*
©Fertymerh Xarah
24
Fauxie na neman gagararsu sun kasa riqeta su kusan biyu, tunanin da sukayi kamar mai
shafar aljannu ya Sanya suka soma yi mata karatu,
Iman ta maida kanta jikin cinyoyinta tana kuka sosai, wannan wace irin rayuwace, daga wannan
sai wannan?
Fiye da minti talatin kafin su samu abin ya saketa sai dai bakinta bai fasa furta sai na kashe shi,
'Waye xaki kashe? Merah ya tambayeta,
'baba xn kashe, ina tashi sai na kashe baba, yaya ka ďauko baba in kashe shi, baba yana min
dariya dan banida lfy, baba yace sai ya kashe anty da yaya nima sai na kasheshi,
Duk sun ruďe da kalamanta wataqila xafin ciwone ke sanyata sambatu haka acewar Merah,
Deedah kamar yaso ya fahimci wani abu agame da maganarta sai ya sunkuya haďe da riqo
hannunta,
'yaushe baba yace xai kashe mu fauxie? Ina kika ganshi yana miki dariya?
'ai nayi mafarki jiya yace sai ya kashemu,kuma Yanxu yaxo yana min dariya,
'ina kika ganshi yana dariya, suka tambaya lokaci ďaya,
Ta nuna masu qofar ďakin inda taganshi tsaye a ďaxu yana tsoratata da kamanni iri iri, tana
faďin
Ai anty ta ganshi na nuna mata shi, iman ta tashi a firgice tana kallonta,
'banga komai ba fauxie,
Deedah ya gyara tsayuwarsa wannan ba ciwon asibiti bane, Merah ma ya tashi yana faďin
nima Abinda na fahimta kenan dan haka xnje da fauxie gidana, wazirina xai dubata harta sami
sauqi yasan irin waďanna matsalolin,
Deedah yace shikenan nima xn qoqarta anan gida mugani,
Iman batace komai ba illah hawayen da takeyi har Merah ya ďauke ta suka fita,
Yana fitowa fadawansa suka taso xasu karbeta ta qanqameshi, yace su barta,
Iman da Deedah na tsaye ya sanyata a mota suka bar asibitin, wani irin kuka Iman take gwani
tausayi, ina fauxie ta haďu da aljannu yarinyar da kullum take tofe ta da addua, Deedah ya riqo
ta,
Is not time to cry Iman, pray for her,
A yanda takeji ko ta tsaya asibitin baxata iya aikata komai ba hankalinta xai karkata gun fauxie
sai ta nufi gida Deedah Kuwa ya nufi gurin aikinsa tare da qudurin idan ya dawo xai sami
babansu yasanshi yasan kowa shi, idan har ya kashe fauxie xai iya tona sa idon duniya Idan
Kuma bai bar fauxie ya daina wahalar da itaba xaiyi masa baraxanar tona masa asiri.
Sima tsaye tana kururuwa da alama Wannan Karon ranta a matuqar bace yake da al'amarin
Alhaji Abdallah,
Shi kansa dake gabanta jikinsa rawa yake bai taba xaton kashe fauxie xai masa wuya haka ba,
yarinyar akwai tsari sosai a jikinta shiyasa ma ta wahala haka da tuni ya kasheta,
Wannan yarinyar taka akwai baki, akwai wayo, batada tsoro Kuma tana da tsari a jiki, bamason
sheďanin yaro abamu jinin fatyma, sima fatyma take so a ynxu jinin fatyma take da buqata
fauxie tafi qarfin mu,
Baba yayi shiru kansa a sunkuye yafi kowa sanin fatyma, yasan duk asuba idan tayi sallah bata
komawa barci takan xauna tana addu'oin tsari, tana karanta Ayatul kursiyyu, Amanarrasulu,
suratul ikhlas, falaqi da nasi, Sannan a koda yaushe xakajita tana faďin,
_Allahumma inni as'alukal afiyata fi dini wa dunyaya wa ahli wa mali, Allahummastur auraati wa
amin rau'aati, Allahumma fazni min baini yadayya wa min khalfi, wa'an yamini wa an shimali, wa
min fauki wa a'uzu bika an ughtaala min tahti (manzon Allah s.a.w baya barin yin wannan
addua safe da yamma)_.
Akwai matsala ya shugabata fatyma tafi fauxie tsari amma me xai hana mu hana mata
kwanciyar hankali Kamar yanda mukayi da mijinta muke hadasu faďa akai akai, meyiwuwa
rashin jituwarsu a Yanxu xaisa tunani yayi mata yawa har ta shagala da yin addua sai mucimma
burinmu akanta, idan an kasheta xamu iya kashe Fauxiya da mijinta,
Sima tayi wata irin dariya mai firgitarwa kamanninta ma abin tsoro ne, tana sanye da wata
doguwar riga baqa mai kyalkyali har qasa rigar ke ja, a gefe Kuma an tsagata har xuwa
cinyoyinta, ga wani irin Gashi ba kyan gani daya xubo a fuskarta da bayanta, tana da wasu irin
haqora masu mugun tsawo har sun fito ta bakinta sai idanunta da baxaka tantance kalar suba
kamar red kamar maroon, akaifun hannuwanta dasu take tsafi suma tsawo ne dasu kamar me,
Ban yarda da wannan shawarar ba Abdallah, mijinta yana sonta duk yanda sukayi faďa sai