Showing 51001 words to 54000 words out of 59977 words
Chapter 18 - BABANA DA MIJINA BOOK COMPLETE Fertymerh Zarah --.pdf
Unknown
22 Mar 2025
4482
aikomin, wannan
kuku da Zahara ya ajiye bai iya komai ba sai yayi girki ba daďi, bana son abincinsa ko kaďan
namiji bai iya girki ba,
Tayi dariya tana kallonsa,
'akwai kukun da ya iya girki baffa ko wata mace albarka kawai dai ba'a dace bane, amma idan
ba damuwa kullum xan riqa aikoma da abinci, shi Kuma kukun abarwa Wanda ya ajiyeshi ya
riqa masa girki, yayi dariya yana kallonta,
'ba damuwa fatyma aike ya'ta ce, Allah yayi maki albarka,
Ta amsa da amin xuciyarta na bugawa idanunta na kansa, yau ne Karo na farko data soma jin
haka da Wanda ta Kira uba a ynxu, tunda take da baba bata tabajin ya Sanya mata albarka ba
kome xatayi masa a duniya sai dai yace ya gode, wannan dalilin yasa taji sanyi a xuciyarta taji
ta qara son baffa ta ďauke shi a matsayin mahaifi ynxu koda Deen kobada Deen ba, ta samu
uba nagari saura miji na gari......
4.pm
Ta fito riqe da Jakarta a hannu a gajiye take, Sa'eed na bayanta har gurin motarta ta buďe ta
xuba kayanta kana ta ďago tana kallonsa,
'kinqi magana, ki gayamin gskyr xuciyarki game da ni,
'haquri xn baka still Sa'eed, bawai bana sonka bane, salima ce matsalata a ynxu, kullum sai ta
kirani ta xageni bnda test ďin da take turomin daban, ban shiga gidan ba tana kiran yarona da
agola, little baxaiyi agolanci a ko ina ba, ina son yaron fiye da tsammaninka Ina sonsa fiye da
mahaifinsa Deedah, baxan lamunci duk wani xagi da cin Fuska daga matarka ba,
'kina tunanin saboda salima xaki qi aure na, saboda me Iman, ba xamanta xakiyi ba xamana
besides ma ba gida ďaya xaku xauna ba, na karbi little a matsayin uba nayi maki alqawari xan
bashi matsayi a xuciyata Kamar Adnan, wallahi Ina sonki, ina sonki tun marigayi na raye bnsan
yanda akayi na fara sonki ba kawai na tsinci kaina da sonki, help me and save my life Iman,
karkiyi tunanin saboda salima bata kula dani xan aure, saboda qaunar danake maki ne,
kinsanni na sanki, inason kasancewa dake, ina son baki farin cikin da baki samu a baya ba
please Iman....
Sai ga hawaye na kwaranya a idanuwanta, sai Numfashi take maidawa batasan yanda xatayi
da rayuwarta ba, idan tace batason Sa'eed ta cutar da xuciyarta to Deen fa? inama Deedah na
raye da hakan bata faru da itaba, da Yanxu suna rungume da ďansu cikin farin ciki da so da
qauna, Kuma ba Wanda tafi cancanta da aure kamar Sa'eed shine abokin mijinta shine yafi
kowa sanin kanta, Deen ma na buqatar taimakonta ko dan baffa, yana buqatar Mace a kusa
dashi, yana buqatar kulawar Mace ya daina struggling rayuwarsa haka, bata manta itace
sanadin mutuwar matarsa hajara.... wani kuka ya xo mata,
'Sa'eed Deen fa ya kakeso nayi dashi he need me too...
'ba sonsa kikeyiba tausayinsa kikeyi, meyasa kika fi baiwa soyayya muhimmanci fiye da kauna?
Love is not the only thing we are to go for in marriage.... there are other important aspects ,
sacrifice and devotion, idan kina tunanin Deen na son kine ni kaunarki nakeyi Iman,
'I have no choice Sa'eed..... dai dai lokacin da Dr Deen ya shigo harabar asibitin yana fitowa
motar suka haďa ido da ita sai da taji faďuwar gaba,
Sa'eed ya lura da irin kallon da sukewa juna nan take yaji wani kishi, xafin so na bugun
xuciyarsa har kwalla yayi,
'ba komai fatyma, ki xauna da Wanda xuciyarki ta aminta dashi, ina sonki ina son farin cikinki,
tunda kin fison Deen kije gaki ga Deen..... yasa kai ya fice, tabi bayansa da kallo kafin ta maida
kallonta ga Deen shima tuni yabar gurin bayansa kawai take hange, ta kalli wannan ta kalli
wancan,
_'Ni ďan halak ne kije gaki ga Sa'eed_,
_'kije gaki ga Deen_,
Me suke nufi? Kada dai sun haqura da itane?
Gashi ta bata goma bata gyaru ba, babu Sa'eed babu Deen, bataga tsuntsu bataga tarko.
Menene makomar rayuwarta a halin yanxu? wa xata aura Sa'eed ko Dr Deen? Ko xatayi ta
xama haka har qarshen rayuwarta ba aure ne?
Rashin sanin haqiqanin waďanna amsoshin ya sanyata rushewa da kuka mai cin rai.
Da kyar ta shiga motarta tabar asibitin tana isowa gida ta samu Suleiman na jiranta tasan baxai
wuce kuďi yakeson tabashi ba,
'ya akayine sarkin son kuďi, yau ba kuďi a hannuna nima,
Yayi dariya yana kallonta,
'hajiya ba mgnr kuďi bace, an sanya maganar aure na wani watan,
'Allah ya Sanya alkhairi, ta nemi guri ta xauna nan harabar gidan batare da ta shiga ciki ba,
'Ina mutuniyarka ko batasan na dawo bane,
'suna bayan gida itada little, yaran ne akwai son wasa hajiya bama kamar little,
Kafin tayi magana motar Dr Deen ta shigo harabar gidan, bai fito daga cikin motar ba yana
xaune ya soma danna horn, ga mamakinta sai ga fauxie da gudu little na bayanta basu damu
da itaba kai tsaye suka nufi motarsa suna dariya,
Fauxie ta buďe motar ta shiga, tana shiga ta rufe tabar little a waje, ya soma kuka,
'buďe masa ya shiga, meyasa xaki rufe masa motar,
'yaya baxamu je dashi ba, bayajin magana ya fiye tsokana,
'Kema bakyaji ai... ya buďe masa ta bangarensa da gudu ya xagayo kamar xai faďi Deen ya
ďauke sa ya sanyashi a mota, ya soma dariya yana tsalle a motar,
Deen yaja motar suka bar gidan, Suleiman ya dubeta,
'hajiya yaran nan naki suna son wannan mutumin, Kuma bashi da matsala yana da kirki, haka
ranar yabani dubu biyar saboda ya ganni da fauxie,
'kai duk wanda xai baka kuďi mai kirki ne a gurinka, da Wannan surutu ka tashi ka shiga cikin
gida, adama ta haďa ma kayan wankinsu ka Kai,
Ya tashi yana faďin an gama hajjaju...
tayi shiru kawai xuciyarta cike da tunani iri iri.....
My wattpad Phertymerh1
Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen2⃣)
WHATSAPP NO:
+2347039625239
*Babana da mijina*
©Fertymerh Xarah
*Dis page is for you, Shafaatu Zurmi, Pherty b-b, and Aneesa A Rimi*
41
Tun daga lokacin bata qara sanya Sa'eed a idanuwanta ba, ga Deen ya daina kulata tuntuni
ma, ta shiga damuwa sosai,
Little ba lfy koda wasa baiyi yunqurin gayamata ba yasan halinta akan ruďewa, duk da Xaxxabi
ne kawai yakeyi, shike Kula da yaron har a asibiti yana tare dashi, bata taba sanin baida lfy ba
har yaron yasami lfy, daga baya ne takejin labarin a gurin baffa.
1 month....
Kai tsaye ta shirya ta nufi bank inda Sa'eed, akayi Sa'a shi kaďai ne a office ďinsa, suna haďa
ido sai da sukaji wani iri a xuciyarsu, yayi qarfin halin ďauke Idanunsa akanta haďe da sakin
malalacin murmushi wanda bai kai xucci ba,
Yanayin fuskarsa ya Sanya ta nufi cikin office ďin cikin kwarin gwiwa ta sami guri ta xauna,
'barka da xuwa, me xan sanya a kawo maki,
'need nothing Sa'eed... sai kuma tayi shiru idanunta sunyi rau, shima shirun yayi xuciyarsa na
bugawa,
'ya su little da fauxie,
'Alhamdulillah...
'ko da matsala ne Iman? ta gyada kai tana kallonsa haďe da share hawayen dana xubo mata,
'why did you hate me Sa'eed?
'saboda me, meyasa kike wannan mgnr iman, duk duniya akwai wanda ya kaini sonki ne, you
hate me shiyasa na barki da Wanda kike so, naga kamar Ina takuraki shiyasa na barki,
'ba haka bane, har ynxu xuciyata ta kasa tantance min xabina, idan nace bana son ka ko bana
son Deen nayi ma qarya, amma fushinka akaina K.... ya katseta,
'ki auri Dr Deen....itace kalma dana fito bakin Sa'eed ta ďago tana kallonsa cike da mamaki,
'I know Kinason Dr Deen, he loves you too, na taba gayamiki ya sameni nan saboda ke, bawai
ya roqeni na barmashi ke ba ya roqeni akan idan na aure ki na kula da ke da yaranki, na baki
farinciki har a qarshen rayuwarki, ba abinda na fahimta a idanuwansa sai xallar soyayyarki, bai
fito ya faďa a baki ba amma idanunsa sun nuna, ina sonki Iman, dole ta sanya xn haqura dake
ki auri Dr Deen domin yafini buqatarki, bashida kowa bayan mahaifinsa, nikuma I have family
matsalar bnda kwanciyar hankali akansu,
Tunda yake magana tayi shiru tana kallonsa ta kasa fahimtar komai a kalamansa Illa na ta auri
Dr Deen, yes xata iya haqura da Sa'eed cos xuciyarta tafi rinjaya kan Deen and she accept it, ta
amince xata auresa ko dan kwanciyar hankalinta dana yaranta,
'but Sa'eed...... Shishshsh ya katseta, kada kidamu dani, Allah is with me idan salima mai
shiriyace Allah ya shiryata ya ganar da Ita, ban kullace kiba, idan kin amince I will be your
brother na har abada kamar mun fito ciki ďaya dake....
Ta gyada kai tana murmushi mai tare da hawaye, farin cikinta a yau, ta rasa yayyunta biyu da
suka rasu yau ga madadinsu, Dr Merah da Sa'eed, kyautace daga Allah Kuma ta karba da
hannu biyu, ta rasa mahaifi ta sami baffa a hannu sai dai fatan miji na gari wannan shi kaďai ne
burinta a Yanxu.
Tare da Sa'eed sukaje suka sami baffa da Mgnr kan ta amince da auren Deen, sosai baffa yayi
farinciki kamar xai haďiye Iman haka yakeji,
Koda baffa ya gayawa Deen Mgnr bai nuna masa farinciki ba amma har a xuciyarsa yaji daďi,
duk da hakan ya basar bai nemeta ba kamar baisan da Mgnr ba,
Dr Merah, Sa'eed da wani kawunta su suka karbi sadakinta, sune waliyyanta,
Sai dai ba yanxu xata tare ba sai tagama shirye shiryen ta kamar yanda Dr Deen shima yana
buqatar lokaci har ya haďa kayan aurenta.
Salima na xaune a falo tare da yaranta taga mutane na shigowa gidan,
'waďannan su Waye ta faďa bayan ta tashi, ga mamakinta sai taga qatuwar Mota da kaya ana
saukewa irin kayan amare ďinnan, maxa ke shigowa da kayan yayin da matan suka nufi ďayan
part ďin da ke rufe, tana gani suka buďe suka shiga,
'no she can't believe it Sa'eed baxai mata haka, tor kodai haya yabada gurin, inajin haya ya
bada gidan, let me confirm it,
Ta sanya hijab ďinta ta fita, cikin maxan masu sauke kaya ta nufa,
'sannu malam,
'sannu hajiya,
'wancan part ďin haya aka ďauke sa kome?
'A'a amaryar mai gidan ce gobe xa'a ďaura aure ta tare,
Batace komai ba amma jikinta har rawa yake saboda tashin hankali,
Koda taje ďakinta kasa xama tayi sai safa da marwa take, ganin ba mafita ta dauki hijab ďinta ta
fice kai tsaye gidan Iman ta nufa ta Kuwa yi Sa'a ta sameta,
Ba Sallama ba komai ta faďa gidan suna haďa ido da fatyma ta soma faďa da xage xage ta inda
take shiga batanan take fita ba,
Iman na xaune da adama tana yanka mata fruits, idan ke mai karatu kin tanka tor Iman ta tanka,
tunda ta maida kanta ga cin fruit bata qara waiwayarta ba, dama iman ga haquri da sanyin hali.
Wannan ne yafi komai baqin ciki da haushi kana faďa ayima shiru amaidaka banxa Hakan ya
qara kufular da salima ta soma ball da duk abinda ke falon,
Iman ta tashi ta dubi adama, ki shiga ki qarasa aikinki adama, idan wannan mahaukaciyar ta
gama haukarta ta bata gurinnan kiyiwa securities magana a fitar min da Ita daga gidan kana a
gyara falon tasa kai ta fice haďe da rufe ďakinta,
Kamar ta sanya ihu haka takeji angama cin amanarta a ganinta, qawarta xata aure mata miji
wallahi bata isa ba, Gashi ta kirata mahaukaciya, kamar daga Sama sai ga Sa'eed a gidan
abinda idanuwansa na gani ya tsoratashi, meya fito da salima da ixinin wa ta fito meyasa tayiwa
falon kaca kaca haka, nan take ya ďauketa da wani Mari sai data ga gilmawar taurari, hancinta
ya fara jini,
Basai na gayamaku irin Faďan da sukayi a ranar ba kamar xasu haďe junansu a haka ya fisgeta
suka bar gidan......
Daren ranar basu kwantaba kwana sukayi bala'i haka ta xamar masa tamkar wata xararriya sai
daya sanyata a ďaki ya rufeta kafin ya sami sa'ida.
Washe gari aka ďaura auren Dr Iman da Dr Deen...
Kana aka ďaura auren Sa'eed da Habbi qawar salima,
Koya xamansu xai kasance da salima, ya salima xata kasance idan ta wayi gari ta sami habbi a
matsayin abokiyar xamanta, qawar dake bata shawara akan yanda xata Kula da mijinta, wani
abin qarin haushi habbi budurwace bata taba aure ba.
My wattpad Phertymer*Babana da mijina*
©Fertymerh Xarah
42
Har ynxu ban fahimce ka ba, idan ba Iman ka aura ba to Waye ka aura, ko kana tunanin
bansan cewa yau aka ďaura aurenka da Iman ba,
'bani ke auren Iman ba, Wanda take aure daban wadda nake aure daban, idan Kina tunanin
saboda haukarki naqi auren Iman tor kina tunanin banxa ne, anjima da dare matata xata tare
koma wacece xaki ganta,
Hankalinta ya qara tashi numfashinta har fita yake da sauri da sauri, qaryane Iman yake aure
idan ba shiba to wake aurenta?
'kagayamin Iman *Matar Waye?* idan har bakai ke aurentaba,
'wannan ne baxakiji a bakina ba, inaji kin saba xuwa gidanta ki sameta ki nuna mata rashin
mutuncinki ynxu ma you are free... ya cigaba da haďa kayansa,
'kayan me kake haďawa Sa'eed, har ynxu ban fahimceka ba me kake nufi ne,
'kayana nake haďawa na maidasu inda amaryata inda xa'a kula dasu da darajasu.... Kafin tayi
magana ya fice,
Kuka take tana haďa kayanta tayi yaji gida xataje, yana ganin lokacin da ta fita da kayan bai
hanata ba, kai tsaye gidansu ta nufa, Ummanta na jin dalilin dawowarta ta rufeta da duka kamar
xata cinyeta,
'ai Sa'eed yamin dai dai wallahi, kinci amanar tarbiyar danayi maki dan ba haka kika taso kika
samu inayi da mahaifinki ba, kina gani da tsufana a ynxu nake kula da mijina, sau nawa yake
kawo qararki gidannan in xaunar dake inyi faďa inyi rarrashi duk bakiji ba,
'xaman gidan kikeso kixo ki xauna muna gugar kafada dake, idan nayiwa mijina kwalliya kema
kiyi masa gaki ga gidan ki xauna tunda kin xabi hakan a rayuwarki,
Kuka take sosai Kamar ranta,
Mahaifinta ma ya tsoma bakinsa,
'idan har kika bari kika kashe auren ki saboda son xuciya bani bake kuma baxaki xauna min a
gida ba, tashi kije kibani guri shashasha kawai,
'na shiga uku *babana da mijina*, babana xai yafeni saboda mijin dayaci amanata, ta tashi tana
kuka ta shiga motarta, wayar habbi ta Kira ko xata sami shawara a gurinta,
Tana ringing ba'a ďauka ba har ta tsinke ta qara kira sai data kusa tsinkewa kana ta ďauka,
'kina gida ne habbi?
'a'a Ina saloon,
'naso naxo ne, Sa'eed aure xai qara yau amaryarsa xata tare, ta fara kuka,
'wannan matsalarkice salima, sanda nake baki shawara bakiji ba ynxu ni banda abinda xn maki,
bikin dake gabana ma ya isheni,
'bikin waye Kuma,
'au bakida labarin aurena ne?
'Hhhhhh wasa kike, har yaushe xakiyi aure baki sanardani ba gobe xn shigo kibani mafita,
'a'a basai kinxo ba ni xnma xo, ta tsinke wayar....
Da dare aka kawo amarya duk a nata tunanin Iman ce amarya musamman data ga little a
sashen Sa'eed yau, tana ji sanda aka shigo da amaryar da guda sai leqe take ta window,
bataga fuskarta ba,
ďakin Sa'eed ta nufa suna haďa ido ta fashe da kuka, yasan xafin kishin da takeji a xuciyarta,
yana son matarsa bawai baya sonta ba halintane ya sanya yayi mata haka,
Ya taso ya rungumeta, rarrashinta yake cikin Kalamai masu sanyaya xuciya, sai abin na bashi
mamaki ganin yau duk inda ya taba a jikinsa bata hanashi, babu harara babu mitar ta gaji sai
ma qara narkewa da tayi a jikinsa tana qara kissing ďinsa....
Da kyar ya sami kansa kamar mai son yi masa fyade a Wannan daren, ya ďauki little dake barci
ya fice da sauri......
Washe garin ranar ta kasa haqura ta isa sashen amarya, dai dai lokacin habbi ta fito da gudu
Sa'eed na biye da Ita daga baya....
Duk suka ja turus ana kallon kallon... Tamkar a mafarki salima ke ganin habbi da mijin da tafi so
fiye da komai a rayuwarta,
'barka da safiya anty xo ki xauna, cewar habbi tana kallonta qasa qasa...
tsananin ruďewa yasa tayi kan habbi suka fara kokawa, da kyar Sa'eed ya rabasu,
'munafuka, snatcher, azzaluma macuciya mai kwacewa mutane miji, sai da kika gama jin sirrina