Showing 33001 words to 36000 words out of 59977 words

Chapter 12 - BABANA DA MIJINA BOOK COMPLETE Fertymerh Zarah --.pdf

Unknown   

22 Mar 2025

4478




Kallo ďaya yayi mata ya gane she is in bad condition, jikinsa har rawa yake Idanunsa sun kawo
kwalla ya sunkuya ya sumbaci goshinta haďe da sarqe hannunsa cikin nata,


'I don't want you to die, pls karkije kibarni, my life will be useful without you,

Ta rumtse idanuwanta cikin azabar ciwo, hawaye ke fitowa a idanuwanta,

'yaushe xn haihu Deen? ya dubi cikin nata kafin ya maida kallonsa gun ta,

'da sauran lokaci but bari na duba Merah yaxo ya duba ki, ya fice da sauri.......

*

'Am tired salima, nagaji da wannan hali naki, aure xn qara.....


Hankalinta inyayi dubu ya tashi da jin kalaman Sa'eed, ta juyo tana kallonsa bayan ta jefar da
wayar dake hannunta,

'aure fa, meyasa Sa'eed?
'you know the reason and you are asking me why? ni xn xauna na koya maki yanda xaki tafiyar
da rayuwar auren kine, can you imagine wai Mai aiki yau ke wanke min undis, oh god wannan
wace irin rayuwace da tonon silili, Ni banida sirrin kaina komai nawa sai mai aiki tasani instead
of you,

'ynxu saboda wannan xaka qara aure Sa'eed, to kayi haquri baxata qara wankewa ba, xn riqa
haďawa mai wanki duka yana wankewa hope is ok?


Yayi shiru Kamar ya rufeta da duka yakeji, ya dafe kansa da hannuwansa duka biyu kallonta
yake cikin tsana da takaici yana tuna soyayyarsu kafin aure yanda take kula dashi kamar xata

haďiye shi dan so, ynxu sunyi auren ba kulawa, idan mai aiki bata mishi ba shi xaima kansa,
ruwan wanka ma shike haďawa kansa, barin ma ta kansa yaransu da basa Samin kulawa, dole
xai qara aure, amma wa yake so waxai aura?


Xuciyarsa nayi matuqar bugawa, matar amininsa yakeso, fatyma yakeso, he will be happy with
her, she is loyal to her husband inama shine, ynda yaga tana kula da Deedah bai damu ba, ya
rumtse idanuwansa, yana matuqar sonta, yana son bata kulawar da ta rasa gun miji itama ta
bashi kulawar da bai samu gun matarsa ba, ganin yayi shiru salima ta matso,
'kayi haquri xn gyara, ya dubeta Idanunsa jawur,
'kiramin Indo,
'me xatayi ma, gayamin xnyi ma,
'ki kiramin Indo nace..... ganin yanayinsa ya sa ta fice da sauri bata jima ba sai gata sun dawo
tare, Indo ta tsugunna gabansa, kallonta yayi,

'xaki aureni Indo..... Tambayar ta xo mata a baxata ta ďago tana kallonsa wani ihu da salima ta
sanya sai da suka tsorata gabaki ďayansu, tayi Kan Indo xata daketa ya tareta,

'wallahi ka aureta sai na kasheta na kasheka, Baka isa ba Sa'eed, ka cuceni ta soma kuka
sosai, yayiwa Indo alama ta fice, ta fita da sauri ya juyo gareta fuskarsa ba alamar Wasa,

'believe me salima and I mean it, idan har baxaki gyara halinki ba, aure xnyi, I can't continue like
this..... ya juya xai fice sai Kuma ya juyo,

'karki yarda ki taba Indo ko ki korata gidannan, idan tabarshi kema kin barshi dan bakida amfani
acikinsa......

Salima ta xauna gefen gado ya shiga duniyar tunani dole xata cnxa halinta ta kawar da Indo
daga mijinta,


*

Dr Merah da Dr. Deen ke tafiya suna tattauna Mgnr ciwon matarsa har suka isa ďakin haihuwa,

Har ynxu da sauran lokaci Deen, in lokacin yayi bata haihu ba dole xa'a mata tiyata,

Deen ya sauke numfashi da kyar yana kallonta itama idonta akansa tsoro ya cika xuciyarta gani
take kamar baxata tashi ba,


Merah ya cigaba da faďin, I don't want to miss my flight so xn damqawa Dr fatyma case ďin, ko

tiyata ne xata iya mata,

'Shikenan Dr. Merah, a tare suka fito suka nufi office ďinta,
Tana xaune tana duba wasu takardu suka shigo, ganinsu ya sanyata cire farin glass ďinta kana
ta tashi cikin girmamawa tana gaidasu,

'Uhm likita case ďin matar Dr Deen, xn damqa miki, idan bata haihu ba ayi mata tiyata ga files
ďin ta, jikinta ya ďauki rawa ta dubesa,


'why me Dr Merah, kabawa wani case ďin, am busy patients sun min yawa,

'I trust you fatyma, help me, Phoenix xnje by 10 o'clock, I nid to see sultan tun last week baida
lfy so I don't want to miss the flight....


'but likita, amma.... uhm.. Muryarta na soma rawa hankalinta ya tashi,

'why are you behaving like this fatyma, wannan bashine Karo na farko da kika soma tiyata ba,
ya ajiye file ďin ya juya da sauri ya bar office ďin, ta maida kallonta ga Deen tuni idanunta sun
kawo kwallah,

'what's wrong likita? ta girgixa kanta bayan ta ďauke guntuwar kwalla da ďan yatsanta, ta ďauki
file ďin tana dubawa,

'Hajara Deen, shine rubuce akai, ta rufe file ďin kamar xatayi kuka tsoronta ďaya ta karbi
haihuwar jaririn yaxo ba rai tafi kowa sanin Waye Dr Deen mutum ne mai matuqar son yara ya
jima yana kwadayin haihuwa sai wannan karon matarsa ta samu, yana aiki a paediatric, amma
saboda son da yakewa matarsa baxai misaltu ba, bashida buri ko mgn a asibiti kamar ita
musamman da xata haifa masa yaron, idan yaron ya mutu a hannunta fa.....

'please fatyma let's go.... ya Katse mata tunani, tayi firgigit tana kallonsa kafin tabi bayansa,

'naquda taxo gadan gadan sai dai baxata iya haihuwa da kantaba dole yasa hannu ayi mata
tiyata, ta Kira nurse's suka turata theater room harda Dr. Deen aka shiga,

Komai akan idonsa yanda fatyma ke tafiyar da aikinta, yana kallon lokacin da ta fasa cikin
matarsa nurses na taimaka mata, tana ganin jinjirin ta kasa cirosa saboda tsoro Kuma yana
raye, sai tayiwa wata nurse da nuni akan ta ciro jaririn da kanta,

Bayan ta ciro suka nufi gurin gyarashi Deen yabi bayansu farin ciki fal a xuciyarsa,

Iman murmushi tayi cikin samun nasara kana ta soma ďinke uwar,

Baba dake ďakin a labe kusa da Iman yana jiran ta karbi haihuwa ya xuqe jinin jaririn ya bata rai
sai dai tsawar da sima tayi masa ta tsoratashi, ba Wanda yaji sai Shikadai kamar yanda bamai
ganinsa,

_'ka ďauki jinin matar tunda ta hana jinjirin, ka kashe uwar._


Bayan sun kammala gyara maman suka nufi amenity da Ita, batasan meyasa take jin mutuwar
jiki ba, har wani Xaxxabi takeji ga xufa dake karyo mata ta ko ina,


Ta fito ta sami Dr Deen rungume da jinjirin sai faman murmushi yake, farin ciki fal a xuciyarsa, ta
leqa yaron kyakkyawan gaske ne tana son karbarsa tana tsoro, murmushi kawai tayi a xuciyarta
tana Allah ya raya yaron,


Wata nurse ta fito da sauri tana faďin,

'she is bleeding through her nose and mouth,

'who? Fatyma ta tambaya hankalinta a tashe, shima Deen ya juya yana kallon nurse ďin jin ko
Waye,

'Mrs Deen....

Fatyma da Deen suka nufi ďakin, bakinta da hancinta sai jini ke xuba, Dr ya miqa jaririn ga wata
nurse ya nufi hajara ya rungumeta xuwa jikinsa, tana son masa mgn ta kasa, akwai abinda
takeson gayamasa bakinta ya qi buďuwa haqoranta sun kafe,

Fatyma Kuwa kusan mutuwar tsaye tayi kamar mutum mutumi ta xama sai kallo da take binsu
dashi idanunta na fitar da kwalla, kafin wani lokaci rai yayi halinsa batasan da haka ba sai da
taji Dr Deen yana faďin,

_'Inna lillahi wa inna ilaihir raji'un_ kusan sau uku, kafin ya ďora kansa jikin matar yana kuka,
itama batasan sanda Kukan ya xo mata ba.



My wattpad Phertymerh1

[20/03, 5:12 p.m.] Pherty :

*Babana da mijina......*


©Fertymerh Xarah


30



Da kyar ta iya janyo qafafuwanta ta fito daga ďakin, idanunta sunyi luhu luhu sun kumbura,
ga xuciyarta dake tashi kamar mai jin amai,

Tana tsaye a corridor tare da Dr Umayma taga an fito da gawar, ta ďauke kanta gefe hawaye
sharrrrr kamar da bakin fanfo,

'ya salam Dr fatyma, kinbi kin damar da kanki tunda bake kika kashe ta ba miye na kuka haka,
kwanakinta suka qare, ba itace gawar farin a hannunki ba meyasa kika damu,

Ta girgixa kanta tana share kwalla,
'ba komai, ina tausayin Dr Deen ne, da jaririn da aka bari,

'hakane amma kidaina damar da kanki,

Iman ta matsa gefe da sauri tana kwararo amai, Dr Umayma sai sannu take mata, ta bata pure
water dake hannunta ta kuskure bakinta,

'xo muje na duba ki, banyarda dake ba likita, iman murmushi kawai tayi tabi bayanta,

'oh God, jininki ya hau sosai 180, narasa gane kanki fatyma, meke damunki,

Iman ta sunkuyar da kanta qasa tana faďin,
'bnda damuwa bayan stress, bana samun barci I don't know why, ga aikin asibiti hutun da kuke
samu bana samu, komai Dr fatyma komai sai ni fa......

'Gaskiyane Kuma fa likita, amma ai Kuna da farin jinine, mgnr gsky ma cikin mu kin fimu haquri
shiyasa kowane likita ya tashi kece,

Iman ta sauke ajiyar xuciya tana yatsina fuskarta,
'Ina ji inada ciki ne, na jima bnsha tablets ďina ba,

'nima nayi xaton haka, Allah ya tsayar da wannan?

'Amin ta faďa xuciyarta a raunane,



Tun da ta dawo gida take kwance, sallah kawai tayi abincima ta kasa ci, fauxie na gefenta sai
surutai take mata,

'kiyi shiru haka fauxie, ke bakya gajiya ne,

'anty kema kina rubuta noise makers ne? Iman ta dubeta,

'eh idan bakiyi shiru ba gobe xnsa anty tayi maki bulala, I fauxie ta matsa baya kaďan da Ita
tana kallonta a shagwabe,

'anty ai ba class bane keba monitor bace,
'tor kije falo kiyi surutunki ko kije indasu adama, kina damuna anan Inaso nayi barci, fauxie ta
dawo jikinta ta kwanta tana faďin,

'anty jiya nayi mafarki,
'mafarkin me,
'baba ya mutu..... sai da gaban Iman na faďi ta dubi yarinyar,
'Kuma anty, malam yace duk wanda ya mutu baya dawowa, wai xa'a sanyashi a rami a rufe da
qasa, baxai qara cin abinci ba kuma baida friends shi kaďai xai xauna wai hakane anty? Iman ta
gyada Kai tana kallonta,

'Kuma anty wai malam yace idan ka riqe sallah itace xata tayaka kwanciyar kabari,

'idan ka riqe karatun qur'ani watarana xai yi ceto a gareka, anty wai hakane? ta gyada Kai tana
kallonta har lokacin jikinta a sanyaye yake da Kalaman yarinya,

'tor anty idan baba ya mutu shi qur'ani baxai cecesa bane?

'inji waye ai shi musulmi ne,

'tor anty ai baya karanta qur'ani, kuma baba baya sallah, na gayawa malam babana baya sallah
a class jiya,

Iman ta xaro ido tana kallonta,
'kin gayawa malam baba baya sallah ke uban Waye ya gaya maki baya sallah, (ta kai mata
duka ta goce tana tunxure baki),

'a'a kajimin yarinya, kewai ba aljannu akan kine Anya ke kaďai kike rayuwa kuwa? dole sai a

gabanki xaiyi sallah ne,

'anty nace malam yaxo yayiwa babana mgn ya dinga sallah shi kaďai nace kuma anty a.....

'shut up silly girl, why can't you control your mouth fauxie, angayamaki agaban kowa ake faďin
kowacce magana ne, shikenan is your life friends ďinki basu sanni ba ke kaďai suka sani xasu
riqa cewa babanki baya sallah tunda baki iya bakinki ba kuma kowa xai sani kiji kunya,

'anty bana jin kunya cos he is not my father, ai yace shi ba babana bane indai na ce masa baba,
wai yaya ne babana, hakane anty?

'ke xo ki fice min daga ďaki inba haka ba bakinki xaiyi jini, ta diro daga Saman gadon ta ďauki
tedy ďin ta tana kallonta,

'Anty Kice adama tayi tuwon semo, da miyan kubewa,
'in kinje ki gayamata,
'Anty in Kira Suleiman?
'me xaiyi min, inace nace ki fice daga ďakin nan ne?
'anty Kice ya siyomin ice cream babu a fridge,
'baxan ce ba ni komai nadaina siya maki a gidannan tunda bakyajin mgn baxaki daina surutu a
rayuwarki ba,

'Anty kiyi haquri nabari baxan qara ba, tayi mata banxa,

'please Anty, nan ma ta kyaleta, ta qara matsowa,
'kinji anty.... tasan baxata kyaleta ba,
'tor naji,
tayi dariya ta fice da gudu tana kiran Suleiman....
[20/03, 9:35 p.m.] Pherty : Bata ganshi a gidansu ba sai ta nufi gidan baba tasan baxai
wuce can ba,

Da ďar ďar ta shiga falon a hankali take kiran,

'Suleiman, Suleiman..... batason wani ya jiyota ko cikin masu aikin gidanne,

Yanajin muryarta ya fito daga wani ďaki a hanxarce,

'yar amana dama ke nake nema, xo kiji,

'anty tace kaxo ka siyomin ice cream,
'tor xo kigani, sirri xamuyi karki gayawa kowa kullum xn riqa goyaki muje yawo a Roba Roba
ďina kina so? ta gyada Kai tana kallonsa da murmushi, ya riqa hannunta yana waiwaye Kada a
ganshi,

'je ďakin baba ki ďibomin kuďi, kiyi sauri Kada wani yazo yagani, batare da tunanin komai ba ta
faďa ďakin tsafinsa, kuďi ne birjik a qasa ta ko ina, Akan gado a qasa sai faďowa suke ďaya
ďaya kamar yanda leaves ke faďowa a itaciya,

Ta kwashi kuďin tana kallon ďakin, har xata fita sai idanunta na sauka akan tedy ďinnan ta tsafi,
ta ďauka, sai taga wata kwalba da ruwa acikinta ga wani abu ja aciki yana yawo aciki
(rayuwarsa ce aciki cewar Sima) sai abin ya birgeta, ta duqa xata ďauka Suleiman ya soma
mgn,
'me kike jirane, ko kaďan ne ki fito Kada wani yagani, buqatata nasami na cnxa waya na kaiwa
ummata sauran, dan ma Ina sata Ina haďa kayan aure ynxu,

Ta juya ta fice tana waiwayen kwalbar Abinda ke ciki yana yawo ke birgeta ta qudira aranta xata
dawo ta ďauka,

Tana fitowa ya ďauketa cike da farinciki cos ta ďebo da yawa suka fito yana faďin,

'wannan kuďin haka kikace anjima naje xnce da baqar Leda, ya karbi kuďin ya cusa aljihunsa
kwata kwata hankalinsa bai kai ga tedy dake hannunta ba azatonsa tatace,

'Kada ki gayawa kowa kinji,
'tor xakaje dani yawo,
'kwarai ma kuwa baby, kina gaban mashin ďina, aike abinso ce gareni, gaki yar fara kyakkyawa
matar Manya ko? tayi murmushi tana kallonsa,

'muje anty tana kiranka,

Tana xuwa takai tedy ďakinta ta boye qarqashin gadonta bataso Iman tagani tayi mata faďa,


Ranar Deedah ya dawo suna xaune ďaki dashi take bashi lbrn abinda ya faru a asibiti,

'Allah yaji qanta amma Waye Dr Deen kamar nasanshi,

'kasanshi mana wannan na paediatric wanda muka taba kai fauxie gurinsa sanda tana Mura,

'na mantashi amma na tausayamishi kodan jaririn,

'idan ka ganshi xaka tuna, wani fari kyakkyawa haka, yanada fara'a sosai,

'kinaso kice yafini kyau kenan?

'chab ni na isa, akwai namijin da yafi mijina kyawu ne, kawai Ina misalta ma shine, yayi
murmushi ya ja dogon hancinta

'you are the best my only wife, Ina sonki Iman, itama murmushin tayi haďe da kwantawa a
qirjinsa,

Bayan sati ďaya tana shiga asibitin kayanta kawai ta ajiye a office ta nufi labour room tun kafin
ta shiga take jiyo kururuwar wata mata, da sauri ta qarasa tana tmbyr meya sameta,

'yauwa Dr help us, tana labour Kuma aljannunta suka tashi,

Iman ta matsa tana kallon matar a bakinta addua take, matar mai aljannu tana juyowa taga
Iman sai taga baba tsaye a gabanta, ita kaďai ke ganinsa saboda aljannunta, ta taso xata capki
Iman a xuwan shi xata riqa akayi Saurin riqata dai dai lokacin haihuwa na xomata,

Kwata kwata Iman ta manta bata hayyacinta saboda tausayin matar, sai kawai ta karbi
haihuwar, yaron na hannunta baba ya soma tsafin,

Idanun matar suka jujjuye, wani qarfi yaxo mata ta xabura da qarfi ta capko wuyan Iman ta
shaqureta iya qarfinta.



My wattpad Phertymerh1

[22/03, 4:45 p.m.] Pherty:


*Babana da mijina....*


©Fertymerh Xarah


31


....Sai na kasheka, sai na kasheka matsiyacin banxa, baka isa ka kashemin yaro ba, idan ya
mutu kaima sai ka mutu,


Idanun iman sun juye, sai kakarin mutuwa takeyi, nurses ďin sai bugun matar suke yayin da
wasu suka fita da gudu kiran masu taimako,

Da gudu Dr Bakori da Dr Deen, da Dr Chris suka shiga ďakin,

Sosai ta galabaita kafin su banbareta daga jikinta, ragwab ta xube gurin a sume, Dr Deen ya
ďauke ta da sauri ya fice da Ita Dr Fulani na bayansa yayinda sauran likitocin suka rufawa
marar lfy suna dubata sai fisge fisge take shi kansa baba tuni yabar ďakin ya bata tun lokacin
da yayi arba da matar yaji hankalinsa ya tashi,

Ba Wanda yayi xargin wani abu inda Iman ta sami sauqi kenan, kuma jaririn ya rayu sai dai har
lokacin Iman bata farfado ba ta jigata sosai,

'ko akira mijintane a sanardashi cewar Fulani,

'A'a kibarta xata farfado, wuyanta yayi ja sosai wannan ba qaramin riqo tayi mata ba cewar
Bakori,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login