Showing 39001 words to 42000 words out of 59977 words
Chapter 14 - BABANA DA MIJINA BOOK COMPLETE Fertymerh Zarah --.pdf
Unknown
22 Mar 2025
4475
for forgiveness Mai yiwuwa Allah xai iya yafe masa, Allah gafurun rahim ne shi mai
yafiyane ako wane lokaci, sai ya soma istigfari yana Mai neman yafiya ga ubangijinsa Mai
yiwuwa xai sami sauqin xuciyarsa,
A waje ya kwana cikin motarsa baya burin komawa Iman a ynxu har sai ya dawo normal, daďin
sa ďaya bai taba kissa ba sai dai yayi harbi a qafa ko kuma ya tsoratar da mutum idan yayi
masa gardama,
Sai da yayi sallar asuba kafin yaja motar yabar gurin, da Wannan Safiyar Deedah ya soma
xuwa inda sukayi sata yana maida kuďin dai dai yanda aka bashi nasa rabon ya nemi gafara,
wani gu akarba wani gu Kuma abar mishi an yafe, manyan kamfani da boutique ne kawai baije
ba, yana mai tsoron bayyanar da kansa gidaje kawai yake xuwa,
Bai manta da mutumin da sukaje gidansa Wanda ya xagesu a mota ba har gidan yaje ya nemi
gafararsa ya Kuma bashi kuďi sosai kafin ya dawo,
Akwai gurare da Dama inda baxai iya xuwa ba ya maida kuďin, sai ya ďauki sauran kuďin yakai
gidan marayu, daga nan ya wuce station yakai kansa ga hukuma shi mai laifine,
Suka masa kallon mamaki, wannan ma da qarfin hali yake sun kasa yarda dashi mai yiwuwa
wani plan ake son haďa masu basu sani ba, sai suka soma korarsa,
Ya basu address ďin su oga nass idan har basu aminceba suje xasu gasgasta yana so hukuma
ta kamasu domin sun dade suna taadanci a rayuwarsu, ya basu lbrn komai, sukace yaje gasu
nan xuwa,
Bayan barinsa gurin ya nufi inda su oga nass.
Bangaren Iman Kuwa, tunda Safiyar ta Waye take jinta wata iri tana suspecting haihuwace sai
ta Kira Sa'eed ko xai taimaka ya kaita asibiti yace yana xuwa baya gidane,
'Anty yau baby xaixo?
'Insha Allah fauxie,
'Anty wane irin abinci xaki bashi,
'madara,
'anty kibashi chocolate irin Wannan Mai daďi,
'jeki kiramin Suleiman fauxie, ta fita da gudu bata jima ba sai gata ta dawo,
'baya nan anty,
Ta Kira number Deedah still switch off, ga Sa'eed har ynxu bai xo ba, ta ďauki kayanta na
haihuwa ta sanya a mota,
'anty xn je asibiti inga baby,
'Aa idan kikaje surutun kima baxai barshi ya fito ba, kijira Suleiman idan yaxo akwai sauran
kayana sai ku kaimin kinji, ta gyada Kai tana kallonta, ta shiga motar har ta tayarda motar ta
juya taga fauxie tana kallonta,
'ki yafemin idan nayi maki wani laifi kinji qanwata,
'anty nima kiyafemin na yafe maki,
Iman tayi murmushi tana ďaga mata hannu itama fauxie ta ďaga mata hannu harta fice, kana ta
juya anan taci Karo da baba sai safa da marwa yake a gidan kamar wani xautacce, sai a lokacin
ta tuna da Abinda ta ďauko a ďakinsa da gudu tayi ďakinta, under bed ta duba suna nan ynda ta
ajiye ta soma dariya xatayi Wasa da kayan tasa hannu ta janyo tukunyar da matsafarsu ce aciki
ta ajiye gefe kana ta janyo kwalbar da rayuwar baba ke ciki, suna rungume a hannunta ta fito
falo,
Tana saukowa Kan step a hankali gudun wani ya ganta yaje ya gayawa baba aniyarta xata
maida masa wadannan sai ta boye tedy ďinsa tana Wasa da ita dan baxata maida ba,
Ta ajiye kayan a qasa taje tana leqa harabar gidan har ynxu yana tsaye bakin falonsa sai waya
yake faman Kira ga abokan harkarsa na gurin sima,
Ta dawo da baya da baya ta ďauki tukunyar, kana ta ďauki kwalbar by mistake tukunyar ta faďi
a hannunta qasa ta tarwatse jikinta ya ďauki rawa sosai taji tsoro shikenan idan baba ya gani
sai ya daketa bata manta Marin da yayi mata ba,
Fashewar tukunyar yayi dai dai da kamawar matsafan su sima da wuta, daga sima har gunkin
da suke bautawa da mutanen danaje gunta a Wannan safiyar sai da suka qone qurmus lokaci
ďaya wutar ta tashi from no where kafin sima tayi wani yunquri tuni takama jikinsu, tanaji tana
gani ta narke a gurin kamar ruwa rayuwarta ta qare,
Baba Kuwa Kamar yaji a jikinsa ynda tsigar jikinsa ke tashi, yana Waya kamar ance ya ďago
Kuwa yaga fauxie da wannan kwalbar,
Hankalinsa ya tashi taya ta sami kwalbar?
'ke fauxie... ke tsaya...
Tana jin muryarsa ta tsorata jikinta yafara karkarwa musamman yanda ya tunkarota, ta soma
gudu tana kuka a tsorace yana biye da Ita shikuma kamar mahaukaci sai ihu yake Acikin gidan
Wanda ya janyo hankalin mutanen gidan garesu,
Sa'eed Kuwa da sauri ya qaraso gidan sai dai a waje yayi parking motarsa shigowarsa gidan
tayi dai dai da faduwar fauxie qasa kwalbar dake hannunta ta gangara gefe ďaya ta fashe har
wani hayaqi ke fita daga cikinta,
Ihu baba ya Sanya yayi kanta da duka, bugunta yake ta ko ina kamar Wanda aka aiko ga
sa'ansa,
Nan take numfashinta na ďauke, bakinta da hancinta sai jini suke fitarwa, da qarfi Sa'eed yayi
kansa bai duba girmansa na kasancewa dajjito ba kawai ya ďauke shi da Mari, qoqarin baba na
ganin ya illata fauxie duk da bata Numfashi burinsa yaga ya kasheta da hannunsa ta mutu,
Sa'eed ya fahimci haka nan take ya ďauketa ya fita da Ita da gudu har lokacin bata numfashi
asibiti ya nufa da Ita,
Baba Kuwa tamkar wata Halitta ya dawo yanayinsa ya tsorata mutanen gidan, haqoransa sun
xaxxago, akaifun hannunsa dana qafafunsa sun qara tsayi kamar na doki, ga wani gashi daya
firfito a jikinsa tamkar wani dabba,
A gaban idon mutane yake cin Naman jikinsa, fisgar jikinsa yake yana ci sosai, wa'iya xubillah,
(Allah yasa mucika da imani muyi kyakkyawan qarshe Amin)
Masu hankali da hangen nesa a gurinne suka soma yi masa addua suna tofa masa daga nesa,
sai ya xube gurin ragwab, bakinsa da hancinsa sai fitar da jini suke kamar fauxie,
Nan take maxan gidan suka taru akansa aka daukesa aka sanya a mota akayi asibiti dashi,
Deedah Kuwa yana shiga gidan ya sami su oga nas kowane fuskarsa ba walwala, bai damu ba
ya sami guri ya xauna,
'ance an ganka station yau mekaje yi Ahmed? Yaji tambayar oga nass daga Sama,
'ba komai naje kan wani case ne Kuma komai ya daidaita,
'bn yarda dakai ba Deedah kwanakinnan ka cnxa mana, lokaci yayi da ya kamata mu rabu
dakai kaje ka huta a taka rayuwar mukuma mu cigaba da jin daďin duniyar mu,
Kafin Deedah ya ankara sai jin saukar bullet yayi a qirjinsa, ya dafe gurin yana kallon mai
Harbin oga nass ne, kafin yayi yunqurin sake Harbin Deedah shima yaji an harbesa a qirji,
police din dake bayan Deedah ne,
Nan take gurin ya kaure da harbe harbe (dama masu irin Wannan sana'a a haka suke qarewa
wasu Kuwa suke kashe junansu da kansu, Allah ya shiryamu da zuri'armu gabaki ďaya Amin)
Police ďin sukayi nasara Wannan karon sun kashesu da Dama yayinda suka kama wasu suka
sanya masu ankwa, oga nass na cikin mutanen da suka mutu,
Deedah Kuwa baisan inda kansa yake ba, numfashinsa ma da kyar yake fita, jikinsa duk jinine
ga bakinsa ma ya soma fitar da jini sai suka garxaya dashi asibiti,
Iman Kuwa tun bayan xuwanta asibitin Dr Merah ya duba ta,
'yace da saura likita, amma kafin lokacin idan kina iyawa kiďan yi exercise ko kaďan ne,
Tayi murmushi dama ba naqudar takeji sosai ba, sai ta fito harabar asibitin anan ta ci Karo da
Dr Deen,
Bayan sun gaisa yake tambayarta lfyr jikinta, tana gayamasa maimakon ya shiga asibitin sai ya
biye mata suna exercise ďin xagayen asibitin suke a tare suna hira,
Haka xuciyarsa take mai tausayin mata ne musamman masu irin Wannan lalurar, yana tuna
matarsa itama yakan sata ta xagaya Acikin gida, kasancewarsa da Iman yau yasa komai ya
dawo masa sabo,
Sun xagayo kenan taga motar Sa'eed ta shigo asibitin taja ta tsaya tana kallonsa,
'Wayyo Sa'eed bai sameni gida ba shine ya biyoni har asibiti, Dr Deen ya juya yana kallon inda
take kallo tana Mgnr dai dai lokacin da Sa'eed ya fito ďauke da fauxie a hannunsa,
Turus taja ta tsaya, fauxie ce meya sameta, taja ta tsaya idanunta a bude hankalinta a tashe har
ya iso,
Yanda taga fuskarta a kumbure Kuma ko ina jini hankalinta yayi matuqar tashi ta fashe da wani
irin kuka tana ganin Dr Deen ya karbeta yayi cikin asibiti da Ita, sai suka juya suka bi bayansa
da sauri,
Lokaci ďaya aka xo da baba da Deedah asibiti, daukarta atare aka nufi emergency dasu domin
suna neman ceton gaggawa,
Dr Fulani taxo ta kirata bata gayamata komai ba sai da suka shiga inda aka kwantar dasu,
Cikinta yayi mata nauyi,
'me nake gani yau ni fatyma, *Babana da mijina*, meke faruwa meya samesu haka, Waye yayi
masu wannan aikin har fauxie,
Sai ta ruďe taje ga Deedah numfashinsa sama sama ne, kuka take sosai ta nufi inda mahaifinta,
Halittarsa ta tsoratata badan fuskarsa da muryarsa ba da ta qaryata Abinda idanuwanta ke
gano mata,
Surutu yake agaban likitocin dake kansa, duk abinda yayi a rayuwarsa tunda ya fara neman
siyasa har kawo ynxu sai da ya faďa,
Believe me Akan ruďewa musamman ma ga mai ciki Iman bata San lokacin da fitsari ke fita a
jikinta ba,
'baba ya kashe mata yayyunta da qannenta, ya kashe mata mahaifiya, ya kashe mata ya'yan da
take samu, ya sanyata a wani hali Acikin asibitin Wanda mutane suka soma xarginta, she can't
believe this ta rufe bakinta da hannayenta duka tana kuka sosai,
Dr Merah kansa jikinsa yayi sanyi sai yaji baxai iya taimakawa baba ba, yayi mummunan abu a
rayuwarsa Wanda Allah kaďai xai iya yafe masa tabbas baba baida imani da tausayi tunda har
xai iya sanya iyalinsa a Wannan hali, xai iya sadaukar da rayuwar iyalinsa saboda dukiya da
duniya to ynxu me gari ya waya, mecece ribar da ya samu a duniyar? Ina dukiyar daya tara
yake tinqaho da Ita, ina sima da yake alfahari da Ita yake bauta mata Waye xai cecesa a ynxu?
Dr Merah ya girgixa kansa shida sauran likitocin suka rufawa Deedah baya, na ganin sun cire
bullet ďin jikinsa sun ceto rayuwarsa,
Hankalinta baya jikinta, fauxie take gani, ga baba ga Deedah, tana ji tana ganin yanda baba ke
fisgar Naman jikinsa ci yake kamar wani dabba yana faďin Duk abinda yayi a rayuwarsa,
Tanaji tana ganin yanda yake shure shuren mutuwa, tana ganin lokacin da numfashinsa na
tsaya cak ya mutu, tana ganin ynda fatar jikinsa ke fita daga jikinsa tana yin wata Kala baqiqirin,
Ta fashe da wani irin kuka mai tsananin gaske wannan wace irin rayuwace take fuskanta,
Muryar Deedah takeji yana kiran sunanta sai ta nufesa da sauri lokacin an gama cire masa
bullet din jikinsa,
Dr Merah da Bakori baxasu jure ganin halin da Salihar mace take ciki ba a ynxu sai suka fice da
sauri suna hawaye cikin tausayamata, itama Fulani kuka take sosai ta fita,
Iman ta faďa jikinsa duk jini,
'ni nasa ka a Wannan halin, kafita kana fushi dani dama kace kome ya sameka nice sanadi, ka
yafe min Deedah, Ina sonka, baba ya mutu karka mutu ka barni Deedah, fauxie na can itama
xata mutu, idan na rasa ka da fauxie my life will be useful please stay with me Ahmed,
(muryarta harta dishe saboda kuka, ga jikinta har lokacin bai daina rawa ba, a rude take Kamar
wata xautacciya, sai faman rungumarsa take tana sumbatarsa,
Shima qanqameta yayi sosai a jikinsa yana tayata kuka,
'ki yafemin Iman na kasance mai laifi a gareki, na cutar da rayuwarki haqqinki ne ya kamani, ki
yafemin,
Ta ďago tana kallonsa tana share hawayen fuskarsa,
'burina a ynxu ka tashi, Dan Allah karka mutu kabarni, karka mutu Deedah, yaron mu xaixo a
yau, karka maidashi MARAYA, ka tausayawa rayuwarta, banda kowa bayan kai da fauxie a
ynxu.......tayi shiru sakamakon jin ynda numfashinsa ke fita, tanajin bakinsa na motsi da alama
kalmar shahada yake, ta tashi a ruďe ta janyo oxygen xata sanya masa, xaninta har ya kwance
a gurin under wear ne kawai a jikinta bata damu ba,
'please Deedah, don't..... karka tafi please,
Ta taba shi baya Numfashi,
'No Deedah will not die, Deedah baxai mutu yabarni ba, Deedah I know suma kayi ka tashi
please, ta soma jijjigashi ta dubi gawar mahaifinta kafin ta maida kallonta garesa,
*BABANA DA MIJINA* baxasu mutu su barni ba, *babana da mijina* basuxo duniya a tare ba
baxasu je su barni ba, *babana da mijina* suka ďai nake da aduniyarnan they can't die at the
same time su barni,
Jin abu nabin qafafuwanta yasa tayi Saurin dubawa, jinine ke xubowa daga qasanta, wani irin
ciwon mara na taso mata lokaci ďaya, qafafuwanta suka riqe.......
My wattpad Phertymerh1
*Babana da mijina*
©Fertymerh Xarah
*Dis page goes to masoyan babana da mijina, tnkuuuu ol for your love and care, Pherty loves
you more*
33
Har lokacin bakinta yaqi rufuwa, Deedah take kira kamar ranta,
Nan ta durqushe qasa riqe da mararta,
Tana haka sai ga likitocin sun shigo,
Ganin yanayinta sukayo kanta ,numfashinta na fita da sauri da sauri kamar xai ďauke,
Dr Fulani da Dr Merah suka riqata ta tashi, suka ďorata akan sick bed ,
Da sauri Dr Deen yaja gadon sukayi waje da ita,
Fauxie a ruďe ta farfado, sai kuka take sosai tana kiran anty, taqi yarda kowa ya tabata daga
cikin nurse ďin saboda a firgice take,
Sa'eed ne a waje tsare da Ita baisan abinda ke faruwa game dasu Deedah ba, yana xaune
yajiyo kukan fauxie a inda aka kwantar da ita, ya tashi da sauri ya shiga ďakin,
Tana xaune akan gadon asibiti, idanunta a rufe take Kukan tana weaving hannunta sai faďi
take,
'don't touch me..... don't touch me,
Ta soma qoqarin saukowa akan gadon ga drip ana sanya mata,
Da sauri yaje ya riqata, tana ganinsa ta qanqame sa yayi Saurin riqa hannun da ake sanya
mata drip,
'yaya ka kaini inda anty, baba ya dakeni ka ramamin,
'ki tsaya da kyau karkiji ciwo, kinga ana qara maki ruwa,
Tabi hannunta da kallo kafin ta maida dubanta garesa,
'yaya ka kaini inda anty, ni ka kaini inda anty... ta cigaba da kuka tana son saukowa Saman
gadon,
'Bari acire mata drip ďin tunda qanwar Dr fatyma ce itama xata iya Kula da Ita,
Suka cire mata drip ďin, yana rungume da Ita a qirjinsa suka fito, idanunta sunyi jawur ga fuskar
ta kumbura, gefen idanunta yayi ja daga ciki baqaramin duka yayi mata ba, sai jikinta yayi xafi
rau, yanda ta qanqameshi ma ajikinsa abin tausayi ne,
Suna xuwa office ďin Iman bata nan ko Jakarta babu aciki,
'fauxie anty batanan Kinsan inda take xuwa,
Ta gyada Kai tana kallonsa, ya rufe office ďin suka fito,
Consultant suka nufa nan ma bata nan ba likita ko ďaya,
Tana ganin haka ta boye fuskarta a qirjinsa tana kuka,
'yaya ka kaini inda anty,
'Ina xnga anty ynxu fauxie, ai bata gida kuma, Ina ne take xuwa karban haihuwa kin sani? Ta
gyada Kai da sauri tana goge hawayen fuskarta,
Tana nuna masa suka iso labour room anan suka ci Karo da Dr Deen sai safa da marwa yake a
bakin qofar ďakin sai kace matarsace ke labour.
Yana ganinsu ya qaraso cikin mamaki,
'meyasa ka fito da Ita, bakaga halin da take ciki bane?
Fauxie naganinsa ta qanqame Sa'eed bataso ya karbeta,
'Dr fatyma muke nema tana kuka sai ta ganta ne,
'batada lafiya haihuwa xatayi,
Gaban Sa'eed ya faďi, yana sauko da fauxie jikinsa taqi sauka, baisan bata lfy ba sam,
meyiwuwa wannan dalilin ne ya sanya ta kirashi ya kaita asibiti,
Sam baiji daďi ba, sai ya ciro wayarsa da ďayan hannunsa a aljihunsa yana dialling number
Deedah, is switched off, ya maida wayar aljihun cikin jin haushin rashin samun Deedah,
Ya dubi Dr Deen sai yaga duk ya damu sosai ko miye dalilinsa na damuwa da halin da Iman
take ciki, nan take yaji wani abu ya taso ya tokare qirjinsa musamman daya qare masa kallo
kyakkyawan gaske ne da alama yana da jini da Shuwa Arab, ko sumar kansa baqa ce wulik a
kwance,
Dr Deen ya dubesa yana faďin,
'Waye yayiwa fauxie irin Wannan duka?
Sa'eed yaja dogon Numfashi yana faďin mahaifinta ne,
'metayi masa haka?
'shine ban sani ba nima, na sameshi yana dukanta ne,
Dr Deen yaja numfashi wannan mutumin bashida imani, ya tsanesa tun lokacin da yaji yana
wannan surutun kan abinda ya aikata a rayuwarsa, Allah wadarai ga mai hali irin nasa,
'amma kai yayan Iman ne?
'no abokin mijinta,
'kasan Baban ya rasu a ynxu, yana emergency aka kawoshi,
Wata irin faďuwar