Showing 27001 words to 30000 words out of 59977 words

Chapter 10 - BABANA DA MIJINA BOOK COMPLETE Fertymerh Zarah --.pdf

Unknown   

22 Mar 2025

4474

sun
shirya, sima na tsananin fushi da fatyma Kuma fushin sima bala'i ne, dan me fatyma xatayi
tsarin iyali bayan tasan cikinta shine abincinmu dashi xaka cimma burinka..... Baba ya dubeta a
raxane,

Tsarin iyali, bnsan tayi ba ya shugabata ynxu mecece mafita,

Mafita ďaya ce duk sanda fatyma xataje karban haihuwa kabita a boye ka karbo mana rayuwar
jaririn Inka sami dama harda uwar jaririn abamu jininta, idan tana tunanin ta hana mana cikinta
mukuma xamu janyo mata baqin jini Wanda mutanen asibiti xasu tsani ta karbi haihuwa har
hakan ya janyo mata matsala ta shiga tunanin duniya ta manta ko ita wacece tadaina addua har
burinmu ya sauka akanta...


Hakan yayi ya shugabata,

Abokinsa dake gefe ya kallesa lallai wannan uban bashi da imani dama an dauki rayuwarsu ne
su huta da quncin duniya,


Abu na biyu kuma xaka maido fauxie a jikinka ka shagaltar da Ita kamaidata kamar da idan
lokaci yayi xn gayama abinda ya kamata kayi,


Ya gyada kansa, godiya nake ya shugabata,

Sima ta juya ga wani da bai dade da shiga harkarba ta nunasa cikin tsawa da fushi,


Mun umurceka kabamu mahaifiyarka kaqi, idan kabari fushin sima ya sauka akanka duniya xata
juyama baya kuma kowa xai qika ya gujeka.....


Kiyi haquri ya shugabata Ina matuqar son mahaifiyata, itace gatana a duniyarnan ta wahala
dani kibarni da Ita.....


Ta ďauki wata mugunyar dariya sai da ilahirin gurin na amsa kafin ta tsaida,


'baka isa ba, kai baka isa ba, dole sai ka bada, kowa da kake gani gurinnan, ya rasa Abinda
yafiso a duniya, wani uwa, wani uba, wani mata, wani Ya'ya dan haka kaima sai kabada, dolene
ka bada, kai kuma kasami abinda kakeso wato *kuďi* ta juya gana kusa dashi,


Sima na godiya da jinin abokinka, ta wadatu anjima xakaga kuďi, da haka tabisu ďaya bayan
ďaya har suka gama meeting ďin su.

*

A daren ranar ya fito daga wanka yana tsane kanshi da ďan qaramin towel,

Tana kwance rigingine a gefen gado cikin doguwar rigar barci mai tsantsi marar hannu, ruwan
madara,


Kyawawan qafafuwanta da cinyoyinta a miqe sambal tayi xurfi acikin tunanin kowane hali fauxie
take ciki a ynxu,

Son matarshi da qaunarta yana qara girgixa xuciyarsa yana hargitsa gangar jikinsa,

Bayan ya gama shirinsa na kayan barci ya kwanta a gefenta sai yaji jikinta xafi rau,

Ya juyo da Ita sosai yana fuskantarta, ta buďe idanuwanta a hankali Waďanda suka qanqance
sukayi jawur tana kallon sa, shima ita yake kallo,

'Naji jikinki da xafi meyake damunki,
'nima ban sani ba,

'you are silly and nonsense doctor Iman, bakisan meke damunki ba, ya tashi a fusace yana
faďin tashi muje asibiti a dubaki,

Ta fashe da wani irin kuka mai tsuma xuciya, jikinta har rawa yake, batasan meke shirin faruwa
da Ita ba nan gaba dan tana da tabbacin xuciyarta gab take da bugawa, ya dawo Saman gadon
yana kallonta,

'meke damunki, tell me,
'ďaxu koda na duba jinina ya hau sosai, bansan inada hawan jini ba sai a yau, ya xnyi da
rayuwata, sosai ya gigice ya riqota xuwa jikinsa,

'hawan jini Iman, menene damuwarki saboda me xaki kamu da wannan cutar, me kika nema
kika rasa a rayuwarki? ta fisge jikinta daga nasa,


'inada wata damuwa ne bayan ta *babana da mijina*,Kune damuwata Kune kuka sanyani a
Wannan halin, ni har sai yaushe xnji daďin rayuwata na xama mace kamar kowacce macen
aure, tun bayan mutuwar mahaifiyata ban qara jin daďin duniya ba.... ta soma kuka sosai,
hankalinsa yayi matuqar tashi da jin shine sanadi, how comes matarsa xata kamu da wannan
cutar ta hypertension, in Kuwa haka ne gwanda ya rasa komai dan farin cikinta gwanda ya rasa
aikinsa da komai dan ya xauna da Ita yabata irin kulawar da takeso, yasani rayuwar fatyma

abar tausayawa ce sosai duk da batasan sirrin babanta da mijinta ba, ya yarda xai bar komai
dan farin cikinta,

'he is ready to do everything for her to make her happy and feel she is the only one in his life,
sai ya matso sosai xuwa jikinta ya juyo da Ita suna fuskantar juna,


'tell me Iman am ready to change and I mean it, menene bakyaso daga gareni, ko aikina kikeso
na ajiye to make you happy?

'fitar dare nake so kadaina, ka xauna damu kaji matsalarmu, ka ďebe mana kewa ka Kuma
bamu farin cikin da Muka rasa, xaka daina yawon dare?

Yayi shiru yana kallonta cikin ido xuciyarsa na bugawa, soyayyarta ta rinjayi xuciyarsa sai ya
maidata qirjinsa ya rungumeta yana shafar kanta,


'nadaina, nadaina Iman kema ki cire damuwa da tunani a ranki, saboda jininki ya sauka
banason Wannan cutar.... Magana yake kamar xaiyi kuka,


Karka damu, ynxu da ya hau sosai yanada nasaba da halin da fauxie take ciki....

'fauxie xata sami sauqi ki kwantar da hankalinki.


Pherty novels.....

[08/03, 8:14 p.m.] Pherty: *Babana da mijina*


©Fertymerh Xarah


25


Da tunani iri iri Deedah ya kwanta a ranar, barci ya kasa daukarsa har lokacin da Iman tayi
barci sai ya gyara mata kwanciyarta ya lullubeta kana ya sauko daga Saman gadon ya fito,


Da sanďa ya fice daga nasu gidan ya nufi gidan baba, ba kowa ko Motsin mutum babu sai na
kukan tsuntsaye,

Batare da tunanin komai ba kai tsaye ya shiga falonsa dai dai lokacin da baba ya fito daga
ďakin bautarsa da kayansa jajjaye na tsafi hannunsa ďauke da kwarya jinine aciki,


Ganin Deedah na qaramin tsoratashi yayi saura qiris kwaryar dake hannunsa ta faďi a qasa,
Karo na biyu Deedah ya kamasa dumu dumu sai ya take fuskarsa bayan ya ajiye kwaryar a
gefe ya juyo yana kallonsa,

'Waye ya Baka ixinin shigo min gida a Wannan lokacin har cikin falo na,

'ba neman kai nake da kaya ba ballantana na nemi ixinin shigowa wannan falon, baba ya buďe
ido sosai yana kallon Deedah da mamaki, me yaron ke nufi kada dai ya rena sa ne yana son ya
manta shi surukinsa ne,


Deedah yacigaba da faďin,
'naxo kan mgnr qanwata fauxiya, nasan ciwon ta baxai rasa nasaba dasa hannunka aciki ba,
idan baka kyaleta ba wani abu ya sameta kasani tamkar a idon duniya ne,

'abin kunya, abin takaici da haushi yarinyar cikinka kake neman salwantar wa saboda neman
duniya, har akwai abinda xaka nema a duniya najin daďi kamar kasancewarka da Iyalanka, ko
kamanta haqqinsu dake kanka, idan yau ka faďi ka mutu gobe kacewa Allah me? Kana tunanin
haqqinsu ma xai barka, meyasa kake son kashe su, kaji daďi har Allah yayi ma kyauta da
yaran, ni shekarata uku da aure matata na samun ciki yana xubewa, ina son yara Kuma still
nake xaune da Ita cikin qauna da aminci,


Baba ya nuna sa da yatsa,
'kashiga taitayinka Ahmed, kafita daga idona ba ruwanka da iyalina,

'inada ruwa dasu kasancewar nike riqonsu suna min kallon miji, yaya kuma uba, wallahi idan
baka cire muguntarka akan su ba, *Ni Ahmed Deedah xan xama ajalinka*, I will not care da kai
ko waye, you are nothing to me, idan har fauxie da fatyma ba ya'yan ka bane don't ever call me
your inlaw ko kuma kariqa min kallon suruki,am not...... ya faďa cikin tsawa yana nunasa da
yatsa daga yanayinsa xaka karanci bacin rai sosai a fuskarsa,


'kafin ka xama ajalina ni xn xama ajalinka Deedah, kana raye kana gani xn kashe matarka da
qanwarka kafin na kasheka Kuma kafin nan sai na wulaqantaku a duniya na toxartaku yanda
kowa xai tsaneku, na rasa matata da Ya'ya na maxa ballantana waďanna mata, *Ni na kashe su
da hannuna*,ya faďa cikin tsawa cikin subutal baki,

'kai ka kashe su Alhaji Abdallah, har kake ikirari da wannan, Subhanallah....jikinsa na soma
rawa,

'na rasa matata na haqura ballantana su, tunda kayi gigin shigo rayuwata sai na kashe ka na
kashe fauxie na kashe fatyma......... kai yaji muryar Deedah tare da Kukan harbin bindiga,

Deedah ne riqe da bindiga ya harba kwaryar dake ajiye a gefe kana ya nuna sa da Ita Idanunsa
jawur,


Kukan Harbin bindigar ya tayar da Iman daga barcin da take, ta duba gefe ba Deedah gabanta
yayi matuqar faďuwa ta sauko da sauri tana kiran sunansa a hankali,


'shoot me Deedah idan kana tunanin bullet xai iya shiga jikina, ko kana xaton a banxa nake
xaune, you can't kill me sai dai ni na kashe ka, get out of my house,


'I promise you ni Deedah na ďauki alqawarin baxaka iya cutar da kowane daga cikin mu, kana
nan xaka ga qarshenka haqqin Waďanda ka kashe ma baxai barka ba nima baxan Barka ba, for
now danasan kowaye nasan mugun abun da ka aikata sai kayi danasanin sanina a rayuwarka,
ta cikin ruwan sanyi slow poison xn xamema Kuma batare da fatyma ta sani ba,
'ka iya bakinka Deedah akaina, a ynxu xn iya nakasaka kaxama abin kwatance a gurin su....


Hankalin fatyma tayi matuqar tashi, tana sanye da hijab ta fito daga gidan, taji Kukan bindiga a
Ina ne, ina Deedah ya shiga a Wannan daren bayan yayi mata alqawari baxai qara fitar dare ba,


Tana tsaye gurin taganshi ya fito gidan baba, a yanda ta lura kuka yakeyi taga yana share
hawayen fuskarsa har kamar baya kallon gabansa, ta maida kallonta gidan baban tana ganin
inuwarsa a tsaye ta window tor meya hadasa da Deedah, yaushe ma Deedah yaje can kuma
Kukan miye Deedah keyi, ta juya tana kallon inda Deedah yake wayam babusa babu alamarsa
ya fice daga gidan, ina ya nufa?


Da sauri taje bakin gate tana dubawa ko inuwarsa babu hankalinta yayi matuqar tashi, kada dai
baba ya kori Deedah ne daga gidan, har xataje inda baban sai ta fasa ta fito nan bakin gate ta
xauna tana jiran Deedah acikin wannan daren babu tsoro a xuciyarta burinta taga mijinta taji
dalilin kukansa.

[08/03, 10:01 p.m.] Pherty: *

Deedah Kuwa tafiya yake yana tunanin maganganun baba, kuka yake sosai bai damu da inda
xaije a wannan daren da nisan tfyr da xaiyiba,

Sai ynxu yake regretting rayuwarsa kasancewarsa ďan fashi, he loves fatyma, yana qaunarta
komai xai iya akanta,yana son kareta da qanwarta ga hannun axxalumin mahaifinsu, yana son
basu kulawa da farin cikin da suka rasa gun uwa da uba, yana son xame masu uwa ba uba
ba......

Tafiya yayi sosai acikin wannan daren kafin ya iso gidan oga nas, qofar ya soma bugawa
ahankali, duk yaran dake gidan suka tashi da sauri kowane da bindiga a hannunsa haka shima
oga nas xaune da qatuwar bindiga a hannunsa yana kallon qofar da Deedah ke bugawa a
tunaninsu hari aka kawo masu,

Mutum ďaya ya buďe qofar tare da nuna Deedah, suna ganinsa suka ajiye bindigoginsu suka
koma suka xauna,

Kai tsaye inda oga nas ya nufa suka sami guri suka kebe dan yayi mamakin xuwan Deedah
haka,


'kayi haquri idan na batama a tsawon xaman da mukayi da kai, daga yau nadaina fashi......
Dariya sosai oga nas keyi har yaransa na jiyosa yana kallon Deedah,


'ta yaro mai take bata qarko, ai baka isaba, idan kaga kabar wannan sana'a to ka mutu
acikintane, inaaaa waye kai,


Deedah ya murtuqe fuska,
'na kasance da kai tsawon shekara uku ina yima aiki, bn taba nuna gaxawata akan kaba, ina
shiga haqqin matata, idan bata yafemin ba Allah baxai barni da haqqinta ba, nagane wannan
sana'a bamai kyau bace agareni da kai Ina roqonka kaima ka shiryu kamar yanda Allah ya
shiryani kadawo hanya kadaina fashi,

'saboda matarka xaka bar wannan aikin, to ai kamar baraxanace ga rayuwarta, nasan ta nasan
asibitin da take aiki acan ma xn iya samunta na ďauke ranta da alburushi Kaga idan ta mutu ai
ba batun haqqinta dake kanka,

Sosai Deedah ya tsorata da Kalaman oga nas, yasan wayeshi yasan abinda xai iya da Wanda
baxai iyaba, wannan qaramin aikinsane dole ta ruwan sanyi xai biyo masa idan yana son suyi
rabuwar arxiki sai yayi shiru yana kallonsa,

'idan kanason kasancewa da matarka lfy ka xauna dani, shekarun baya musu bai taba hadani
dakaiba karka Bari mu somayi dakai Deedah,


Deedah ya tashi ya fice ransa a bace batare da yayi mgn ba, oga ya bisa da kallo Deedah
nason Wasa dani idan yayi sake sai in kashe sa dashi har matar tasa....


Koda Deedah ya dawo yasami Iman xaune bakin gate tana jiransa, tambayar duniya tayi masa
yaqi ya gayamata komai sai kuka da yake har wannan lokacin, ynxu shida iyalinsa suna tsaka
mai wuya,

Kukansa ya daďa tayar da Nata hankalin itama sai ta tsinci kanta cikin tayasa Kukan, a Wannan
ranar daga shi har ita bawanda ya rumtsa sai juye juye da suke faman yi,


Washe gari har sukayi shirinsu bamai walwala a fuska breakfast ma basuyi ba suka fice kowa
ya nufi gurin aikinsa,

Tana office ďinta xaune tana tunanin idan ta tashi xataje ta duba fauxie sai ga Deedah ya shigo
jikinsa a sanyaye,

Ta dubi agogo to ten ynxu, ta maida dubanta garesa bayan ya xauna farar takarda ya miqa
mata idanunsa jawur kamar xaiyi kuka,


Jikinta na rawa ta karba kada Deedah ya saketa ne, da kyar ta warware tana dubawa, ta barin
aiki ce.. ...ta ďago da sauri tana kallonsa,

Wane aiki Deedah?

'farin cikin ki shine nawa Iman, I promise to change, inason kasancewa dake kamar yanda kike
so nabaki farin ciki irin wace mata ke buqata a gurin mijinta shiyasa na bar aikina na banki a
yau, are you happy Iman?


'happy with what Deedah? Ta faďa da tsananin mamaki tana kallonsa ido a buďe,

'why xaka bar aikinka saboda ni, ni nace kabar aikinka, tell me Deedah idan Baka aiki what did
you want to do? Gida xaka xauna ni nafito aiki or what, akwai abinda ke faruwa tun jiya kaqi ka
sanardani, pls tell me miye damuwarka Deedah?

Ya xare baqin glass ďin idonsa, sai a lokacin ta lura da yanda idanunsa sukayi jawur da alama
yasha kuka, nan da nan hankalinta na tashi idanunta suka kawo kwallah,

'ba haka nake nufi ba Deedah, bnce kabar aikin ka saboda ni ba, training dakace na dare
kanayi nace Kabari, fitar dare nace kadaina Deedah ba aikinka ba.....


Pherty novels

*Babana da mijina.....*


©Fertymerh Xarah


26


Yayi shiru kawai yana kallonta, baisan yanda xai gayamata fitar dare baxata yiwu ya daina ba
saboda abinda oga nas ya faďa masa a daren jiya,


'Naga you have not sign it, so baxaka bar aikin ba, ta yage paper into pieces kana ta xuba a
dustbin, ta dubesa,


'kaje gurin aikinka tunda bnda muhimmanci da xaka gayamin damuwar ka, jiya naganka ka fito
gidan baba kana kuka, meyasa? Meya haďa ka dashi? Me ya kaika gidanshi bayan na gayama
abinda ke faruwa ynxu, kai tsaye ya bata amsa,

'saboda lfyr fauxie naje, tayi masa wani irin kallo,

'ban fahimceka ba, miye hadinsa da lfyrta mutumin da bai damu da Ita ba,

'yana da sa hannun a ciwonta, bakiga ynda ta rikice tana kiran sunansa ba tana sai ta kashe
shi, bakiyi noticing komai akai ba,


Tayi shiru tana tunani, mgnr Deedah gsky ce idan tayi laakari da Mgnr fauxie da ta gayamata

biscuits yabata taci, meke nan baba sihiri yakeyi ko malamai yake bibiya dan yaga bayanmu, ya
salam ta furta a hankali bayan ta dafe kanta da hannuwanta duka biyu xuciyarta har wani xafi
takeyi,


Deedah yace muyita addua Iman, kada ki tambayeni dalili, amma mu dage da addua Kuma
fauxie xata sami sauqi,

Tayi shiru tana kallon sa da tagumi idanunta sunyi jawur, dole tasa ido sosai akan mahaifinta
tana son sanin me yakeyi, nan da nan kwakwalwarta na soma tunano mata wasu abubuwa,

'lah anty dubi irin kayan baba....
'anty shi baba baxai shiga aljanna ba,
'baba baya shan sobo a cup ko battle sai dai a kwarya,
'baba yace sai ya kasheni, ya kashe ki kuma ya kashe yaya,
'anty ga baba can, kibarni in kashe shi,

Ta bigi teburin dake gabanta,
'Nooooooo ta faďa da qarfi, impossible.... Sai da Deedah ya tsorata da yanayinta,

'me kike tunani?tayi shiru,

'baba baxaiyi haka ba, baba baxai aikata haka ba, Akan wane dalili bayan yana da kuďi, mexai
nema a duniya ynxu? Astagafirullah tayi gaggawar tuba kan xarginsa da tayi haďe da kawar da
tunanin daga kanta, ta dubi Deedah,

'muje muga jikin fauxie....

*

Tana ďauke da wata qatuwar tedy a hannunta sai gudu take tana xagaye falon tana dariya,
Amira na bayanta yarinyar Merah kusan sa'anin juna ne,


Affiya dake xaune a tsakiyar falon ta dubesu,
'baxaku daina gudun ba sai kun faďi kunji ciwo?
'Mummy kice ta bani tedy ďita tunda ba daddynta ya siyamin ba,

'fauxie tace nima baba ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login