Showing 48001 words to 51000 words out of 59977 words
Chapter 17 - BABANA DA MIJINA BOOK COMPLETE Fertymerh Zarah --.pdf
Unknown
22 Mar 2025
4476
'kina tunanin har akwai wani abu daya shafi rayuwarki a baya wanda ban sani ba, fiye da
shekara muna tare kina nufin bakisan hali na bakisan ko waye niba, ban taba roqon mace ta
soni ba sai akan ki Iman, kinsan yawan matan dake bibiyata domin na auresu naqi saboda kece
a xuciyata Kuma baffa yafi amincewa dake, mecece ribar aurenki da mai mata kije masa da
qanwarki da yaronki....
'Acikin yan matan dake bibiyarka ka xabi ďaya ka aura Dr Deen, qanwata da yarona ko bada
aure ba xn iya Kula dasu domin Nafison rayuwarsu akan tawa Nafison farin cikinsu akan nawa,
Wannan Karon ya harzuqa and he mean it, ya haqura da Iman a ynxu bai taba rarrashin mace
ko roqonta akan taso Shiba sai akanta kuma take wulaqantashi, duk girmansa da ajinsa,
'Na tabbata ďan halak fatyma, kije gaki ga Sa'eed, ya tashi ya fice batare daya qara kallonta ba,
Nan take taji xuciyarta ta buga tabisa da kallo kada dai ya haqura da itane?
Daga inda take xaune tana jinsa yana kiran little akan yaxo su tafi,
She knows it Dr Deen yana sonta, kuma shi yafi dacewa data aura, shine baida mata shi kaďai
xai iya riqe yaranta ba tsangwama gashi yaran sunyi sabo sosai da baffa, amma Sa'eed fa?
Shima yana sonta shima xai iya riqa yaranta haka shima yana buqatar kulawar Mace tunda bai
samu agurin matar saba.....
Har dare yaran basu dawo ba tasan baxai wuce acan xasu kwana ba, ita a ynxu yaye little
xatayi ta huta tunda dama bai damu dashan mamma ba, idan ba Ita ta matseshi tabashi ba
baxai nema ba yanacin abincinsa sosai ga bakinsa ya saba dacin daďi kamar irin na fauxie duk
kalar kwalama xaka Deen ya siyo ya kawowa yaran harma Sa'eed.
Kwana biyu bata qara sanya Deen a ido ba ko a asibiti sun daina haďuwa, ya daina kiranta a
waya sai tayi qoqarin kiransa sai ta fasa kada dai da gaske yake ya haqura da ita,
A xahirin damuwarta a ynxu Iman na wani hali na soyayya, Wanda ita kanta batasan cewar
soyayyar ce ke dawainiya da xuciyarta ba, soyayyar Dr Deen Wanda a halin ynxu batasan halin
da yake ciki ba, ita dashi sai gani a nesa ko idan yaxo maida little shima daga gate,
Soyayyarsa a xuciyarta sai qara linkuwa take Kamar ana iza wuta, ta tuna ranar rabuwarsu ta
qarshe,
_'Na tabbata ďan halak fatyma kije gaki ga Sa'eed._
Sautin dake ta mata kururuwa a kunne kenan a duk lokacin data xauna ita kaďai, wanda ke
qara ruruta wutar nadamarta, irin nadamar da RAIHAN yayi a SALIMA MAKAUNIYA (shima
littafin Pherty ne), to amma rabuwar ta xamo mata jifa'i...dai dai wannan halin data tsinci
xuciyarta da ruhinta aciki na bege daso da qaunar gabaki ďaya,
Ta yarda harshe mugun abu ne, ya Allah kabamu linxaminshi a hannunmu, harshe yana kaimu
ga wuta, yana kaimu sa'ira Kuma yana kaimu aljanna, again yana lalata mana rayuwa, mu
dinga riqeshi ta hanyar tauna magana kafin mu faďeta,
Idan ya furta baya taba mayarda ita komai daďinta ko ďacinta, da Hausa (harshe), da turanci
(tongue) da larabci (Lisan), wata tsokace mai amfani daban daban da Allah ya halitta a cikin
bakinmu wadda in muka iya controlling ďinta xamu iya controlling ďin duka al'amuran
rayuwarmu,
Me xatayi tayi repenting kuskuren data tafka a baya, Dr Merah ya kamata ta tunkara ko baffa?
Waye xabinta a ciki, Dr Deen ko Sa'eed?......
My wattpad Phertymerh1
*Babana da mijina*
©Fertymerh Xarah
39
Yinin yau duk suna tare da Sa'eed, yana xaune a office ďinta tana duba patient, little kuwa
yana gun Deen tun jiya da yaje dashi bai dawo mata da shi ba,
Deen yaga xuwan Sa'eed asibitin bai damu ba a ynxu da yake yaqi da xuciyarsa na ganin ya
fiddata a ransa,
Sanda Sa'eed xai tafi taje ta rakasa ta dawo kenan ta tsinkayo Dr Deen da wata budurwa a
tsaye tana ďauke da little, yanayin ynda suke tafiya murmushi a fuskarsu kaďai xai nuna ma
masoya ne, nan take taji wani abu ya taso ya tokare qirjinta,
Kai tsaye ta nufesu, little dake hannun yarinyar ta fisge, budurwar tayi tsaye tana kallonta da
mamaki little kuwa kuka ya fara yana qoqarin sauka jikinta tare da miqowa Dr Deen hannunsa
alamar ya karbesa,
Dukkansu an rasa mai bakin mgn har ta nufi office ďinta, Deen yayiwa budurwar Sallama ya fice
da sauri yabi bayanta,
A office sai qoqarin goya yaron take amma yaqi, ya miqe mata a baya sai kuka yake,
Cikin xafin nama ya fisgo yaron daga bayanta haďe da hankaďata gefe, yaron ya qanqameshi
sai ajiyar xuciya yake,
Sosai little ya saba da Deen fiye da mahaifiyarsa, yasan Deen sosai ko muryarsa yaji da gudu
yake tunkararsa yana dariya,
Shi yake kallo a matsayin mahaifinsa, bai kuma aje shi nan kusa a xuciyarsa ba, Don ko kuka
yakewa uwar idan bai sa baki ya rarrashesa ba baxai yi shiru ba, haka inya qi cin cereal ko
abinci a hannunta indai yana gidan shike bashi,
Ta dubesa ranta a bace,
'kabani yarona,
Bai tankataba sai yaga little nason xuwa inda take da alama mamma yake son ta bashi, ba
musu ya miqa mata yaron ta karbesa a fusace ta ajiye akan sofa kana ta xagaya ta xauna inda
take duba patient, har lokacin kuma bai daina kuka ba,
Yasan baxata bashi ya sha ba yanda yaga ranta yake a bace to miye dalilin wannan fushin
nata?
Fushin bai sauka daga fuskarsa ba amma ya sassauta murya,
'Kiyi haquri ki manta komai ki daukesa kibashi abinci,
Cikin bala'i tace
'idan kai ka haifar min shi sai kagayamin haqqinsa dake kanka, Yanxu incire inbaka abinka,
Yayi murmushi ya ďauki yaron yaje ya ďora a jikinta,
'naji bani na haifesa ba, nima Kuma bn fidda rai ba inaji a jikina Allah xai bani nawa,
Sai taga idanunshi sun juye sun koma luv colour wani irin situation ne da baxata iya mantawa
da shi ba,irin halin da Deedah ke shiga kenan idan yana biďarta ba sai yayi mgn ba take
ganewa, dan haka sai taji tsoron shayar dashi a gabansa ballantana ma tun jiya ta yayeshi, sai
ta ďauko empty feeder tasa masa a baki yaqi karba, ta dubesa a raunane Idanunsa akanta cikin
bacin rai,
'tun jiya na yayeshi..
'what? Kin yayeshi wannan wane irin yaye ne?
'na yayeshi ďana ne nikeda haqqi akansa,
Ransa ya qara baci har ya juya sai Kuma ya dawo ya ďauki yaron ya fice a fusace ta bisa da ido
kawai,
Bata damu ba ta maida hankalinta ga duba files,
4pm ta isa gida yau, anan take jin labarin Deen yaxo ya kwashi kayan little duka ya tafi dashi,
ba Wannan ne damuwarta ba a Yanxu, qirjinta ke ciwo sun cicciko tun jiya ba'a sha su ba, ga
wani nauyi da suka mata har Xaxxabi take ji, daďin ta ďaya fauxie taje islamiya da xata dameta
ne da surutu, tana fashin sallah sai ta kwanta kawai batare da taci abinci ba,
Shiru shiru bata fito ba har magrib, fauxie ma batasan tana gidan ba tana can cikin gida tana
wasa, Adama ta shigo ta ganta a kwance,
'hajiya ba lfy ne yau kika xauna a ďaki,
'yauwa, kunun alkama ko kunun farar Shinkafa nake so kimin,
Shikenan tasa kai ta fice da sauri, sai ga fauxie ta shigo,
'anty ki Kira yaya yaxo yaje dani inda baffa tun jiya yaje da little bada niba,
Tayi mata banxa,
'kinji anty.... nan ma ta kyaleta dai dai lokacin wayarta na ďauki qara, tana dubawa taga sunan
salima kamar baxata ďauka ba sai ta ďauka,
'kin ban mamaki fatyma, ki rasa inda xakiyi xawarcinki sai akan mijina, kinci amanar
qawancenmu Kuma kinci amanar Deedah, abokin mijinki da qawarki saboda bakida hankali, to
ga gidan ki shigo ki xauna kigani idan xaki iya kishi dani, kuma kisani agola baxai xauna mana a
gida ba, ya Mtsewwwwww ta tsinke wayar,
'agola? Iman ta nanata sunan tana kallon wayarta, Yanxu yaronta ake kira agola?
'kinji anty... Fauxie ta katseta,
Cikin tsawa tace, ke kimin shiru banxa, get out please, da sauri ta fice cikin tsoron yanayinta,
*
Wallahi baka isa ba, kayi kaďan Sa'eed, kai ko kunya bakaji ka auri matar amininka,
'iyakar qarshen rashin kunyar kenan in aureta in kula da Ita in kula da yaronta shine na riqe
amana, inason Iman baki isa ki hanamin auren taba,
'wallahi koni ko ita a gidan,
'na zabi Iman,
'haka kace, haka kace?
'eh haka nace, to me kike min a gidannan ba abinda kikemin ba kulawarki ba kulawar yarana,
su kansu na tabbata idan na kawo Iman a gidannan xasuji daďin kasancewa da Ita, kewai ko
kunya bakyaji kullum sai anyi miki faďa akan yanda xaki kula da miji da gidanki, duk sanda xn
sami habbi a gidannan inajin yanda take maki faďa kike gwatsaleta, nagaji da xama a hakan
shiyasa na gayamiki xn auri Iman,
Kuka take shabe shabe, duk abinda ta samu a ďakin jifansa take dashi, yau takai salima harda
xagin Sa'eed, kuma tayi rantsuwa Iman bata isa ta shigo gidan ba indai tana raye, yasa kai ya
fice bai qara bi ta kanta ba....
Tunowa da Deedah da kalmar da aka jefi ďanta da Ita yasanyata kuka a ranar, har safiya bata
rumtsa ba kuma Sa'eed yaxo da kansa yabata haquri tare da rarrashinta, baxai haďe su a gida
ďaya ba kowa da nata gidan sai taji sanyi a xuciyarta ta qara amincewa da son da Sa'eed ke yi
mata.
Yau kwana uku kenan bataje asibiti ba tana gida ba lafiya, Deen bai gantaba Kuma bai damu
ba, amma yau yayi niyar kaimata little meyiwuwa tayi xuciya da yaron ne shiyasa ta daina fitowa
asibiti,
Tana xaune falo sanye da hijab ya shiga da Sallama, bai bari sun haďa ido ba, yanayin fuskarsa
kaďai xai nuna mata har lokacin yana fushi da Ita, duk sai taji wani iri a jikinta ta xuba masa
idanuwa tana kallonsa,
Gayen ya haďu qarshe ga iya shiga ta suit da shadda, kai har white cotton lace da qananan
kaya ma kyau suke masa, idaniya basa gajiya da kallonshi harga maza yan uwansa bama mata
kaďai ba, ga yawan sumar jiki data kai, bata taba ganinshi cikin rashin walwala ba kamar yau,
Taji sabon al'amari yana fisgar xuciyarta game dashi, tsigar jikinta na tashi, ji take kamar ta ďora
kanta a kafadunsa taji dalilin damuwar da yake ciki inda hali ma ta rungumeshi,
Kai tsaye ya nufeta ya ajiye little a gefenta, qamshin turarensa dana hucinsa suka gauraye suka
daki hancinta,
Ya ilahi ta furta a hankali tare da kai hannunta ta dafe qirjinta sabida Karfin bugunsa daya qaru,
meke damuna ne yau akan Deen? Juyowar nan da xatayi sai idanunsu cikin na juna yayi maza
ya ďaure fuska ita kuma duk kunya ta kamata tunda ya kamata tana mishi kallon kurilla kamar
bata taba ganinshi,
Daga kallon da yayi mata nan take ya gane bata lfy, idanunta sun xurma kaďan fuskarta tayi
rama har xaiyi mata mgn sai Kuma ya fasa yasakai ya bar falon, ta bisa da kallo,
Ta yarda ta saduda ta amince Deen ya haramta gareta, soyayyarsu ta xama mafarki mai daďi
irin Wanda ďan Adam kanyi ya farka yana mai cixon yatsar sa kasancewarsa reality,
_'dreams are concerned but not all dreams are born alive, some are aborted, others are still
born._
Kalaman..... Noble Laureate ZAINAB ALKALI.....
My wattpad Phertymerh1
*BABANA DA MIJINA*
©Fertymerh Xarah
40
Shin menene ya shiga kantane daya makantar da idanunta ga soyayyar Deen? Me Deen
yayi mata? Menene aibunsa? Me take nema agurin namiji da babu a gurin Deen? Sa'eed ma
yana da qualities ďin da duk mace take so ta mallaka a gun namiji, first class....
ta sauke ajiyar xuciya lokacin da taji little na qoqarin cusa hannunsa a rigarta da alama
abincinsa yake so, ta ciro hannunsa tana kallonsa,
'you are big enough da shan wannan yanxu little, xaka sha tea? ya girgixa kansa yana janye
hijabin jikinta, ta riqa hannunsa tana kallonsa ya fara kuka yana son kaimata cizo a hannu, ta
soma dariya tana yi masa gwalo, ya mintsini Kumatunta,
'tace wash wash, ya kyalkyace da dariya,
'dole kayi dariya tunda kayi mugunta, ta tashi dashi goye a bayanta ta nufi kitchen dashi...
Yana ganin tana haďa tea yasan ba mamma xata bashi ba ya soma kuka yana cusa hannunsa
cikin riga, ta fito dashi tana faďin,
'yau me ya shiga kankane na son mamma, ai idan kasha wannan yau xaka mutu, and I don't
want to lose you my boy, ta sumbacesa ya janye fuskarsa yana kuka, bata ankaraba cup ďin
dake hannunta yasa qafa ya bige, tea ďin ya xube, ta dubesa sai ma ya bata dariya,
Kukansa ya fito da dijeh tana faďin,
'Ashe mai gida ya dawo, Kukan me yake haka,
'yau rigima yakeji sai na bashi mamma, kinga yanda ya xubar da tea ďin dana haďa masa kixo
ki gyara gurin,
Tayi harabar gidan dashi inda motocin sa na wasa, idan tayi qoqarin sanya sa yaqi xama ya
qanqameta yana kuka, keke ma yaqi ya hau, duk inda tasan yake so takaisa yaqi, ta bashi ball
yaqi, abincinsa yake so, yau fitinar yaye xai mata ko banxa dama gashi da rigimar kuka, suna
haka sai ga Sa'eed yaxo, ya karbesa yana faďin,
'waya taba little yau,
'rigimar yaye yakeyi yau,
'kin yaye shine? Ta gyada Kai tana kallonsa,
'ai nayi qoqari shekara ďaya da wata takwas fa,
'yace hakane kam, ya juya dashi yana faďin bari muje mu dawo....tana tsaye suka fice cikin
mota ga mamakinta sai taga little yana dariya acikin motar sai tsalle yake batasan meyasa
yaron keson yawo ba kuma da maxa kodan ya kasance namijine oho? tayi cikin gida.....
2 days.....
Har lokacin ta rasa sukuni a xuciyarta kwata kwata Deen ya canxa mata ba kamar da ba, ita
dashi sai gaisuwa ko yaxo gidan inda fauxie da little xai xo, suyi wasar su ya fice wani sa'in ma
ya tafi dasu batare da ya kulataba, sai tayi qoqarin mantashi da ciresa a xuciyarta amma ta
kasa ba dan komai ba sai yanda yake Kula da yaran, yanda ya saki jiki dasu suma yaran suka
shaqu dashi sosai ranar da duk bai xo ba batada kwanciyar hankali musamman a gurin little xai
ta mata fitina har sai ta haďa sa da driver ya kaishi inda baffa, wannan na ďaya daga cikin dalilin
dayasa ta kasa cire Deen a xuciyarta, Mai son naka shine... (na manta hausar)
A yau ta shirya ta nufi gidansu Deen inda baffa tun kafin takai ga gidan ta tsinkayo motar Deen
a waje, taja tayi parking gefen titi, tana xaune cikin motar taga fitowarsa abinda bata sani ba tun
fitowarsa yaga motarta sai ya basar ya shiga motar sa yaja, ta madubi yake kallonta lokacin da
tayi parking gate ďin gidan,
Tana shiga gidan part ďin baffa ta nufa, a kullum xaka samesa da tulin littafan addini agabansa
yana dubawa, da Sallama ta shiga falon,
Ya amsa sallamar yana kallonta fuskarsa da walwala,
'nayi fushi, ance ďiya mata sunfi Ya'ya maxa kulawa da mahaifansu amma banda Fatima, yau
sati biyu ban sanyaki a idanuwana ba,
Murmushi tayi cikin jin kunyarsa ta qarasa ta xauna kan sofa tana gaidashi,
'baxan Karbi gaisuwar ki ba,
'kayi haquri baffa baxan qara ba ynxuma dan nayi fama da ciwo ne,
'Subhanallah kinga ban sani ba danaje duba ki, Anya Zaharadeen ya sani kuwa?
Tayi shiru kawai tana murmushi, tasan yasani bai damu ba a ynxu tunda baya son ta, tayi rau
rau da idanu ta, yanayin fuskarta ya fuskanci kamar da matsala,
'ko akwai damuwa ne fatyma? ta girgixa kanta har lokacin kanta na sunkuye, ya gyara xamansa
yana fuskantarta,
'ko har yanxu baki bani matsayin uba a xuciyarki ba, keda Zahara duk ďaya na ďauke ku ba
banbanci, ki gayamin damuwarki a matsayin uba ba matsayin uban Zahara ba,
'dama.. dama baffa Deen ya cnxa ne kwata kwata, naga ya daina walwala bansan meke
damunsa ba,
'ni banga ya canxa ba har ynxu yana yin komai nasa kamar da, haka yana walwala meyiwuwa
kece bakya gani amma kin tuntube sa da Mgnr? Ta girgixa kanta,
'xn tambayesa inji koda damuwa a tare da shi,
'amma baffa kada kace ni nace, yayi murmushi yana kallonta,
'tor shikenan fatyma, yau bakije asibiti ba,
'Gobe nakeso nafara fita, baffa xn maida little nan da mai rainonsa saboda yaron baya son
xama acan yafison nan,
'A'a kibar mai rainon, masu aikin gidannan ma xasu Kula dashi ya saba dasu sosai watarana
ma acan yake yini tare dasu,
Ta tashi tana faďin shikenan ba abinda xanyi ma ne?
'ba komai sai dai idan xaki dawo kixo min da irin Wannan dambun da kike