Showing 30001 words to 33000 words out of 59977 words
Chapter 11 - BABANA DA MIJINA BOOK COMPLETE Fertymerh Zarah --.pdf
Unknown
22 Mar 2025
4494
siyamin nawa, anty ta siyamin kuma ranar yaya ya qara siyamin wata
qatuwa,
Affiya tace ki aramata Amira, she is your new friend bakiga batada lfy ba,
Amira ta make kafadarta tana buga qafafunta a qasa,
'Ni baxan aramata ba sai ta bani, ta fashe da kuka dai dai da saukowar Merah, yanajin duk
abinda ke faruwa,
Amira baxaki arama qawarki tedy ba, ta gyada kai tana kuka, Merah ya karbi tedy hannun
fauxie ya miqa mata,
'ga kayanki, ba ruwana dake munyi faďa, juyowar da xaiyi sai yaga fauxie na kuka sai share
hawayen ta take da rigarta, ya dubi Affiya,
'Ina tedys dake gidannan,
'suna ďakin Ameera,
Ya riqa hannun fauxie daina kuka muje inbaki wata kibarta da abinta, Ameera tayi Saurin miqo
mata tana faďin,
'daddy gashi na aramata,
Fauxie taqi karba,
'daddy wai bataso kace ta karba..... Sallamar su Iman ta Katse su, da sauri fauxie ta juya jin
muryarta suna haďa ido ta saki hannun Merah taje da gudu ta rungumeta, sosai Iman ta
qanqameta a jikinta cikin tsantsar farin ciki ganin ta sami lfy,
Slaves ďin dake falon suka soma fita da sauri yayinda wasu suka fara hidima da tarbon baqi,
Deedah ya bashi hannun suka gaisa kana suna xaxxauna, iman ta gaisa da affiya da Merah,
'Dr kinga fauxie ta sami lfy tun kafin ayi mata komai abin kamar sihiri, tayi murmushin yaqe
xuciyarta na bugawa,
'Ina godiya sosai Dr Merah, farin ciki na a yau ynda na sami fauxie Allah ya qara kiyayewa duk
suka amsa da Amin,
'Ameera taxo ta kawo mata tedy ďin ta aramata,
'Banso ai anty nima inada tawa tedy ko? ta gyada Kai tana kallonta,
'Kuma ai anty tafi tata kyau ko, iman ta girgixa kanta, fauxie ta bata fuska xatayi kuka,
'tafi tata kyau,
Ameera Tace ai nima inada su da yawa daddy ya siyamin, ke kuma babanki bai siyamaki ba
Yaya ai baba ya siyamin ko? Kuma babana yafi daddy ki kuďi ai,
'qarya kike daddy yafi babanki kuďi,
Kuyi shiru hakanan, faďa ya qare cewar Iman,
Merah yace qurciya ke damunsu kibarsu, yau Ina off shiyasa bn shiga asibiti ba,
'naga alama ai,
(Faďan dai bai qare ba tsakaninsu)
'daddy ya siyamin keke da Mota, kuma yace xai kaini Phoenix inda yaya sultan inyi karatu,
'ai nima baba yace xaije dani India inyi karatu irin na anty, kuma ya siyamin Mota, harda soja
aciki da bindiga, kuma ya siyamin gida qatoto harda jirgi, Amira ta dubi Merah,
'daddy nima xaka siyamin gida da jirgi? Ya gyada kansa yaran ma mamaki suke ba kowa a
falon, ta dubi fauxie tana dariya,
'nima daddy xai siyamin,
'fauxie tace ai baida kuďi irin babana,
'daddy yana da kuďi masu yawa acikin drawer,
'baba yana da kuďi da yawa da yawa acikin ďakinsa, sun xubo da yawa qasa a Sama ma suke
faďowa ko anty? Ta juya tana kallon Iman cikin shigar tambaya.....
*BABANA DA MIJINA......*
©Fertymerh Xarah
27
Babana yana da kuďi da yawa da yawa acikin ďakinsa, sun xubo da yawa qasa a Sama ma
suke faďowa ko anty? Ta juya tana kallon Iman cikin shigar tambaya......
Deedah yayi xuruf yace waďanda aka ďora akan drawer ne ke xubowa, kuma ai bamasu yawa
bane, ta juya tana kallon Amira,
'tor kingani, tayi mata gwalo tana dariya, Amira ta faďa jikin Merah tana kuka, ya cirata yana
faďin,
'is ok, daddy ma akwai kuďi har akan drawer, itama ta juyo tana yiwa fauxie gwalo,
Sosai yaran sun baiwa affiya dariya, iman Kuwa na xaune hankalinta baya jikinta sosai,
Sanda xasuje da fauxie suka je gida bayan sunyi godiya, gida suka nufa sunyi parking sun fito
dai dai da fitowar baba danashi escort a bayansa, daga Iman har Deedah ba Wanda ya kallesa,
fauxie Kuwa tunda suka haďa ido dashi take harararsa tana Jan tsaki da qaramin bakinta,
Ya tsaya yana kallon yarinyar cikin tsananin mamaki har suka fice,
Ke tsakin me kike, wakike harara haka? Cewar Deedah
Yaya babane, I hate him,
Yayi shiru kawai.....
*
Tana tsaye tana xare safar hannunta jikinta har wani rawa yake idanunta sunyi jawur,
Safiyar yau sau uku tana karban haihuwa jaririn yana mutuwa, abinda bata taba samu ba,
Lafia Lau suke haihuwa komai normal but kafin ta gama yankan cibi jaririn xai mutu,
Nurses ďin da take aiki tare dasu taga damuwa a tare da fuskokinsu da kyar ta iya jan qafafunta
ta nufi office ďinta da file guda uku a hannunta na dead case,
She is not happy today duk da san basuda tsawon Numfashi a duniya ne, taja numfashi a
hankali tana kallon time,
'wow fauxie is back from school, so batason barinta ita kaďai a gida saboda baba karka ya cutar
da Ita, ta tashi ta soma haďa kayanta, ta fito daga asibitin,
Ta buďe motar ta xuba shirgin dake hannunta, wata nurse ya qaraso da gudu tana haki,
"Dr fatyma ","Dr fatyma",
ta juya tana kallonta harta qaraso,
'kixo ki taimaka please wata patient aka kawo yanxu, baxata iya haihuwa da kantaba and she is
also bleeding, ta yatsina fuskarta,
'I have alot to do at home, ki Kira Dr Fulani ko Umayma,
'duk sun shiga meeting basu fito ba har ynxu,
Kasancewarta Mai sanyin xuciya Kuma xuciyarta Mai laushi da haquri batada Wulaqanci ko
kaďan ya Sanya likitoci da nurses suke qaunarta har patient ma domin ta iya tafiyar da marar
lafiya cikin sauqi,
Ta rufe motarta suka koma cikin asibitin,
Tana tsaye akan matar sosai ta galabaita da kyar Iman ta samu ta ciro yaron, kuka yaron keyi
kafin wani lokaci Kuma sai sukaji shiru, dubawar da xatayi baya Numfashi, wannan Karon har
xufa ke xubowa daga goshinta, baxaka iya gane wane irin yanayi take kai ba,
Cikin qarfin hali ta miqawa nurses jaririn, ba Wanda ke xarginta da komai sai dai yau sun rasa
gane meyasa jariri baya tsayawa a yau, ta wanke hannunta kana ta fice nurses su gyarata.
4:00pm
Deedah ya dawo gidan tayi mamakin ganinsa ta tambayesa, ya gayamata ynxu 4 yake tashi
daga gurin aiki har Sa'eed ma,
A yanda ya lura tana cikin damuwar sosai sai ya tambayeta, ta kasa boye masa damuwarta ta
xaiyana masa komai, ya dawo ya xauna kusa da ita,
Ba abin damuwa bane Iman, duk Wanda kikaga ya mutu lokacin sa ne yayi, inace agaban
nurses kike karban haihuwar, ta gyada kai tana kallonsa,
'so kinga ba Wanda xai xargeki kawai su ba rayayyi bane, ki riqa addua a kowane lokaci idan
zaki shiga haihuwa,
'shikenan nagode,
'haďa min ruwan wanka, ta tashi tana faďin,
'anjima xn fita super market,
Sai da gabansa na faďi daya tuna anjima xasu shiga wurin,
'ki canxa super market,
'meyasa ta tambeyasa tana kallonsa da mamaki,
'ba komai amma kada kije can,
'customers ďina duk acan suke Kuma abinda xn siye xn sameshi a can batare dana wahala ba,
'you can make customer in any where, banason kije Kuma kada kije, tayi shiru batare da ta
tankaba tayi shigewarta toilet,
To 6pm ta shirya ta nufi super market lokacin Deedah ma ya fita, bataga dalilin dayasa xata
canxa guri ba bayan ga inda ta saba siyayyarta, tabar Fauxie gida tana shan golden morn,
tana cikin super market din ta juyo Kukan bindiga, mutanen dake ciki suka soma fita da gudu
wasu Kuwa na neman mafaka,
Ta rikice ta rasa ta Ina xatabi, oh shiyasa deedah ya hanamata xuwa amma ta dage taxo,
Tana tsaye ta hangosu suna shigowa wasu sun tsaya daga waje ko wane fuskarsa a rufe
idanunsu ne kawai a waje,
Sosai sunyi barna a ciki Kuma sun kwashi kuďi da yawa, Deedah Kuwa baiyi niyar shiga ciki ba
amma tunda yaga motar Iman a waje hankalinsa na tashi ransa inyayi dubu ya baci wato sai da
taxo, da bindiga a hannunsa ya shiga yana nemanta tsoronsa kada a harbeta,
Iman Kuwa jikinta rawa yake sosai kayan dake hannunta duk ta xubar burinta taga ta fita daga
ciki, tana lababe kada su ganta dan taqi kwanciya a qasa kamar yanda sauran mutane sukayi,
Kicibis sukayi karo da juna, a raxane ta juyo cikin tsoro har hawaye sun soma xubo mata, yayi
Saurin toshe mata baki da tafin hannunsa ganin xatayi masa ihu, qamshin turarensa ya daki
hancinta gabanta yayi matuqar faduwa bai bari sun haďa ido ba yayi waje da Ita, ita kuwa
idanunta akan fuskarsa tana son gane wani abu,
Yana fitowa ya cillata a waje,tayi tangal tangal xata fadi,wani ya saita bindiga xai harbeta yayi
Saurin katsesa,
'Nooo don't shoot.....
tayi saurin tsaida hankalinta jin muryar da ta fito daga bakin mutumin daya fito da Ita waje kafin
ta juyo tuni mutumin yabar gurin bata gansa ba ta soma waiwaye,
'ke kibar gurinnan kada na ďauki numfashinki a ynxu....
da sauri ta juya jikinta har bari yake saboda tsoro da raxana.
My wattpad Phertymerh1
*Babana da mijina....*
©fertymerh Xarah
28
Tana shiga motar ta tabar gurin, bata jima da ficewa ba suka fito dai dai da qarasowar police,
Duk ynda sukayi basu ci nasarar kama ko ďaya ba kuma sunqi su bisu saboda suna tsoron
makaman dake hannunsu,
Deedah kuwa har sukaje suka kai Kuďin baya cikin walwala, iman ta taka dokar da yabata, da
wani abu ya same ta fa, sai ya nufi gida bayan sallar isha'i,
Niyarshi yau sai Allah kaďai xai saukar dashi daga fushinshi,
'duk daďin bakin nan nata da tattausan labbanta masu mantar da wani ďa namiji 'duk wani jinkai
taqama da muqaminsa,
'duk kissa da kisisinarta,
'duk lailaya da rarrashinta,
'duk taushin hannunta,
'duk kukanta da shagwabarta sunyi kaďan su sauke fushinsa akanta,
Amma Kuma sai me suna haďa ido da ita duk sai yaji jikinsa yayi sanyi, wani sonta na ratsa
xuciyarsa, sai ya ďauke kansa daga gareta ya nufi ďakinsa, fauxie na yaya sannu da xuwa bai
tankata ba, iman Kuwa kallo tabisa dashi kallone na tuhuma,
ta dawo da kallonta ga fauxie,
'sai me ya rage kuma?
'anty saura tracing,
'ke baxaki iya tracing cow bane, kiyi da kanki a exam baxaki ganni ba ballantana kiyi tsammani
xn maki,
tayi shiru tana kallon littafin, pencil a bakinta ta dubi Iman,
'anty yaushe xaki kaini inda Amira,
'ba ynxu ba sai kunyi hutu,
ta cigaba da tracing Iman na gyara mata harta kammala, ta maida littafin a Jakarta, fauxie ta
kwanta a jikinta tana waqe waqenta na makaranta har tayi barci, iman ta dubeta har wani daďi
taji datayi barci da wuri, Fauxiya akwai rigima masu aikin gidan ma bata bari ba, ga surutu
kamar hauka, ta dubi qaramin bakinta ta tsukeshi sosai, tayi murmushi ta cigaba da kallon da
takeyi,
Ta jima sosai kana ta ďauki fauxie tayi ďakinta da Ita, addua tayi mata dai dai kunnenta kana ta
fice,
Deedah na xaune da laptop ďinsa ta shigo, fuskarsa ba walwala batasan meke damunsa ba,
taje ta sauya kayanta xuwa na barci kafin ta dubesa,
'kagayamin dalilinka na hanani xuwa super market yau, kamar baxaiyi mgn ba sai Kuma ya bata
amsa batare daya kalletaba,
'meyasa tun farko baki nemi sanin dalilin ba sai ynxu bayan kinje kin dawo,
'na tambayeka ne baka gayamin ba shiyasa naje cos baka taba hanamin xuwa ba,
'ban taba hanaki ba kuma dana hanaki sai kikaje saboda bn isa da ke, da wani abu ya sameki
fa?
'taya akayi kasan naje can? ya ďan dubeta,
'labari naji kuma an gayamin har fito dake akayi waje,
'Waye ya gayama, ai Kaine Deedah, kagayamin ko Kai Waye xn jure komai a rayuwa amma
banda xama da barawo, ya mata wani irin duba
'ni ne barawo Iman, ni kika jifa da wannan mummunan kalma,
'Naji muryanka Deedah, Naji qamshin turarenka duk da banga fuskarka da idanuwanka ba, idan
xargin da nake Gaskiyane ka cutar da rayuwata Deedah,
'wannan ba hujja bace Iman, am a good man with a good personality, kowa ya sani kema
shaidace, turare bani kaďai ke dashi ba kuma na maxa ne, murya Kuma amonta kikaji amma
bani bane banje super market ba sai dai kuma an gayamin an ganki wani ya fito dake, Waye
shi? Miye haďinki dashi daxai taimakeki har ya riqa hannunki,
Hankalinta inyayi dubu ya tashi, qafafunta na neman gagarar ďaukarta, muryarta har rawa
takeyi musamman yanda taga fuskarsa a ďaure kada wannan dalilin ne yasanya yake ta fushi
tun ďaxu,
'ni bakomai tsakani na dashi, ban sanshi ba bansan dalilinsa na taimakona ba, nayarda ya riqa
hannuna saboda turarenka danaji a jikinsa Ina xaton kaine,
'saboda kin daukeni barawo, ban yarda dake ba idan ba kin sanshi ba baxai taimake kiba,
Hankalinta ya tashi ta soma rantse rantse tana hawaye, yana kallonta yaji daďi cos ya sami
dabarar wanke kansa,
'Ni yau kake xargi, shekara nawa muna tare dake,
'kema xargina kike yi bakiduba tsawon lokacin da muke tare dake ba kai tsaye xaki kirani
barawo,
'ban tabbatar ba Ina so nagane ne amma kayi haquri baxan qara tsallake umarninka ba, kuma
ba xarginka nake ba kawai hasashe ne,
'nima hasashe ne, xo ki kwanta, ta saki ajiyar xuciya fuskarta da murmushi ta kwanta haďe da
lumshe idanuwanta, kallonta yake kafin ya maida kansa kan abinda yake, shi kaďai yasan
planning da yake haďawa su oga nas dan baxai iya cigaba da xama dasu ba, duk da ynxu
yadaina fashi ya daina harbi sai dai yayi rakiya kawai ya qudira a ransa ko police suka biyosu
baxaiyi harbi ba sai dai ya nemi hanyar tsira amma baxai taimaki kowa ba, lokaci yake jira.....
2 days~
Tana xaune da fauxie a falo, kanta take gyaramata, tana mamakin irin tsawo da cikar kai na
fauxie, gashi da tsantsi shiyasa ba'a fiye yimata kitso ba warwarewa yakeyi sai dai kalaba,
'anty kinga baba ya ganni wai inxo yabani chocolate,
'karkije kome ya baki kada kici,
'ai anty ban karba ba, harararsa nayi nace banaso,
'good girl gwanda da baki karba ba amma kada ki qara harararsa,
'Kuma anty naganshi ya siyo sabuwar tedy xnje yabani,
_(ba tedy bace jikinta ne kamar tedy acikinta duk kayan tsafinsu ne da sima ta qara
rabamasu duk ynda xasu tafiyar da alamuransu xasu yi da ita, duk Wanda tashi ta sami matsala
ya sami matsala cewar Sima)_
'idan na sami lbrn kije ko gidannan sai nayi maki duka a gidannan Kuma muyi faďa dake, kibari
yaya yaxo ya qara siyomaki wata,
Ta soma dariya taji daďi amma tasanya a ranta sai taje ta ďauko wannan,
*
A hospital yau ma kamar kullum ta karbi haihuwa jaririn baixo da rai ba, tana tsaye nurses xasu
karbi haihuwa Kuma yaran su rayu sai ta shiga tsoron kanta, har aka tashi aiki bata qara leqa
labour room ba sosai ta shiga damuwa,
Da dare bayan sun gama shirinsu na kwanciya ta sanardashi abinda ke faruwa, yayi shiru yana
naxari bai taba kawo baba bane a tunaninsa sai ya qara rarrashinta tare da kwantar mata da
hankali, inda yayi ta bata misalai da yawa da suka qunshi haka, yace su dage da addua Allah
xai shige masu gaba, sai ta saki ranta murmushi a fuskarta taja dogon hancinsa,
Deedah ya canxa I agreed, yana xaunawa yaji matsalata ya Kuma sharemin hawaye na,
Murmushi yayi Wanda ya qara fito da kyawun fuskarsa,
'Ina son Iman da farin cikinta dole na cnxa,
'Ina son mijina, xn jure xama dashi a kowane hali... ta sumbacesa a gefen kumatunsa ta kwanta
tana murmushi tana jin sonsa ta ko ina a jikinta,
Yayi mata wani irin murmushi da har abada baxai gushe daga xuciyarta ba,
Yabi bayanta ya kwanta hot kisses yake blowing ta kowacce kusurwar jikinta, ita kanta batasan
Ahmed ya iyasu ba sai a yau ya mantar da Ita damuwarta, ya ďauke ta ya jefata a duniyar
soyayya harta manta damuwarta da halin da take ciki har batasan lokacin da tasa hannu ta
rungume abinta sosai a qirjinta ba.
Asuba ta gari Iman & Deedah,
Getting better, tnx for your du'a, still nid ur prayers.
My wattpad Phertymerh1
*BABANA DA MIJINA....*
*©Fertymerh Xarah *
29
Dr. Deen ya fito daga office ďinsa hankalinsa a tashe, yanayinsa xai nuna ma baya cikin
kwanciyar hankali,
Kicibis sukayi karo da juna, files ďin dake hannunta suka xube a qasa,
'oh gosh, am sorry Dr. Fatyma...... sai ya fice da sauri, tabi bayansa da kallo bayan ta girgixa
kanta kana ta sunkuya ta kwashe files ďin ta fice,