Showing 57001 words to 59977 words out of 59977 words
Chapter 20 - BABANA DA MIJINA BOOK COMPLETE Fertymerh Zarah --.pdf
Unknown
22 Mar 2025
4477
kallonsa,
'tor shikenan ina jiranki a falo idan kin gama shirin, yasa kai ya fice......
*
Salima tayi nadama, nadama sosai, bata bar gidan ba kamar ynda tace saboda Kalaman
mahaifinta gareta, sai dai Sa'eed ya ďauke yaransa ya maida gurin habbi, sosai suke samun
kulawa Kuma sunji daďin xama da Ita fiye da mahaifiyarsu,
Salima ta rame koda yaushe cikin kuka, duk sanda ta ganshi tana rokonshi ya yafe mata xata
canxa, shima yana tausayin matar tashi sai dai yanason ta gane kuskurenta sosai,
Ya sallami Indo taje hutu, sai ga salima da gyare gyaran gidan duk da ba yaran, ynxu har girki
take Kuma dama can ta iya girkin iya shege ne, kullum sau biyu take shiga ďakinsa ta gyara,
xatayi shara tayi mopping tayi wanka ta gyara jikinta, gidanta a ynxu akoda yaushe xaka
sameshi tsaf yana qamshi, sallah ma Yanxu da wuri takeyi tana roqon Allah fatanta Sa'eed ya
maida aurensu tana sonsa batason rasashi,
Ta shirya taje inda Iman ta roqi gafararta, dayake Iman batada riqo ga haquri sai ta yafemata
Kuma ta roqa mata Sa'eed ya maida ta.....
A Daren yau dai ya rantse sai ya gane abinda Iman take nufi dashi, bata sonshine ko iya shege
ne? Ita ba yarinya ba balle ayimata uxurin qurciya, sai dai tayita cika cikinshi da abinci amma ba
komai Gashi harta koma aiki,
Tana tsaye bakin mirrow tana tufke gashin kanta ya shigo da alama wanka ta fito ganinta ďaure
da towel, suna haďa ido tayi Saurin ďauke kanta jikinta na rawa,
Yayi dariya qasa qasa ya tako har inda take tsaye ya sunkuya dai dai kunneta yana faďin,
'komai wayon amarya dai ta riga taxo hannu, sai idan mai itane baiga dama ba, harararshi tayi
ta gefen idonta, yasa hannu ya karbi reborn ďin datake qoqarin tufke gashinta, ya warware
gashin ya xubo a doron bayanta, batayi aune ba sai ji tayi ya sunkuceta, bai direta ba sai cikin
Jacuzzi, ta dubesa a raunane cikin matsinaciyar kunyarsa,
'Yanxu fa nayi wanka..... bai sauraretaba ya janye towel ďin jikinta tayi Saurin rumtse
idanuwanta, ya manna bakinta da nashi da wasu irin matsiyatan kisses da bata taba sanin
akwai irinsu a duniyartaba,
Ya saki shower akansu cikin wani sabon al'amari da Iman bata taba tsintar kanta a
kwatankwancin sa ba, tasan tana wanka tare da Deedah, ya cuďata ta cuďashi wani sa'in idan
suna sauri sai dai kowa yayi nasa...
A daddafe suka gama wankan suka fito, ranar taga tarairaya so da qauna, Ashe dai wannan
itace soyayya na baya duk shirmene wane Deedah da soyayyarsa, wadannan manyan maxa ke
magana Waďanda basa furta kalmar so a fatar baki sai dai xuciya da gangar jikinsu ya nuna....
Ta rumtse idanuwanta hawaye na xubo mata, yau ta kwanta da wani ďa namiji ba Deedah
ba......
Asuba ta gari Dr Deen and Dr Iman....
My wattpad Phertymerh1*Babana da mijina*
©fertymerh Xarah
I like the novel Badakala
45
Tayi juyi a hankali ta buďe idanuwanta wadanda ke cike da barci da gajiya suka haďa ido kunya
ta kamata, Deen ďin sai ya qara lumshe mata idanu, ta sunne kanta cikin yalwatacciyar sumar
data cika qirjinsa, xuciyarta fal da so da qaunar mijinta Wanda ya siye duk wata soyayya da
Allah ya halittawa ďan Adam cikin xuciyarsa a dare ďaya kacal,
Ta lumshe idanuwanta cikin tunanin Deedah, bata taba tunanin kasancewarta matar wani bayan
shi ba, hawaye suka xubo mata, ko ba'a faďa ba yasan tsohon mijinta ta tuna ta qara
rungumeta a qirjinsa tare da gayamata kalamai masu sanyaya xuciya......
Bayan ta gama wanka tayi sallah ta nufi kitchen, anan ta samesa yana kiciniyar ďora breakfast
har lokacin yana sanye da kayan barci, ta fashe da dariyar dana janyo hankalinsa gareta ganin
ynda yake fere arish duk ya xubar da rabin a banxa, ya juyo yana kallonta, murmushi kawai yayi
ya ďauke kansa, ta qarasa kicin ďin haďe da riqe wuqar dake hannunsa,
'daka bari ai xn fito nayi, da can danakeyi bakama sani ba, ya sakarmata wuqar ya xagaya ta
bayanta haďe da sumbatarta a wuyanta, ya kwantar da kansa a kafadunta,
'na yau daban ne dana kullum, jiya na ďora miki gajiya nasan baxaki iyaba,
'a naka tunanin kenan, na hutar da kai wannan ba aikin ka bane, kaje kayi wanka ka shirya dan
idan na shirya baxan jirakaba, baiyi mgn ba sai kallonta yake tasa hannu cikin nasa ta ciro arish
ďin tana kallonsa,
'ko ina kaga ana fere dankali haka, fauxie ma baxatayi wannan ba.... Duk ynda tayi dashi yaqi
tafiya dole a tare sukayi aikin, miqo wannan ajiye wannan, duk shine sunayi cikin farin ciki da
qaunar juna abinda bata taba samu a gurin Deedah ba, ba irin Wannan kulawar da shaquwa
tsakaninta da Deedah, *wani hani ga Allah baiwa ne*, sai taji Deen ya sami matsayin babba a
xuciyarta,
A tare suka haďa komai a dinning ta ďauki nasu baffa ta kaimasu shikuma ya shiga wanka....
Soyayya ruwan zuma gangariya ake gudanarwa a gida da asibiti cikin yan kwanakinnan da
suka biyo baya, a mota ďaya suke xuwa asibiti, idan ta rigashi gama aiki shike maidata gida ya
dawo wani sa'in Kuma tare suke tashi,
Kallo ďaya xakayi mata kaga kwanciyar hankali da jin daďi a tare da Ita, ta canxa har wata yar
qiba tayi, Sa'eed yaji daďin ganin ynda Iman ta sami kwanciyar hankali a gidan mijinta hakama
Merah, baffa ma na qoqari akansu ya maye masu gurbin baba, basu da kamarshi a ynxu suna
darajashi sosai,
Yau ma tare suka fita asibiti bayan sun gaisa baffa, fauxie tuni an wuce skul, little yana jikin
baffa bai damu da suba a ynxu yafi sabawa da baffa,
A asibiti binni binni xaka ganshi Gynaec yaxo dubinta,
'mekike so, kina buqatar wani abu, akwai matsala? sai ta girgixa kanta tana kallonsa da
murmushi,
'need nothing just only you..... idan da mutane a office ďin sai dai yayi murmushi ya fice idan ba
kowa sai ya sumbace ta ya fice ta bisa da kallo fuskarta da murmushi, kowa nayi masu kallon
birgewa......
Karfe biyu ta tashi daga wurin aiki yau kai tsaye office ďinsa ta nufa, yana ganinta ya taso ya
rungumeta, ta dubesa da murmushi a fuskarta,
'natashi aiki xnje gida saboda girki nasan baffa yana jirana,
'banason kina wahalarda kanki, akwai adama ga dijeh xasu Kula da girkin, ki jirani nan da
2hours xn kammala sai mutafi tare,
Ta ajiye Jakarta haďe da cire labcoat ďinta, ta cire agogon hannunta tana faďin,
'Olryt bari nayi sallah, ta nufi hanyar toilet ďinsa kafin ta fito har ya shimfida mata darduma....
Shi da yace 2hours sai gasu har bayan isha'i patient suka masa yawa, tana xaune akan sofa da
laptop ďinsa a hannunta tana kallo, da kyar ya samu ya kammala suka fito, yana ďauke da
jakarta da labcoat ďinta, ta dubesa tana dariya,
'Yanxu sai ace ďan kwali yaja hula, baka kunyar mutane musamman abokan aikinka, idan na
qasa dakai suka ganka da jakar mata a hannunka ai girma ya faďi,
Ya ďan dubeta yana yatsina fuskarsa,
'Dama mata sun fiye sa ido, inba wannan ba miye damuwarki da duk wanda ya ganni, jakar
matata na ďauka ba budurwata ba, ni bn yarda dake ba kin tsaya bayana kina min dariya shiga
gaba,
Tayi dariya ta wuce tana gaba yana biye da Ita har gurin motarsu, ita ta buďe masa ya shiga ta
rufe kana ta sunkuyo tana murmushi,
'your excellency, Iman na godiya,
'idan kika qara mgn xn tafi in barkine, Kuma xakije a qasa ba lift ba napep.... tayi dariya haďe da
sumbatar kumatunsa ta xagaya da sauri ta shiga motar ya bita da idanuwa yana kallonta har ta
xauna ta rufe kana yaja motar, sunyi Rabin tafiya yayi parking ya fito,
'ni nagaji bayana ke ciwo kixo ki qarasa, ina driving sai kallona kike kamar yau kika fara ganina,
tayi murmushi ta karbi key, ya shiga motar ta xagaya taja, sai da suka xo bakin gate tayi horn
Maigadi ya buďe gate ďin ta soma qoqarin fita ya riqo hannunta,
'Ina xakije...
'ni na gaji, bayana ke ciwo, ina driving kana kallona kamar yau kafara ganina,
'yi haquri nadaina kallonki, ki qarasa ladarki, ya ďauke kansa gefe tayi murmushi taja motar.
Sashen baffa suka fara xuwa yana xaune da qur'ani a hannunsa fauxie na gefensa danata a
hannu yana koya mata karatu, tana ganinsu taje ta rungumesu tana masu sannu da xuwa,
Deen ya ciko chocolate masu yawa a aljihunsa ya xuba a tafin hannuwanta,
'ki ajiye wa little nasa idan kika shanye *Ni da ke* a gidannan, ta karba tana dariya ta dubi Iman,
'kefa anty me kika siyo min,
'komai sai gobe,
Sukayi masu sai da safe, suna isa falonsu bai bari ta koma takawaba, ďaukarta yayi bai
diretaba sai a lafiyayyen gadonsa, da kanshi ya haďa mata ruwan wanka, tsugunnawa yayi dai
dai gwiwoyinta, ya cire mata sarqa da yan kunne ya ajiyesu a gefe, ya tayata rage kayan jikinta
ya rage daga ita sai shimi,
'get ready maman little, taja dogon hancinsa idanunta akansa,
'get ready too Baban little, ta tashi ta nufi toilet.
Kitchen ya nufa ya duba cikin microwave, kaza ce gasashiya taji yaji albasa da tumatir, ya
dorata akan tire, ya ďauki chips and Scottish salad da ruwa da juice ya nufi ďakinsa,
Ya samu harta fito tana Shafa'i da wutri, ya ajiye agabanta bayan ta sallame, ta ďago ta dubeshi
idanunta taf da barci ga gajiya,
'sannu da qoqari, bai bata amsa ba illah murmushi da yayi ya soma ci yana faďin,
'kici da kanki baxan baki ba nagane wayon harda min wani sannu,
Itama dariya tayi ta janyo tiren gabanta,
'ni xn baka, sai ta soma bashi a baki,
Wannan kulawa da kyautayi ga babban mutum irinsa ya taba xuciyarta shiyasa take qara sonsa
take ganin ba wani kamarshi a duniyarta,
Bayan sun gama ta jasa toilet da kanta ta cuďasa suka fito sukayi shirin kwanciyarsu a tare
bayan sunyi light off.
Suka buďa sabon shafin soyayya, gabaki ďaya Deen ya gigitata, haka ya cigaba da shayar da
Ita mamaki cikin fannonin qauna da soyayya daban daban daba duk maza Allah keyiwa
baiwarsu ba, ita kam ta yarda tayi miji a ynxu loving and caring husband irin Dr Zaharadeen......
My wattpad Phertymerh1
*Babana da mijina*
©Fertymerh Xarah
*Dedicated dis buk to Rabi'atu Sk Mhs, Serdia Lawal bala & Aysher Gambo*
46
A gurguje
Rayuwa ta miqa, so da shaquwa sai daďa qaruwa take tsakanin Su,
Xuwa Yanxu Iman ta gama sanin ko Waye mijinta Zaharadeen , ta yarda ita kaďaice a
xuciyarsa,
Mutum ne dayasan ciwon kansa, ya kuma San mutuncin ďan Adam da kuma darajar aure,
Haka Kuma mutum ne da ya San soyayya mai tsayawa mutum a qoqon rai, barta kyawun
halittarsa Deen is Classique da kowacce ďiya mace da tasan ciwon kanta xata yiwa kanta burin
mallakarsa,
Xuwa ynxu soyayyar mijinta ta ratsa kowacce jijiya mai gudanar da jini a jikinta ta ratsa qashi da
bargo,
Duk dukiyar da suke da bai damu ba, ba ruwanshi da dukiyarsu burinsa ya sauke haqqinsu
dake kanta,
Iman knows her husband for now, tasan waye shi tasan aikinsa, ta bashi amana da yarda 99%
tasan baxai cutar da rayuwarta ba,
Daga Deen har mahaifinsa tafisu kuďi amma basa barinta taba dukiyarta sai dai suyi amfani da
tasu, hankalinta da xuciyarta sunfi kwantawa a ynxu she loves Deen tana masa wani irin son da
bata taba yiwa wani namiji irin sa ba,
A da ta ďauka Deedah kaďai ne a xuciyarta, Deedah kaďai xata so har qarshen rayuwarta,
Deedah ne masoyinta amma ynxu Deen ya mamaye wannan gurbin na Deedah, idan tana tare
da Deen harta Kan manta kanta da wani Deedah, sai dai idan ta kalli little tayi masa addua,
Ko a ynxu xata iya shaidawa duniya she have the best father and husband a ynxu, mutanen
nan biyu tana alfahari dasu a ko ina and she will never forget them in her life, presently *Babana
da mijina*, tayi murmushi tana kallon baffa dake tsokanar fauxie,
'matar sultan, matar sultan, yarinya tun tana qarama anyi mata kamen miji...
'ni ba matar sa bace baffa, bana sonsa..... ya soma yi mata dariya,
'shikenan irin auren nan da akeyi a da shi xa'a yiwa wata, Wayyo bata san mijinta ba sai dai a
ďauketa akai masa, kinma ji daďi xakije gidan sarauta, akwai Wanda yafiki Sa'a Kuwa na
kasancewarki surukar Dr Merah,
Kuka take sosai ta faďa jikin Iman, daga baffa har iman dariya suke mata ganin da gaske kuka
take suka kyaleta, akwai bidiri kenan a *Sultan Merah*,
Ko ina kuka hango min salima
Salima Yanxu ta xama cikakkiyar mace wace ko wane namiji yake alfaharin samun irinta,
Believe me Sa'eed har cewa yake da haka take tun farko da ba'a abinda xai sanyashi auren
habbi, duk da haka baya regretting na auren habbi itace sanadiyar shiriyar salima,
Xama suke na amana duk da baxaa rasa irin kishin nan namu na mata ba, (kamar Serdiyer
Lawal bala) suna ďan tattatabawa watarana amma ba kullum ba,
Kowace tana kula da mijinta da ganin ta kyautatamasa, kowacce tana son tafi yar uwarta a
xuciyar mijinta, yana sonsu Kuma yana kwatanta adalci tsakaninsu gwargwado iyawarsa.....
Ta fito sanye da doguwar riga ta shadda, cikinta ya turo sosai Kamar yau xata haihu, Deen na
bayanta da plate ďin sinasir ďayan hannunsa juice ya riqo, rarrashinta yake akan taci abincin
taqi, duk inda tayi yana biye da Ita,
Suna isowa falon ya ajiye kayan ya juyo yana kallonta lokacin take qoqarin xama,
'har sai yaushe xaki daina wahalar dani, idan baki ci abinci ba taya kike tunanin nima xn iya cin
nawa, ta tsuke baki tana kallonsa, ya xauna kusa da ita haďe da ďora hannunsa akan nata
hannu,
'Bari na baka kaci tukunna, bana son kana xama da yunwa saboda ni likitana, all I have is
you.... taja dogon hancinsa tana murmushi, yayi murmushi ya janyo sinasir ďin yana kallonta,
'sai kinci xnci, kina so baby na ya xama raggo baida kuxari ko, to baxan yarda ba ďure xn maki
a ynxu, ta kwanta a kafadarsa tana murmushi,
'Baban little kana so ka nuna min kafison babyn dani... yayi shiru bai tanka ba ya soma cin
sinasir ďin,
'kinga ni ki Kyaleni Kada ki dameni tunda baxakici abinci ba kuma ba ruwanki dani munyi faďa,
Dariya tayi haďe da sanya hannunta a plate ďin suka soma ci tare....
Watan haihuwar ta na shigowa suka ďauki annual leave a asibiti sukayi Dubai, acan ta haihu ta
sami baby girl,
Rayuwa suke mai daďi wacce aka gina ginshiqin ta da soyayya ta gaskiya da amana, irin wacce
tayi qaranci a Wannan xamanin, rayuwace mai cike da qauna da soyayya yarda da girmama
juna, babu abinda suka sanya a gaba daga aikinsu, sai Kula da yaransu da kuma junansu,
Kwanciyar hankali da jin daďi tare da Iman a ynxu, ko yaushe xaka ganta fuskarta da farinciki
sabanin da, bata da damuwa ynxu ko fargabar rayuwa,
Dr Deen shi ya taimakamata wajen ganin ta gina qatuwar islamiya mai ďauke da sunan baba da
Deedah, adduarta ladar ta isa garesu a koda yaushe kuma Allah ya yafe masu kurakurensu,
Lokaci lokaci take masu sadaka, bata manta da waďannan mutanen biyu masu muhimmanci a
rayuwarta ba komai kin daďin da take ciki, suna nan maqale a xuciyarta Kuma tana yi masu
addua a koda yaushe,
Allah yaji qan maxan jiya ta faďa fuskarta da murmushi tana kallon Deen,
Ya amsa mata da amin, yana cigaba da danna laptop ďinsa, ta kwanta ta bayansa haďe da
lumshe idanuwanta,
'Ina son mijina, ina alfahari da mijina, ko a ynxu xan iya bawa duniya labarin *Babana da
mijina*, ba abinda xance sai Allah ya saka masu da gidan aljanna,
'wannan adduar tare dake fatyma, bani da mata a aljanna sai ke da hajara, kun bani farinciki a
rayuwata bn taba dana sanin auren ku ba, the best wife's in the world, proudly to have you,
Ta qanqameshi sosai,
'my husband is the best too.. Suka rungume juna cikin tsantsan farin ciki da qaunar junansu.
Masha Allah lakuwwata illah billah!, Anan na kawo qarshen littafin *BABANA DA MIJINA*,
kuskuren dake ciki Allah ya yafemin,
Ina Godiya ga duk makarantar littafan *Pherty*, Allah ya sada mu da alherinsa Amin.
Kuyi haquri da yanda qarshen littafin ya xo maku, a gurguje nayi komai exam Monday....
Sai mun haďu a *Sultan Merah* dan jin qarshen rayuwar fauxy,
*Sultan Merah* yana referring kowanne motion ďin sa akan *Mulki ko Sarauta* kamar
mahaifinsa Dr Merah, ko ya rayuwarsu xata kasance tsakaninsa da fauxie?
*love you all*
My wattpad Phertymerh1