Showing 54001 words to 57000 words out of 59977 words

Chapter 19 - BABANA DA MIJINA BOOK COMPLETE Fertymerh Zarah --.pdf

Unknown   

22 Mar 2025

4479


xaki aure min miji Wlhy baxan taba yafe maki ba, kaima baxan yafe ma ba Sa'eed ta soma
kuka, basu ankaraba sai ganin kawai sukayi ta ďauki kwalbar malt dake ajiye ta jefata ga
plasma t.v ,tayi ratsaratsa, duk abinda tasan mai fasuwa ne tabi tana fasawa, Sa'eed na fisgota
ya ďauketa da Mari kana yajata ya fiddata gidan suka rufe...

Kamar habbi xatayi kuka haka take tsaye ganin yanda aka farfasa mata kaya, jiya jiya da
kawowata,

Haquri ya soma bata anjima xaisa akawo mata duk abinda salima ta fasa, tana jin haka ta saki
ranta ta rungume shi tana kissing,

Tare sukayi wanka sukayi breakfast, daďin da Sa'eed keji baya misaltuwa, bai taba samun irin
Wannan kulawar ba, ta rakasa har motarsa sai da taga yabar gidan kana ta ďauki qaton icce ta
nufi motar salima,

Salima na ganin tana farfasa mata mota ta window kafin ta fito tuni habbi tayi shigewarta cikin
gidanta ta rufe, tabi motar da kallo Kamar xata sanya ihu dan haushi da takaici.......

*

Bayan wasu kwanaki Iman ta haďa duka ma'aikatan gidan guri ďaya, ta roqesu gafara kana ta
sallamesu, irin sallamar da tayi masu baxasu taba mantawa da Ita ba saboda ta cikasu da
dimbin alheri mai tarin yawa, sunyi rabuwar arxiki mai cike da shaquwa da kewar mace mai
hankali da taqwa kamar Iman...
Mutum uku kawai tabari a tare da Ita, Suleiman, dijeh da adama,

Tun bayan auren su da Deen bata qara sanyashi a ido ba, sai dai taji muryarsa a falo shida su
fauxie,

Parking tayi sosai duk abinda take buqata ta hadasu guri ďaya saboda rufe gidan xasuyi, ansa
ranar tarewarta lokacin da Deen ya aiko kayan lefenta kamar na wata budurwa,

kaya ne masu kyau da tsada na gani a faďa, haka little da fauxie sai da yayiwa kowa set ďaya...


Sa'eed na bank ta kirashi ta sanardashi abinda habbi tayi, tsaki yayi ya tsinke Wayar hankalinsa
a dagule wannan masifa dame tayi kama yasan duk laifin salima ne,


Da yadawo ya hadasu yayi masu faďa sosai akan su haďa kansu shi baxai ďauki wannan kishin

tsiyar ba,

Habbi ta bashi haquri tace baxata qara ba xata xamo mai biyayya garesa, yaji daďin haka
amma salima Kuwa buďar bakinta sai cewa tayi,

'maganar motata a gyaramin...

'yace xa'a gyara itama xn siya mata tata...

'idan har ka siyamata sabawa nima sai an canxamin Kai bnmason gyaran wata nakeso a
canxamin,

'duk ba matsala bane salima indai xaku haďa kanku ku xauna cikin yardar juna....

Habbi ta dubesa tana kashe masa ido,
'sweet muje intayaka kayi wanka kaci abinci inyima tausa nasan a gajiye kake, ya saki
murmushi yana kallonta ko baiyi magana ba kasan yaji daďi, ba gardama ya tashi yabi bayanta
bai qara waiwayen salima ba haushi kamar xai kasheta,

Tunda yabita part ďinta bata qara jin duriyarsa ko motsinsa ba sai faman leqe take ta window ko
xata ganshi shiru kakeji har Washe gari, tana tsaye a window taga fitowarsu, habbi na ďauke da
briefcase ďinsa shi Kuma ya riqa hannunta har gurin motarsa,

Tana ganin lokacin daya Karbi briefcase ďinsa ya shiga mota habbi ta sunkuya ta sumbacesa
kana ta soma yi masa bye bye shima yana yi mata har ya fice, wannan ranar harda kuka tayi,
tunda take dashi ko falo bata taba rakashi ba ballantana hr gurin motarsa.


Amarya Iman sai faman shirye shiryen biki ake tasha qunshi ja abinka da farar mace qafafunta
da hannuwanta sun fito sosai tayi kyau ga xoben xinari dake sanye a yatsun hannuwanta
Wanda ya qara fito da kyawun lallenta,

Affiya, Dr Fulani da Dr Umayma sune abokanta suke tsaye a kanta na ganin sun shirya amarya
sosai ciki da wajenta ta fito,

Fauxie itama Anyi mata tata shigar cikin gown fara, haka shima little cikin suit duk suna gurin
Merah.....


Amarya kawai ake jira ta fito ango na cikin Mota yana jiranta, Sa'eed xaija motar amarya da
ango xuwa gurin dinner....

Duk ya qagu ta fito cos sunyi late kamar ance ya ďago akayi Sa'a su affiya sun fito da Ita, an

rufe fuskarta da wani net duk da haka baxaka rasa ganin fuskarta ba, ba qaramin kyawu tayi ba
har ya kasa ďauke idanuwansa akanta, bama shiba har Sa'eed da sauri ya ďauke kansa gareta
yana sauke numfashi, Iman yayi asararta ya fada ahankali,

Dr Fulani na bude motar ta shiga kana suda Affiya suka nufi nasu motocin,

Tunda ta shigo ta xauna qamshin turaren ta mai sanyin qamshi da daďin gaske ya mamaye
motar, ga wani qamshin amarcin da take,

Sa'eed yaja motar a hankali jikinsa a sanyaye...

Duk qoqarinsa na ganin ya kauce mata ya kasa, he can't, yaga kyawun Iman sosai, kayan dake
sanye a jikinta sun fito da shape ďinta wanda baisan Iman ďin haka take ba duk ganin da yake
mata acikin hijab da labcoat ne amma yau ya ganta in her real image, no hijab, no labcoat,

Ya juya yana kallonta kanta na sunkuye, bata Kalle sa ba kuma batayi masa mgn ba sai dai
xuciyarta ta kasa nutsuwa ta rasa dalilin shariyar da yake mata har wannan lokacin da ta
amince na xamowa matarsa.

A hankali ya sauke kwayar Idanunsa akan hannuwanta inda yayi arba da Jan qunshinta, Dama
gashi da son qunshi yana sha'awar yaga mace da lalle balle wannan da ta xama tasa
mallakinsa, baisan lokacin daya ďora hannunsa akan nata ba ya haďe yatsunsu guri ďaya yana
murzawa a hankali.......


Nima ina shirin xuwa dinner ne‍♀, nasan su Xuhura da Pherty novels ma suna can suna shirin
xuwa dinner.


My wattpad Phertymerh1*Babana da mijina*


©Fertymerh Xarah


43


*Dedicated dis page to Ayusha Muhd, Rash Kardam, Fido Sodangi, Ummi Ahmed, Uwani
Tahir & Sumayya Dikko*

Hakan bai sa ta ďago ta dubesa ba kuma bata janye hannunta daga garesa ba,

Har suka iso ba Wanda ya tanka acikinsu, a tare suka fito motar ga mutane tsaye ana jiransu
hotel ďin cike yake da jama'a samari da yan mata,

Suna fitowa aka soma watsa flowers a gefenta fauxie ce cikin irin tata gown, shikuma little yana
gefensa cikin suit kamar Dr Deen, sunyi matuqar kyau sosai,

Nan da nan masu camera suka fara aikinsu, masu yi a waya suka soma, Sa'eed ma sai
daukarsu yake, ga fertymerh Xarah novels ma kowa da wayarsa qoqarinsa yaga Dr Iman da Dr
Deen a wayarsa, bama kamar Pherty novels dake ture ture burinsu suxo gaba su ďauki amarya,
sai da Dr Deen yasa hannu ya kare fuskar iman ganin hasken camera sunyi yawa akanta�.

Habbi kusa da Sa'eed ta xauna dama yabarta taxo, aka xaxxauna, nan aka fara gudanar da
bikin cikin farin ciki da jin daďi,

Deen ya sunkuya dai dai kunneta,

'Na kasa haqura amma dole xn gayamiki kinyi kyau sosai har Ina kishin dubban maxan dake
gurinnan....

Ta dubesa suna haďa ido ta saki murmushi cikin jin kunyarsa, shima murmushin yayi dai dai
lokacin da mai camera ya daukesu....

Ana cikin yin dinner sai ga salima taxo gurin yanda tayi parking ma xai tabbatar ma da a fusace
take,

Tana tsaye tana neman inda xataga habbi, Iman ta ganta sai ta ďauke kanta gefe kamar bata
ganta ba, Dr Deen ma ya ganta sai dai baisan ko Wacece ba,

Kamar daga Sama ta hango Sa'eed da habbi suna dariya ba xato ba tsammani habbi taji duka,
nan fa suka shiga kokawa dambe suke sosai,

Nan fa gurin ya qaure da ihu, lafiyayyun Mari biyu Sa'eed yayi mata amma bata damu ba ga
hancinta na jini burinta kawai ta illata habbi, ganin yanda ta xama tamkar mahaukaciya a gurin
kowa na soma neman inda yayi komai ta samu jifan mutane take dashi,

Dr Merah yaja Affiya saboda hankalinsa na gunta baya son komai ya sameta ko kaďan dan ma
basuxo da yaran suba,

Dr Fulani taja hannu fauxie da little tayi Mota dasu, kowa ta kansa yake dan salima bata bar
kowa ba har mijinta ta jimasa ciwo a hannu, bai taba tunanin haka take ba balle harta iya aikata

hakan,

Iman a tunaninta duk saboda itane salima ke wannan haukan, a ruďe take ganin take xataxo ta
jimata ciwo ne, sai ta qanqame Deen sosai Kamar xata shiga cikinsa, shi Kuma hankalinsa na
gun su fauxie sai dayaga an sanyasu Mota kana ya maida hankalinsa ga riqon da Iman tayi
masa, idanunta a lumshe sai hawaye take abu kaďan ke ruďata baisan irin xuciyarta ba, yasa
wayarsa ya ďauketa pic batare da ta sani ba kana yasa hannunsa ďaya ya rungumota..

Da kyar wasu maza suka rirriqeta, Sa'eed ya ďaure ta da wata waya sai faďi yake,

'batada hankali daga gidan mahaukata ta fito, ta qara xabura

'qarya kake, kunci amanata ne Kuma baxan barku ba,

Ya ďaure bakinta da gyalen habbi, sai kuka take ya ďauketa ya nufi motarta da Ita ya sanyata
ciki ya Kulle motar sai xufa yake, wannan wahalar dame tayi kama, ga hannunsa sai jini yake
habbi ta riqosa tana hawaye,

'dear muje asibiti dan Allah,
Ya dubi hannun kafin ya nufi inda Deen yake tsaye da Iman,

'Dan Allah kuyi haquri d....... Deen ya katsesa,

'ba komai Sa'eed kayi sauri kaje asibiti, iman ta ďago tana kallonsa cikin tausaya shi har sai
yaushe xai sami kwanciyar hankalin wannan matar? Suna haďa ido dashi ta qara fashewa da
kuka ta maida kanta jikin Deen, Sa'eed kuma da sauri ya juya nan cikin motar suka barta habbi
ta jasa suka nufi asibiti.....
Kowa ya watse sai gasu ci biki ynxu ake xuwa, Ummi Aysher, Faxyfashion, Serdia, Halimcy,
Zarah dange, miss Aysher, baby Bello, Kdeey, Kwaise, Lilmeerahcute, Xuhura Ajiya, Meenah,
Rabi'atu Sk, Didi Aneesa, Afrah bhai, Anty maijidda musa, Khadija Sidi, Shafa Umar, Maryam
kaumi, Sally, Teemah cool, Anka, H.Melody, RAZ, Nusee, Pherty, Rukayya Umar, Hafsat rano,
Zarah Bukar, Zee yabour, Faty Shuwa, Hindatu Arzika, Hamidata, ya salam gasu nan dai
dayawa har bn iya lissafaku am sorry please ,

Sukaja suka yi turus ganin ana watsewa, Dr Merah tuni yabar gurin, Dr Deen da Iman ba motar
shiga dama da ta Sa'eed suka xo kuma sunyi asibiti,

Suka tsaya cirko cirko suna kallon mutanen dake shiga mota suna barin gurin, suna kallon
salima acikin motar, haka kawai Deen yaji ya tsaneta, ya juya yana kallon Iman dake qanqame
da hannunsa,

'ita wannan wai wacece, meyasa tayi haka?

'matar Sa'eed ce, uwargidansa, tana kishina saboda Sa'eed, amma bansan dalilinta nayin haka
ba,

Ya gyada kai cikin gamsuwa batare daya kalletaba, suna tsaye sai ga mota tayi parking gurin,
sunsan motar Merah ce, suka buďe suka shiga har yakai affiya gida,

Acikin motar Dr Deen da Dr Merah suka cigaba da nanata mgnr kowane ransa a bace
fuskokinsu kawai xaka gani ka karanci hakan, iman na baya tayi shiru tana saurarensu, ita suka
fara ajiyewa gida kana suka fice kowane ba walwala a fuskarsa ita kanta bataji daďi ba she will
never forget salima in her life....
Sa'eed sai da akayi masa ďinki a hannu, koda suka dawo ta galabaita sai xufa take tana kuka,
shi yaja motarta habbi taja motarsa suka nufi gida, suna xuwa gida ya fito da Ita motar ya cillata
gefe ďaya ta faďi, ya nunata da yatsa ransa a matuqar bace,

'kije na sake ki saki ďaya.... ta buga wani ihu a harabar gidan har yaranta suka fito,

'wallahi baka isaba, kayi kaďan ka sakeni saboda wannan yar iskar, ba inda xanje nida kai mutu
ka raba, tana kuka ta nufi cikin gidanta.....

Sa'eed yaje ya bawa Iman haquri sosai, ta nuna masa ba komai, suna xaune Deen ya shigo
gidan yanda ya gansu a falo su kaďai xaune sai dayaji wani kishi, fuskarsa kadaran kadahan
suka gaisa da Sa'eed, Iman ta karanci yanayin fuskarsa sai taji jikinta ba daďi,

Sa'eed ya qara bawa Deen haquri duk ya damu ba daďi ace matarka ce sillar duk wata matsala
dake afkuwa,

Deen ya nuna masa ba komai kana ya ajiyewa Iman wata alkyabba mai kyau da tsada sai
qamshi take wadda xata sanya anjima idan anxo ďaukar amarya, baiyi mata mgn ba ya fice ta
tashi tabi bayansa har gurin motarsa ya dubeta,

'kin fito kuma kinbar baqonki, Ashe bakida karamci.... xuciyarta na buga tasan mgn ya
gayamata ta dubesa,

'ya xone fa kan mgnr salima, bayan wannan Sa'eed is a brother to me a ynxu,

Ya tabe bakinsa batare da yayi mgn ba yaja motarsa....

Da dare amarya tayi kyau cikin alkyabba, manyan motoci suka xo ďaukar amarya harda yan
karere irinsu Pherty novels motarsu daban,

Motar Merah amarya ta shiga tare da Fulani, sauran qawaye da abokan arxiki da yan uwa suka

shiga sauran motoci, kana aka ďauki hanyar gidan Dr Deen.......


My wattpad Phertymerh1
*Babana da mijina*


©Fertymerh Xarah


44


Basuyi wata doguwar tafiya ba suka iso, sai da akaje da Ita sashen baffa kana suka nufi part
ďinta da Ita, ita tsaruwa ya tsaru, komai na gidan Deen ya cnxa har fenti,

Nan su affiya suka xauna kusa da ita kowa da abinda yake gayamata cikin tsokana sai dariya
suke, kwata kwata hankalinta baya kansu tana tuna farkon auren ta da Deedah, ta tuna baba da
kansa ya rakata har ďakin mijinta a wancan lokacin, tana tuna rayuwarta da Deedah ynxu Kuma
batasan ynda rayuwarta xata kasance a Wannan gidan ba, lokaci ďaya kuka ya xo mata Wanda
a tunaninsu affiya saboda tsokanar da suke mata ne,

'daga mgn sai kuka amarya, kiyi haquri Kada kisa angonki ya koramu waje cewar Dr Fulani

Suka ďauki dariya harda sowa kafin su koma rarrashinta,

Bayan wani lokaci kowacce ta tashi tasan inda dare nayi mata suka barta ita kaďai a qaton falon
ta sai kallon falon take ba laifi tasan ta kashe masa kuďi, kuma yayi kyau,

She is missing little, ko ina yake? tun safe rabonta dashi, tayi kewar rigimarsa,

Harta qaraci xamanta Deen bai shigo ba, ta tashi ta nufi inda take xaton ďakinta ne, taga su
affiya sun shiga kafin su tafi, ta sauya kayanta xuwa na barci bayan tayi adduo'i tabi lafiyar
gadon ta kwanta batare da damuwa a xuciyarta ba...,

Dr Deen Kuwa fitowarsa kenan daga theater room, yana tafe yana cire kayan aikinsa a
hanxarce ya isa office ďinsa, ya ďauki kayansa hankalinsa da tunaninsa duk yana Kan
amaryarsa yasan ta gaji da jiransa a ynxu, wannan ba damuwa bane tunda yayi qoqarin ceto
rayuwa ne fatansa yarinyar da yayiwa aiki ta sami sauqi,
Tafiya yake yana tuqi yana tausayin wanna yarinyar, life is nothing....

Horn yayi mai gadi yaxo da gudu ya buďe gate ďin, bayan yayi parking ya fito kai tsaye inda

baffansa ya nufa, ga mamakinsa yayi barci ga little a kusa dashi shima yayi barci ba komai a
jikinsa sai pampers, ya ajiye kayansa gefe yaje inda kayansa suke ya sami riga marar nauyi ya
Sanya masa kana ya fice, sai da yaje ďakin da aka bawa fauxie da Ita da dijeh ma sunyi barci,
dijeh na qasa akan mattress fauxie Kuwa na akan gado,
Koda yaje sashensu wanka kawai yayi ya shirya cikin kayan barci ya nufi dakinta, itama tayi
barci tuni, ya sauke ajiyar xuciya yana kallon fuskarta,

'ya akayi kowa yayi barci a gidan da wuri haka, to twelve ynxu bawai dare yayi sosai bane, ya
sunkuya ya sumbaci goshinta kana yayi mata light off ya juya ya bar ďakin,

Kitchen ya nufa domin samawa cikinsa abinda xaici, da kansa ya dafa indomie ya soya kwai, ya
xube a plate ya fito, tun bayan mutuwar matarsa ya soma qoqarin koyon girki,

Washe gari bayan ta gama sallah kitchen ta nufa ta soma qoqarin haďa breakfast, tanayi sai ga
adama, sai sukayi a tare,

Ta bada na baffa ta kaimasu, ta jera sauran a dinning kana ta nufi toilet,

Ta fito kenan taji ana buga qofar ďakin, hijab ta sanya taje ta buďe ďakin,

Yana sanye cikin caftan na wagambari mai hasken sararin samaniya, yau kam glass ďin idonsa
fari ne Wanda ya fiddo da xahirin cikar kamalarshi na cikakken namiji, Wanda rayuwa take
garawa tare dashi,ga bokon ga opportunity Sannan ga mahaďin su kuďi da kyau,

Taji kunya sosai ta wuce ciki yabi bayanta suka xauna a bakin gado lokaci ďaya, kanta a
sunkuye tace,

'barka da asuba,
'barka an tashi lfy,
'Alhamdulillah ,
'jiya sai kikayi barci baki jirani ba, tayi murmushi tana kallonsa batare da tayi mgn ba, she don't
have anything to say, kunyarsa takeji shima ya lura da hakan,

'hutun kwana nawa suka baki a asibiti, ta yatsina fuska
'uku ne,
'uku ashe ba yawa,kinga ni basuma bani ba, ynxu haka inada patient da xn duba a asibiti
wadda nayiwa aiki jiya,

'Allah ya taimaka,
'Amin ya tashi yana qoqarin ficewa ta dubesa,
'breakfast ďin fa? ya dubeta da mamaki,
'kina nufin har kin kammala breakfast? ta gyada Kai tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login