Showing 27001 words to 30000 words out of 73196 words
Chapter 10 - AHALINA (Aure uke series)na chuchu.pdf
musamman idan na kalli wannan
shegiyar yarinyar Nadiya wadda ke ganin tafi kowa ,naji kina da komai,ga kuɗi ga family Mai
kyau,amma yau da kike ƙarƙashina fa ?
Sai yarda nayi daku sannan ina san ku sani dole ku zabi wanda zai mutu ko uwarku ko kuma
mijin uwarku ,dan dole guda ɗaya ya mutu,
A lokacin da mahaifiyata na gadan mutuwa bata gushe ba saida ta sake jadada mun yarda
imam paki da karuwarsa Umaimah suka wulaƙantata suka tozartata bayan yayi mata fyaɗe
Zuri'ar gidan su suka juya mata baya suka ƙaryata ta ,suka mata korar kare a lokacin image
ɗinku da reputation ɗinku yafi na kowa ko?
Ku godewa Allah ni dana tashi zuwa maku da case ɗin fyaɗe na ban bata image ɗin gidanku ba
a duniya amma na b'ata na zuciyarku ".
Dariya Mami ta saka duk da yarda take jin wuƙar a wuyanta amma bakinta bai mutu ba,cike
da tsana irin ta sameera tace"banyi mamakin maganar da kika faɗa ba wadda ta fito daga bakin
sameerah ,dama Ai maƙaryaciyace ,amma abunda yafi bani mamaki shine yarda tana ƙokari
komawa gurin wanda Ya halicceta amma sai da ta durawa ƴarta gubar ƙaryar da ta saba ,
Bance kiji nawa ba amma inaso ki sani babu wanda yayi wa sameera fyaɗe sai dai ita da ta
takurawa rayuwarmu har Allah yayi mana maganinta,"
Danna wuƙar Anisa tayi da karfi wanda Ya saka Mami saka wata irin ƙara yayin da yaran da
Papa sukayi ƙoƙarin tasowa amma kowa Ya tsaya sakamakon Tsawar da Anisa ta daka tana
maiyi masu alamu da su koma su zauna inda suke,
Kama jelar gashin Mami tayi wanda akayiwa All back tace "idan bakinki Ya sake faɗin sunan
mahaifiyata tabbas sai na baki mutuwar da zaki roƙeni na kasheki lokaci ɗaya ki huta,duk wani
makircinki da iskancinki da kikayi a lokacin yana tafin hannuna sannan ina san ki sani lokacin ki
Ya wuce yanzu namu ne ,ko ince nawa saboda hatta ita tsagerar yarinyar da kike da ita yau
tana ƙarƙashin ikona saboda ina rike da weakness ɗinta,
Cikin kwantar da hankali Nadiya tace "what on earth do you want Anisa ,Mai kike so ayi
maki?"
Nuna Nadiya tayi ta wuƙar tace "Good question ,ina san mijin Umaimah babban munafukin nan
Ya dawowa da Mahaifiyata budurcinta da rayuwarta da ta rasa ,idan kuma bazai iya ba sai ku
zaba ko shi ko ita ,dole za'ayi ɗaya cikin biyun nan shine abunda nake so."
Tasowa Nadiya tayi tana Dariya wadda ta ɗauki Anisa da mamaki,
Tafi Nadiya ta fara tana Mai Takowa inda Anisa take,
Nunata Anisa ta fara da yatsa tana faɗin"kar ki kuma gangancin Takowa kusa dani,"
Murmushi Nadiya tayi tace idan nayi zaki kashe Mami ba?
To kashe ta mana indai zaki iya,
Sake danna wuƙar Anisa tayi cikin ciwan da tafara jiwa mami tace "One step Nadiya just take
one step and im gonna kill this old hag.
Kafun Anisa tayi Aune taji an kamo dukkan Hannayenta ta baya an murɗesu,
Da sauri Nadiya ta taro mami dake ƙokarin faduwa inda take Papa Ya taso yana Mai kiran
sunan Mami a kidime,Kallan Abdallah yayi yace "maza Abdallah je dauko first aid box".
Da gudu Abdallah ya tafi ɗaukowa yayin da Nameer Ya saka saban hanky ɗin dake aljihunsa
gurin ciwan.
Takawa Nadiya tayi tana kallan yarda Anisa ke ƙokarin ƙwatar Kanta daga hannun ƙatti biyun
da suka rukunkumeta,
Tafi Nadiya tayi Mai sound biyu a gefe ɗaya ,yayin da ta sake wani Mai sound biyu ɗin a gefe
ɗaya ,matsawa tayi daf da Anisa tana Mai ɗago hab'arta da hannu ɗaya tayi wani sound na
tausayi da bakin ta tace "Ya kika ga yarda nawa wasan Ya juya ,"Hannunta ta ɗaga sama tace
"Allah sarki,kina tunanin zamu zauna ne Akan hannunmu ki kashe mu ki wuce sai kace wasu
kaji? "
You must be a fool idan har koda sau ɗayane kin yarda da hakan,
Duk gogewarkanki baki kai karfi da girma na yan uwan taka ba.
Kuskure guda ɗaya kikayi wanda shine nuna mun ke ba mutuniyar Arziƙi bace tun farko,
Dama i had My doubts amma kikayi min Clearing a ranar da kike sake jadada mun mu agololi
ne .
Wata irin dariya Anisa tasa tace "Kina tunanin kun ci galaba akaina ne?"
na yarda kun sameni off guard amma ku sani bazan je prison ba ,i refuse to go,ba ku san
kungiyar da na fito daga ba ko,muna karkashin Strong Mafians wanda a yanzu idan nayi
commiting suicide sai sunyi wiping duk zuriar ku .
Dariya Nadiya tasa kafun tace be My guest,
Kafun Anisa ta farga Nadiya ta ɗauke ta da mari,bata bari ta fito daga shock ɗin marin ba ta
ɗauketa da wani tace"wannan marin Na disrespecting Mami nane da kikayi ,ɗayan kuma na
yiwa Papa sharri ne ,ƙara mata wani tayi tace"wannan kuma nayiwa Hamma na ƙazafi ne da
kuma kawo yaran da baki Chanchanci kawowa duniya ba,you're a disgrace to All mothers
,sannan inaso ki sani wannan karan tunda zaki prison ta hannun mu sai na tabbata kin samu
sentence na life 'in prisonment sannan Mafian da kike taƙama da Babu abunda suka isa suyi
cos you've messed with the wrong people ,
Kiyi ta addua kar su bibiyeki a Chan dan yanzu haka maganarsu da kika fara anyi recording dan
bada hujja akanki a kuto,
Mu haɗu a court,saseen take her out.
Handcuff aka saka mata a hannu yayin da matar da ta saka mata handcuff ɗin ta kaɗa
ƙeyarta ,
Tirjewa tayi tana Mai kallan Nadiya tace"kafun naje prison ɗin sai da na tabbata na bar maki
tukuici,"Yarona Mahmood kila da dake akai DNA za'a samu Positive result ,cos ƙaninki ne
wanda na samu da Ubanki Belal ta hanyar zina .
Tana kai ƙarshen maganarta ta juya ta cigaba da tafiya tana Mai kece dariya.
Wata irin juwace ta ƙwashi Nadiya,Tana ƙokarin faɗuwa Nameer ya Tare ta,wasu irin hawaye
Taji suna mata yawo a kunci ɗaya bayan ɗaya,
"Kamata Ka kaita kan kujera Nameer tayaya yazama tukuici a gurinki bayan wanda take ikirarin
Ɗansa ne baki da alaƙa dashi,
Mami ta faɗa duk da tana cikin raɗaɗi.
"Haka nan taji kirjin ta yayi mata wani irin zafi bata san lokacin da ta fashe da wani irin kuka ba.
Babu wanda yace mata tayi shiru dan ko ance tayi shirun ma bayi zatayi ba ,
Haka nan ta gama batare da ta cewa kowa komai ba ta wuce ɗakinta,
A hakan nan ba Tare da kowa yace komai ba suka wuce ɗakunan su inda Mami tasaka Mai
aikinsu ta ƙwanta da Mahmood tunda dama ana basa madara.
Washe gari haka nan kowa ya tashi da abunda yake damunsa ,breakfast ma kowa daban
yayi ranar,Basu suka tashi haɗuwa ba dukkansu sai Wurin 10 ,
Nadiya ne ta fara magana inda take cewa"Mami saseen yace ankai maganar Anisa court amma
yanzu tana kulle gobe idan Allah ya kaimu za'ayi Zama ,babu wani Complication Za'a Yanke
Mata Hukunci Tunda Akwai Evidence Sosai Da Yake Pointing Kanta ,
Mami takama hannunta tace "kar ki damu Nadiya ,babu abunda Ya haɗa ki da bilal kar ki
ɗorawa kanki damuwar Abunda Anisa ta faɗa maki,and jibi nida Nameer da Abdallah da
Papanki zamu kai mahmood gidansu gurin mahaifinsa"
Kukan da take dannewa ne Ya ƙwace mata tace "Mami still jininsa ke yawo a jikina ,shine
yayi silar kawoni duniya,im pretending kamar komai is okay amma Its not cos a kullum idan na
tuna jininsa ke yawo jikina sai naji kamar na buɗe jikina na kwashe jininsa,"
And mami ki kalli Mahmood fa,yaro ne bai masan komai ba a duniya ,ki kalla ta hanyar da aka
samesa,uwa bata gari ba haka zalika uba,har gwanda ni Zan daki kirji nayi alfahari da samun
uwa kamar ki,
Kamo hannun Mami tayi idanunta na zubar hawaye tace "Mami 'dan Allah kar ki maidawa Bilal
mahmood ,yaran abun tausayi ne ,koda za'a basa shi ba yanzu ba,dan Allah mami nasan da
wuya amma ki taimaka ki bawa ƙanina mahaifiya ta gari da baya dashi. ,"
Shiru Mami tayi tana kallan Nadiya yayin da zuciyarta ta karaya sosai,
Hannunta da taji Papa Ya dafa ne yasaka ɗagowa ta kallesa,
Cikin kwantar mata da hankali yace"maganar da Nadiya ta faɗa abun a duba ne ,ni kaina tun
jiya da maganar na ƙwana ,we can adopt him kamar Yarda Nadiya ta faɗa gidan Bilal ba gurin
da innocent yaro kamar mahmood zai tashi bane,na tabbata we can give him a Good life.,"
Ƙwallace ta ciko idanun Mami tana Mai kallansa tace "ka karbi yarana wanda Bakai ka
haifesu ba amma ka basu uba ,baka tab'a nunawa koda sau ɗaya ba Akan ba naka bane
sannan yanzu zaka karbi Yaran mijina wanda ni kaina bana da alaƙa dashi,Shin wane irin
zuciya ne da kai,?
Why are you this kind?"
Cikin kwantar mata da hankali yace"kar ki damu matata,idan baya da Alaƙa dake yana da
alaƙa da Nadiya sannan kar ki manta Nadiya na ɗaya daga cikin yara mafi soyuwa a zuciyata
,sannan shi ɗa Ai na kowane kika san wanda zai mana rana,kar ki damu Daga yau Mahmood
Ya Zama ɗaya daga cikin AHALINMU ,insha Allahu zamu basa kulawa kamar yarda zamu bawa
namu."
Cikin kuka Nadiya ta rungumesa tana mai faɗin"Allah ya baka Aljanna mafificiya Papa,kai
babban mutum ne Mai babbar zuciya ,Allah Ya kula maka da zuriar ka ko bayan babu kai."
Sallamar da akayice ta katse masu hanzarinsu,
A tare baki ɗayansu suka kalli ƙofar ,Baba maigadi ne Ya shigo,
Abdallah ne yace "barka Baba lafiya dai ko?"
"Wata lafiyarce ta ƙaraso ɗaga cameroon."
CHUCHUJAY ✍
[3/6, 5:14 PM] Chuchujay✍️: AHALINA
(Siblings of different father's)
Book two 'in Aure uku series
By
CHUCHUJAY ✍
EPISODE2⃣5⃣➡2⃣6⃣
Cikin takunta na ƙasaita da isa ta fito daga bayan Baba Mai gadi wanda suka gama rigima
kafun ta shigo,dan tsabar isa har cewa tayi sai tayi silar barin sa Aiki a gidan ,
Tsoro yasaka yayi mata iso jin tafara maganar sanadiyar barin sa Aiki gidan tunda bai san
menene matsayinta a ciki ba .
A zabure Nameer Ya tashi yace"Mai kikeyi anan?"
Cikin mamaki Nadiya ma ta Kalleta tace "Nima dai abunda nake shirin tambayar ta kenan
Hamma ka rigani,ina kasan wannan rasa kunya beran tankar ,dan wannan matar a gamon da
mukayi na farko nasan bata da ɗa'a and im sure bibiyata take yi wanda shine yasaka ta zo
gidan nan,gashi ni kuma a yanzu bani da lokacin ta dan Allah ka fitar da ita daga gidan nan dan
ban shirya ɗaukar models ba im sure gurin zama ta rasa,"
Murmushi tayi ta karaso ta zauna akwatinta da kit ɗin ta wanda baba Mai gadi Ya dauko mata
gabanta,hannunta kuma ɗauke da lollipop tana tsotsa,
Ajiyar zuciya tayi tace "Nadiya kalli ya wuce mana ,abunda Ya faru tsakanina dake a airport
rashin sanin juna ne,na tabbata da ace munsan juna a lokacin farin ciki zamuyi na haɗuwa da
juna,amma yanzu tunda na gano wacece ke ina farin ciki na samun sister Mai irin taste dina
,komai Ya wuce,"
Kallan mami tayi tana Mai faɗaɗa murmushinta tace"daga gani wannan ce mom ɗin mu,ga
dad,barka da gida."
Cike da mutukar fushi Nameer yace"JAMAIMA watch it sannan kafun ranki yayi mutukar b'aci
kizo ki bar gidan nan,"
Kallansa Mami tayi tace"menene Haka NAMEER?"
Saboda mai ranta zai b'aci and wacece wannan d'in daga gani kasanta ,yanayin ka kawai ya
nuna mun you're not pleased da ganin ta,meke faruwa?.
Mutuwar zaune Nadiya da Abdallah sukayi jin sunan da NAMEER Ya ambata,so wannan ce
Jamaimah,
Nadiya na ƙokarin magana Jamaimah ta rigata ta hanyar faɗin"Mom kiyi hakuri da yarda na zo
maki baku gayyace ni ba cos im high class nasan yarda zuwan baƙo uninvited yake ,amma
Mom ni ba baƙuwa bace ba,ni ƴarkice saboda tsakani na da NAMEER akwai igiyiyoyin Aure
guda uku,."
AURE?
Mami da Papa suka maimaita Kalmar da mutukar mamaki.
Cikin yanayi na ko 'in kula Jamaima tace "uhum,bai faɗawa kowa ba kenan,"Juyowa tayi tana
Mai kallansa yarda yaka tafarfasa kamar zai ƙone tace "baby na faɗa maka lokacin da mukayi
Aure Akan Kagama gujegujenka da duk wani abu a zakayi idan ma Aurene kayi amma kasani
'ina nan Zan dawo rayuwarka,which im sure a yanayin da na sameka baka da Aure wanda
hakan yana nufin ka rike mun alƙwari ,menene abun boyewa yan gidan ku, tho nima na boyewa
mahaifina maimartaba Rais amma mahaifiyata babbar gimbiya tasan da maganar ,magana ake
tayi min aure nikuma bana san wanda za'a Aura mun,infact bani da niyar bautawa ko wanne
lamido da sunan sarauniya wadda ta basa mulki bugu da ƙari kuma bana san aikata laifin Aure
Akan aure tunda dai niɗin matar Aure ce kuma ina san mijina so na hakika 'dan haka na yanke
shawarar barin kowa da komai Nazo gareku,"
Kallan mami da Papa tayi waɗanda suke speechless tace"ina fatan zakuyi haƙuri dani ku
ƙarb'eni a yarda nake ta bangarena kuma nayi alƙwarin zanyi iya bakin kokarina wajen ganin na
ƙwantar da kaina gareku a matsayin ku na surukaina duk da abune wanda ban iya ba,"
Gyara zamanta ta sake tace "kuyi haƙuri ban samu damar gabatar maku da kaina ba,sunana
Jamaimah Rais ,yar asalin garin cameroon haifafiyar masarautar Dilah,"
Ni kaɗai nake gurin iyayena sannan nice ke da hakkin nada lamido Ta hanyar Aure,haka
al'adarmu yake ,ni kuma ina san ɗanku shi yasa Na bar komai domin sa.
Hannunta NAMEER yakama yace "tashi kibar gidan nan Jamaimah kafun raina yayi mutukar
baci naki Kema Ya b'aci,kizo ki koma inda kika fito."
Tsawar da Mami ta daka masa itace ta saka Ya saketa ,
Kallansa tayi ranta a mutuƙar bace tace"samu guri ka zauna ,Bana san iskanci yanzu Zan b'ata
maka sosai da sosai."
Kallan su Nadiya tayi waɗanda a kallo ɗaya zakayi masu kasan cewa sun san da maganar
Jamaima,ƙaramar dariya tayi tace "so its true,fuskar kannenka ma Ya faɗa Sun san komai so
nida Papanku ne yan iska waɗanda bamu da darajar da zamu san abunda kayi ko,"
Katab'a zuwa kace kana san Aure munce baza muyi maka ba?
Shine har zakayi Aure a wani guri NAMEER bamu sani ba?
Yaushe zamu samu peace sau ɗaya a gidan nan ne,jiya da daren nan muka fita daga wata
fitinar gashi wata ta mana sallama,
Tashi tayi idanunta cike da ƙwalla ,
Cike da tashin hankali NAMEER ya bita yana Mai faɗin"mami i can explain please,"
Da fitina cikin idanunta ta juyo tana kallansa tace"idan ka sake taku ɗaya ka biyoni sai na sab'a
maka ,Zan maka abunda zakayi dana sani nima nayi,sannan bana san na fito naganka kai da
yarinya Chan a cikin gidan nan ,ka ɗauke ta tunda Allah yayi kana da naka gidan ka kaita,Ai
kaine ka haifi kanka baka neman shawarar kowa kaje kayi abinda kaga dama da rayuwarka."
Durƙusawa yayi a gurin yana kuka saboda irin tsananin bacin ran da Ya gani a cikin idanun
Mami,yana wannan kukan Papa ya gifta ta gefensa ba Tare da yace masa komai ba yabi bayan
matarsa ,
Tasowa Nadiya tayi ta Dafasa tace "Hamma wannan kukan bashine solution ba,Ka tashi
yanzu kamar yarda Mami tace zamu san yarda za'ayi ,"
Tasowa Abdallah yayi shima yana Mai faɗin"hamma we will sort everything out insha Allah."
Tashi yayi yana Mai kallan inda mami tayi kana Ya share hawayensa Ya maida kallansa kan
Jamaima wadda take mamaki zaman da yayi yana kuka,
Tasowa tayi tace "ni Bansan menene abun tashin hankali ba Akan maganar Auren nan,naji ba'a
kyauta ba amma Ai the damage has been done maine abun kuka ,"
Cikin wani yanayi na b'acin rai Nadiya Tace"na tabbata baki san menene girman abunda kika
aikata ba ko nace baki san menene ake kira da mutunci family ba shi yasa zaki tambaya menen
abun kuka."
Barin gurin tayi 'dan idan ta cigaba da Zama a anan gurin zata yiwa Jamaimah wulaƙancin da
har abada bazata manta ba,
Da wani iri yanayi NAMEER Ya kaleta yace "kisan inda dare yayi maki domin bana tunanin
darenki yana tattare dani,"
Cikin nutsuwa Abdallah yace"hamma idan har Auranka kai da ita kaima kasan Aurene maganar
ta Kama gabanta bai taso ba,"
Yarda mami ta faɗa ka ɗauketa ku tafi gidan ka 'in yaso daga baya komai zai gyaru.
Cikin ido Nameer ya kallesa inda shi kuma Ya bashi assurance da ido,
Bai ce da ita komai ba ya shiga ɗakinsa ɗan ɗauko mukullin motansa dana gidan.
Zama abdallah yayi kujerar dake kusa da ita yace"ni tabbata ba kisan wanene hamma ba,ta
iyu kin Aure sa amma bana tunanin kinsan menene ma'anar Aure ,nuna lollipop ɗin da Take sha
yayi yace "na farko wannan alawar da kike tsotsa gaban su Mami kina magana cikin kalamai
marasa da'a Shine abu na farko da zai fara baki matsala,'dan a iya zuwanki yau na tabbatar
ladabinki da sauki,
Ta iyu a inda kika fito kowa yana duƙa maki amma annan kuwa Babu Mai duƙa maki muddin
baki sauke girman kai da yake damun ki ba dan akwai sa,
Anyi kuskure