Showing 15001 words to 18000 words out of 73196 words

Chapter 6 - AHALINA (Aure uke series)na chuchu.pdf

Advertisement

08 Jul 2025

2301

bamu isa mu rushe sa
ba,"i Feel something towards you i wont deny it,amma nafi jingina sa da Attraction ɗin da bazai
tab'a cika ba,"
We have different religion ,Culture,beliefs da bazai tab'a barinmu tare ba,bazan iya Aurenka ba
not because Bana sanka sai dai 'dan Addinina bai yarda na Aure ka ba muddin baka musulunta
ba,

Sannan ni bazan boye maka ba,"i will never convert to Christianity dan mutanenka su karb'eni
,bazan iya ba,wanda nasan kaima bazaka iya barin Addininka ba,so im begging you,dan mu
yiwa kanmu katanga da heart break lets end every desire we have towards each other ,and
banyi worthing kayi commiting suicide saboda ni ba,i know a Addininka ma haramun ne so
please kar ka sake faɗan haka,

And yes i suggest we be frnds With No string attached ,i promise zaka samu wadda tafini, i
know it ,

You're handsome,rich,And kind. "

    A hankali Ya zare hanunsa daga riƙon da tayi masa,

Kallanta yayi da wani irin yanayi na rashin jin daɗin conversation ɗin da ya shiga tsakaninsu
kafun yace "Good night cikin sassanyar murya kafin ya buɗe mota Ya shiga nasa,"

A yanayin yarda Ya figi motan ta san zuciyarsa babu daɗi,

Ajiyan zuciya tayi tana Mai karawa kanta ƙwarin gwiwa Akan abunda tayi shine dai dai.

  *

     Zaune take Akan gadonta daure da towel a kirjinta hannunta dauke da wayarta,

Basai ta faɗa maka ba kasan daga wanka ta fito,tashi tayi ta nufi walk 'in closet dinta 'dan
shiryawa,

Turus tayi lokacin da ta fito taga Aneesa zaune bakin gadon ta,

Ƙaramun tsaki tayi tace "lafiya?"

Mai kike mun a ɗaki.

Kallanta Anisa tayi daga sama zuwa ƙasa kana tace ,ɗakin ki?

Taƙama 'fa kike da gaibu domin ko yanzu Mai gidan nan Ya faɗi Ya mutu baku da gadon ko
tsinke Ya kamata kiyiwa kanki faɗa ki nemo miji kiyi Aure ba ki ɗauki wani katon Arne ba ki kai
gidan Auntynku,dan na tabbata sai dai s*x ɗin wadda nasan ita yake binki domin,


Da mamaki Nadiya tace "stalking ɗina kika fara?"

Kallanta tayi daga sama har kasa cikin yar karamar rigar baccin dake jikinta kafin ta kara da
cewa"zaki iya sakawa a haka idan hakan yayi maki,jikinki kam Mai kyau,dama Mai za'ayi
expecting gurin model,jiki kam zai kyau amma bamu da tabbacin HQ ɗinsu cos gurine da ake
rabawa ko wanne kazami 'dan  a samu connection,gashi kuma Alhamdulillah kinsamu cos
Agency ɗinki har Abroad kinga HQ ya Biya,i just hope a jiƙe yake,idan kuma abushe kike akwai
wata ƙwata Mai kayan mata plug zata taimaka maki,Ni kaina idan nasha maganinta ihun da
yayanki yake Ya isheki zama wet,".

    Ba tare da Nadiya tace wani abu ba ta koma koma walk 'in closet dinta ta ɗauko belt dan Baki
bazai isheta tayiwa Anisa abunda take san mata ba sai dai belt ɗin,

Tana fitowa kafin Anisa ta farga ta fara buga mata karfen belt d'in,

A razane Anisa ta miƙe ta kama bakin belt ɗin ta rike gam gam,

Kokawa suka fara wanda ta Nan Nadiya ta fahimci Anisa is trained ganin yarda take binta ta
hanyoyi da dama 'dan ganin ta mata illa,to itama ɗin ta san hanyoyi na self defence 'dan haka
Ta Shiga kare kanta inda Allah Ya bata dama ta buga kan Anisa A bango wadda ta faɗi a sume,

Tsaki tayi da ta tabbatar suma tayi ta jata wajen dakinta ta ɗauko jug d'in ruwan da take ajjewa
gefen gadonta saboda tashin dare ta sheƙa mata jikinta,

Sai da ta bari ta farfaɗo tace"Gobe idan kika ƙara shigo mun ɗaki sai naci uwarki,sannan ki fara
lissafin ƙwanakin da suka rage maki gidan nan,karuwar banza yar iska kawai."

    Tana kai karshen maganarta ta bugo kofa ,zama tayi tana Mai mayar da ajiyar zuciya tana
Mai sake tariyo ƙarfin da taji tattare da Anisa,Shin wacece wannan yarinyar?

Ƙarar da wayarta yayi ne Ya dawo da ita daga duniyar da ta shiga na tunanin wacece Anisa ,

Sako ne Ya shigo mata ta Email,da saurinta ta shiga jikinta na bata abun Alheri ne,ille kuwa
tana shiga Biodata ɗin Anisa ne harda hotonta,

Suna:Suwaiba (Aneesah) Idris meta.

Ƙasa:Nigeria

Gari:Niger state'

Sunan Mahaifi:Idris meta

Sunan Mahaifiya:Sameera Idris Meta.

Aiki:Gungur Assassin trained for four years/killed 25 people /once a stripper in Custo Club
Newyork.

Riƙe baki Nadiya tayi maganar Fawzan na dawo mata da yake faɗin yasanta  a New york ne
wanda ta tabbata akwai more about yarinyar nan,

Tabbas yanzu ta fahimci daga inda karfin Anisa yake ,

To ko menene zai kawo Assassin gidansu?

Saurin dialing numbern gayen da ya tura mata Info d'in tayi,

Yana ɗauka tace "why is this girl moving the world freely When she killed 25 ,for God sake 25
people ,like nothing happened?."

Daga ɗaya bangaren yace:ma'am kungiyar da suke ƙarkashinta kungiyace da take Active for 20
years kenan wadda nake tunanin akwai manya dake ɗaukar nauyinsu wanda im sure shine
dalilin da Ya saka take waje har yanzu,amma ma'am abunda nake san ki sani shine she's
dangerous beyond tunaninki,just be careful sannan har yanzu muna kan bincike Akan dalilin
zuwanta Nan gidan ,idan ma dai anyi hayarta ne our team is capable zamu gano dalili.

Ajiyar zuciya tayi tace "thank you very much ,Zan wiring naka sauran payment ɗinku and i will
be expecting you,"

Hanging wayan tayi tana Mai cizan yatsanta tana tunanin yarda zata bullowa al'amarin.




CHUCHUJAY ✍
Follow My whatapp channel
https://whatsapp.com/channel/0029Va9RLKT2P59fHSa7Ia1j
[3/6, 5:11 PM] Chuchujay✍️: AHALINA

(Siblings of different father's)

Book 2 of Aure uku series

          By

CHUCHUJAY

Episode 1⃣5⃣▶1⃣6⃣

     Adda ,Adddaa..

A zabure ta amsa tana Mai fitowa daga duniyar tunanin da ta shiga,

Hannu ta saka akanta tana Mai saita kanta kafun tace Ya akayi FAWZAN,

Yaushe ka shigo,

Guri Ya samu Ya zauna yace "tun ɗazu nake miki knocking amma shiru and PA ɗinki Ya
tabbatar mun kina ciki so na shigo 'dan tabbatarwa cos yau baki ɗayanki na kula ko a gida you
looked disturbed ,lafiya kuwa?"

Gyara zamanta tayi tace "lafiya Fawzan jikina yau kawai na tashi duk Ya mutu bana cikin wani
mood Mai dadi,

So what's up ba yau zaku wuce ba,  "

Zama yayi kan desk ɗinta yace"yes Yau ne amma night flight zamu bi ne,and Fauza da Fawha
suka saka cos sun cema Papa bazasu koma ba idan ba ke da Hamma,da Hamma Abdallah
suka raka mu Airport ba ,and gladly ina goyan bayansu,

    Dariya tayi tace"its okay Ai its not a big deal tunda ku da ƙasar nan da yarda kuke ƙaunarta
idan kuka koma sai dai mu biku kan kuzo,"

    Faɗaɗa fara'arsa yayi yace ,shi yasa muke bragging na yayyi Ai,wayansa Ya ciro yace yauwa
Adda Akan Anisa,kamar yarda nace maki zansaka amun bincike,jiya Abokina Ya tura mun,"she
was a stripper and an kamata da drugs na Mexican mafian's ,shekararta ɗaya aka fito da ita
maimakon shekaru bakwai da zatayi,inda ake zargin Maxicans ɗin suka fito da ita,and tana da
murder case a ƙasa wanda shima aka kullesa ,amma Bansan komai akanta ba bayan barinta
New york ba.

    Cije leben tayi tace "send me evidence ɗin ta Email ɗina sannan kaja bakinka kayi shiru,and
make sure a sauran yininka gida kayi avoiding ɗinta and be careful."

Dan shiru yayi yana kallanta kafun yace"abun is serious haka".

Kamar jira take Ya tambaya ta amsa tace "ƙwarai ,'dan haka be careful ,Tashi yayi yana Mai
saka hannunsa Aljihu kafin yace "nasan ko mene tazo dashi Family ɗinmu yafi karfinta cos kan
mu a haɗe yake babu wanda zai iya rabamu ,saboda wanann ƙaunar ma nake so yanzu kasaka
mun 20k zan ɗan fita,kuma banda mai"
    Dariya tayi tace"naughty boy,ko wacce mota a gida cike take,kai dai kace mun zaka je yawo
and its okay zan tura maka 50k"

Da murnarsa Ya fita office ɗin nata,

Bayan ta gama ayyukanta itama wurin lunch time Abdallah Ya kirata Akan su haɗu zai zo da
Fadil,

    Ita ta rigasu zuwa restaurant ɗin kana suka zo,

Kallanta Fadil yayi kafun Ya zauna yace "Nadiya right" .

Ƙaramun murmushi tayi tace "yes Nadiya,naji daɗin haduwa da kai fuska da fuska,"

Bismillah zauna .

    Babu musu ya zauna,waiter ne yazo sukayi ordering abinci,

Kallan Fadil tayi kafun tace"kai Abokin Hamma Nameer ne ko kuma Abokin Salis"?,

Ba wani ƙwana ƙwana ya kawoni ba saboda abubuwan da na bari kafin nazo nan suna da
yawa,

    Da mamaki Fadil Ya Kalleta yace "ina kika san Salis,sannan wannan tambayan na ji ƙamshin
trouble cikin ta hope im safe,

Ruwan ta ɗauka ta ƙurba kana tace"Eh kamar kana cikin gaskiya a hangena,kamar yarda nace
maka im a busy woman to ba wasa nake ba,let me cut to the chase,"

Wayarta ta ɗauko ta kunna recording  ɗin hirarta da Salis tace"ka saurara da kyau".

    Nutsuwa yayi dan saurara yana Mai sake kallanta cos yarda yake ganinta a hoto ta taka haka
a fili sannan duk wani abu da take a yanzun ji yake tana wani sake burgesa,Amma Nameer
shegene,yana da Zan ƙaɗeɗiyar ƙanwa tun fil azal yayi masu shiru Ai Da tun tana da ƙananun
shekarunta zai gina mata soyayyarsa dan shifa Ya kamu,

Ɗago kai yayi yana Mai kallanta lokacin da sautin Ya hau kan muryarsa ,

Ɗaga masa gira ɗaya tayi tace "Ba sai ka tambayeni ba ,lokacin da kuke waya ina zaune a
office ɗinsa ,"

Jan wayarta tayi da ta tabbatar ankai inda Ya kamata yaji,

Mayarwa tayi handbag ɗinta tace "ka fara magana,ka dai saurari abunda abokin ku yace
,sannan da wanda ka faɗa a yayin da Ya kira ka,menene gaskiya a ciki sannan idan kamun
ƙarya bazan ƙasa a gwiwa ba wajen sanarwa da Hamma Nameer da irin micijin da yake tare,

Hannu Abdallah Ya saka a ƙafarta jin yarda take wa Fadil ɗin magana yace Adda mana.

    Murmushi Mai sauti Fadil yayi yace "kar ka damu Abdallah,Ai duk wanda yake hot seat bai
kamata Ayi masa sauki ba sannan nima yanzu Akansa nake Its okay,"Wato ainayin magana
fisabilillahi duk abunda Salis Ya faɗa maki ƙaryane ,

Nameer mutum ne wanda ko drugs kake yana tare dakai zai rabu da kai,shi Salis ɗin da yake
wani maganar An Kama Nameer da Drugs ƙarya yake yi,maganar da yake shine aka Kama da
Drugs masu haɗarin gaske ,mu muka fara ganinsa dashi so we asked him yayi turning kansa in
amma yaƙi so mukayi reporting ɗin sa wanda shine babban Abunda Ya saka muka yanke alaƙa
dashi,

Sannan magana da yake na Nameer na bin mata ,ƙarya yakeyi,nayi imani da Allah da kikaje
gurin sa Ya nuna miki ɗaya daga Cikin halayyarsa na dabbobi im sure,

Amma kirana da yayi akan maganar Jamaimah tunda ya fara miki maganar bari na Faɗa maki
Ya abun ya faru,

Cikin kwanciyar hankali yayi mata Narrating yarda Auren Jamaimah da Nameer Ya kasance.

Dukan table ɗin Nadiya tayi tace "a cikin zancen nan Fadil kaine ummul abaisin komai da Ya
faru "

Kamo hannunta Abdallah yayi yace "Adda Hamma is equal responsible ko nace miki ma yafi
kowa laifi cos Aurensa muke magana akai wanda Am sure a lokacin yana da isashen ilimin
addinin da yasan cewa Auren da yayi Ya ɗauro,the damage has been done kawai yanzu
solution' zamu nemo ,amma tukunna Ya maganar Anisa,
    Kallan Fadil tayi "tace Thank you,Zan iya samun numbern Jamaimah gurinka ko kuma wata
hanya da Zan sameta?

Murmushi yayi yace "you're welcome and wallahi tun gama makarantar mu bani da wani contact
da ita ,amma dai yar kamaru ce ,sannan kuma ɗiyar sarkice shi kaɗai na sani.

Abincin da sukayi order aka kawo musu, bayan sun gama ci Fadil Ya kalli Nadiya yana Mai
shirin barinsu yace "Zan iya samun numbern ki?"

Murmushi tayi ta buɗe jakarta ta ciro office card ɗinta ta miƙa masa tace "gashi ,kana da jiki mai
kyau ,sai dai kana da bukatar motsa jiki sosai,

Duk lokacin da kaji aiki a company ɗin yayana Ya isheka kazo muna da gurin aje ka  .

    Dariya yayi wadda ta bayyana hakoransa yace "nine da godia Hajiya Nadiya sannan kamar
yarda kika Bani wannan tayin Zan ƙoƙari naga nayi amfani dashi,"

Yana bari gurin Nadiya ta kalli Abdallah tace "kake wani tambayana maganar Anisa gabansa
,ba wani hurumi da yake dashi na jin wacece ita,amafaninsa na muji tabbacin Auren Hamma ne
kuma munji cos Anisa da kake gani serial killer ce ,Assassin sannan she's dangerous fiye da
Tunanin ka,  "
Abunda ta samo na dangane da ita ta nuna masa,da mamaki yace kamata yayi Info ɗin nan
yanzu yana gurin police 'fa,

    Karbar wayar Nadiya tayi tace"as if,"

Kana tunanin police zasu wani ɗauki Wani hukunci kanta?

Idan zasu dauka Mai takeyi har yanzu a waje,

Bro abun wannan yarinyar is beyond tunanin ka ,babu ruwan mu da kisanta da dalilin rashin
kamata da ba'ayi ba,yanzu mu babban damuwar mu shine tayaya zamu gano dalilin zuwanta
gidan mu,sannan mu sakata tayi wani fuck up ko sau ɗayane mu bada hujjar da zaisaka ta
zuwa gidan yari,shikenan,
We need her out of our home and our lives.

Sannan Maganar Jamaimah dole muyi confronting Hamma ,wannan ba abu bane na boyewa
cos idan Ya bar abun nan a boye nan gaba Outcome ɗinsa babu kyau,

Kaɗa kai yayi cikin gamsuwa da shawararta ,bayan sun gama cin abinci kowa Ya koma kan
aikinsa Akan idan suka koma gida zasuyi magana da Nameer.


**************

CAMEROON DILAH PALACE  .

     Jamaimah bazan gaji da faɗa miki ba kinyi girman da masarauta ke buƙatar kiyi Aure
,sannan kinfi kowa sanin Al'adar mu babu wani namiji da zaki Aura bayan wanda muka zab'a
miki shima ɗan AHALINMU,Saboda shi kaɗai ne wanda zamu ɗora kan kujerarmu saboda
kinsan dai mazan Mata ke sarauta ba gado ba,shi yasa muke zaban na jikinmu,masarautar nan
baki ɗaya kece mace wanda mijinki zai gajeni.

Tun Kina yarinya muke miki abunda kike so kika zaba ,kama da abunda zakici zuwa sutura
,zuwa zabin karatu,wanda ke Kina kallo yarda akayi tataburza zuwanki China,

Yanzu kuma Lokacine da magabata suka zab'a maki mijin Aure HARITH bana san azo an'a
wayace Jamaimah,

Mahaifinta Sarki Rais Ya faɗa ciki harshensu na Fulanin cameroon fuskarsa fal dumuwa.

    Gyara zamanta tayi tana mai kallan girman faɗar mahaifinata wanda Ya gada guri mahaifin
Mamanta ,kamar yarda baban nata Ya faɗa dukkansu idan kabi zagayen masarautar da tarihin
mulkinta maza da matansu AHALI ɗaya ne,shi yasa Aurensu mace ɗaya wanda a haka
aladarsu ta tafi muddin zakayi mulki macen nan guda ɗaya,
Kallan mahaifinta tayi cike da fitsara cikin yaren nasu da kuma salo na amfani da soyayyar da
mahaifin nata yake nata tace "Lamiɗo ,kafi gane nayi Aure cikin wannan masarautar nazama
baiwar wani wanda saboda ni yake mulki badan Ya kai yayi ba,,

Kamar 'fa kaine Lamiɗo, yarda Dada na ta ɗoraka kan kujerar nan amma kana kallo abinci nan
bata ci sai ka gama tukunna taci sauranka indai Kana gurin wai da sunan al'ada,alada a mey?

Ni gaskiya Lamiɗo ka yafe ni ,dan babu wani da Zan Aura wanda kuka zab'a 'dan kawai na
maidashi Lamiɗo,sai dai sarautar nan tabar ɗakinmu ta koma wani ɗakin tunda Ai masarautar
nan akwai yaƴan mata da kakannin akwai yarda zakuyi ku ɗora harith d'in idan shi kuke so,ga
yan mata a gidan,amma banda Jamaimah 'dan yarda nake zab'an duk wani abu da nake so a
bisa yarda kuka lalatani da zab'ar abinda nake So haka nan yanzu ma zaku barni da wannan
lalatar na zab'i wanda nake san Aura dan har nama zab'a .

    Da fuskar lallashi lamido Ya Kalleta yace "idan kin sakko zamu sake magana yar Albarka
,naga alamun yanzu bazaki fahimci Mai nake nufi ba,"

Tashi tayi tana Mai sake basa girmansa kana Ya fita a fadar wadda dama daga ita sai shi ,

Tana ƙokarin fitowa wani bafaɗe yana koƙarin shiga inda bai Aune ba sukayi gware,

Ɗago kai da yayi yaga itace ba ƙaramun rawar jiki Ya fara ba 'dan yasan rashin mutuncin
Gimbiya Jamaimah yau zai hau kansa,

Ille kuwa bai Aune ba ta ɗauke fuskarsa da wani irin tafi wanda yayi bala'in gigitasa,

Alƙabarta da Ya goga ta cire ta cilla masa kana ta miƙa hannunta wanda ƙuyangunta sarai sun
fahimci Mai take nufi,

Da gudu ɗaya ta ƙaraso da ƙwarya a hannu ɗaya kuma da ruwa a wani tulu ta fara zuba Mata
tana ɗauraye hannun data mari bafaden dashi,

Alamu tayi da hannu zuwa ga bafaɗen wanda sarai Kungarta ta hannun dama ta fahimta ,kai
tsaye gurin Bafaden tayi da ƙokan da ta wanke hannu ta kama kanta ta kafa masa ruwan sai da
Ya shanye tasa kana tace "a ɗauke mun shi akaisa gidan gyaran hali ,ruwan nan da yasha shi
kaɗai nake san Ya riƙesa har gobe ."
Take kamar jira suke kar suyi wani laifin suka kama dakarin wanda yake ta ihun bata haƙuri
amma taƙi koda sauraransa,

Kai tsaye sashen mahaifiyarta ta nufa wanda yaji kayan Alatu na sarauta,a kishingiɗe ta tarar
da ita,

Kuyangun na ganinta suka fita dan basu guri 'dan yanzu Gimbiya Jamaimah zata maka
wulaƙancin da zakaji baki ɗaya ka tsani kanka,

Zama tayi kusa da ita tana Mai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login