Showing 60001 words to 63000 words out of 73196 words

Chapter 21 - AHALINA (Aure uke series)na chuchu.pdf

Advertisement

08 Jul 2025

2299

cewa" Alhaji Belal Ya kawo ƙarar tsohuwar matarsa ,Dr umaimah akan ɗora yarinyarsa
da suka samu tare akan hanyar banza saboda kiyayyarsa sannan daga bisani take san
salwantar mata da rayuwa ta hanyar Aurar da ita ga kafiri wanda suke ƙaryar Ya musulunta dan
haka yake neman custody ."
Lawyern Bilal ne Ya tashi Kana na Umaimah bisa umarnin Alƙali kafun shariar ta fara gudana,
Lawyer ɗinsa ne Ya tashi Ya fara da cewa"Dr Umaimah kowa Ya santa da halayyar biye biye
koda lokacin tana da Auran bilal shekaru ishirin da takwas da suka gabata domin silar
rabuwarsu Ya farune dalilin kamata da yayi da wani a ɗakinsu kan gadon su na sunnah ,sannan
ba wannan kawai ba shekarun da suka gabata Yaɗuwa na clip na tsiraici yayi yawo a yanar gizo
wanda ya wanzo tsakanin Dr umaimah da Mijinta da take Aure Dr Imam ,kukan wanda nake
karewa anan shine Alhaji bilal Ya tabbatar da cewa umaimah diyarsa ce sannan yana gudun
cigaban zamanta da mahaifiyarta saboda a yanzu ta ɗauko hanyar sabawa addini mutuƙa
,gudun cigaban lalacewar ƴar tasa yake roƙon wannan kotu Mai alfarma akan ta karba
jagorancin rayuwar Nadiya Bilal daga hannun Dr umaimah bulama domin shine Ya chanchanta
matsayin sa na uba da Ya cigaba da kulawa da ita har Ya aurar da ita gudun cigaban
lalacewarta nagode Ya Mai sharia"
Samun guri yayi Ya zauna yayin da Lawyern su ya tashi domin fara Nashi aikin ,cikin kwarewa a
aikin nasa ya kalli Bilal yace "idan kotu zata Bani Dama ina San zanwa Alhaji Bilal tambayoyi
biyu ."
Kada kai judge din yayi yace an baka.
Godiya yayi kana ya juya ga Bilal yace "Alhaji Bilal ina San na maka tambaya akan shin ka taba
ganawa da shi wannan saurayi na Nadiya da magana ta fara ta kansa tayaya ka gane shi din
ba musulmi bane? "
Dan shiru yayi kana yace"ni ban taba ganin sa ba ido da ido,amma ba Sai an fada,mun ba
musulmi bane tunda dai ai yana ghanian film wannan kowa yasan arene ne.

Karamun murmushi lawyer din yayi yace "a Sanina a lokacin baya kayi tantamar kasancewar
Nadiya yarinyar ka menene yasa a yanzu ka dawo akan ita din takace har kake barazana
wajen ganin ka kwaceta haka nada hadi da san zuciya ?
Lauya din bilal ne ya tashi yana mai fadin Objection my Lord,barrister salik yana kokarin waje
wuce iyakarsa.
Kallan barrister salik Babban alkali yayi kana yace "ka gyara salan tambayarka"
Cike da girmamawa ya karbi gyaransa kana yace"ya mai girma mai sharia,gudun zaunar da
kotu da bata mata lokaci yasa nake san na kawo hujojina na nuna lallai Alhaji Bilal bai
chanchanci Zama wanda yake da hakkin rike Nadiya ba,ba wai ina cewa ba mahaifinta bane ba
shi amma ina tsoran sanar da kotu cewa a suna ne kawai domin kuwa tun daga yarintar Nadiya
zuwa ga girmanta Alhaji Bilal bai san hakkin koda da siyan Kwayar shinkafa ba,sannan ina mai
san sanar wa da kotu mai Alfarma akan cewa shekaru da suka wuce,Alhaji Bilal ya sadaukar da
custody din Nadiya ga mahaifiyarta inda a wannan document din da nake shirin gabatarwa ya
saka Hannu akan tabbas idan yazo da maganar san s bashi ita a kamasa ayi masa hukunci.
Sannan magana akan halayyar Dr Umaimah duk karyane"
Zazzare ido bilal yafara yana mai fadin"karyane ya mai sharia ban taba saka hannu a abu
makamancin wannan ba,
Murmushi barrister Salik yayi yace idan kotu ta bani dama zan shigo da shaida wanda na
tabbata bazai ma Alhaji Bilal karya ba.
Dama aka basa inda ya bada izini da a shigo da Shaidar.
Shigowar mahaifin Bilal shine abunda ya sake bawa Bilal mamaki wanda nan take ya tuna
yarda akayi ya saka hannu a wannan document da ake magana akai.
Shaida maihaifinsa ya bada akan tabbas shi da kansa ya bawa Bilal wannan file ya cike kumaa
a cikin hankalinsa ba a maye ba sannan ni mahaifinsa shaidane akan hakan bazan taba bada
shaidar ƙarya ba .
Haka Lawyer din su shima ya tashi suka cigaba da fafatawa kowa na kokarin kare wanda yake
karewa cikin iyawa da gwaninta,
Hutun awa daya alkalin ya bada akan idan an dawo zaiji ta Bakin Nadiya kana ya yanke
hukunci.
Sun fita mahaifiyar Bilal ta kalli mijinta tace "Amma Alhaji baka duba wannan al'amarin ba domin
kuwa kasan cewa Nadiya ita kadai ce jinin Bilal kuma dole ne yau mu tafi da ita gida.
Ajiyar zuciya yayi yace"ke dai shaidace akan abunda Bilal yayi ma umaimah ke ganau ce ba
jiyau ba,sannan ina san ku sani Alhaji Bulama a shirye yake da ya fafata da duk wani wanda zai
taba masa iyalinsa kar ma ace kai Bilal ,so dole nazo da kaina Kafun shi yazo da kansa wanda
kai Bilal kasan cewa wallahi idan yazo babu dadi,shiru baki dayansu sukayi yayin da kowa ke
saka da warwara akan al'amarin amma tabbas suna bukatar Nadiya a tattare dasu.
Bayan lokacin da Alƙali ya yanke baki daya suka koma domin jin wanda yayi nasara cikinsu ,
fitowa Nadiya tayi bisa umarnin Alƙali mahmood a sabe a kafaɗarta,
Cikin girma irin na Alƙalin yace "Nadiya ga dai shari'a anayi dominki kuma shari'ar tsakanin
iyayanki ne guda biyu gasu nan ,wane kike san zama da a cikin su?"
Kalan iyayann nata guda biyu tayi tace"mahaifiyata ta daukeni a cikinta tsawan wata tara ,tayi
dauwaniyya dani tun ina ciki har zuwana duniya wanda a cikin rayuwata da ita ban taba sanin
babu ba,duk wani abu da nake So a rayuwata ita tayi mun shi,itace uwata itace ubana sannan a

wannan zama na rayuwa ta sama mun uba wanda bani da ya shi a rayuwata,
Gefe guda kuma wanda ya bada gudunmawar irinsane aka samar dani wanda tun fari yana
kokwaton kasancewa tasa shin idan na zavesa sama da mahafiyata duniya baza tayi Allah
wadai dani ba?
Shin menene gudunmawarsa a kasancewarsa mahaifina?
Babu ya mai girma mai shariah, mahaifina bai bari mun komai ba face kayan kunya da kayan
gori,
Nuna mahmood tayi da hannunta tace"wannan yaran dake hannun a cikin halayyasa marasa
kyau ya sameshi,yaro abun tausayi wanda bansan taya zan fara masa bayani menene
ainahinsa ba a lokacin da ya biɗa yasan hakan,"
shiru gurin ya dauka lokacin da Alkalin ya bukaci hakan,kallan Nadiya alkalin yayi yace kina
nufin kice shima wannan din ɗansa ne.
Kaɗa kai Nadiya tayi tace"tabbas na sane wanda ya samesa da Aneeesa wadda ta bamu
matsala cikin Ahalinmu a rayuwa dagaa bisani kuma bayan laifin da ya kaita gidan yari Allah ya
karbeta ,kafun nan kuwa ta shaida mun Mahmood jini na ne saboda Dan mahaifinane,na
tabbatar da Hakane sakamakon zuwa da mahaifina yayi gidan mu akan maganar komawata
gurinsa wanda nayi amfani da hakan na cire gashin kansa Nayi DNA dana Mahmood . "
Barrister salik ya dauki file din ya mikawa Alƙalin wanda ya tabbata da ba fake bane sannan ya
sake bashi document wanda Mami da Papa sukayi adopting Mahmood legally .
Bakin lawyer din Bilal ya mutu murus a yayin da Bilal ke faman rarraba ido yana kallan Nadiya
da Mahmood cos 'ya tabbatar da maganarta tunda tace Anisa amma a iya saninsa rabonsaa da
ita bata taba sanar masa tana da ciki ba, a zahirin yanzu kuma yana mutuƙar buƙatar jininsa a
tattare da shi. Bayan shaidu da hujoji kotu tayi facali da ƙarar Bilal sannan ta damƙawa Umaimah custody
ɗin Nadiya,a Haka ƙarar ta watse.
A tare Ahalin Umaimah suka fito cikin murnar cin nasara,suna kokarin shiga mota Alhji Bilal
yazo gabansu,tsaye dukkansu sukayi suna san ganin mene zaiyyi,
Durkusawa yayi kan gwiwarsa 'ya hada hannayensa guri biyu yace"Dan Allah Umaimah kiyi
hakuri nasan na cutar dake,bakina ma kunyar fada yake,amma ki yi mun rai ki tausaya mu ko
shi mahmood ɗiin ki bani na gyara kuskurena ta hanyar bashi rayuwa mai kyau da inganci."
Wani irin kallo mami ta bashi sannan tace,maganar banza kake Bilal,nayi imani da Allah baka
da rayuwa mai kyau din da zaka iya bawa Kowa a rayuwarka ,ba Nadiya ba haka zalika ba
Mahmood ba dan Haka ka dauki wannan a matsayin fansa ta akankah,wallahi bazan baka
mahmood ba sannan kasa a ranka Ni da Imam ne iyayansa ,ka godewa Allah Nadiya tasan
wanene kai da Bazata taba sani ba,ka shirya wata rayuwar wadda zaka rayu da sanin kana da
ɗa a waje wanda baka da iko dashi,
"Aikuwa karyarki umaimah Dan wallahi babu mai sakewa tuwo suna,dole ne mu daukaka ƙara
ki bamu yaranmu ,sannan abun kunya ai ba kansa farau ba ba kuma kansa ƙarau ba ehe,".
Muryar kakar Nadiya ta karaɗe gurin.
Murmushi Mami tayi tace"Allah sarki Mama Aikuwa zancenki dutse ba'a fara dashi ba kuma
baza a ƙare dashi ba dan haka mu haɗu gaba idan kun daukaka karar a shirye muke fiye da
yarda kuka shirya".
Basu kuma ce masu komai ba suka bar harabar gurin.

Durƙushe Alhaji Bilal yayi yana mai zayyano dana sani iri iri a ransa domin kuwa a wannan gejin
'ya tabbatar da ya rasa jininsa guda biyu wanda bincike 'ya nuna su kaɗai ne jininsa har ya
koma ga Allah sakamakon hatsarin da ya samu kwanakin baya,
Haka mahaifiyarsa ta ƙaraci banbaminta suka bar gurin .

A/N
Fatan 'na sameku lafiya ,So wayata ta samu damuwa yanzu kuma dana samu nayi kokarin
mayar dashi yaƙi dole 'na sake number ,
08130229878
Itace sabuwar numberta ta whatsapp sannan ina cigiyar Fatima tayi payment 'na littafi wanda
nasan tayi mun magana da wancan layina,ban riƙe surname dinta ba cos nayi missing alert ɗin
please idan kin gani kimin magana a layiina domin 'na baki littafin ki, nagode❤
CHUCHUJAY✍️
TBC
AHALINA

(Siblings of different father's)

Book two 'in Aure uku series

By

CHUCHUJAY ✍️

EPISODE 53&54

Koda suka koma gida sunyi mamakin tararar da Jamaimah gidan cos its not like her .

Kallo daaya mami tayi mata ta maida kalllanta kan Nameer tace "Ya maka Kyau da kowa ya
hallarci zaman ƙanwarka bandaa kai sannan ina fatan zuwan nan da kayi da matarka gidan nan
kasan ka karya Magana ta saboda 'na faɗa maka gaban yan uwanka bakaji ba ,inajin sai na
maimaita maka gabanta,kar ka ƙara zuwa mun da wannan yarinyar mara kunya muddin ba
sake banzan ɗabiunta tayi ba ,Dan Haka ka tashi ku fitar mun a gida kafun nayi mugun saba
muku sosai da sosai,."

Juyawa tayi Dan barin gurin tana mai ignoring yarda Papa ke mata signal 'na tayi shiru da ido,

Rike mata ƙafa da akayii ne ya tsayar da ita,juyowa tayi Dan ganin wanene, Jamaimah ce kan
gwiwowinta idanunta ɗauke da hawaye shabe shabe,Dan goge hawayen tayi ta fara magana
tana mai faɗin"ban san mai zance yayi justifying abunda nayi maku ba ,it was very stupid of
me,babu bakin da zan iya buɗewa na kare kaina dashi,Dan Allah mami kiyi mun rai ki hakuri ki
yafe mun ,'na maki Alƙwari bazan taba baki damar da zakiyi kuka dani ba,duk wani abu da ban
iya ba zan dage 'na koya da n ganin 'na zama kamar yarda kike So matar ɗanki ta kasance ,dan

Allah Mami kiyi mun aikin gafara ke da Papa da ku su Nadiya,wallahi nayi Alkwarin gyara duk
wani abu da yake ba dai dai ba Dangane dani ,idan nayi mara kyau a gyara mun zan gyara
domin ni ban tashi ana nuna mun wannan ba dai dai Bane ,ku yafe mun dan Allah. "

Shiru dukkansu sukayi suna masu jin tausayinta ganin Mami taƙi koda juyowa ta kalleta,

Matsawa Papa yayi kusa da ita yace "Maminmu Abunda kike So kenan fa kuma tayi Alƙwarin
chanzawa ,why don't we give her a chance . "

Dan kallansa tayi yayi mata alamu da ido kan ta duba,mayar da kalllanta tayi kan Jamaimah
wadda hawaye ke bi ta ko ina a kuncinta,sassaita haɗe ranta tayi ta ɗuƙa tana mai kallanta cikin
rashin sakin fuska baki ɗaya,

Kamota tayi ta ɗagata tana mai kallanta cikin ido ,murmushi ta saki kana tayi hugging ɗinta
wanda yin haka ya saka Jamaimah sake fashewa da wani kukan cos ba abunda tayi tsammani
ba,

Shafa bayanta Mami ta fara tana dariya kana tace "mene 'na kukan kuma,"

Cikin kukan tace "nazata zaki koreni ne Mami ,kukan 'na murna ne".

Baki ɗaya suka suka dariya.

Kamota Mami tayi tace "Ya isa ,zauna ki goge hawayen nan bana san sa,"

Hannu tasa ta goge tace "'na goge Mami ,sunki su tsaya ne".

Murmushi Mami tayi tasa hannunta ta goge mata hawayen kana tace"ita rashin biyayya ba
ƙaramun rashin daɗi take haifa maka ba tsakaninka da mutane,musamman idan yau akace
macece bata da kunya da biyayya,"Tun da fari Jamaimah ban tsane ki ba kawai halayyar da
kika zo mana da itace ta bata mun rai fiye da maganar Aurenku 'na wauta,Amma Alhamdulillah
ai yana da kyau dama kayi ba dai dai ba kasan kayi,we have a big plan for you muna jirane
dama ki san menene zakiyi ma Aurenki Kafun mu mu saka baki,sai gashi Alhamdulillah kin
nemo hanyar gyaraawa,insha Allahu kuma zamu taimaka miki wajen yin haka .

Zama Papa yayi daga gefen Mami yana mai faɗaɗa murmushinsa yace "haka maganar Mami
take,ki saka a ranki a kasar nan mu iyayankii ne ba iyayen mijinki ba,sannan insha Zamu je
gurin iyayenki zamu gyara komai".

Batare da jin kunyarsu ba Jamaimah tace "Papa bazasu rabani da Nameer ba?

Wallahi da gaske Nake 'na bar halayyataa ta da,"

Babu Abunda Nameer yake sai blushing,kallansa Mami tayi tace"yana ta faman blushing,wane
ya faɗa maki ana nuna wa namiji wannann son 'na i cant do without you"?

Gyaran murya Papa yayi yace "well wasn't expecting This from you,kinga Nan Jamaimah ki
nuna ma mijinki He's your everything cos kullum sai ta faɗa mun she cant do without me a
thousand times without numbers So kar ma Ki fara biyeta ne. "

Dariya suka saka baki ɗayansu yayin da Jamaimah ta duƙar da kanta suddenly tana mai jin
kunyarsu.

Abincin da ta kawo musu wanda tayi da taimakon hafsa wadda taje gida Aunty shatuh tayi
musu introducing ,daɗi sosai Jamaimah ke ji ganin yarda suke nuna santin Abincin ,tabbas da
tasan haka normal family yake da tuni ta ƙwatar da wuya ta zauna sun nuna mata soyayya irin
wadda suke nuna mata a yau koda kuwa bata kai adadin ta yau ɗin ba.
Bayan sun gama ne Mami ta umarci Nameer da ya kaita gidan su Ummu da Gidan Daddy
Bulama ta gaidasu ,a nan ɗin ma ba karamar soyayya Jamaimah ta gani ba ,soyayyar familyn
mijin nata take ta mamaye dukkan wani sashe 'na zuciyarta domin sun karramata a rana guda
kawai.
Kallan Nameer wanda ke driving ɗinsu Dan komawa gida tayi ,murmushi tayi ta kama
hannunsa tace "baby 'na lura kana mutuƙar cikin farin ciki ,".

Shafa hannun nata yayi a hankali yana mai facing titi yace "'na tuna nace miki ki taimaka mun
na taimake ki,abunda nake nufi kenan,family na nasani basu da damuwa ,and dama 'na faɗa
miki kece Kaɗai zaki iya daidaita komai wanda you Just did and bazan boye miki ba hakan ba
ƙaramun gurbi ya sake buɗa miki ba a zuciyata,you earned more of My love ,My Queen,i love
you To the Moon And back and 'i cant wait To show you that tonight,its gonna be steamy,"

Maganar ya ƙarasa yan mai cije lebensa 'na ƙasa.

Dukan wasa ta kaimasa tace "get lost you naughty boy."

A tare suka saka dariya cike da nishaɗi,

Serious face ta saka tace"kana tunanin zuwa Dilah is a good idea?

Cos tsoro nake ji sosai wallahi."

Murmushi yayi yana mai rubbing hannunta yace "its a good idea hayatee domin kuwa Ya
kamata ace 'in laws ɗina sun san dani and only God knows 'in mutuƙaar san na gana da iyayen
da suka haifa mun wannan kyakyawar halittar nayi masu godiya domin babu abunda zanyi 'na
Biyasu,

Hannun nata ya kama yayi kissing wanda yayi dai dai da danna horn ɗin da yayi bakin gate
ɗinsu ".

Cikin lokacin ƙanƙani gateman Ya buɗe masa Ya danna kan motarsa ciki,har ya shiga gidan
tana kallansa,sai da yayi parking kana ya kalleta Ya ɗaga girarsa guda ɗaya yace"nasan ina da
kyau ki daina kallo na haka after all im all yours kiyi yarda kika ga dama dani."

Murmushi tayi tana mai tsintar kanta da yin blushing ,cikin fuskar tausayin kanta idan sunje
kamaru tace "ina tunanin yarda family na zasu ƙarbi Aure na da kai,Ina jin tsoro kar su rabani da
kai ,zasu soka kamar yarda family ɗinka suka so ni?"

Juyowa yayi yan facing ɗinta sosai yace"abu guda ɗaya na yarda dashi wanda shine ni dake
Allah yayi mu domin juna,ke kaddara tace nima ƙaddararki ne,it been ages tsakanina dake But
kin riƙe mun kankii da Aurena, and lastly we came together' a yanzu yarda nake jina mutuwa ce
kawai zata iya rabani dake ba mutum ba,so kima cirewa kanki damuwa ki ƙwantar da
hankaliki,and maganar familynki bazasu soni ba haba ke kam who will resist me?"

Habarta Ya kamo yace"kalleni fa"

Duka ta kaimasa tace get out you bragger.

A tare suka saka dariya a yayin da suka fito a motan Suka taka ciki a tare.

Falon tsaf hafsa ta gyara kafun ta fita cos har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login