Showing 66001 words to 69000 words out of 73196 words

Chapter 23 - AHALINA (Aure uke series)na chuchu.pdf

Advertisement

08 Jul 2025

2300

da dukkan rayuwata ,a wannan abun
daya faru na sake samun gamsuwa da kaina 'na cewa tabbas ina buƙatar ki kusa dani,Ina san
ki zamo mallakina matata,zan baki duk wani kulawa da ya kamata ace Namiji ya bawa matarsa
,sannan na gama yanke shawarar binki ƙasarki inda nasan nan hankaliki zaifi kwanciya,idan
kuma ba Nigeria ba ki zabi ko wacce ƙasa kike so zan biki mu gina rayuwa mai tsafta a tare
domin duk inda kike nan ne ƙasata"

Saurin goge hawayenta tayi kana tace"shi yasa ai ka ƙwana biyu baka kirani ba,"

Murmshi yayi mai kyau yace "aiki yasa ban kiraki ba shima kuma Babu yarda zanyi ne ,Ina
samun lokaci kuma da sauri na bibiyi schedule ɗinki na dawo Ghana gareki na ƙarba miki rauni
ya sarauniyata"

Tsintar kanta tayi da yin ƙasa da kanta cike da kunya saboda maganar da tayi domin kuwa tama
rasa abun faɗa ne duba da yarda kalaman sa suka sace mata zuciya,

Hannun sa yasa ya ɗago habarta yace "ai kuwa ki cire kunyar nan ki kalleni,cos bana san kunya
tsakani na dake,Babu kunya sai soyayya,"

Ɗankwace fuskarta tayi tace "da gaske kake zaka bini duk kasar da nake so,?idan kuma su
Dad basu amince ba fa?,

Ni ban so ne yau a wayi gari na zama silar rabaka da iyayenka ,nice mace kuma nice nake da
Alhakin binka duk wata ƙasa da kace nan kake so ,idan kana nan ni gidana a nan gurin yake"

Yasan Babu wata kyauta da zai bata da ya wuce aje ta a ƙasarta dan shi kan sa yana buƙatar
chanji na gurin zama,cikin ƙwantar mata da hankali yace"Nine zan zauna dake ba iyaye na ba
,sannan Aurena dake ba shine yake nufin na butulcewa maganarsu ba ko kuma na juya masu
baya dole da amincewarsu a ciki domin ni ke nake so kuma ke na zaba dan haka suma ke zasu
zaba,sannan nima Ina buƙatar chanza guri wanda ke nake so ki zaba.

Faɗaɗa murmushin ta tayi tace"Nigeria"

Tafa hannayensa guda biyu yan mai darawa ganin yarda ya sakata nishaɗi kana yace "deal and
done yanzu abu guda ɗaya ya rage wanda shine Aurenki dan Allah muyi Aure."

Kafun tayi magana aka turo ƙofar,turus Mom ɗinsa tayi bayanta ƙanwarsa Mercy sai Dad dinsa
wanda ya shigo yan mai faɗin Oge"

Saurin tashi Nadiya tayi tana mai zazzare idanunta kamar An Kaɗa jaba a buta,kame kame ta
fara kana tace "Good morning"

Takowa Mom ɗinsa tayi tana mai sakin fuskarta tace "yarinyata Good morning,kafun na kiraki
kunzo ashe,wannan soyayyar taku sai Allah"

Ƙasa tayi da kanta cos She's appeared To be desperate wanda bazata ƙaryata ba She's
desperate ɗin ,dafa kafadarta Mercy tayi tace "A fili ma kinfi kyau akan hoto,gaskiya yayana ya
iya zabe,"

Murmushi kawai Nadiya take bangare guda kuma tana satar kallan Dad ɗin Ahmed wanda ya
zauna kusa dashi yana mai tambayarsa 'ya jikinsa,

Ɗaukar jakarta ta tayi tana mai faɗin"bari na wuce mom"

Kamo hannunta tayi tace"im sure baki karya ba dan haka ki zauna kuyi beakfast ke da Evans,"

Rasa ƙaryar da zata gilla tayi dan haka cikin saurin Ɗaukar yanayin tace"ai Ina azumi ne"

Sanin nauyi ne ya saka bazata zauna ɗinba yasa Mom cewa ,"its Okay ki dawo da rana ki kula

dashi cos nida Dad din sa zamu fita and Mercy Nada rehearsal na rawa,and make sure kin
masa abinci mai daɗi ya koshi,Ina san naga idan kunyi Aure zaki kula dashi .

Cike da zumuɗi ta mata godiya inda gogan yake ta kallanta kamar zai cinyeta da ido,ta masu
sallama tana ƙokarin fita muryar Dad ta katseta inda yake faɗin"ki kira mutanenki zamu zo muyi
maganar Aurenku,

Kamar a mafarki haka taji zancen nasa,cike da murnar da ta kasa boyewa ta fara masa godiya
domin ta fahimci ya amince da ita ,sannan a wannan gejin tasan Allah ne kawai zai hanata da
Ahmed mallakar juna a matsayin mata da miji.



***********

A bangaren Hafsa da Abdallah kuwa soyayyace suka tsakanin junansu mai tsafta da
aminci,tunda ta koma gidan Aunty shatuh shima ya ɗaura ɗamara domin bama ya kunya ko
tsoran wani yasa suna san juna tunda ba haramci suke Aikatawa ba domin kuwa ya gama
gamsar da kansa akan muddin idan ba Ba wata kadaraba Allah ya tsara masu daba To shifa
yayi mata.

Kamar kullum a yarda yake zuwa gidan Aunty shatuh yauma haka yazo,taba hira yayi da Antin
nasa amma bai ga Hafsa ba,kasa jurewa yayi yace "Aunty wai nikam ina hafsa ta shiga cikin
daren nan?"

Murmushi tayi tace"Nazata ai bazaka tambaya ba ,To taje gidan Innarta zata kwana biyu,"Dan
turus yayi sannan yace"amma jiya ma munyi waya da safe amma bata faɗaa mun ba,"

Yar dariya Aunty shatuh tasa tace"Abdallah na kenan,To ai yanzu bata ƙarkashinka tukunna ,"

Sinarr da kai yayi yace"Aunty ba wai haka nake nufi ba fa,"Dariya tasa tace "nasani ai
nima,yanzu dai ba sai ka tsaya tambayata mai ya faru ba ga nan address ɗinta zan baka sai
kaje.

Murmushi yayi yace "nasan gidan ai ,kin tuna na taba kaita,tsokanarsa ta fara ,Babu bata lokaci
ya tashi 'ya gudu"

Koda yaje gidan ya jima yana kiran layinta bai sameta ba,yana wannan ƙokarin ya hango
muhammadu ya aikasa 'ya kira masa ita,

Koda muhammadu 'ya sanar mata charaf inna tace kaje kace 'ya shigo tunda bazata fito fili ta
faɗamun ba ko ta haɗani dashi,

Kafun tace wani abu muhammadu 'ya koma yi masa iso,da gudu ta faɗa ɗakinta domin
kimtsawa,bayan lokaci kalilan kuwa sai ga Abdallah nan bisa jagorancin Muhammadu,

Cike da maraba inna tayi masa iso zuwa matsakaicin falonta ,da fara'arta ta amshesa tana mai
yi masa maraba maraba kana ta ƙara da cewa "Hafsatu ba zai fito haka nan ba sai kin bata
masa lokaci"

Murmushi shi dai kawai yake kan 'ya samu gurin a kan carpet ɗin da aka shimfiɗa masa 'ya
zauna dan Falon Babu kujeru,

Cikin mutunci da girmamawa ya gaida Inna wadda ta amasashi cikin nata karamcin tana mai
kiran muhammadu da yazo 'ya siyo masa ruwa mai sanyi"

Bayan fitar Inna ta fito cikin nutsuwa bakinta ɗauke da sallama,kallanta yayi cike da
kauna,zama tayi chan gefe dashi tana mai faɗin "barka da zuwa,Ina wuni,"

Shiru yayi bai amasata ba har saida ta kuma gaidashi cike da kunyar kallan da yake mata,shafa
sajensa yayi yace"Amma dai kinsan ko nan da nan idan ki kayi ina shiga damuwa ko?"

Dan sunnar da kai tayi cikin rashin san haɗa ido dashi tace"gidan Inna ne kawai nazo fa and
lastly ba gashi nan kazo ba,cos duk nan da nan ɗin da zanyi na tabbata bazai wuce saninka
ba,"

Murmushi yayi mai kyau kan 'yace"kinyi magana domin kuwa duk inda kikaje ina nan tare dake
cos zuciyata 'na faɗa mun,

Ruwa Muhammad 'ya basa 'ya fita,ɗaukan ruwa yayi tare da yin bismillah ,ajewa yayi ya kalleta
yace"Hafsa inasan 'na tura magabatana gurin magabantanki domin ina san na mallakeki
matsayin matata,kila zakice ina rushing amma ni a tunanina idan kin amince dani kin gamsu da
nutsuwata da kuma kwaɗaitar kasancewa dani Babu Abunda ya rage wanda ya wuce mu
kasance ma'aurata mu cika sunnah ta ma'aiki salllahu Allaihi wasallam,beside ma'aurata da
yawa sai bayan Aurene suke nutsuwa su ƙara sanin Abokin rayuwarsu ta fanni daban daban
saboda Auratayyaar da ta haɗasu wadda muke fatan ɗaya ya binne ɗaya,so please hayatee ki
bani wannan damar da zan kasance mai kare maki duk wani hakinki 'na rayuwa ,

Kallansa tayi a karo 'na farko idanunta cikin nasa tace "Ina sanka sosai ,amma bazan iya
boye maka ba,ni marainicaye ta fanin Uwa sannan ukubar kishiya uwa ya dawo dani gurin
innata,mu talakawa ne sai dai mun godewa Allah,ina jin tsoran ta yarda zzan farawa mahaifina
maganarka domin kuwa ta ko ina ni ba tsararka bace,amma tabbas nima Ina kwaɗaayin zama
matarka,"

Ya jima yana nazarin ta kafun yace "shikenan damuwarki?"

Daga masa kai tayi,murmushi yayi kana yace"dani dake Babu wanda yafi kowa ta hanyar
halitta,dukkanmu da abu ɗaya aka yimu sannan ta hanya ɗaya mukazo duniya kuma ta ita
zamu koma dan haka zanyi fushi sosai idan kika kuma jona status a dangantaka ta dake"

Kafun 'ya ɗora da wani Abu Inna dake make bakin kofa tana sauraransu ta ziro kai cikin falan
tana mai faɗin"ka bar 'yar kaniya Abdullahi ni nabaka izini ka turo magabatanka yau ɗin nan zan
kira mahaifinta muyi magana".

Dan turo baki Hafsa tayi tace kai Inna wai dama kina 'nan kina jin mu,

"Eh mana dole 'na zauna dan tabbatar da hannun wa kika faɗa"

Shi dai Abdallah Babu abunda yake sai godia inda daga bisani yayi masu sallama bayan
ihsanin daya sha tataburza da Inna kafun ta karba,daɗi kamar yayi mene dan 'ya ƙosa yaje 'ya
kaima iyayensa labarin nan mai daɗin saurare.

Bayan fitarsa haka Inna taketa zolayarta da haka har ta sake Akan hanata zuwa garinsu da
mahaifinta yayi akan shi zaizo cos har yanzu gidan babu daɗi tunda ta tafi.







IFTAAR MUBARAK HABIBATIES

AHALINA yazo gangar .



CHUCHUJAY ✍️
[3/19, 11:53 AM] Chuchujay✍️: AHALINA

(Siblings of different fathers )

Book two 'in Aure uku series

By

CHUCHUJAY

EPISODE 5⃣9⃣◽6⃣0⃣

Bayan jaddada bincike mai yawa iyayen 'na bagare huɗu suka zauna suka tattauna

Aka tsayar da magana ta Aure tsakanin Ahmed da Nadiya,Abdallah da Hafsa,

Tsaye Nameer yake bakin mirror ɗin dakinsa yana mai sake duba kansa ,

A hankali Jamaimah ta shigo ɗakin hannunta boye a bayanta,

Jingina tayi da bakin kofa tace"honey wannan kyau ɗin da kayi gaskiya ban yarda ba cos ko
ranar Aure na dakai ƙananun kayane jikin ka,im hating the method amma bana dana sanin
Result ɗin,"

Murmushi yayi 'ya ɗauko hular tangaran ɗin dake kan mudubi 'ya tako gareta,hannu 'ya miƙa
mata ,Babu musu ta kama ,juyata yayi ,dariya tasa kana yace "Kar ki damu abar kaunata kar ki
damu kullum zanna miki shiga irin wadda kikeso , yanzu dai ki ƙarasa shiryani naje Na karba
ma ƙannaki Aure domin idan na cigaba da tsayuwa a cikin gidannan cikin ɗakin nan tare dake
To komai nawa zai iya tsayawa na cire wannan farar shaddar nayi making love gareki ta ko
wanne fanni,kashe idansa guda ɗaya yayi yace"kinsan dai yarda nake a gado dan ni ɗin baban
Dan kwallo ne Dan a yanzu haka na tabbata Na jefa kwallo a raga. "

Taune lips ɗinta Na ƙasa tayi kan ta karbi hular hannunsa ta ɗora akansa kana ta fesa masa
turaren da ta shigo dashi kafun ta kama sajensa tace"ni kuma kasan bana wasa wajen chabe
kwallo ,domin a yanzu haka yazo ina da yaƙinin ƙwallanka tayi saiti".

Rufe bakinsa yayi cike da murna yace"you're pregnant?dont tell me this "

Faɗaɗa farin cikinta tayi tace"im telling you This habiby im one month pregnant "

Cike da mirna ya ɗagata sama yana mai fadin"ALHAMDULILLAH 'ya rabbi,kissing fuskarta 'ya
fara ta ko ina 'yana mai saka mata albarka,"

Dan janye jikinta tayi tana mai sake gyara masa jikinsa tana cewa"ni dai yanzu kazo ka tafi
ɗaurin Auren nan murnar kuma ka bari sai ka dawo kayi iya yinka ,da kyar 'ya hakura ya fita dan
da ace ba ɗaurin Auren Abdallah da Nadiya akeyi ba da Babu abunda zai saka 'ya fita yabarta,"

Ɗaurin Auren Nadiya Bilal da Adam Hans aka fara da karfe takwas Na safe kana aka ɗaura 'na
Abdallah Hafiz da amaryarsa Hafsat Balarabe wanda aka ɗaura gidan mahaifinta,

Tun a yanayin mutanen da suka zo amsar Auren Hafsa Mama laure ta sare,kai ba ma ita ba,
Babu wanda a garin baiyyin yamaɗiɗi da maganar ba mussamman da yakasance Mahaifin
Hafsa 'ya nemi da Hafsa ta cigaba da zamanta gidan Innarta shi da kansa zaizo ayi duk wani
Abu da za'ayi dan da fari ma a Adamawa yaso a ɗaura Auren Amma Daddy Bulamaa yace kar

ya damu Zuwa Adamawa bazai taba zuma musu abu mai wahala ba after All hakkinta ne aje
har gidan mahaifinta a amsa Auren ta,

Bayan ɗaurin Aure wanda ya tara jama'ar yankin garin da sukazo shaida wannan ɗaurin Aure
,Malam Balarabe mahaifin Hafsa 'ya shiga gida gurin yan uwansa da suka hallarci bikin da ba
amarya domin sake gaisawa dasu,wata Innar Mama laure ce da tazo daga cikin garin katsina ta
saka akayi mata magana dashi,
Cike da girmamawa yazo ya duka yace "inna usai gani,"

Ciike da kunmfar baki tace "ai Balarabe ba sai kayi mun mur mur da ido na munafukai ba naji
komai,idan ba lalacewa ba ta yaya za'ace Hafsatu na Aure babu ita garin da ubanta yake,bana
tunanin ko binciken kirki kayi akan ɗan nan saboda ƙwalama da ka saka a gaba tunda ance
Malamine ɗiya masu kuɗi,To bari kaji ko gwamna Hafsatu Ta Aura Laure ce domin kuwa da
bata raineta ba lokacin da uwarta ta mutu ta barta da ba'a Kai nan ba dan kilan ma da tabi
uwarta,To ina san kasan Abu ɗaya da bazar Laure Hafsatu ke taka rawa. "

Da mamaki Malam balarabe 'ya kalli Inna kana yace "amma hala inna kin manta da dukkan
ukubar da Laure tayiwa hafsa hala,duk wani cin kashi da azabtar da ita da tayi duk baki gani ba
kin manta,To bari kiji na faɗa miki wani abu,duk abunda hafsa ta zama a rayuwa ƙaddarar tace
ba tsarin Laure ba domin kuwa da ace Ta Laure ce da yarda taso da tuni Hafsa ta zama
ƙaramar bazawara domin kowa yasan wanda tayi niyar Aurawa matsiyacine wanda baisan
darajar mutum ba,zaman Ta a chan Adamawa kuwa Nine na saka domin Babu wanda yake da
iko mun da ɗiya,idan kuma kuna san ganinta ne sai ku bari idan sunzo bankwana ita da mijinta
sai kuyi domin da Allah ya tashi ɗagata bayan wata biyu a Nigeria zasu wuce ƙasa mai tsarki
danyin rayuwarsu,idan kuma da mai saƙon da zai faɗa mata cikinku to 'ya bayar danni uban
ɗiya zani Adamawa.

Tashi yayi dan barin gurin muryar Laure ta katse sa ta hanyar faɗin"kazata bamu san ubansa
Dan fashi Bane,uwarsa kuma mai biye biye ce Dan da ta fara irga Aure sai da tayi goma,idan
da ƙwadayi ai da wahala."

Murmushi Yayi yace"nine da godiya Laure sannan waɗannan da kike lissafi haka akansu su 'na
zaba 'na bawa ɗiyata kiyi abunda zakiyi ita yarki da kike san Aurawa Dan mai gari gashi ai 'ya
mata ciki 'ya gudu ya barta "

Bai jira cewarta ba ya bar gurin Dan Tafiya Adamawa,banbami da sumbatu Mama Laure ta
ɗingayi tana zagin malam Balarabe wanda ko ta kanta baibi b inda 'yan uwanta suka dinga
tayata suna tsinewa Balarabe da yarsa .

Jirgi Papa yayi ma Mahaifin Hafsa zuwa Adamawa wanda babu wani bata lokaci ya sauka
a Adamawa wanda driver yana nan yana jiransa,inda 'ya nemi su kaisa nan suka ajesa wato
gida Inna,koda aka ajesa Yayi mamakin ganin yan uwa na kusa da nesaa da suka masa kara

,tabbas ya yarda Laure ce Babbar mutum wadda ta ja katangar karfe tsakaanisa da yan uwansa
,chan ya haɗu da amaryar ɗiyarsa wadda dukkan wani nauyin gyarata Aunty shatuh ta dauka
'dan sai ana gobe daurin Auren ma ta koma gidan Innarta,karamci iya karamci Aunty shatuh ta
nuna masu domin komai na hafsa ita ta daukesa ,
Dukkan wani kuɗi da ta samu tsakanin Innarta da mahaifinta ta raba su wanda da kyar suka
karba, musamman ma inna da aka dauke mata karatun Muhammadu har ya gama,

Da rana dangin Abdallah sukazo 'dan tafiya da ita family house ɗinsu wanda nan zata fara
zama kafun su wuce ita da mijinta,nasiha sosai mahaifinta yayi mata mai ratsa jiki,kuka sosai
take yi haka zalika shima mahaifin nata wanda ya kasa riƙe hawayen da ke neman kwace
masa,tabbas Aure yana kai mace ko ina amma baiyyi tunanin zai ɗauke hafsa da ƙasarta ta
haihuwa ba.

***

Ya maganar gidansu Amaryaa Nadiya kumafa?

Tun a wajen gidan Dr Imam da Dr Umaimah zaka san ana bikin kuɗi a gida ,shige da fice shine
abu n'a farko da zai faɗa maka Hakan ,yan uwa na kusa da nesa duk sunzo ciki kuwa harda su
Fawza,Fawzan,Fawha wadanda suka baro karatunsu domin zuwa taya yan uwansu murna
domin abun murna ne a yi masu yasan mutum biyu a gida ,
Bikine akayi gangariya n'a gani na faɗa wanda ya yaɗa kasa da ketarenta baki ɗaya,mahaifin
Nadiya yazo amma cikin bakin daurin Aure wanda babu wanda ya nuna masa wani abu face
karamci wanda babu daɗewa ya bar gurin domin zaren ba kalar yadin Bane domin kuwa yasani
ya rasa Nadiya da mahmud har abada,
Gagarumun liyafar da aka haɗa wa amaren da angwayen an haɗa tane cikin gidan Dr Imam
wanda aka haɗe da baby shower Na Jamaimah wadda bata samu wani liyafa ba na Aure 'dan
haka itama aka tsantsarata cikin shiya irin ta amaren hakazalika Nameer wanda shima ya haɗe
cikin shiga irinta Angwayen ,bada labari na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login