Showing 42001 words to 45000 words out of 73196 words

Chapter 15 - AHALINA (Aure uke series)na chuchu.pdf

Advertisement

08 Jul 2025

2298

'dan haka cike da
mamaki tace "mene kace?"
Licking lips ɗinsa na ƙasa yayi yace "cewa nayi so nake ki bani dama na baki haƙuri akan
abunda na faɗa maki mara daɗi,ranar raina ne a bace amma ba halina bane batawa wani,'dan
Allah kiyi hakuri ki yafe wa Abdallah ko zaiji daɗi.
    Da inda inda tace "ni ba'abunda kamun ,n yafe maka sannan kayi hakuri manjan da na watsa
maka cikin rashin sani ne wallahi bada gangan ba."
    Accent ɗinta na magana ba ƙaramun burgesa yake ba,
Taba madaidaicin sajen Fuskarsa yayi yace "na yafe miki Hafsat and ni Ai a daɗi na ne na aje
mistake ɗin Auntyn Arif da yaketa ƙodawa,kinga idan ina kallan rigar nan zan na tuna Auntynsa
tayi mistake sau daya"

    "Babu wanda baya mistake Ai a rayuwa,daukan mu yan adam ne ajizai"
Ta faɗa tana Mai zuba ganyen ogu cikin abincin a zuciyarta kuma tana Allah Allah yatashi Ya
fita domin burgeta da yake kafin Ya zageta dawomata yake kamar an koro ruwa,
Wayarsa ya ciro ya miƙa mata,kallansa tayi alamun mene zatayi dashi,
Gira ɗaya ya ɗaga mata yace "ki ƙarba mana ki saka mun numbernki saboda muna gaisawa
akai akai kinsan zumunci nada amfani sannan na ganki naji ina san kulla zumuci dake."
Murmushi ta tsinci kanta dayi kana ta ƙarbi wayan ta rubuta masa numbernta ta mika masa tace
gashi.
Kina da saurayi?
Shine tambayar da yayi mata cikin rashin zato da tsammani.
Kaɗa kai tayi cike da kunya cos bata taba tunanin tambaya makamanciyar wannan zata shiga
tsakaninsu ba.
    Sai me za'ayi idan bata da saurayi Abdullahi,
A tare suka kalli kofar inda ya furta Adda Nadiya?
Cikin salo na tambaya,
    Takowa ciki tayi tana mai boye dariyarta tace "ina sauraranka ,dama nan ka zo kenan ana ta
neman layinka baya tafiya ,Grandpa Bulama ya kira meeting".
Kallan wayar tasa yayi yace "kuma wayata lafiya ƙalau fa saidai network".
Ganin hankalin Nadiya baya garesa yasa shi kallan Hafsa da ta ƙurawa ido,
Cikin yanayi na rashin sakewa hafsa tace "ina wuni"
    da fara'a Nadiya ta amsa tana mai faɗin"yayi confessing soyayyarsa ko ni nayi masa?"
Saukowa Abdallah yayi daga kan cabinet ɗin ya kamo hannun Nadiya yace"Adda muje ya
maganar zuwa Gidan Bulaman. "
    Hafsa na jiyo dariyarsu ,haka nan ta tsinci kanta cikin wani yanayi da bazata iya fassarawa
ba,sauke tukunyar abincinta da ya nuna tayi tana mai sake jadadawa kanta wasa ne sukeyi
nasu amma babu yarda za'ayi Abdallah yaso yarinya kamar ta.
A cikin ƙaton kula ta juye abincin ta fita dashi ta aje kan dining,babu kowa a falon amma tana
jiyo muryarsu daga falon Sama.
    Komawa tayi kitchen ɗin ta ɗauko cocktail ɗin da Aunty shatuh ta haɗa jiya,ta dawo ta aje tayi
arranging table ɗin kana ta koma kitchen ɗin ta gyara ta zuba nata abincin cikin yar ƙaramar
roba dan kaima muhammadu,
Shirinta tagama fes kafun ta haura kamar barauniya ta sanar dasu abinci ya sauka,
Kamar kuwa tana jira suna amsawa ta sauko ta koma ɗakinta dake ƙasan..

********************************************
    Kamar yarda Ahaji Bulama ya kira taron gaggawa lokacin da labarin Nameer ya iskesa haka
suka bayyana domin amsa gagarumin kiran nasa,
Nameer ne na ƙarshen zuwa wanda baiyyi gigin zuwa da Jamaimah ba dan yasan mai zai
jawowa kansa,
Dan idan batayi wasa ba babu shiri zata koma kamaru dan kakansa mutum ne mara daukar
shashanci,
Kowa ya hallaci zaman wanda abun ya shafa ,
Koda Nameer ya gaida kowa Mami ƙin amsashi tayi dan ko da ta koresa yaci a ce a waya ya

kirata ya sake bata hakuri koda bazata saurara ba Amma shiru kamar dama jira yake ta koresa.
Bayan addua na buɗe zaman kamar koda yaushe idan sunyi Grandpa ya fara magana kamar
haka"Nameer shin maganar da naji daga bakin Maminka haka take ko kuwa zakayi mana karin
bayani."
    Kasa yayi da kansa cike da girmamawa yace "kuyi haƙuri grandpa ,kuskure ne na riga da
nayisa wanda ban taba tsammanin zai dawo min ba a wannan lokacin da bamu daɗe da fita
daga wata matsala ba,"
Amma dan Allah Amun hakuri bayanshi Babu abinda zan faɗa im guilty.
    Shiru ɗakin yayi babu wanda yace komai kafun Grandpa ya katse shirun Yace"idan nace
baka bamu kunya ba NAMEER na yaudareki domin ka bamu kunya mutuƙa,domin kayi wasa da
irin ilimin addinin da muka baka har kake tunanin wai bakayi tsammanin kuskuren zai dawo
maka ba,"Haba Nameer Aure fa Kayi dungurugum,mai kake Tunanin duniya zata faɗa akamu
bayan kasan mu ɗin abun magana ne a duniya haba Nameer ,ka bani kunya mutuka.
    Yaya Abubakar dake gefe ne yace "bai kyauta ba dan rashin kyautawa daddy amma dan
Allah ayi masa hakuri sai afara tunanin ta hanyar da za'a gyara."
    Wanne gyara kuma baya ya b'ata,Allah yasa bai santa ba tun tana waje ,dan wallahi ni ba
laifinsa na ke gani ba na umaimah ne wannan laifin ,
Hajiya matar Alhji Bulama wadda tsanar umaimah da Ahalinta har a lokacin tana ranta ta fada
tana mai ya mutsa baki.
    Ayi hakuri Hajiya""Mami ta fada ranta a mutukar bace,
Nadiya dake jin haushin Hajiya sosai ce tace,idan bazaki gyara ba hajiya ba sai kin hura wutar
ba,mene na maganar saninta a waje kuma.
    Kamar hajiya Zata cinyeta ta hayyayƙo tace "naci ubanki wallahi sosai babu ƙaƙƙautawa ,ke
idan ana magana ma zakiyi,nan ɗan zinar ubanki ma saida ya dawo maku amma kike nan zaki
mun rashin kunya."
Cikin zaƙala Nadiya tace "dan ma dai kowa na da kashi a maƙale ."
Tsawar da Mami da Grandpa suka daka lokaci guda ne ya saka Nadiya hadiye abunda tayi
niyar yi,
Cike da fushi mami tace "maza bata hakuri,ni zaki wulaƙanta kicima mahaifiyata mutunci har
kina neman fada mata magana,to bari kiji wannan da kike gani zaune duk da ba ita tayi nakuda
ta ba ni kallan uwa nake mata".
Dunƙule hannu Nadiya tayi tana mai tuno abubuwan da tayi masu suna yara ita da yaranta da
matansu da jikokinta banda yaran uncle Abubakar dashi,tana sane sarai ta kasa manta wannan
bangaren a yarintata,
    Kiyi hakuri sannan nima ai bada rashin kunya nake mata magana ba ina maganane ta jika da
kaka ,ai kakatace.
Cike da balai hajiya tace"ni ba kakar ki bace,kakar ki na chan kasa ni su sultana ne jikokina
domin iskanci da ɗiban albarkar da kike mun su basu mun saboda sun san muhimmancina sun
kuma san nice na haifi ubansu"
Dakatar da ita da Grandpa yayi ne ya saka Nadiya kin bata amsar da ta dace da ita ,
  Kan Nameer ya koma yace"gareka Nameer yanzu dai maganar rabuwa da matarka bai taso
ba tunda nasan tunda kukayi wanchan shakiyancin nasan da soyayya tsakaninku koda kuwa
babu ita dole kacikaga ba da zama da ita,sannan naji ance yar kamaru ce sannann diyar sarki

Rais ce dake dilah ,zamuje chan ayi maslaha tunda ko ina a cikin addini ita din matarkace kuma
Aurenku ingantacce ne,hanyar da kukabice mara daɗi,dan haka kaje gida ku shirya."
    Ƙasa Nameer ya kuma yi da kai yace "daddy ayi mun alfama dan Allah,da gaske ina san
Jamaimah amma halayyarta ce bana so wanda a yanzu ina kan hanyar ganin ta gyara tukunna
sai muje chan gurin iyayane nata,a yanzu kam duk wata halayya ta rashin girmama na gaba ta
iya,so nake koda za'a je chan ɗin ya zamana ta koma a mace ta daban,wanda a wanann
lokacinne Mami tace zata amsheta amma banda yanzu"
    Grandpa zai nuna rashin lamuncewar sa papa ya shigar masa ya tayasa roƙo.
A haka aka yanke shawarar kamar yarda Nameer yaso,
Bayan tashinsu kai tsaye mami ta shige motarta dan bata san sauraran Nameer wanda ke da
zuci zucin mata magana,
Nameer na ƙokarin shiga motarss muryar Ibrahim yaran Yaya usman yayan mami ya katsesa
inda yake fadi"haji Nameer rayuwa,kai wai mene damuwarka daga mai mai cikin shege sai
kuma Auren boye,"Wani
Banzan kallo Nameer ya basa domin dama tsakaninsa da Ib babu jituwa tun yarinta,
Motarsa ya bude ya fada ,yana kokarin mata key sultan ya shigo ɗayan seat ɗin yace "ɗan
uwana muje mana ka aje ni a saint plaza wallahi motana ya lalace,"
wani kallan banza Nameer ya basa yace"idan na kaika wane zai daukoka?"
Sannan duk motocin gidanan baka da wadda zaka dauka ,ko zakace mun dukka motocinka uku
ne suka lalace?
Murmushi sultan yayi yana mai shafa lafiyyane sajensa yace "nayi missing dinka ne kawai,kaga
muje tare nasiya turare sai mu tab'a hirar yaushe gamo sai ka dawo dani gida,"
    Dariya Nameer yasa dan ya kasa rike ta kana yaja motar yana mai fadi kaji haushi .
Yana jin muryar Ibi basu yayi gaba.
    Murmushi Nadiya dake kallan duk abunda ya faru tayi ta taka inda yake tana mai kaɗa car
key ɗinta tace "adai nemi sana'a."
Cike da balai yace"ki dai ji da kanki da abunda ke damunki ,shegiya figagiya,kina nan kina
faman buɗe jiki da sunan sana'a mene amfanin taki sana'ar ba har gwanda kazauna babu
ba,shegiya yar isa".
    Dariya sultana dake bayansa ta saka tana mai fadin "Nadiya akwai vacancy ne a company
dinki ,Laila matar Hamma ibi na san modeling"
A fasace ibrahim ya juya wanda tana ganinsa ta juya da gudu tana ƙwalawa hajiya kira.
Kaɗa kai Nadiya tayi a fili tace "bazaka taba chanzawa ba Ibi".
Da haka ta tashi motarta tana tunanin zuwa gidan Aunty shatuh domin magana akan Hafsa kan
saban plan ɗinsu dan gane da jamaimah,
Message din Evans da ya shigo mata ne ya katse ta daga tukin da take wanda yake cewa
"Gani a Nigeria da mommy na akan maganar Aurenmu. "

Chuchujay ✍

https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK
[3/6, 5:19 PM] Chuchujay✍️: https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK
AHALINA

(Siblings of different fathers)

Book 2 in Aure uki series

         By chuchujay

Episode 3⃣9⃣➡4⃣0⃣

   Bayan isar Nameer ya aje Sultan a gida kai tsaye gida ya nufa dan ya gaji so yake kawai ya
huta dan haka ya barwa Fadil meeting ɗin da zasuyi yaje a maimakon sa,

Key yasa ya buɗe gidan ya shiga , a falo ya tarar da Jamaimah tana cin fried rice &chicken da
coke a gefenta tana wani yumm  kamar an bata duniya,sallama yayi bata amsa ba dan haka ya
wuce 

Ganin ya wuce ta ɗinne ya sakata ɗan daga murya tace "tunda ance idan na fita Allah ya isa
kaga ai mai kuɗi da kuɗinsa sai abunda yayi niyyah idan kuma yin order tazo har gida itama
haramun ne sai a faɗa mun naji ya sheik".

Tsintar kansa yayi da murmusawa ,yasani dama za'azo nan da zata fara online order shiyasa
koda Nadiya ta faɗa masa plan ɗinta ya amince babu bata lokaci,

Yana ƙokarin kulle ƙofarsa ta sako ƙafa a bakin kofar,matsawa yayi da ya fahimci jidali take ji
dashi.

    Shiigowa tayI ciki tace "malam magana nake maka tun jiya amma ka kasa bani amsa,"mene
ya saka Nadiya tazo tayi abunda tayi mun jiya,"

Walk in closet ɗinsa ya faɗa yana ignoring ɗinta,

Binsa tayi tana cewa "wai Nameer nikam mai ka ɗauki Aure ne ?"

Why are you treating me this way for crying out loud .

ba tare da ya juyoba ya fara cire rigarsa yace yarda kika ɗauki Aure haka na Ɗaukesa
jamaimah,sannan duk yarda kika shirya tafiyar da rayuwar Auren mu haka zan tafiyar dake na
tayaki ta yarda kike so,

Takawa tayi garesa a hankali ta saka hannunta tayi hugging ɗinsa ta baya,baki ɗaya yaji wani
tunani nasa ya tsaya,

Lafar da kanta tayi a bayan nasa tace"Baby dan Allah mu daina azabtar da rayuwarmu, lets live

a peaceful life style ,im hurting bana jin daɗin abunda ke faruwa tsakani na da kai,har  wani na
shiga,sannan Bazan boye maka ba banji dadin abunda Nadiya tazo tayi mun ba wanda na
tabbata da sanenka domin idan babu ba yarda za'ayi tazo tayi girki a cikin gidana domin kai
sannan wai tace ta aje mun ƙanzo da wuya,imagine babe,sannan har tana faɗa mun zakayi
Aure which idan kayi Aure zan iya rasa rayuwata saboda tunanin haɗaka da wata ƴa mace
kawai yana sani shiga tashin hankali,"

    Cikin shesheƙar kuka tace"is it a crime dan ban iya giriki ba?

Mata nawa ne basu iya girki ba kuma suke zaune cikin gidajensu da mazajensu cikin soyayya
da ƙauna,

Wallahi Nameer ina Mutuwar sanka ,ina maka sanda bana yiwa kaina shi why wont you give us
a chance?"

    A hankali yake jin kukan nata yana ratsa dukkan wani sashe na jikinsa,jikinsa da ta ƙwanta
kuma ji yake kamar ana hura masa wuta a dukkanin jikinsa,tabbas yana san jamaima shima ya
sani kuma ya yarda amma bazai iya dealing da yarda take tafiyar da rayuwarta cikin rashin
biyayya ba da sanin ya kamata ga ɗan adam,
A barshi ace ya amince da rashin iya girkinta ,zasu dawama ne a cin abinci a waje domin bama
ta da niyar koya ,ko kuwa zasu ƙare a yan aikine,

Shin yan aiki ne zasu na kula da ɗakinsa su gyara masa har abada?

A tunaninsa ɗakinsa sirrinsa ne wanda matarsa kawai ya hallartarwa,ko kuwa zasu zauna a
haka ne bata ganin mutunci da girman danginsa duk a sunan ita ɗiyar sarautace shin ita
sarautar hauka ce?

    Kukan nata bai daina sauti ba ,ajiyar zuciya yayi ya juyota tana kallansa ya kamo hannunta a
hankali ya zaunar da ita kan couch din dake cikin gurin ya ɗuka gabanta ,hannunsa yasa a
hankali yana mai share yar ƙwallar dake idanun ta yace"menene na kukan kuma?"

Duk fa abunnan bai kai ga nayin kuka ba,look jamaima i want a romantic simple life with my
wife,ni da kika kalleni a tsari na babu Auren mace biyu saboda babu yarda za'ayi na haɗa sansu
guri daya nayi adalci saboda nasan kaina,so i choose you duk da Aurenmu was nothing close to
okay amma a haka nake san ɗaukan responsibility ɗina na kula da dukka hakkinki da Allah ya
dora mun amma baki san bani dama domin kuwa a hadurwaki ta farko da iyayena kin basu
expression a kanki mara dadi wanda yayi leading da ni kaina aka koreni daga gida ke shaida
ce,

Im a family man jamaimah AHALINA suna gaba min da komai sannan a shirye nake na bata da
duk wani wanda zai kawo mun matsala cikinsu,

Ni dake ba soyayya mukayi a baya ba mun tsinci kanmu ne kawai a cikin san juna bayan
wannan abun na Aure ya faru.

    Cikin shagwaba ta katsesa tace "sai dai idan kai amma nikam i loved you since day one,idan
ba haka ba taya zan involving kaina a komai so don't speak for me".

    Murmushi yayi ganin yarda ta wani shagawabe fuska yace "to naji i wont speak for you,
amma ki sani ina sanki sosai amma kina san bani matsala wajen nuna miki ina sanki,so na kike
yi amma baki san ni wanene ba,AHALINA nada tarihi da history wanda bazaki taba tsammani
ba,na tabbata a maganar da nake baki san ina da kanne yan uku a America ba sanann baki san
cewa ni dasu da Nadiya da Abdallah dukkan mu Siblings ne daga different fathers amma same
mother,amma still we fight for each other and love each other ,i love them da dukkan rayuwata,

Sannan aje kan Mami na ,itace komai Nawa,ita ta bani uba a lokacin da nake mutukar bukatar
daya wanda shine Papa mijinta a yanzu,ya bamu rayuwa mai kyau sannan yabada babbar
gudunmawa wajen ganin mun zama abunda muka zama yanzu ,badan kuɗi ba saboda muna
dashi,dangin mahifiyarmu kuɗi ne haka zalika mahaifiyarmu kuɗice amma ya bamu
gudunmawar da kuɗi bazasu bamu ba,

Ko kinsan mahaifina dana Nadiya suna nan a raye?

Amma mene amfanin rayuwarsu garemu bayan munada wanda yafiso sau dubu wanda a koda
yaushe zai zabemu sau babu iyaka ya bamu gudunmawa rayuwa kamar yarda yake kan bamu,

Tayaya kike tunanin zan zauna na kalle ki kina disrespecting ɗinsu?

Abun da kikayi ranar was awful and very bad .

I can help you wejen ganin kin iya duk wani abu da baki iya ba amma fa sai kin taimakeni
tukkuna kin taimaki kanki zan iya taimaka miki ,muyi rayuwa mai kyau da inganci abun sha'awa
ga kowa.

    Narai narai haka idanunta ke kallan nasa kana ta sake damƙe hannunsa tace "da gaske nake
bazan iya rayuwa babu kai ba and tunanin wata mace tare da kai yana sani cikin mutuƙar tashin
hankali domin duk ranar da ka kawo wata cikin gidan nan matsayin matarka to zan mutu ne,mai
zai saka bazamuyi rayuwarmu daga ni sai kai,i left everything for you cant you do the same for
me?

Bazaka iya mun hakan ba please honey,i will try and adjust naga na fara yi maka girki koda ba
daɗi a haka har ya fara yin daɗi,rayuwata tunda aka haifeni bayan iyayena babu wanda nake
ma kallan sama cos ina kallansa matsayin ƙasƙanci a haka aka raine ni wanda bana tunanin
zan iya chanzawa zuwa wata daban,abu daya na sani shine ina mutuƙar maka soyayyar da zan

iya saudaukar da kaina domin kai amma bazan iya chanza kaina ba ,kazo muyi rayuwarmu mu
biyu please".

    Bai san lokacin da wata dariya ta ƙwace masa ba ,sai da yayi mai isarsa ya dago yaga tana
kallansa cike da confusion ,baki iya wa kowa kallan sama ba ,ni ma kenan bazaki taba iya mun
kallan sama dake ba right?

Snipping tayi tace "ni da kai ai abu guda ne"

Tashi tsaye yayi yana kaɗa kansa yace "yanzu na ƙara tabbatar da baki da ilimin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login