Showing 45001 words to 48000 words out of 73196 words

Chapter 16 - AHALINA (Aure uke series)na chuchu.pdf

Advertisement

08 Jul 2025

2286

addini isashe,"

Magana kuma dake muddin baki fahimci wadda namiki yanzu ba bata da amfani,

Rigarsa mara nauyi ya ɗauko da sweat pants ya kalleta yace "ki shirya zama da kishiya dan
bazan taba iya zama da jahilar mace ba Ita kaɗai ,sannan kuma ki sani kina nan matsayin
matata amma baki da wata power akaina domin bazan taba kusantar mace kamarki ba saboda
ina gudu da takaicin haɗa zuria da wadda bata san menene Biyayya ba."
Yana ƙai karshen zancensa ya fita yabarta nan zaune maganar tayi mugun dukanta musamman
maganarsa ta ƙarshe da kuma kiran ta jahila da yayi .

Wani irin ihu ta saka wanda yana bayi yana jinta ,rufe idanunsa yayi ruwan dumin na ratsa ko
ina na jikinsa ,a haka ya jiyo fitarta ta hanyar buga ƙofarsa da tayi tana kuka.


               ***************************

Kai tsaye Nadiya na ganin message ɗin Evans ta fara kiran layinsa wanda har ta katse bai
ɗauka ba,sai da ta kirasa a karo na biyu kana aka ɗauka wanda ta tsinkayi muryar mace tana
mai faɗin"come to SAMMY GUEST PALACE ,im Evans mom and i wanna see you right now ".

Da mamaki Nadiya ta cire wayan a kunneta kana ta sake mayarwa tace"is everything okay
Ma?"

Cikin yanayi wanda Nadiya bazata fassara ha tace"its not,room 2009 is the room number"

Dit taji an kashe wayar,

Wata zuciyar ke gargadinta da kar taje,har fara tafiyarta inda tayi niyyan zuwa kuma taga ƙin
amsa kiran nata kamar wulaƙanci ne da kuma rashin girmamawa gareta dan haka ta tura
Abdallah saƙo kamar haka"na tafi Sammy guest palace,incase kunji ban dawo gida ba har gobe
something is wrong,dont call me yanzun"

Yar dariya tayi da tayi realizing abunda ta yi,

Amma ai gaskiyarta ne cos tone din matar was not pleasing sannan bata santa ba bata kuma
san menene zata iya yimata ba,sanin ƙabilancinsu yasa haka,

Juya kan motarta ta tayi dan amsa kiran,mintuna marasa yawa ne suka kaita hotel din,ta jima a
parking lodge tana Sake sake kafun taf addua ta fito domin shiga ciki,ta dai san komene baza'a
kashe ta ba.

    Tsaye take bakin kofar tana mai danna door bell,

Sai da tayi sau uku kana akazo aka buɗe mata,da mamaki Evans yake kallanta jikinsa sanye da
rigar da buttons ɗinsu ke bude wanda ta bayyana shafaffan cikisa mai ɗauke da 6 packs,
hannunsa kuma ɗauke da towel yan goge jiƙaƙen kansa wanda hakan ya tabbatar mata da ya
fitone a wanka,
Cike da mamaki da kuma alamar tambaya yace "babe?"

Saurin ɗauke idanunta tayi ta juya masa baya tana mai fadin"im sorry and mene zaka  buɗe
kofa jikinka a buɗe?

Idan kuma bani bace bafa?

    Murmushi yayi inda yana ƙokarin magana mahaifiyarsa ta jawosa baya tana mai faɗin"i can
see someone is jealous,welcome"

Dam gabanta ya faɗi,da sauri ta juyo inda idanunta suka sauka kanta ,dattijuwace amma hakan
bai hana kyanta fitowa sosai ba sanann uwa uba haskenta wanda baya da alamar disashewa
,cike da dan duburburcewa Nadiya tace"Good afternoon ma".

Kallanta tayi da kyau kana tace "its evening come inside".

Riƙota Evans yayi yace "mommy please why do you call Nadiya here i thought we talked about
this?"

Cikin inyamiranci tace"bazan iya jira har sai ta bamu izini ba,na kosa naga wadda take da guts
ɗin da ya saka yarona yayi converting ba tare da kiftawar ido ba,"

Cikin rashin sanin abunda suke faɗi Nadiya tabi bayansu suka shiga ɗakin ,

Alamu mommyn tayima Nadiya akan ta zauna kan couch wamda babu musu ta zauna tana ɗari
ɗari yayinda cikin yare tace"kai kuma zaka rufe kirjinka ne ko sai ka gama hargitsa mata
tunanin?"

    Sosa kansa yayi kana ya fara balle maballansa,

Sake gaidata Nadiya tayi yayinda ita kuma take binta da ido kamar zata cinyeta,

Cikin harshen turanci tace mata "shekarar ki nawa".

Cike da girmamawa Nadiya tace"29"

Ɗan bude baki mommy tayi tace"bana san wasa 29?"

Ƙasa Nadiya tayi da kai tace yes ma"

Da mamaki ta sake kallanta kana tace zaki iya haihuwa kuwa?

Da sauri Evans yazo ya zauna kusa da ita yace mommy mana?

Wani irin kallo ta bashi kana tace"bana so fa ,kar ka shiga mun,bansan mene yanayi na
haihuwa hausawa ba amma ni nasan yarinya yar yarenmu idan takai 29 ana kwana biyu kan
tayi ciki shi yasa muke gwadawa tukkuna,inajin wannan ma sai mun gwada."

    Dariya Evans yasa yace mommy mu musulmai ne and sex kafun Aure haramune ,

Wani banzan kallo ta bashi tana mai faɗin kar ka fara mun maganar musulinci kafin kashiga kai
Christian ne and babu laifi idan zaka gwada ne kaga matar da zaka Aura zata iya haihuwa ne
ko kuwa bazata iya ba ba haramci a al'adarmu.

    Ɗan ƙaramun murmushi Nadiya tayi da ya zamana ba da yare suke maganar ba,cikin rashin
san tafaɗi maganar da bazata ma mommyn dadi ba tace"mahaifiyata ta sake Aure tana da
shekara 29 amma shekaran da ya zagayo ta haifi yan uku."

    Da mamaki mommy tace "yan uku?"

Washe baki tayi tace"kilan kema ki haifa wa Evans so ke virgin ce"?

Sake kama hannunta Evans yayi yace"mommy ki bari mana its embarrassing."

    Hannun nasa ta ture tace biko rabu dani,ina so na san wane yarona zai Aura,

Cike da kunya Nadiya tace"im a virgin mommy".

Kaɗa kai tayi tace ina zuwa,

Tana tashi Evans ya sauko a akan gadon da suke zaune yazo inda Nadiya take yace "Nady
baby im sorry about this please,mommy mean no harm".

    Ɗan yake tayi tace "ba damuwa Evans im good"

Zai sake magana sai ga mommy nan da tape dinta tace "oya tashi,"

Da mamaki dukkansu suka kalleta,takowa tayi ko ajikinta ta janye gyalen Nadiya wanda tazo
mata a bazata,

Evans zai magana tace"ka koma ka zauna kafun raina ya baci da kai,inayin komai ne dominka,"

Tape ɗin ta bude taje daidai kan Duwawun Nadiya ta saka tape ɗin tana mai fadin "zan Auna
girmansa ne naga zaki samu ciki da wuri sannan zakiyi qualities din da igbo girls suke
dashi,zaki iya ɗaukar bukatun Igbo man,".

Cike da rashin jin daɗi Evans yace "im Ghanian for God sake ba inyamiri ba".

    Dakuwa tayi masa da hannu tace "amma ai kasha nonon igbo woman bazakuma ka ƙaryarta
hakan ba"

Janye tape din tayi tana mai kallan measurement ɗIn kana ta saka hannu ta kamo duwawun
tace hope baki saka ciko ba,

Ɗan ja da baya Nadiya tayi a ranta tana mai mutuƙar rashin jin dadin wanann iskancin amma ta
danne tace "No mommy ban saka ba and boobs size ɗina 37 ba sai kin Auna ba i mean it".

Dan kallanta mommy tayi tace "i know you're not happy with me ,nasan baki jin dadin abunda
nake maki amma a matsayin uwa dole na damu musamman da ya zamana soyayyarki nada
farashi,har yanzu na kasa yarda SABODA ke Evans ya karbi musulinci,ina sone kawai nasan
kina masa san da yake maki"
    Da mamaki Nadiya ta kallesa domin ba faɗa mata ba ,kaɗa mata kai yayi wanda lokaci daya
taji hawaye na bi mata kuncita,saurin gogewa tayi ta kallesa cikin harshen hausa  tace "dan me
ka karbi shahada"

Sanin bata san mahaifiyasa ta fahimci mai suke fadi ne ya saka cikin hausan yace"domin na
yarda kuma na gamsu shine addini na gaskiya,sannan soyyarki ta sake bani kwarin gwiwa
wajen yin hakan."

    Faɗaɗa murmushi ta tayi tace "mene sunan ka,"

Licking lips dinsa yayi yace "ke na ajewa wannan gurbin".

Murmushi tayi sosai kana tace"AHMED"the praised sunnan Annabi Muhammad,first person to
present imperfect!

And na shirya Aurenka a ko yaushe ,indai ina numfashi babu wani ɗa namiji da zan mallakawa
soyayyata bayankai,wannan alkwarine daga musulmar da ta saka ka fara shawa'awar
musulunci har ka samu shiga.

    Gyaran murya Mommy tayi tace"meke faruwa dai?"

Baki ɗaya ma Nadiya ta manta da ita,

Goge hawayenta tayi ta rugume Mommy babu zato babu tsammani tace"mommy i love your
son with every fibre in me and i promise to treat him like a king and insha Allahu i will give him
beautiful kids insha Allah ."

Da gudu ta juya tabar ɗakin.

Kallan kofar tayi kana ta kalli Evans tace"kai mai kukace da wancan yaran and mai ya shigeta".

Daga kafaɗarsa yayi ya mara mata baya yana dariya.




School dey give me woto woto kuyi hakuri oo,weeks to exams,kuna ɗagan ƙafa na zama yar
jaridar nan already mu huta.

Xx

Chuchujay✍

TBC
[3/6, 5:19 PM] Chuchujay✍️: GARABASA GARABASA BONANZA
    2024 Shin kuna sane da ban bada garabasa ba?
To ku kwantar da hankalinku ga chuchu dai tazo maku da garabasar sabuwar shekara,
Shin kin fara kin fara karanta YAR AREWA labarin captain Jasmine Bilal shareef da captain
Shuraym Sadauki,
Ta tashi da mafarkin zama pilot a yayinda shi da yake kan aikin yake kusheta Akan tayaya ɗiya
mace Yar Arewa zata zama matuƙiyar jirgin sama?
Soyayyar da ta shiga tsakaninsu ba tsammani wadda take ƙokarin danne kiyayya .
Ko kuwa kin fara karanta littafin ABLA ADNAN ne labari na matashiyar budurwa wadda bata
barin taƙwana ,budurwar da tazamarwa masu kuɗin gaske barazana ,

Shin baki fara karantashi ba ko kin fara kin tsaya saboda kuɗin Ya maki yawa?
Maza zo na maki sauki ki ji yarda soyayyar ABLA take farawa da PRINCE
WASEEMUDDIN,kowa na kiranta karuwa harda shima Shin ita ɗin karuwarce?
Maza garzayo gareni ka samu amsa,
Normal price na YAR Arewa book 1&2 N700
ABLA ADNAN N700 complete amma a wanann lokaci na garabasa kuzo na baku ,Yar arewa
1&2 da ABLA adnan Akan farashin naira N600 dukka biyun ɗari shida kacal �ragin N800?
Kamar yayi yawa amma a haka dai Zan baku wannan garabasar ,masu cemun sati yayi kaɗa
ga shi kanan sai 1st February 2024
maza kar ayi baku.
0264267657
Gt bank
Amina jamil adam.
09058191213
Dm me

AHALINA.
(Siblings of different fathers)
Book two 'in Aure uku series.
          By
Chuchujay ✍
(Amina jamil Adam)�
ِ
مْسِب ِ
هَّللا ِنَمْحَّرلا
ِ
ميِحَّرلا
Episode 4⃣1⃣➡4⃣2⃣
Zaune Nameer yake a office ɗin Nadiya hankali sa yayi mutuƙar tafiya nesa,tunani kala kala
yake kan Jamaimah,yakamata ace a iya maganganun da Ya zauna Ya faɗa mata ta zama Mai
fahimta da hangen nesa,a iya tunanin sa duk wani Mai hankali idan ka zauna kayi masa bayani
kamar yarda yayi mata zai fahimta yasan menene dai dai ,amma ina kamar Ya sake tura mata
rashin fahimta akanta.
Yana cikin wannan tunanin Nadiya ta shigo daga meeting ɗin da sukayi,
Zama tayi tana Mai faɗin"wash komai is stressing a rayuwarnan ,amma Ya mutum zaiyyi idan
yana neman cigaba".
Ganin baice mata komai bane yasa ta kallesa da kyau tace "Hamma?,amma still shiru,ajiyar
zuciya tayi da ta fahimci Ya tafi tunani ne,hannun ta saka tayi snapping a fuskarsa wanda hakan
Ya sakashi dawowa daga duniyar tunanin da Ya tafi yace"Nadiya kin dawo kenan."
    Cike da kulawa tace "Hammanmu 'dan Allah ka daina wannan tunanin da kake yawan yi kar
yazo Ya zamar Maka damuwa,kar ka manta fa,komenene Allah Ya ɗorawa mutum to akwai dalili
,sannan shi mumini baya tab'a wuce ƙadarar sa kuma kasan ba'a jarabtar kowa sai mumini
wanda nasan insha Allahu kai Mai cin wannan jarabawar da Allah Ya ɗorawa maka ne,'dan
Allah kabar wannan tunanin,kar ka manta AHALINKA na tare da kai a duk wani step na rayuwa
da zaka taka.
    Sosa gefan fuskarsa yayi yace"amma dai Nadiya Kema kinsan babban jigon AHALINA bata
tare dani ko?"

Mami bata amsa wayana ,yanzu maganar da nake sai da na biya gida Amma ko inda Nake
mami bata kalla ba ,ko gaisuwana bata amsa ba duk yarda Papa yayi da ita,last naje Asibiti na
sameta amma Mami magana take mun kamar mara lafiyar da yazo ganin likita ,wai sai nayi
booking Appointment . Ƙaramar dariya Nadiya tasaka wanda Ya sa Nameer kallanta yace"mene na dariya"?
Hannunsa ta kamo tace "kawai mami ce ke bani dariya,yanzu fa Ya kamata ace kasan wacece
mami,to wallahi tafi kowa zama tare da kai kawai dai ranta ne Ya baci dangane da abunda
yafaru,kasa kanka a wannan matsayin mana,kana matsayin iyaye ɗanka yayi irin abunda kayi
kasan dole zakaji babu daɗi and you will feel less,amma Mami kam ko yau da asuba da naje
gaisheta najita tana Addu'an Allah Ya fitar da kai duk wani hali da kake mara kyau yasa kayi
overcoming,amma man ina shiga ta bari".
    Ɗan shiru yayi kana yace "Nadiya ki yarda what i did was not intentionally sannan banyi ba
domin Mami taji ƙanƙanta,wallahi kuskurene wanda baya wuce ranarsa"
Kaɗa masa kai tayi tace na sani Hamma and insha Allahu kuskuren nan zamu mayar dashi
abunda kowa zaiyyi alfahari dashi.
Gyara zamansa yayi yace"banga Alama ba domin Jamaima ta wuce dukkan wani tunani
ki,rashin fahimtarta da tunaninta zan ce maki yafi na jahilin da bai zauna a aji ba baki ɗaya "
Ɗan shiru Nadiya tayi kafin tace "inaji a jikina komai zaizo Ya wuce kamar bai faru ba time ne
kawai ".
Ɗan karamun murmushi yayi yace "Allah Ya nuna mun time ɗinnan na ƙosa cos im exhausted
already,"
Kafun ta Sake wani magana telephone ɗinta yayi ƙara wanda tasan sakatariyar tace,dagawa
tayi ta Kara a kunne inda take sanar da ita tana da baƙo,
Sanin wanene baƙon yasaka ta cewa Ya shigo,
Da sallama a bakinsa Ya shigo,haka nan ta tsinci kanta cikin wani irin farin ciki da ta tuna fa a
yanzu shi ɗin musulmine kamar ita sannan yasan ƙaidoji da dama na musulunci wanda cikin sa
harda idan kaje guri kayi sallama,
Juyawa Nameer yayi lokacin da Ya kallo fuskarta yaga wani irin annuri da farin ciki da take
kallan Mai sallamar dan haka Ya juya 'dan ganin wanda Ya saka Nadiya wannan Nishaɗin.
Ganin Nameer Ya saka AHMED(Evans )saita kansa yana Mai nutsuwa domin ko ba'a faɗa
masa ba yasan wannan ne brother ɗin ta Nameer cos kamar su ma kawai ta baka amsa ba sai
anyi magana ba,
Ƙarasowa yayi cike da girmamawa ya mika masa hannu yana Mai faɗin Sallamu alaikum.
    Kallan hannun Nameer yayi kana ya kalli fuskarsa da kyau yana san sanin inda
yasansa,karban hannun yayi yace"Sallamu alaikum".
Ganin yarda Ya tsaya Nervously ne Ya saka Nadiya saka ƙaramar dariya tace "ka zauna mana
,ko ganin future brother in law ɗinka Ya saka ka shiga kiɗima ne".
Murmushi yayi Ya jawo kujerar dake kallan Nameer ya zauna yace"ba dole ba cos yarda nake
tunanin zanga Brothern ɗin mu Ya fi haka and i was not thinking zamu haɗu a nan"
Gyara zama Nameer yayi yace "kamar nasanka ko kuma nace nasan Mai kama da kai ,amma
wanda nake mistaking ɗinka dashi bama musulmi bane ,and He's a ghanian Actor which nasan
babu abunda zai haɗasa da kanwata Nadiya nan,and idan fahimta  takai inda nake tunani kai
da ita ɗin kuna soyayya ne,so mind idan nasan more about you?

Ya karasa maganar da irin tone ɗin nan na babban yaya.
    Kallanta Ahmed(Evans)yayi alamun Mai zaice,ɗaga kafaɗarta tayi tace "kajisa ai ka amsa
masa tambayarsa ,he's My elser brother Nameer and yana san sanin wanene kai wanda na
tabbata ba sai nayi masa bayani ba daga bakinka zaifi daɗi cos in baka manta ba nima nayi
undergoing wannan investigation ɗin  but trust me nawa kawai magana ne"     Ƙaramar dariya yayi da Ya fahimci abunda take nufi kafun Ya maida kallansa kan Nameer
wanda Ya zuba masa ido yana Mai san tabbatar da ba Evans bane cos duk da a screen Ya
saba ganinsa amma yawan kallasa a screen ɗin baya tunanin idan Ya gansa a zahiri zaiyyi
masa wahalar ganewa,amma abu guda ɗaya Ya sani wanda shine Evans bazai saka jallabiya
da hula ba,koda kuwa zai saka jallabiya bazai saka hula irin ta ustazai din nan da mutane Kema
laƙani da"tashi kafiya naci"ba,sannan babbar maganar ma kuma itace babu wata alaka da zata
shiga tsakaninsa da Nadiya.
    Cike da rashin sakewa Ahmed(Evans )yace "sunana Ahmed Hans wanda ada nake Evans
sannan Bakayi kuskure wajen gane wanene ni ba nine Evans Hans ghanian movie Actor and a
model,i was a Christian amma a yanzu ni musulmine ,sannan ina san ƙanwarka ne tsakanina
da Allah san kuma da nake mata na Aure ne bana wasa ba cos maganar da nake maka a
yanzu mahaifiyata tana garin nan tana san ganawa da iyayen Nadiya domin suyi magana ".
    Kallan Nameer Nadiya tayi tana kallan yarda Ya shiga Cikin shock da mamaki na confession
ɗin Ahmed,
Yar karamar dariya yayi yace "you're not joking ko?,wait idan kai musulmine yanzu taya akayi
kazama,Kana so kace mun saboda Nadiya?"
Kodai musuluncin ka wata mafakace ta yaudarar Nadiya?
Bana fahimta ka fahimtar dani,
Kallansa Ahmed yayi cike da gaskiyarsa yace "wallahi yayan mu ban karbi musuluncin ba dan
na yaudari Nadiya ba,ina mata soyayyar da babu yaudara acikin ta,na yarda itace mukulllin
shiga musulunci na amma dana shiga na fahimci nanne wajen zamana inda zan samu
kwanciyar hankali Mai daurewa wanda nake fata,dama kawai nake nema na samu na kula da
Nadiya fiye da yarda zan kula da kaina. "
    Shiru Nameer yayi yana kallan Ahmed da wata irin fuska Mai tsoratar da mutum idan yana
gaban sirikai,
Ajiyar zuciya Nameer yayi yace"addinin mu bai hana mu aurawa ƴarmu wanda Ya karbi
shahada ba abun dadine sannan abun alfahari ne gare mu ace dan Nadiya ce sanadin
musuluntar ka sannan magana tana ga manyamu amma kafin nan sai ka nemi soyayyar ita
Nadiyar" Kafun kowannen su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login