Showing 3001 words to 6000 words out of 73196 words

Chapter 2 - AHALINA (Aure uke series)na chuchu.pdf

Advertisement

08 Jul 2025

2277


"Fawha ne dake gefen Abdallah tace "nikam Papa sai dai fauza taje Allah ,nifa na kai ta ɗaki
jiya,i hate her guts".

Tashi mamin su tayi tace "bari ni naje na kai mata tunda dukkanku babu wanda zai iya kai
mata,"

Da sauri Fauza ta miƙe ta shiga kitchen tana Mai faɗin bari naje na kai mata ,Allah ma yasa
Papa Ya dawo zamu yi getting rid of her.

    Kafun Papa yace wani Abu Mami tace"koma menene dai ai yayanku gashi nan Shine Ya
jawo maku sannan idan yayi creating mess Ai ba Papan ne zaibi ya gyara masa ba ,shi ɗin da
Ya b'ata Shine zai bi Ya gyara ."

Kamo hannunta Papa yayi yace "sarauniyata Ya isa haka nan zo zauna ki daina wannan faɗan
'dan Allah ".

Zama tayi tana Mai karamin murmushi .

    Gyaran murya yayi yace "kaga nan Nameer kowa yana making mistake a rayuwa wadda ta

shafi zamantakewa,nima akwai abubuwa da dama da nayi mistake akai ,amma a kullum
maminku nakusa dani kuma tana tare dani a duk mistake ɗin da nayi muna gyarawa a tare so
Son talk to me duk wani mistake da zakayi a rayuwanka muna tare da kai sannan zamu
gyarasa a tare cos babu ɗan adam ɗin da ya wuce aikata kuskure."
    Ajiyar zuciya Nameer yayi yana Mai jin papan nasa a ransa cos duk da bashine Ya haifesa ba
amma baya taba nuna masu wariya tsakaninsu da Fawha,Fauza da Fawzan ,

Yasan yarda yake fahimtar sa mahaifinsa da Ya haifesa ma bazai tab'a fahimtarsa ba duk da
Mahaifin nasa yakan je Ya gansa wanda a yanzu bazai ma iya faɗin yaushe rabo ba ,

Sosai yake jin Haushin mahaifinsa musamman idan yana tuna abubuwan da yayi wa
mahaifiyarsa lokacin yarintarsa sai yaji ƙiyayyarsa ta tsananta a zuciyarsa ,shi yasa gudun nuna
masa ƙiyayya Mai yawa yasakashi limiting ganinsa ,

Kallan Papa yayi da gajiyayyun idanunsa yace"Papa wallahi wannan yarinyar tun jiya nake
faɗawa Mami ban santa ba ban tab'a ganinta ba,na yarda Akwai mistakes da dama da nayi
cikin sani da rashin sani,amma nayi maku alƙwari fyaɗe baya cikinsa ,wallahi ban san ta ba ban
kuma taba yiwa wata ɗiya mace fyaɗe ba,cikin sani da kuma rashin sa,Allah kaɗai yasan
menene manufarta da kuma abinda ke tafe da ita .

    Shiru Papa yayi na wani lokaci kafin yace "Ai abun ma yazo da sauƙi cos yanzu maganace ta
technology,a zamanin baya mahaifiya ita kaɗa ke da say akan ɗan da ta haifa na wanene amma
banda yanzu ,'dan haka ta shirya anjima zamuje asibiti tare Ai DNA test."

    Tafa hannu Nadiya tayi tace "Papa you're always the best ,kaganmu nan dukkan mu babu
wanda yayi tunanin yin wani DNA har DR Mami,"

Dariya suka saka baki ɗayansu banda Mami wadda jikinta ke bata wani irin baƙwan yanayi,ji
take a jikinta koda anyi DNA ɗin result d'in zai fito akan yaran ɗan Nameer ne .

    Kamar yarda suka yanke shawara Bayan gama cin Abincin Anisa da Mami da Papa da
Nameer suka nufi asibitin 'dan daukar jinin yaro a gwada,

Bayan fitarsu Nadiya ta koma ɗakinta cos boyayyen masoyinta a yau yake san bayyana mata
kansa wanda take Zuci zucin ganinsa tana addu'an Allah yasa dream Man ɗinta ne cos duk da
dumbin masoyanta hankalinta yakasa ƙwanciya koda da mutum ɗayane.

    Gyara fuskarta ta sakeyi kana ta shirya cikin highwaist silk maroon wando da off White long
sleeve,

Cotton maroon veil ta yafa kana ta ɗora kimono a sama ,talakmin Dolce ta saka flat Mai kyau
Fari kana ta ɗauki ƙaramar purse ɗinta da Car key ɗinta ta fita a ɗakin tana mai jin farin cikin

cos abu biyu zasu faru,na ɗaya zata gana da EH ,na biyu kuma Anisa zata fita a rayuwarsu da
so Call babyn ta,

    Tana ƙokarin fita ta jiyo muryar Abdallah yana Mai faɗin"Addy a haka za'a fita?"

Kallan Kanta tayi for a moment kana tace "mene abun banza a shiga ta?

Fauza check me out,"

Fauza dake zaune tana Mai kallanta ne tayi mata alamu da hannu tace"My fav super model
Babu,Kin gama haɗewa sannan kin gama kashe ni,ke Mai kyauce wallahi, you look so innalillahi
wainna ilaihir rajiun..

Jifarta da Abdallah yayi ne yasaka ta rugawa da gudu tana dariya,"

Kusa dashi Nadiya ta koma ta zauna tace "dear Malam Abdallah na faɗa maka Im pure and
clean,tun farko kake ƙin career ta amma trust me im not doing wani abu da yake against
addinina ,namaka Alƙwari ,sannan Kasani shi hijab a zuciya yake,

Tashi tayi tana Mai sake kallan kanta tace "kalleni 'fa Ba shigan banza nayi ba,wandona is
baggy and nasaka kimono sanann ga veil ."

    Shiru yayi yana kallanta kana yace"ina zakije yanzu,"

Murmushi tayi da ta tuna inda zataje tana Mai ji a ranta da ace Abdallah yayan ta ne da ta gama
ganin boni,

Dafasa tayi tace "zanje wani business ne da zai benefiting ɗina,Inajin kun kosa na kawo miji
ba?"

Na kusa 30 fa so im not getting any younger shi yasa Zan bawa wani chance just wait idan na
dawo akwai gist mai zafiiiii.

    Just be careful and ina nan ina jiran dawowarki im eager nima naji wannan gist ɗin sannan
nasan wanene wannan da Addy na ke rawar jikin zuwa ta gansa"Ya faɗa yana mai
murmusawa"

Bashi da hayaniya ,sannan shi mutum ne da baya san damuwa ,idan kaji hirarsa Mai yawa to
da Nadiya ne wadda jininsu yayi mugun haɗuwa,duk da kuwa da ƙannensa ma sukan
tab'awa,amma Nameer kuwa ba wai sun cika zaman hira bane tunda shima Nameer ɗin akwai
nashi miskilancin,'dan nashi Ya taka na kowa a gidan.
    Kai tsaye bayan Nadiya ta bar gidan Location ɗin da boyayyen masoyinta Ya tura mata tabi,

Crescent Food &grills Shine inda ta nufa,babban gurin cin Abinci ne da sai wane da wane 'dan
haka bai da hayaniya,

A gurin da aka tanada domin adana motocin baƙi ta aje tata kana ta fito tana Mai b'in saƙon sa
'dan zuwa inda yake .

Tsaye tayi a bakin VVIP na gurin tana tunanin ina zata gansa 'dan bata san fuskarsa ba,wanda
hakan ke ƙara bata mamaki tana Mai mamakin kanta sosai,

Kalle kalle take ganin babu kowa a gurin,waiter namijine Ya zo gareta yace"Nadiya Belal right?"

Kaɗa masa kai tayi inda yayi mata jagora suka shiga gurin.

    Romantic theme dake gurin Shine abunda Ya Fara mata sallama,ganin babu kowa a gurin ne
Ya tabbatar mata da cewa ya Kama gurin ne baki ɗaya,

Kujerar da waiter ɗin Ya nuna mata ta zauna akai tana Mai kalle kallan yarda gurin yayi kyau
sosai mood na soyayya.

Ita kaɗai ta tsinci kanta da Blushing tana Mai san saka wanann bawan Allah a cikin idanunta,

A hankali silent kiɗa Ya fara tashi wanda yake da daɗi a kunnen mai saurare,

Gyara zamanta tayi lokacin da ta hango shadow ɗinsa,shigowarsa ce ta saka dukkan wani
tunani nata tsayawa ,

Ƙyaƙyawan murmushi da Ya sakar mata shine abunda Ya dawo dan ita cikin nutsuwarta,

Tabbas ta gane sa cos bayan haɗuwarsu ta farko kuma around her take tajin suruntunsa wanda
hakan yasaka har ta gansa a yanar gizo inda tanan ne take sanin shi ɗin model ne sannan
kuma Actor na Nollywood,abunka da bawai ma'abociyar kalla bace ,

Saurin tashi tayi musamman da hankalinta Ya dawo mata ya bata cewa "He's Evan Hans
sannan christian wanda ƙatuwar ice ɗin dake wuyansa ta cross ta Kara tabbatar mata da
hakan,take hankalinta Ya bata tazo wrong guri ne 'dan haka ba tare da b'ata lokaci ba tayi
saurin tashi tana Mai ɗaukar Jakarta tace "im Sorry i think i'm 'in the wrong room.
" Sorry " Ta sake faɗa tana Mai ɗanyin karamin murmushi .

Takowa yayi inda take yana Mai sake faɗaɗa murmushi kafun Ya sha gab'anta yace"My
cupcake bana tunanin kinyi mistake na zuwa nan ."

Wata irin faɗuwa gabanta yayi lokacin da ƙwaƙwalwarta ke shirin tattori mata abinda ke shirin
faruwa sannan of course a cikin abun bata cire mamakin accent ɗinsa na hausa ba,

Ƙaramin murmushi tayi lokacin da zuciyarta ke shaida mata wasa ne kawai yayi da ƙwaƙwalwar
ta,

Mukullin motarta ta ɗauka kana ta kallesa tace"naji dadi da Ya zamana kanajin hausa yarda
bazan azabtar da turanci na Wajen faɗa maka ka kiyayeni ba ,bana san wasan banza, Dont
mess With me cos ka yarda dani im d last person da zakayi messing da,i will let This slide
amma Next time Bani ba kar kasake wasa da emotion ɗin wani ,and dama nazo ne 'dan nayi
maka kashedi sannan lastly ina fatan kasan cewa Nadiya da Evan bazasu taba haɗuwa ba
incase Bakasani ni musulmace,

Juyawa tayi 'dan fita ,riƙe mata hannun da yayi ne yazo mata a bazata inda marin da ta ɗauke
masa fuskarsa dashi shima yazo masa a bazata.

Dafe kuncinsa yayi ,bata tsaya bi takansa ko abunda zai faɗa ba ta fice a gurin.

    Komawa yayi Ya zauna yana me shafa inda ta maresa kana yayi wani irin murmushi
yace"Nadiya you're mine and i know Kema kinzo nan ne domin Kina jin wani abu akaina ko
yaya ƙanƙantarsa take,

Amma menene laifi 'dan ba addininmu ɗaya ba,a tunaninsa ba wani aibu bane ba dan sunyi
Aure, yana ganin kowa zai iya yin nasa addinin daban amma soyayya Ai ba addini bace kuma
babu ruwan ta da addini,

Cup ɗin dake aje gurin Ya jawo Ya buɗe wine ɗin da ke gurin Ya zuba Kaɗan yana Mai kurb'a
,murmushi yayi yace "She's cute and i know we are meant to be".




Chuchujay ✍
[3/6, 4:54 PM] Chuchujay✍️: .https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK

AHALINA

    (Siblings of different Father's)

(Book two in Aure uku series)

            By

   CHUCHUJAY ✍

Gamasu san a tallata masu hajarsu cikin farashi Mai rahusa 09058191213 .

EPISODE 5⃣➡6⃣

    A hankali Nameer yake tuki a yayin da motar ta ɗauki shiru cos tabbas idan yayi magana shi
kansa yasan bazai iya mayar da ita bakinsa ba duba da yarda zuciyar sa ke tafarfasa ,

Murmushi Anisa dake gefen sa tayi tace"Baby tunda muka taho bakin ka shiru kaƙi magana
amma wani abu da baka sani ba shine ,ni a kowanne yanayi naganka burgeni yake ,shafa kan
jaririn hannunta tayi tace "bashi da suna fa har yanzu cos dama uba ke bawa yaran sa suna
'dan haka wannan lokacin ma akan yarona hakan ne zai faru ,ka bashi suna and trust me DNA
test ɗin Chan da zai fito 99% positive ne ,ni banga menene amfanin wahalar da kai ba. "

    Wani irin wawan burki yayi Ya Kalleta cikin fushi mai mutuƙar yawa yace "fita a motar nan ,"

Kallan sa take tana wannan murmushin wanda yake ji kamar ya yagesa a fuskarta ,hannunta ta
kai ta ɗora a nasa tace "Nameer Stop trying ,mene amfanin ƙokarin da kasan babu wani
outcome Mai kyau da zai fito a cikinsa?"

Kazo mu rufawa juna asiri muyi Aure mu bawa yaranmu rayuwa Mai kyau da inganci,babu
wanda Ya gani babu wanda yaji please,

    Hannunta da ta saka Akan nasa Ya yakice da ƙarfin gaske kana yace "ke duk wani guntun
haukaki fa inaji dashi,kila ma yafi na kanki ,sannan nasan duk hanyar da zanbi naci maki
mutunci wallahi fiye da yarda baki zato 'dan haka kafun na wulakantaki ki fitar mun a mota
tunda bata ubaki bace."
Ƙaramun murmushi tayi Mai ci masa rai kana tace "Cool down Man,"Bude murfin motar tayi ta
fita tana Mai faɗin ,mu haɗu a gida uban ƴaƴana,

Wani irin figar motar yayi wanda Ya sakata saurin ja da baya tana Mai darawa tana juya wayarta
da tayi recording abunda ya faɗa yanzu nayi mata rashin mutunci kana ta danna numbern uwar
ɗakinta,

Kira ɗaya ta ɗauka ,murmushi tayi kamar tana kallanta kafun tace "uwar ɗakina ina fatan kin
gama da Asibiti?"

Licking lebenta na ƙasa tayi tace "Allah yabarmu tare ,sannan a yanzu maganar da nake maki
na samu wata hujja da babu yarda iyayen Nameer zasuyi dole su yarda,

Lokacine da yakamata ace sun girbi abunda suka shuka musamman Imam paki da matarsa
Umaimah Bulama,ina jin suna jin labarin kiyayya da fansa amma bana taba tunanin sun tab'a
ganin irin tawa ƙiyayyar da fansar dake dumama acikin zuciyata da b'argona wadda nake ji
kamar na soke dukkanin acting ɗin da nake na kashesu a zuwa ɗaya,kin san nayi training wajen
yin kisa ko wacce irice ballantana kuma akai ga maƙirici,

Dariya tayi kana ta kashe wayan tana Mai faɗin"Wallahi da ni yarinya ce Mai hali na gari,amma
dukkan wannan halayyar ta gari ta ƙare ne a lokacin da na rasa mahaifiyata kuma kash sai Ya
zamana kafun ta tafi ta sanar min da waɗanda sukayi silar mutuwarta,dukkan godiya ta tafi
gareta da ta barni da ƙyautar fansa da ƙiyayya,wadda na rantse da Ubangijin da na yarda dashi
bazan tab'a gushewa ba sai na ƙarar da zuri'ar Paki da duk abunda suka mallaka. "

    Da haka ta nufi gidan 'dan shirya saban tuggunta.

******************************************** 

  Bayan Rabuwar Nadiya da Evan ta daɗe tana saka da warwara a cikin zuciyarta kafun ta nufi
gida kai tsaye dan ko office bata san zuwa,

Abu guda ɗaya ya tsaya mata a zuciya wanda shine yarda Evan yasan Abubawa da dama
akanta ciki kuwa har da inda take zama,

Babu abunda yake sake b'ata mata rai da damunta kamar idan ta binciki zuciyarta taji har a
lokacin akwai wani Abu tattare dashi wanda bazata iya fassarawa da baki ba ,

Tana shiga gida Motar Nameer Ya tabbatar mata da sun dawo ,ajiyar zuciya tayi atleast idan
nata matsalar baiyyi working out ba na Hammanta ta tabbatar da yayi,

Tana Mai koƙarin fita a motanta bayan ta fakata a mazauninta Anisa ta buɗe ta zauna a
mazaunin Mai zaman banza,

Wani banzan kallo Aneesa ta bata musamman da taji yarda Annoying kukan babyn da bai ji bai
gani ba yana tashi,

Baki ɗayanta a foul mood take wanda idan Anisa ba tayi wasa ba zata iya juyewa akanta
,ɗaukar Jakarta tayi tana Mai faɗin"Get out of My car".

    Wata irin dariya Anisa tayi tace"na daɗe da lura Alhalin gidan nan arrogance ɗinsu abu
ɗayane kamar yarda suke abu ɗaya,kamar kuma an tsinkuleta ko irin ka faɗin abu ba dai dai ba
tace"a'h Afuwan fa ashe dake da Nameer ɗina da Abdallah zaman agolanci kuke a gidan
nan,'dan naji sirikina da Ya haifi Nameer har Porn clip ɗin mahaifiyarki da Mijin ta na yanzu
ma'ana mahaifin su Fawzan Ya ɗora wanda kuɗi yasa aka kashe maganar aka ƙaryata alhalin
babu wanda bai san iskancin da suke yi a city hospital ba,

    Dafe bakin ta tayi tana Mai Kallan Nadiya da murmushi rainin hankali tace"amma fa rumours
ne nima' wai 'naji suna iskanci a 'da amma bana tunanin jita jita da ya tashi a lokacin baya na
kama mahaifiyarki da Mahaifinki Bilal yayi da gardi Akan gadonsa ƙarya ne ,sannan naji ance
yana ƙokwantan kasancewar ki ƴarsa,After All baya nemanki " .
Sake dafa baki tayi tace "a'h shima nafi yarda da jita jita ne 'dan mother 'in law na batayi kama
da Mai rabawa maza Pun@ ɗinta  ba duk da kuwa ta raba ga maza iri huɗu da sunan Aure.

Family ɗinmu nada reputation gaskiya .


    Buɗe murfin motar Nadiya tayi ta fito kana ta zagaya inda Anisa ke zaune ta buɗe ta finciko
ta,kafun Anisa tayi Aune ta sharara mata wani irin zazzafan mari yayin da babu abunda bakinta
keyi sai karkarwa ,ƙokari sosai tayi wajen danne kukan da yake san zubo mata 'dan sosai
maganganun Aneesa sukayi mata zafi,tana ƙokarin sake marin ta sakamakon dariyar da Anisa
ke Mata taji an riƙe mata hannu,

Juyawa tayi 'dan ganin wanene,Papa ne tsaye gefensa Mami,kaɗa mata kai yayi yace"No My
princess bana san ki Aikata mistake ɗin nan ,"

Hawayen da take ƙokarin zubo mata ne suka fara neman hanyarsu ,ba tare da ta boye ba tace
"Papa kalli yarinyar nan na tabbata ko Abdallah ƙanina Ya girmeta and trust me idan kaji
maganganun da ta faɗa mun kai zaka mareta Bani ba,amma tunda kace na Bari Zan bari,nuna
Anisa tayi da hannu tace "ki sani i will be your downfall sannan lokacin da Zan wulaƙantaki a
gidan nan na maki koran kare lokacinne Zan baki amsa dai dai da abunda kika faɗa mun
,Stupid freaking Gold digging bitch .

    Ta juya dan barin gurin ta tsinci muryar Mami na faɗin"stupid freaking Gold digging bitch ɗin
nan ina san kisa aranki babu ranar da zaki koreta,ki wulaƙantata cos zaman ta da Ahalinku
yanzu ta fara cos tana ɗauke da ɗan da yake jinin gidan nan,"

    Wata irin murmushi frustration Nadiya tayii jin Abunda mami tace sannan sarai ta fahimci
abunda Mamin ke nufi ma'ana dai Dna Ya nuna yaran dan Nameer ne,

Juyowa tayi ta kalle su kana tace "ban san menene kuka yarda dashi ba amma ni abu ɗaya na
sani na yarda dashi wanda bana tunanin kun fahimce sa wanda shine"wannan yarinyar is fake
and a cheat cos ada kokwanto nake amma a yau maganar da ta faɗa mun bana koƙwanto
sannan sai na kawo ƙarshen maƙiricin ta cos naga Alama ni ta zab'a a gidan nan na kawo mata
ƙarshen ta"

Fuu ta wuce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login