Showing 33001 words to 36000 words out of 73196 words

Chapter 12 - AHALINA (Aure uke series)na chuchu.pdf

Advertisement

08 Jul 2025

2291

yace "ga ɗaki Chan ki kai
kayanki sannan kiyi amfani dashi,"

Cike da mamaki ta juyo ta kallesa tace"ni bazan zauna ni kaɗai ba a ɗaki idan Babu kai sannan
naga gidan dagani sai kai ,ina yan aiki dan ni wallahi bazan iya aiki ba",

    Baice mata komai ba Ya juya dan shiga ɗakin dake nasa yace "idan bazaki iya aiki ba
gimbiya JAMAIMA zaki iya komawa gidan ku ,amma ki sani da Aurena zakiyi ta yawo dan
wanann karen nima yin kaina bazan sakeki ba.

Yana kai karshen maganarsa Ya shige ɗaki na huɗu dake daga Chan ƙarshen corridor Ya barta
tsaye.

    Tab'e bakinta tayi taja kayanta tana mai faɗin"zaka biyu ne indai muna gida ɗaya".

    Bayan shigar Nameer shahararren ɗakinsa kan gadonsa Ya faɗa yana Mai duba lokaci ƙarfe
Ɗaya da rabi na rana,wayarsa Ya ɗauko yayo ordering pizza dan bashi da komai na abinci
gidan sannan pizza ɗin yake sha'awa amma yana fita zai siyo mata kayan abinci duk da kuwa
yasan ba iya girkin tayi ba amma a hakan sai Ya gyara mata zama tasa ita ba kowa bace.
Wayarsace ta fara ruri,Nadiya ke kiransa, kira ɗaya Ya ɗaga,conference ne su uku,daga ɗayan
bangaren Nadiya tace "Hamma are you okay?"

Ajiyar zuciya yayi yace "im Okay Nadiya and nasan yarda zanyi da Jamaimah Yes i was
planning to talk about her da su mami idan komai Ya lafa cos ina santa ,we made mistake
amma Aurenmu a ko ina Aure ne wanda ya ɗauro,amma yarda tazo wa su mami dole ne nayi
da gaske wajen ganin na gyara mata zama."
Daga ɗayan bangaren Abdallah yace "Hamma ka dai kula kar ka shiga hakkin ta cos tun ranar
da aka ɗaura maku Aure hakkinta ya hau kanka.

    Rufe idanunsa Yayi kamar yana gabansu yace"Insha Allahu bazan cutar da ita ba ,Ni dai
alfarma ɗaya zakuyi mun wanda shine ku tayani wa mami magana da Papa dan Allah."

Assuring ɗinsa sukayi inda Abdallah Ya fara fita a wayan Akan zaije wani taro da aka gayyace,

Yar hira Kaɗan suka taba da Nadiya wadda duka akan lallashin junane kafun sukayi hanging
Call ɗin .

    Pizza ɗinsa ce tazo ya fita ya shigo da ita,

A ƙaton dining table Ya zauna bayan Ya ɗauko holandia da cup,

Ya buɗe zai faraci ta fito a dakin nata cikin buguwar riga mara Nauyi baƙa wadda ta ɗauki farar
fatarta sosai,

Saurin ɗauke idanunsa yayi akanta yana Mai gutsurar pizzan da Ya ɗauko,

Cikin wani irin Yanayin ta tako garesa tana Mai yarfe hannu tace"Baby pizza God abunda nake
craving kenan."

Zama tayi tana Mai ɗauko cup d'in da Ya zuba hollandia ɗin tayi sipping,bai hana taba sanann
shima bai hanata sha ba ,a haka suka fara cin abincin suna shan hollandia ɗin a cup ɗaya yana
Kara masu,

Bayan sun gama Ya kalleta yace "anjima zan kawo Food stuffs zanki fara girki".

    Wata irin dariya ta saka har tana ƙwarewa tace"amma wasa kake ba?"

I mean hatta ruwan wankan kaimun ake a gidan mu ,ni ko ruwan zafi bansan Ya zan ɗaura ba.

Tashi yayi bayan ya goge bakinsa yace "Ai kin iya kunna data dan haka kiyi browsing,"

Wayarta dake gefenta Ya ɗauka yasa numbernsa yayi dialing tana shiga Ya kashe yana Mai aje
mata yace "Ni zan fita ki kula mun da gida sannan bathroom ɗina yayi datti kije ki wanke
mun,bana san na dawo nagansa haka nan."

    Kafun tace wani abu Ya fita a gidan,

Murmushi tayi bayan fitar sa tace "abu na technology ,kafun ka dawo na samo yar aikin da zata
wanke maka bayin amma ni kam sai dai a soni a lallab'a ni. "

    CHUCHUJAY ✍

*
[3/6, 5:17 PM] Chuchujay✍️: AHALINA
(Siblings of different fathers )
Book two 'in Aure uku series
       By chuchujay
Episode 3⃣1⃣➡3⃣2⃣.
   NASREE VENUE.
Cike Nasree Venue yake ,katafaren guri da aka ƙirkiresa saboda taro irin na manyan malamai
da walima,
Taro ne ake a gurin na manyan malamai waɗanda kana kallansu kasan malamai ne na gaske
da gaske ,
Duk cikin su malami ɗayane yaro wanda bazai wuce shekaru Talatin da tara ba da haihuwa,
Wani dattijan malami ne Ya tashi yana Mai gabatar wa ta buɗe seminar ɗin da suka taro domin
ita,
Kiran babban baƙo aka fara wanda shine Abdallah amma bai ƙaraso ba.
    Tunda ya iso harabar gurin yake jinsa gashi nan dai amma hankalin sa ba kwance ba baki
ɗaya,
Daliban da suka taru dan bawa ilimi a gefe Ya kalla bayan Shigarsa gurin bayan sa da masu
basa tsaro,
Yana shiga Ya samu gurin da aka tanada dominsa ya zauna ,
Bayan wasu mintuna aka gayyacesa domin zuwa kan stage yayi jawabi,
Tafi guri Ya ɗauka inda shikuma ya taka yana Mai faɗaɗa fara'arsa ,
Bayan yayi sallama yafara jawabinsa cikin iyawa da sani,
Bayan wasu lokuta ya bada filin tambaya inda yake amsawa duk wani Mai tambaya cikin hikima
da ilimi,
Daga chan baya guy d'in dake baya ne fuskarsa ɗauke da face mask Ya ɗaga hannu alamun
zaiyyi tambaya inda aka basa dama yayi,
Daga zaune mic na hannunsa yace "akaramakallahu munajin labarai akanka wanda muke da
yakinin gaskiya ne amma muna so ka sake sanar mana da gaskiyar akan maganar tunda mu
nan kowa yanaso ne a ɗora ka a kujerar shugaban matasan malamai,"
Tambaya ta anan kuma itace"shin menene gaskiyar zama mahaifinka ɗan shan jini wanda Ya
tara dukiya da kuɗin jinin mutanen da basuji ba basu gani ba,sannan mun tsinci labarin cewa ka
gaji wani abu daga cikin dukiyarsa ta haram ,Shin menene gaskiyar Al'amarin?"
Shin ka zama babban malamine a yarda kake yanzu dan kawai ka boye tabon mahaifinka da
baka san mutane su faɗa?
    Daga kusa dashi ɗayan yace "Haka maganar take dan Babu wanda bai sani ba dan hatta
mahaifiyarsa ance kafun ta Auri mijinta na uku abu yayi ta yaɗuwa Akan suna zaman daduro ne
."
Daga nan sauran abokan da suka zo tare suka fara fadin "a faɗa mana gaskiyar Al'amari,"
Take jikin Abdallah Ya fara karkarwa dan a rayuwarsa ta duniya babu abunda bayaso kamar
ace yau ana masa magana kan mahaifinsa ko Akan clip ɗin mahaifiyar sa da yayi yawo a baya

wanda yake ƙanzan kurege ,
Haka nan yaji jikinsa Ya fara kyarma musamman da yaga kowa kallan sa yake yana jiran yaji ta
bakinsa sannan ga yan jarida kowa na faman haska masa camera suna san ɗaukar zazzafan
shayi ,wani irin jiri yake ɗibansa,cikin nutsuwa ba tare da yace komai ba Ya fita daga kan
mambarin yana mai jin kamar zai faɗi, Ɗaya daga cikin waɗanda suke basa tsaro ne yayi saurin zuwa Ya kamosa inda suka taimaka
masa suka fitar dashi a gurin yayin da kowa ke ihu da ikirarin Ya dawo Ya fadi gaskiyar abinda
ake faɗa ɗin yayin da shikuma yake jin muryoyi da yawa suna masa tsiwa a kunne ,
Yana zuwa bakin motarsa hannu Ya ɗagawa wanda Ya  kawosa inda Ya fahimta yaja baya,
Ya jima a motar shi kaɗai yana san kansa Ya dai daita kafun yaja motar yabar harabar gurin,
Shikadai yake bulayi a titi dan baya san zuwa gida a haka,so yake yayi kuka sannan yana so
wani Ya ara masa kafaɗarsa yayi  ,bashi da kowa a wannan lokacin da Ya wuce yan uwansa
biyu,Nameer da Nadiya waɗanda bazaiso takura masu da damuwarsa ba Ya ƙara masu ciwo
Akan wanda yake damunsu,hakazalika iyayensu sunfi kowa shiga damuwa dan me zai ƙara
masu da nashi,
    Duk cikin yan uwansa shine wanda Ya samu uba mafi muni wanda Ya barmasa tabo mafi
muni,duk yarda yaso Ya nuna He's okay amma abun yaci tura He's not and yau Ya kara
tabbatar da He's not,
Duk ƙokarin da yake wajen zama mutum nagari amma sai da aka samu waɗanda suka binciko
bakin mumunan bayansa suka yab'a masa a wajen taro mafi muhimmanci gurinsa,a gurin taro
da matasan dalibai ke dubansa a matsayin abun koyinsu manyan malamai suke ganinsa da
daraja amma a yau magana ɗaya wadda take dole tana jikinsa ta zubar masa da dukkan
wannan kimar ,
Yana wannan tunani tunannin ya juya kan sitiyarin motarsa ya nufi gidan Auntynsa shatuh
wadda sau da dama takan basa shawara ga damuwarsa sannan yaji hankalinsa Ya kwanta da
shawarar saboda iirin shakuwa da yayi da ita tun yarinta,sau tari idan komai yayi masa zafi
gidanta yakanje yayi Clearing kansa na kwana biyu.     Yana isa bakin gate ɗin yayi horn ,Mai gadin na lekowa yaga motarsa babu tambaya Ya buɗe
masa,ganin bai kulasa ba Ya saka shi tabbatarwa da lallai yau Abdallah ba kalau ba.
Parking motarsa yayi yana Mai ajiyar zuciya kana ya fito yana Mai takunsa cikin nutsuwa kamar
babu komai a cikin ransa amma ransa fal yake da baci da damuwa ,
Yana ƙokarin shiga sashen yaji yayi gware da mutum inda manjan dake riƙe a hannun Mai
fitowar Ya zubar masa jikin farar shaddarsa ɗa tayi worthing kuɗi masu yawa,
Bama ta shaddar yake ba tukkuna, ɗaga kai yayi ransa a mutuƙar bace yana san ganin fuskar
wanda Ya ƙara masa bacin rai cikin wanda yake ciki.
*
  GARABASA GARABASA BONANZA
    2024 Shin kuna sane da ban bada garabasa ba?
To ku kwantar da hankalinku ga chuchu dai tazo maku da garabasar sabuwar shekara,
Shin kin fara kin fara karanta YAR AREWA labarin captain Jasmine Bilal shareef da captain
Shuraym Sadauki,
Ta tashi da mafarkin zama pilot a yayinda shi da yake kan aikin yake kusheta Akan tayaya ɗiya
mace Yar Arewa zata zama matuƙiyar jirgin sama?

Soyayyar da ta shiga tsakaninsu ba tsammani wadda take ƙokarin danne kiyayya .
Ko kuwa kin fara karanta littafin ABLA ADNAN ne labari na matashiyar budurwa wadda bata
barin taƙwana ,budurwar da tazamarwa masu kuɗin gaske barazana ,
Shin baki fara karantashi ba ko kin fara kin tsaya saboda kuɗin Ya maki yawa?
Maza zo na maki sauki ki ji yarda soyayyar ABLA take farawa da PRINCE
WASEEMUDDIN,kowa na kiranta karuwa harda shima Shin ita ɗin karuwarce?
Maza garzayo gareni ka samu amsa,
Normal price na YAR Arewa book 1&2 N700
ABLA ADNAN N700 complete amma a wanann lokaci na garabasa kuzo na baku ,Yar arewa
1&2 da ABLA adnan Akan farashin naira N600 dukka biyun ɗari shida kacal �ragin N800?
Kamar yayi yawa amma a haka dai Ya zanyi na baku wannan garabasar ta sati,maza kar ayi
baku.
0264267657
Gt bank
Amina jamil adam.
09058191213
Dm me
*
    Wata irin karkarwa jikin HAFSA Ya fara ganin ta'asar da tayi,tana ƙokarin basa haƙuri bakinta
Ya sarke sakamakon ganin mutumin da har ta mutu bata taba tunanin zata sakashi cikin ido ba,
Bakinta na rawa tace "Malam Abdallah?"
Cike da fushi yace"shine Kalmar haƙuri wadda aka koya maki a gidanku?"
Ke makauniyace ko kuma Hankalinki ne ba dai dai ba kina tafiya baki kalla gabanki saboda
hauka ko menene?
Dame kuke so mutum yaji ne ,da abunda Ya damesa koda rashin nutsuwarku?
Shashanci banza kawai.
Wani dogon tsaki yaja bayan Ya kai karshen maganarsa yana Mai kallan rigarsa cike da takaici
kafun Ya juya Ya koma motarsa,
Rigar Ya cire daga shi sai singlet Ya ninketa ya aje a gefe kana yayiwa motar key yabar harabar
gidan kamar zai tashi sama.
    Wani irin zazzafan hawaye Hafsa taji yana mata zarya a kumatunta,tasan lafinta ne amma
dan me zai kirata da mara hankali,mutumin da take mafarkin gani a rayuwarta ta bawa guri mafi
girma a zuciyarta yau gamon su da zaginta Ya fara,
Shin mene Ma yazo yi gidan?
Jin muryar Aunty shatuh ne Ya saka tayi saurin goge hawayenta tana Mai tsugunnawa domin
kwashe manjan da ya zube.
Tsaye Aunt shatuh tayi kanta tace "naji kamar muryar Abdallah ina sallah ina kuma yake?"
Kamar jira take a tambayeta wane Ya dake ki taji hawaye yana reto a idanunta kamar suna
jira,ƙokarin gogewa ta fara amma Aunty shatuh ta riga da ta gani,
Kamota tayi tace "subhanallah hafsa mene Ya faru,"
Cikin karyayiyar zuciya tace "Aunty ban sani bane na zuba masa manja a jikinsa,Shine ransa ya
baci. "
Da mamaki Aunty shatuh ta Kalleta tace"ran Abdallah ya baci?"

Abun da mamaki,amma dai ba wani abu yayi maki ko yace maki ba dai ko?
Kaɗai kai tayi tace "babu abunda yayi mun Aunty,"
Cikin nutsuwa ta Kalleta ,ta tabbatar wani abun yayi mata amma bata san faɗa dan haka tace
"shikenan maza gyara gurin dan kansa zai dawo,"
Babu musu ta koma ciki dan gyara inda ta bata hankalinta kashe kan Abdallah tana tunanin
menene alaƙarsa da masu gidan?
Tabbas ita ƙaddara a rubuce take babu yarda za'ayi ka chanza ta domin a rayuwarta ta gama
yarda da babu yarda za'ayi ta ga Abdallah ko ta taka inda Ya taka,ashe a kaddararsu zasu haɗu
a yanayin da bata taba tsammanin zasu haɗu ba domin a dukkan tunaninta Abdallah mutum ne
da baya fushi ballantana har yakai ga faɗawa wani magana mara daɗi, Amma Mai take tsammani ?
Shima d'in dan adam ne Mai zuciyar da idan aka daɗaɗa mata zata ji daɗi idan kuma aka b'ata
mata zataji babu daɗi kamar ko wanne ɗan adam.
    Bangaren Abdallah kuwa tunda ya figi motarsa tunanin Hafsat da yanayin da fuskarta ta nuna
mutuƙar tsoro ne kawai yake damunsa ,
Shi ba mutum bane Mai wulaƙanci amma muddin ransa ya b'aci kamar na yau zai faɗawa
mutum maganar da zata damesa sai kuma shi daga baya Ya dawo yana dana sani,
Karamin tsaki yayi yana Mai shafa kansa cike da ɗumbin damuwa ,kai tsaye gida Ya wuce da
zummar idan yaje yayi wanka zai koma gidan Aunty shatuh Ya bawa wanann baiwar Allah
haƙuri idan Ya sameta ,idan kuma bai sameta ba Ya saka Aunty shatuh ta bata haƙuri a
madadin sa, Yana shiga gida sashen sa yayi kai tsaye hannunsa ɗauke de rigarsa da ta b'aci,
Bathroom Ya shige Ya sakarwa kana ruwan mai dumi ,bayan ya gama shirin sa cikin navy blue
kaftan Ya fito domin komawa gidan Aunty shatuh ,yana ƙokarin fita ta kitchen muryar mami ta
Katsesa ,
Sunansa ta kira ,juyowa yayi ya hangota a babban falo a zaune,
Shigowa yayi yana Mai buye damuwarsa sosai yace "Mami ina wuni ,"
Yar ƙaramar fara'a tayi tace zo nan zauna.
    Babu musu yazo Ya zauna a kujerar dake kusa da ita,
Hannunsa ta kamo tace "i saw everything on the live news,caressing hannunsa ta fara tace "ka
yarda dani ko?"
Ƙaɗa mata kai yayi idanun sa na cikowa da Ƙwalla yace "mami na yarda dake fiye da yarda na
yarda da kaina."
Kaɗa kai tayi tana Mai goge ƙwallar dake idanunsa yayin da take ƙokari wajen ganin ta boye
tata karayar gabansa .
    Duk cikin yaranta babu wanda Take tausayawa irin Abdallah duk da kuwa shiɗin yarone Mai
ƙwazo da sanin Ya kamata tun yarintarsa sannan uwa uba tausayi ,
Cikin sanyin murya tace "duk wata tambaya da wani zaiyyi maka Abdallah a kullum ka sa a
ranka kuma ka sani Mamin ka ba mutuniyar banza bace ,sannan mahaifinka yayi zunubai mafi
muni a duniya wanda Ko ni kaina ina tir amma a kullum ban gushe ba wajen nema masa sauki
da rahmar ubangiji,sannan kaima na koya maka haka tun yarintarka sannan ina da yaƙinin kana
masa Addu'ar neman rahma a kullum,"
Goge ƙwallar dake shirin zuba mata tayi tace "kafun Papanku mahaifinka shine mutum na farko

da na Aura saboda soyayya inda shima na yarda kuma na yarda da soyayyarsa gareni gaskiya
ce ,lokacin da na samu cikinka ,irin kulawa da Ya bani ba'a cewa komai duk da yana da yawan
zafi ,tunda na haifeka kuma yake nuna maka soyayya Mai girma wadda a kullum idan Ya
ɗaukeka sai tsoro Ya bayyana a idanunsa wanda bansan na menene ba tunda bani da idea ɗin
abunda yake yi a boye,"
Tabbas samunka nayi imani da Allah ya haifarwa da Hafiz babbar nadama Akan abunda Ya
tsunduma kansa wanda Danginsa suna da babbar gudunmawa wajen faɗawa halaka
,marayane wanda suka wofintar ,bashi da komai bashi da maiyyi masa sannan ko wacce
hanyar samun sa ta toshe.     Katseta Abdallah yayi yana Mai kuka yace "amma mami Ai dan komai nasa Ya toshe Ai Allah
baice ka bijirce masa ba ta hanyar aikata haram,Shin shi ba musulmi bane wanda yayi imani da
ƙaddara Mai kyau da mara kyau".
    Ƙaramun murmushi mami tayi tace "ita kanta wannan da kagani ƙaddararsa ce,ba wai ina
karesa bane dan wani dalili,mutum duk rashin imaninsa bazai rasa wani hali Mai kyau ba
,sannan ina faɗa maka abunda baka sani ba,Nasan hakkin jinin mutum abune Mai girma amma
mahaifinka kafun Ya koma ga ubangijinsa yayi nadama mafi girma ,yaji tsoran Allah wanda ada
Baiji ba a lokacin da Ya tabbatar za'a kashesa ne sannan baya da aikin da zai kalli ubangijinsa
bayan sallah da azumi,Abdallah amfaninka ma mahaifinka a yanzu shine ka kasance iya
tsawan adadadin rayuwarka kana masa Addu'ar samun sauki,
Iya rayuwata da kai nayi ƙokari wajen ganin na maidaka mutumin kirki wanda yazamana kai a
yanzu Malami ne Mai tunatar da mutane wanda babban mafarkine na mahaifinka,
Sannan kuɗin da na baka kaƙi tabawa na cikin dukiyar da Ya bar maka ,zan iya tsaya masa a
ko ina kudin halak ne wanda Ya aje maka da gumin sa ,nasan kasan ta yarda zaka juyasa Ya
amfani al'umma,haka na raini Abdallah na sannan ina alfahari dashi"
    Kansa ya ɗora kan kafaɗarta yace "Mami Allah baya yafe hakkin wani."
Shafa kansa ta fara a hankali tace "nasani amma mucigaba da nema masa rahma bamusan ta
inda Allah zai masa rahma ba,ka sani yawaitar adduarmu da aikin ladan da zamuyi danshi su
biya masa hakkin rai sannan su rage Ya shiga Aljanna."
 

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login