Showing 6001 words to 9000 words out of 73196 words

Chapter 3 - AHALINA (Aure uke series)na chuchu.pdf

Advertisement

08 Jul 2025

2280

ciki inda Anisa ta wani langwab'e kai tana Mai faɗin"interesting a zuciyarta ,mami
na kallanta ta marairaice fuska ,Hannu mami ta miƙamata alamun ta bata yaran ,babu musu ta

b'ata ,kallansa sosai mami Take tana san gano da uban da yayi Kama a zuria'rsu amma
babu,babban kuma abunda Ya kuma ɗaure mata kai shine yarda DNA ɗin yaran yayi matching
dana Nameer, bata tunanin anyi tempering dan a asibitinsu akayi bata tunanin zasu back
stabbing ɗinta haka.
    Papa ya fara barin gurin kafun ta mara masa baya Anisa na biye dasu tana Mai jin daɗin
defeat d'in da ta gani a kan fuskokinsu ,

Kaɗan ma suka fara gani A cikin irin abubuwan da ta shirya masu indai itace.


***********************

    Nameer zaka Auri Anisa nan da sati ɗaya sannan a yanzu zaka raɗa ma yaranku suna dan
nauyin ka ne,idan kuma ban isa ba ban kai nasaka ka ba dan Allah ka bijirce mun.

    A zabure Ya kalli mami yace "Mami wallahi tallahi wannan yaran banawa bane sannan
wallahi ban tab'a ganin yarinyar nan ba ballantana har na bata cikin da zata haifa mun yaro
shima kuma ta hanyar fyaɗe ,mami zaki yarda da wannan yarinyar sama dani da kika haifa ne?

Papa say something.

    Ɗauke kai Papa yayi cos duk yarda yaso Ya yarda da maganar Nameer gaskiyace sai yaji
kamar baiyyiwa Anisa adalci ba sanann yaso kansa .

Jefa masa result d'in DNA ɗin mami tayi tace "Ba yarda nayi da ita sama da kai ba result ɗin da
na tabbatar babu kuskure shi nayarda dashi,zaka faɗi wani abu bayan nan ne,?

Zubewa tayi a ƙasa duk juriyarta ta saka wani irin kuka Mai cin rai tace"kalle ni nan Nameer  ba
sai na faɗa maka ba nasan kana da wayan sanin abubuwan da nayi facing through kafun
Papanku,ko ban kai uwa enough ba wani cikinku Ya fada mu,im a not That Good enough da
kuke san dole sai kun tona mun asiri,dame na rageka Nameer,i gave you a father ,gashi nan
zaune wanda Ya ɗauke ku kamar nasa duk da abunda duniya ta ringa Faɗa bai damu ba,he
gave you guys a Good life and d father's warmth ,bai isa ba?

Idan baku guje mun abun magana domin ni ba zaku guje dominshi,amma sai da kayi yarda kayi
ka nuna mun ban isa na goge jinin Habib a jikin ka ba atleast ka gado wani abu nasa.

    Da sauri Papa Ya ƙarasa gareta yana mai hanata faɗan abunda zatayi dana sani,

Goge hawayenta tayi tana Mai Kallan Papa tace "im Sorry ,kayi haƙuri da abunda Nameer Ya
jawo mana and yau bazaka shigar masa ba cos you've pampered him enough,

Goge hawayeta tayi ta mike ta nufi gurin Anisa ta karbo babyn ta ɗorasa kan cinyar Nameer
wanda yayi saurin tallafesa gudun kar ya faɗi.

Nuna yaran tayi tace He's yours dan haka ka bashi suna sannan dole ka Auri Mamansa for
damage ɗin da kai causing mata idan kuma ba haka ba Zan tsaya mata iya ƙarfina a ƙwatar
mata yancin ta and kasani idan na shiga sai kaje jail na maka alƙawari ".

    Wasu irin hawaye ne ke bi masa kumatunsa a yayin da yake kallan yaran dake cinyarsa yana
Mai jin dama wani zai zo Ya Dafasa yace masa Ya tashi daga mumunan mafarkin da yake yi.

Huɗuba yayi ma yaran a kunne na hagu dana dama kana yace Na raɗa masa suna MAHMOOD
saboda ina fatan nan gaba bazai bari past ɗinsa Ya dame sa ba zai zama abun alfahari Ya
mallaki ma'anar sunan wato wanda za'ana yabawa anan praising ɗin sa,

Sannan Zan Aureta nan da sati kamar yarda kikace Mami,ni nasan Allah a kullum yana tare da
mai gaskiya, makirici da mugunta bata tab'a cin galaba Akan gaskiya,

Kallan mami yayi wadda jikinta yayi sanyi yace "Mami im not like Habib kuma  bazan taba zama
kamar sa ba na maki alƙwari"

    Tashi yayi da mahmood a hannunsa Ya nufi gurin Anisa Ya ɗora mata shi kan hannunta cikin
kulawa yace"Bansan Mai yasa kike yin abunda kike yi ba ,amma ina so ki sani Allah baya bacci
,kin sakani a tsaka mai wahala ke ƴar adam kenan wadda baki iya fidda mutum cikin matsala
,baki kasheshi in lokacin sa baiyyi ba baki rayasa,baki da wuta baki da Aljanna,
Ki shirya dan bazakiji daɗi ba lokacin da Allahn da na yarda zai fitar dani Ya jefaki cikin tsaka
Mai wuya.

Yana ƙarashen maganarsa Ya bar Falon,

Haka zalika Abdallah da Nadiya waɗanda akayi a gabansu ,

Juyawa mami tayi ta kalli Anisa tana Mai murmushin yaƙe tace "ki saki jikinki sannan ki daina
damuwa cos nan yanzu gidan ku ne sannan zuwa gobe ina san za muje tare dan mu gana da
iyayenki Ayi magana ta fahimta,tashi kije ciki idan Kina buƙatar wani abu kiyi magana,

Babu musu Anisa ta miƙe tana Mai jinta kamar wadda aka saka a aljanna cos mission step one
is completed.

Sannan bata buƙatar basu wani recording dan batayi tunanin abun zai zo mata da sauki haka
ba.

********************************************

    Zaune take bakin tashar ɗan marna gefen ta robar furar da tasha daka ,kallo ɗaya zakayi ma
furar kaji ta burgeka,babu abunda Hafsa ta tsana irin fita tallan furar nan da Mama laure ke aza
mata duk da girmanta da mutuncin ta,wani lokacin takanji kamar tayi rebelling amma tunawa da
karatunta yake hanata dan Mama laure ta faɗa ta kuma jadadawa mahaifinta muddin Ya hanata
siyar mata da fura to karatunta zai tsaya duk balai kuma sai ta aurar da ita ga mutum mafi
kaskanci,

Dafata taji anyi wanda hakan Ya fito da ita daga duniyar tunanin da ita shiga,dagowa tayi taga
lawisa ƙawarta da suke zowa gurin tallah tare,

Goge karamar kwallar dake shirin zubo mata tayi tace "lawisa yaushe kika zo",

Gyara zama lawisa tayi tace"ina zaki gane nazo kina zaune Kina tunanin da kika saba na babu
gaira babu dalili ,ni Bansan mainene duwarki ba hassatu,dan kawai kin daukowa Mama laure
tallah?"Ni ki kalle ni mana,Bani ga tsuntsu Bani ga tarko,ni dake tare muka fara karatu tun
firamare amma kina ganina jiya e yau banda ma Zawarci da nake a ƙanƙantar shekaruna ,ni ba
wani kyau ba,wallahi nasani shi yasa kika ga ko tsohon mijinta Halliru zai fada mun mumuna
ban damuwa dan shine kawai maganar da Ya fada ta gaskiya duk da karyarsa ,ki kalli bakin nan
nawa,

Buɗe ƙaton bakinta tayi wanda yasaka Hafsa darawa dan dama abunda Lawisa d'in taka so
kenan,

Ita da lawisa tare suka tashi,duk da ba halinsu ɗaya ba,lawisa na da rawar kai inda hafsa take
shiru shiru babu wata hatsaniya amma hakan bai saka abotarsu ta lalace,suna da banbancin
ra'ayi amma abotarsu gaskiya ce shine gaba,

Kamo hannunta lawisa tayi ganin tana dariyar tace"ke kyakyawace sannan ni na yarda ina
gaban iyayena sanann babu wanda Ya isa yamun keta ,tanan kawai na fiki amma bayan nan ki
ringa duba abubuwa da dama misali Mai zai faru dake nan da shekaru Goma idan Allah Ya
nuna mana,
Wannan sana'ar furar sai dai kiyi labarin ta dan jikina na bani a ofishi Mai gilasai zakiyi aiki, idan
Kika gama karatu sannan insha Allahu sai kin zama matar Malam Abdallah."

    Dariya sosai hafsa ta saka tana Mai jin lawisa har ranta sannan tana mata addu'a Allah Ya
basu rayuwa Mai kyau baki ɗayasu.


Chuchujay ✍
[3/6, 4:54 PM] Chuchujay✍️: AHALINA

    (Siblings of different Father's)

(Book two in Aure uku series)

               By

      CHUCHUJAY ✍

EPISODE 7⃣▶8⃣

Sautin kiɗa ke tashi wanda idan kana saurara muddin ba Mai san damuwa irin wannan bane
tabbas sai Ya hau kanka,magana kuwa idan har ba'a kusa da kai akayita ba itama da ƙara baza
kaji da kyau ba,

Mathew Club kenan " .

Zaune yake bakin Bar hannunsa ɗauke da glass cup ɗin da whiskey ke ciki ,

Dafa sa yaji anyi ,saurin juyawa yayi 'dan ganin wanda Ya dafa sa ɗin ,Yarinyar dake faman
shige masa ce Alicia ,

Zama tayi a kujerar dake kusa dashi tana Mai jan cup d'in whiskey ɗin ta saka a bakinta kana ta
saka ƙafarta tana zungurin sa cikin yanayi Mai daukar hankali.

    Ƙaramun murmushi yayi da Ya fahimci abunda take nufi cos ta daɗe tana hitting nasa sai ya
nuna mata bai ma fahimta ba,

Matsowa tayi daf dashi tana Mai zuwa saitin kunnesa ta raɗa masa "Hit me somewhere nice ,im
sure you must be lonely and i promise no string attached, " .

    Murmushi yayi cos a yanzu Babu wata mace dake gaban sa banda Nadiya ,duk da dama shi
ba mazinanci bane wanda dalilin hakan abokansa ke masa kallan gay cos duk abun mace bata
isa Ya kaita gado ba ,kawai baya da wannan interest ɗin ,wannan shine Babban abunda yasa
baya aje budurwa saboda ko wacce na expecting sex wanda yake finding hard to give ,
Tashi yayi yana Mai aje wa bartender ɗin kuɗin bear ɗin da yasha sannan yace ya bata wata
cos yaga alamun tana buƙata,

Ba tare da ya kuma cewa komai ba Ya juya Ya bar Bar ɗin,

Ya daɗe a motarsa yana tunanin yarda zai shawo kan Nadiya domin kuwa santa yayi masa
nisan da zai iya sacrificing duk wani abu da yake mallakinsa,

Wayan sa Ya ciro a karo na farko zai kirata ba aika mata sako ba,

Ringing uku tayi kafun ta ɗauka cikin sassanyar muryarta tace" Hello its Nadiya Balal speaking ,

Murmushi yayi jin sautin muryarta.

Gyaran murya yayi yace "its Evan and please im Begging you in the name of God not to hang
up on me ,please,"

Shiru tayi tana sauratansa kafin ta sauke ajiyar zuciya tace "5 min lokacinka Ya fara."

    Kamar tana ganin sa Ya sanyaya mirmushinsa Yace "please Nadiya give me a chance,i Love
You With All My being and im not lying,bazan wasa dake da tunani ki ba saboda i find it fun,i did
All i did because i was scared ,i was scared da yarda zaki dauke ni and lastly na tara courage
nazo na sameki please don't do this to us.
Shiru tayi tana mai jin wani irin yanayi a tattare dashi wanda bata san ta daina ji,

Scrunching hancinta tayi tace "where are you?"

Kamar bai fahimci zancen nata ba yace pardon?

Sake maimaita tambayar tayi inda cikin rashin b'ata lokaci yace "na koma Ghana wani aiki Mai
amfani,cos akwai wani project da management ɗinmu yayi signing i was called for it" .

    Danne dariyata tayi gudun kar yajita kana tace "meet me tomorrow at my Office,i want to see
something ,

Kafun yayi magana ta kashe wayan tana Mai murmusawa,

Shima he was dumbfounded da fari kana abunda take nufi yayi hitting masa kai,tana so ta
gwada karfin soyayyarsa, duk da yace mata yana da aiki tana so ta gani ne zai iya sacrificing
Akan soyyayarta. "

Murmushi yayi Yayi dialing number ,an'a ɗagawa yace "i will be flying to Nigeria 'in the
morning,kashewa yayi yana Mai ɗora kansa bisa sitiyarin sa ,hes sure bazai baro Naija ba sai
da amsawar soyayyarsa daga bakin Nadiya."

    Murmushi kawai Nadiya take Akan Swing ɗin dake harabar gidansu hannunta ɗauke da cup
ɗin smoothie hannu ɗaya kuma ɗauke da wayar da tagama da Evan tana Mai tunanin zaizo ɗin
.

Dawowar Abdallah kenan gida wanda ya hangota tun daga nesa murmushin nan ya ƙi daukewa

Akan fuskarta,

Bayan Ya aje motasa Ya tako inda take ,zama yayi a swing ɗin kusa da ita yana Mai ƙarban cup
ɗin hannunta yayi taking smoothie ɗin kana yace "Addyna whats the occasion ?"

Juyowa tayi tana Mai kallansa kafun tace "Abdallah Mai yasa forbidden Fruit yafi ko wanne fruit
daɗi?  "

Kallanta yayi cikin yanayin rashin fahimta kafun yace "saboda its forbidden and ko wanne Abu
Ida aka hana Lokacin yafi komai  daɗi i hope ba ɗaya kike san ci ba,hannu Ya saka a bakinsa
yace"i hope you're not commiting a sin?"

Dariya ta saka sosai ganin yarda Ya waro ido yana kallanta,hannu tasa ta shafa kumatunsa
tace"chill and keep calm bro babu abunda nake mara kyau,cos inada ƙani malami ,sannan
inada Mami da yanzu zata zamar maka tiger ka kasa gane sama ka kasa gane ƙasa,that
woman is very emotional and scary ."
    Relaxing yayi Akan lilan yana swinging ɗinsa a hankali kana Ya saka fuskar damuwa yace
"dole fa mami ta zama emotional cos abunda tayi going through a rayuwanta is not a joke ,so
any disappointment daga garemu babba take ɗaukansa ,And kinsan wani Abu i trust Hamma
duk da evidence ɗin dake nuna sa ,ba wai san kai ba ,but i trust him da duk abinda nake dashi
while wannan yarinyar kwata kwata na kasa samu a wani bangare na zuciyata na yarda da
ita,its just weird."

    "las las wani yana magana a gidan nan,i was scared ne yasa ban magana ba but wallahi ni
natab'a ganin ta a gurin da bai kamata na ganta ba ,na dai rasa a ina ne."

A tare suka juya 'dan kallan Mai maganar,

Fawzan ?

Suka fada a tare ,ƙarasowa yayi Ya zauna a lilan dake kusa da Nadiya yace "i was passing by
naji kuna magana so na ɗan tsaya na saurara bada wani abu ba,"

Dama tsoro nake ko dukkanku kun yarda da mahmood yaran hamma ne shiyasa nima nayi
shiru cos nasan Mami,

Shiru yayi na wani lokaci yana tunani kafun yace "a'h i remembered wallahi a newyork nasan ta
And duk inda nasanta ba gurine Mai kyau ba . "

    Kai Ya akayi kasan ta a guri mara kyau ?

Nadiya da Abdallah suka haɗa baki wajen tambayarsa da mamaki,jin yana ta faman ambatan

ba a guri Mai kyau yasanta ba,.

Kallansu yayi side to side kafun yasa dariya yace "trust me im not doing anything bad there,
Yayar Ummu Aunty sally kawai taishe mutum idan yayi rashin ji a garin nan,Its just that nasanta
fr,amma akwai wani frnd ɗina Uzzy He's a private investigator Yana new York Zan tura masa
hoton ta indai itace zai tura mun data ɗinta duk irin adadin buyan da tayi achan sannan sanin ita
ɗince zaisa muje button ɗin ita wacece kilan har identity' ɗin babynta. "

    Dan shiru sukayi nawani lokaci kafin Nadiya tace"yayi and dole mu aje maganar nan as
secret mu uku kawai ko Hamma kar Ya sani ,And kai kuma Fawzan saura hira tayi dadi ka
faɗama waɗanann abokan haihuwar taka da basu shiru, garin hira ma har su saka Anisa taji ta
dauki wani action cos she's evil."
    Hannu ya saka bakinsa yace "zipped".

Haka sukayi ta hirar yarda zasu haɗa abun,shiru Nadiya tayi da abunda ke zuciyarta cos ko a
lokacin tana bincike ne kan Nameer da rayuwan sa a china duk badan kuma bata yarda dashi
ba sai dai kawai 'dan yiwa Anisa tarko wanda she's sure zata mata,And a yanzu bincikenta yayi
leading dinta zuwa ga abokinsa Salis marafa wanda yake a garin Abuja .
Bincike da tayi akansa yayi leading dinta ga inda zata gansa a ofishinsu na Arch &tch dake
garin Abujan wanda take san zuwa a gobe duk da tasan da zuwan Evan ,Hamman ta first.

      ************************************

    Abinci Nameer yake ci kamar bazai ci ba a restaurant ɗin dake kusa da company ɗinsa
,kallan Fadil yayi yace "kai wai yaushe zaka koma garin ku ne,"

Ƙaramar dariya Fadil yasa yace "maza babu inda zani ,ni da kaduna kuma sai na yi Arziƙi a
garinku 'dan haka kawai ka ƙarbi business proposal ɗina nayi aiki a kasan ka ,i dont mind the
position And yes nasan yan matan garinku akwai kyau,ina so na samu mata anan ko a
ƙannenka ne,dafe kirjinsa yayi yace musamman Sister ɗinka model ɗinnan Nadiya ,maza she's
flawless 'dan wallahi na sameta yini Zan nayi gida".

    Dariya Nameer yayi a karo na farko tun kafin Anisa tashigo rayuwarsa kana yace "kai ɗan
iskane as if kama manta damuwa ta,guy im trapped,"

Serious face Fadil yasa yace " Bansan wanda Ya kawo anisa rayuwarka ba,duk munsan karya
take ,maybe su Mami ɗin ka sun sani amma that Dna man ,yace positive fa,amma ni kasan Mai
nake tunanin ka saci hair d'in yaran a boye muje a sake wani.

Kallansa Nameer yayi yace "wanene zai yarda?"

Maganar 'fa da nake maka a asibintin mu akayi DNA d'in kana tunanin mami zata yarda da
wani?

Cewa zatayi karya nake inasan boye laifi nane,im just confused.

Shiru fadil yayi na wani lokacin kana yace "guy we will sort it out ,zamu gono wacece ita ,batace
yar kano bace,come o'n mu ke da kano da connection zamu gano wacece ita da wanda Ya aiko
ta koma wane."

Shafa kai Nameer yayi 'in frustration kana Ya cigaba da cin abinci sa,

Yana kai loma ta uku Fadil yace"ni Bansan Mai ma zai saka ayiwa Mai mata Aure ba ,"

Take Ya ƙware jin abunda Fadil yace ,da sauri Ya miƙa masa cup d'in ruwa yana Mai faɗin "bi a
hankali fa".

Bayan Ya daidaita ya kalli Fadil yace "a'a duniya ne dani ba mata ba,bana san iskanci fa fadil
,zaka wuce garinku yau ɗinann".

    Dariya fadil yasa yace "maza gaskiya ce daga ƙinta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login