Showing 51001 words to 54000 words out of 73196 words
Chapter 18 - AHALINA (Aure uke series)na chuchu.pdf
Tofa ....
CHUCHUJAY ✍
[3/6, 5:21 PM] Chuchujay✍️: AHALINA
(Siblings of different fathers)
Book two 'in Aure uki series
By
CHUCHUJAY ✍
EPISODE4⃣5⃣➡4⃣6⃣
Lokaci guda ji da fahimtar Jamaimah Ya dauke domin maganar tazo mata ne a bazata
sannan kamar ƙanzan kurege wanda tama san shine ,
Dariya tasa Mai sauti tana Mai Nuna Nadiya ,sai da tayi Mai isarta sannan tace "kalli Nadiya
nasan muna da differences namu tsakanina dake ,and nasan abunda nayi miki ranar da kikazo
bai kamata ba,sannan Kema wanda kika mun bai kamata ba,Ya wuce lets bygones be bygones
,muyi moving on ,amma wannan kam ba Wasa bane ,idan kuma wasane Ya bani dariya ba
sosai ba,so please mudaina kalar wasan nan,im sure sabuwar yar Aiki ce Mami ta bani ko? "
Zama tayi tana Mai crossing Kafarta tace "kin iya zaba mata daki kuwa ba sai nasha wahalar
ƙawala mata kira ba ko ita ta b'ata min lokaci,ni dama nasan Mami zata ji dani,dole gobe na
shirya naje nayi mata godia,"
Wani irin Kallo Nadiya ta bita dashi Kana ta ɗora yatsunta guda biyu gefen kunnen ta tace"are
you nuts"?
Ko kuma wani abu akanki yana miki yumm yumm da yake hana ki gane lissafi?
To bari kiji na faɗa miki,maganar da kike ɗauka kanzan kurege gaskiya ce wadda babu ƙarya ko
wani wasa a cikin ta a yanzu wata daya kenan da Auren su kamar yarda akayi naki babu wanda
Ya sani,to suma haka akayi nasu wanda ita a wannan karan iyayanmu sun sani kuma sun
amince maganar da nake miki a yanzu ma cikin ne a jikinta ,wata guda kinga kuwa tana shiga
tayi tuntube dashi, idan baki fahimta ba bari na fasa miki baƙi ,ita da Hamma Nameer sun san
juna sun zama abu ɗaya,sunyi consummating Auren su wanda a process ɗin aka samu rabo
Mai amfani sannan....
Katsewa maganar Nadiya tayi sakamakon marin da Jamaimah ta ɗauketa dashi ,tana ƙokarin
zuba mata wani Nadiya ta kama hannunta tamau tace "kar ki kuma,idan kuma kika kuma zan
manta ke matar Hamma ce na ɗaukeki da wanda ba'a tab'a miki ba,kuma Aurene yayi idan
kinso ki kashe kanki babu wanda zai hana ki ,na dai san duk jahilcin ki kinsan makomar wanda
Ya kashe kansa,So back off zama kuma da kishiya dole. "
Kallan Hafsa Jamaimah tayi da kyau,wani irin faɗuwar gaba ce ta dirar mata musamman
yarda taga kyanta Mai ɗaukar hankali Ya bayyana a gareta,
A hankali ta fara takawa gun Hafsat tana Mai faɗin"wanne gangancin Ya sakaki Auren
Nameer?"
Mene nayi maki,ban sanki ba baki sanni ba domin mene zaki nemi ki tarwatsa mun farin cikina
kin shiga rayuwata kinyi kane kane har ki san mijina wanda ni ban sani ba har da ciki?
Ke ɗin yar gidan uban wace da har kike Da wannan zarar,wanene ubanki a duniya?
Gaban Hafsa Nadiya ta shiga tace "kar ki kai hannunki jikinta koda kuwa da wasa,domin ita
keda ragamar hamma a yanzu.
Kamar an tsinkuli hafsa tace "to mene kike maganar me kika mun na auri mijinki na tarwatsa
maki farin cikinki,
Ni babu wanda nayi miki a ciki ,ki kalleki da girmanki amma sai ance miki ki kula da mijinki
gudun kar Ya gano wata a waje?
Ni a tunanina duk abunda kike takama dashi bai kai ya farin ciki da bawa mijinki na sunna
kulawa ba ,ubana ba kowa bane kuma ni ba yar gidan uban kowa bace ba aduniya face ɗiyar
manomi wanda ke zaune a ƙauye ,hasalima bani da uwa ,ban samu gatan mahaifiyar da zata
faɗamun dai dai ba,amma dai dai gyargwado nasan dai dai nasan kuma menene hakkin mijina
akaina ,ba wani girman kai tsakanina dashi sannan gaban iyayensa nima ƴace kamar yarda
yake ɗansu,sannan da kike magana ko tunanin na kwacesa Ai abunda Ya kamata Yana samun
mata masu sakin mazajensu da rashin sanin kimarsu kenan,kin sake shine Ya faɗo fatsa ta inda
na nuna masa soyayya da biyyayar da bai samu a gidansa ba sannan insha Allahu ita zan
cigaba da bashi da yardar Allah sannan kema ina fatan zakiyi koyi dani ki sake duk wani
taƙama mu bawa mijin mu kulawa ,ni wallahi ba da sharri nazo gidan nan ba ,burina mu haɗa
kanmu mu koya ga junanmu mu mutunta juna,babu wanda zai cutu,kiyi haƙuri Adda na nasan
kishi yana da zafi,kar mu bari Ya saka muna wa juna kallan mowa da bora.
Wata dariya ke san Kwacewa Nadiya amma ta danneta tana Mai gudun kecewarta
musamman da ta kalli irin reaction d'in dake kan fuskar Jamaimah,bata san Hafsa ta san takan
iya shege ba domin dama fargabar tafiya ta barta da JAMAIMA take ganin bata da magana
sosai ashe ba ƙanwar lasa bace. Wata irin dariya Jamaimah ta saka tace"the guts for me ,just the guts,and the liver,hannunta ta
yarfa tace "Nadiya abuna kuka koya mata ta faɗa mun kenan ko?"
Tafa Hannayenta ta farayi guda biyu tace"kin shiga lion den ki saka a ranki domin wallahi
magananganun nan da kika faɗa mun sai kinyi dana sanin su zan tabbatar da hakan,ba dai ni
kike faɗawa magana marasa daɗi ba ,zaki san kinyi dani gimbiyar babbar masarautar Dilah"
Ƙaramun murmushi hafsa tayi tace "ni ba magana na faɗa miki ba amma idan kin ɗauketa
magana kiyi hakuri ni ba faɗa nazo gidan nan muyi ba ,koda kuwa nace zan faɗa Ai ke Mai
hananice saboda ina ɗauke da cikin abunda kike so,kiyi hakuri Addana ta kaina gimbiya a
babbar masarautar Dilah kawai". Rasa abun faɗa Jamaimah tayi 'dan haka ta yi snapping hannu ta bawa Hafsa wani irin mugun
kallo Kana ta koma kan Nadiya wadda ta ɗaga mata gira guda ɗaya ,ƙwafa tayi kamar an
hurata da iska ta fita a Falon kamar guguwa,
Dariyar da Nadiya ke san riƙewa ce ta Ƙwace sosai har tana faɗuwa,kallan Hafsa wadda ke
faman murmusawa tayi tace"you're Naughty ,kinga fuskar gimbiya kuwa"?
Dariya Hafsa itama tasa kana tace "Ni dai Aunty tsoro nake ji kar cikin dare tazo ta shaƙe ni"
Dariya Nadiya ta kuma sawa tana Mai nuna Hafsa tace "You're kidding me ko?"
Lokacin da kika saka gimbiya dimuwa ban sani ba kinga kuwa idan tazo shaƙeki yau da
daddare ina gidan Papana Babu abunda Yayi mun dumi,wato gimbiya a babbar masarautar
Dilah ko? .
Da sauri hafsa ta taso cos tafara tsorata tace "amma Ai Aunty kina nan fa baki hanani ba ,ni
dai sai dai Nabiki gidan Papan gobe sai na dawo"
Dariya sosai Nadiya tasa ganin tsoron fuskar Hafsa ,zama tayi da ita tace "Look What you did
was amazing like ban ma taba tunanin zaki saka ta wurinta ba a ɗan wannan lokacin,amma naji
daɗi sosai da Ya zamana kina da zarrar domin Jamaimah sai Mai zarra,kinga yanzu da kika
mata haka im sure shakkarki ta shigeta sannan Hamma gidannan zai kwana babu abunda ta
isa tayi miki duk haukanta kuwa ,responsibility ɗinki na kan Hamma wanda im sure zai kula
dashi ɗari bisa ɗari bani da wannan shakkar,dan haka yanzu ki tashi mu shiga kitchen na tayaki
haɗa dinner kafun na wuce ,shima wani babban bangarene na Plan ɗinmu".
Bayan sun gama komai suka wuce kitchen domin haɗa dinner inda Nadiya ta barwa Hafsa
ragamar Girkin ta wuce ɗakin Nameer domin gyara masa,basu ji muryar ko motsin Jamaimah
ba wanda Ya tabbatar musu da bata gidan ne.
Tunda Jamaimah ta fito daga ɗakin hafsa take kiran wayar Nameer amma ƙarshe sai
message Ya tura mata na yana meeting ne wanda Ya sake hassalata ta nufi office din nasa
domin ci masa mutunci a chan,
Tuƙi kawai take amma Kana kallanta ba sai ta faɗa maka tana cikin tashin hankali mara
misaltuwa ba,idanunta yaƙi daina zubar Ƙwalla wanda batayi kokari wajen hanna ƙwallar zuba
ba domin ta yarda da Ya kamata ace ta zuba ɗin,
Kai tsaye tana isa company ɗin Nameer Sashen da zai sadata da ofishin sa ta nufa tunda ba
ranar ne zuwanta na farko ba,kamar ance Fadil Ya ɗaga kai ya hangota ,da fara'arsa Ya ƙarasa
gareta yace "wa nake gani kamar Jamaimah ,uwar gida ran gida idan babu ke babu gida,yana
kai ƙarshen maganarsa yayi dai dai da sauke masa yatsunta da tayi a fuska ta nuna sa da
Yatsa tace"munafiki annamimi,ko me Nameer zaiyyi da sannayyarka tun ba yau ba nasan Ai ku
abokan shawarar juna ne daga Mai kyau zuwa mara kyau shine yau iskancinku da ta'addanciku
zai fara ta kaina ko? "
Zaka wani ɗauko kayan dirty mouth ɗinka Kana wani faɗamun uwar gida ran gida,ko ba uwar
gida ba,to wallahi Ahir ɗinku,Aure na da Nameer babu wanda Ya isa Ya lalata sa idan ba Allah
ba,
wallahi sai na ci muku mutunci tunda kuka ci nawa,har ni za'a kaiwa wannan yar shillar gida
matsayin kishiya?
Aikuwa wallahi sai dai idan Ya zab'a koni ko ita idan ba haka ba kuwa za'a mutu.
Wanene zai mutu?
Muryarsa ta ziyarcesu .
Ɗaga idanunta tayi ta sauke cikin nashi,tsaye daga ɗan nesa dasu hanunsa cikin aljihuns yana
Mai binsu da kallo,
Cikin haɗe rai Sosa Ya tako gurin yace "mene kike yi anan wanda bazaki iya jirana na dawo
gida ba har sai kinzo wurin aikina kin tara mun mutane,Inajin na faɗa miki ina meeting ne".
Wani irin Abu ne Ya tsaya mata a wuya jin abunda Ya faɗa mata wanda Ya sake tabbatar
mata da maganar Hafsa na ta Ƙwace mata shi wanda Babu Ma yarda za'ayi hakan ya iyu.
Ganin bata ce komai ba sai ruwan hawaye dake zuba a idanunta ne Ya saka shi takawa
gareta Ya kamo hannunta Ya jata suka fara tafiya,bai tsaya ba sai da Ya kaita motan da tazo
dashi ya sakata ciki kana yace "bani key"
Kamar tana jira ta jefesa dashi,bai ce mata komai ba Ya tashi motar suka nufi gida,duk tukin bai
ce komai ba ,babu abunda ke tashi a bakin Jamaimah sai sautin kuka Mai cin rai,
Koda suka isa gidan bai ƙasa a gwiwa ba Ya zagaya Ya buɗe mata amma taƙi fitowa,ganin
zata bata masa lokaci Ya sakashi ɗaukar ta bridal style Ya tura ƙofar da ƙafarsa,kamar Mai jira
ta lafe jikinsa ta cigaba da kukan da bai lallashe ta ba.
Bayan shigarsu ciki ɗakinta ya kaita ,yana jin motsin su Nadiya a ɗakin da Ya bawa Hafsa
cos dama yace Nadiya ta jirashi Ya dawo ,
Zaunar da crying JAMAIMA yayi a kan gado Ya tsaya yana Mai saka hannunsa a ƙugunshi
yace "abu na farko da nake san ki sani kuma ki saka a bayan zuciyarki da ƙwaƙwalwarki wanda
shine "bana so koda wasa ki sake zuwa mun office a yanayin da kikaje mun yau ,duk wani
shirme dake kanki ki bari idan na dawo gida kiyi shi amma banda gurin Aikina cos a nan gurin ni
abun girmamawa ne dan haka baki isa Kina ƙasana kije har gurin da nake shugaba ba
tozartani,wannan Ya zama na karshe da zan miki kashedi."
Yana kai ƙarshen maganarsa Ya juya zai bar ɗakin,
Da sauri ta kamo rigarsa ta fashe da wani irin kuka tace "me nayi maka da kake neman kasheni
Nameer?"
Mene nayi maka da kake so ka raba mun rayuwata da gangar jikina,Mai yasa zaka mun
wulakanci mafi muni kamar haɗa jikin ka da wata har kayi mata ciki ,ciki fa Nameer yana nufin
kunyi having sexual intercourse wanda koda wasa baka tab'a attempting sa akaina ba,
Tashi tayi tsaye tana Mai juyawa da kyau tace"ka kalleni mana,Shin banyi tsarin da zaka nema
bane ko kuma bani da ɗaukar hankalin da zaka kusance ni,"?
Wani irin kuka ta fashe dashi tace "wallahi bazai tab'a iyuwa ba ,bazan taba yarda ba
,wancan cikin dake jikin ta sai an zubar dashi,idan kaga an haifesa to na mutu ne sannan
yarinyar chan da take kiran kanta matarka ko da tsiya koda Arziƙi sai tabar gidan nan ,wallahi
bazan yarda ba idan kuma ba haka ba za'a fitar da gawar ta ". Fizage rigarsa yayi yana mata wani irin kallo,bai san inda maganar ciki ta fito ba amma shima
ɗin wani abu ne,tabbas yana mutuwar san Jamaimah ta yarda yake jin bazai iya rayuwa da
kowacce mace ba face ita ,amma halayyar ta abun ƙyama ce wadda take buƙatar gyara muddin
kuwa tana san tsira,gyara tsayuwarsa yayi Ya nemo dukkan wata fitina Ya saka a idanunsa
yace "dan Allah jamaima ki gwada zubar da cikin da ke jikin yar Aljanna kiga yarda zan maki
dukan kato gidan nan ,kina maganar a fitar da gawar ta ko?"
To dan Allah ki taba ta kiga yarda zan baki mamakin da baki taba tunanin zan baki ba sabida
yar Aljanna a yanzu da kike gani itace rayuwa ta saboda ita ɗin macece maratussalaha ,ki sani
kuma ki saka a ranki xama a gidan nan yanzu ta farashi a ƙarƙashin soyayyata da kulawata
,tunda ita ɗin nan da kike gani na farko bata da girman kai,sannan bata da raina na gaba da ita
da abubuwa da dama wanda na san idan kina zaune zaki fahimta ki gane dalilin da yasa ta
mamaye ko ina na zuciyata ta,tsakanina kuma dake babu saki na faɗa maki ina sake faɗa miki
,idan kin ga dama a gobe saboda yar Aljanna ki koma Masarautar Dilah amma fa ki sani da
Aurena akanki zaki koma domin idan kinga Aurena Ya kunce daga kanki mutuwa nayi indai nine
zan sakeki kima cire batun akanki,sannan Zama da yar aljanna dole.
Juyawa yayi ya fara tafiya,cike da balai tace "Ai ni yar wuta ce idan kuma ka ganni cikin
Aljanna ka maidani wuta,kuma wallahi koda kaƙi koda kaso ni kaɗai zaka so a
rayuwarka,sannan wannan yarinyar zata sani"
Dariya Ya saka Ya Kalleta yace "Allah sarki nima bance bana sanki ba Ai kawai dai ina san ki
sani a yanzu Yar aljanna ta ƙwashe rabi da kwata na zuciyata ,ke kuwa sai rabe rabe ,sannan
kema bana fatan ki shiga wuta sai dai idan bakiyi wasa ba a borata zakije aljanna"
Yana kai ƙarshe ya fice,wani iirin ihu ta saka tana Mai watsi da duk wani abu dake kan mirror
ɗinta .
Kai Tsaye Nameer na fita ɗakin Hafsa ya shiga ,
Yana shiga ya fashe da wata irin dariya ,duk da Nadiya bata san Mai Yakewa dariya ba amma
haka dan tasan Jamaimah tayi wani abun,
Kallan Hafsa yayi yace "ina kuka samo maganar ciki?"
Dariya Nadiya ta kuma darawa da tace "Ai ta gama ihunta a haka zata haƙura ta sauko ,ce
mata nayi Ai ciki ne da hafsa".
A tare suka dara suna maida zancen
CHUCHUJAY ✍
[3/6, 5:21 PM] Chuchujay✍️: AHALINA
(Siblings of different fathers)
Book two of Aure uku series .
By
CHUCHUJAY ✍
Episode 4⃣7⃣➡4⃣8⃣
GARABASA GARABASA BONANZA
2024 Shin kuna sane da ban bada garabasa ba?
To ku kwantar da hankalinku ga chuchu dai tazo maku da garabasar sabuwar shekara,
Shin kin fara kin fara karanta YAR AREWA labarin captain Jasmine Bilal shareef da captain
Shuraym Sadauki,
Ta tashi da mafarkin zama pilot a yayinda shi da yake kan aikin yake kusheta Akan tayaya ɗiya
mace Yar Arewa zata zama matuƙiyar jirgin sama?
Soyayyar da ta shiga tsakaninsu ba tsammani wadda take ƙokarin danne kiyayya .
Ko kuwa kin fara karanta littafin ABLA ADNAN ne labari na matashiyar budurwa wadda bata
barin taƙwana ,budurwar da tazamarwa masu kuɗin gaske barazana ,
Shin baki fara karantashi ba ko kin fara kin tsaya saboda kuɗin Ya maki yawa?
Maza zo na maki sauki ki ji yarda soyayyar ABLA take farawa da PRINCE
WASEEMUDDIN,kowa na kiranta karuwa harda shima Shin ita ɗin karuwarce?
Maza garzayo gareni ka samu amsa,
Normal price na YAR Arewa book 1&2 N700
ABLA ADNAN N700 complete amma a wanann lokaci na garabasa kuzo na baku ,Yar arewa
1&2 da ABLA adnan Akan farashin naira N600 dukka biyun ɗari shida kacal ragin N800?
Kamar yayi yawa amma a haka dai Zan baku wannan garabasar ,masu cemun sati yayi kaɗa
ga shi kanan sai 1st February 2024,Ya kusa karewa 'fa.
maza kar ayi baku.
0264267657
Gt bank
Amina jamil adam.
09058191213
Dm me
ِ
مْسِب ِ
هَّللا ِنَمْحَّرلا
ِ
ميِحَّرلا
Tunda Abdallah ya koma gida hankalinsa yaƙi kwanciya baki ɗaya ya karkata gun Hafsa,Ya
gama yarda da yana santa ,idan da za'a bi ta tashi kuwa wannan tsarin da ba'a yisa ba domin
hankalinsa bai gamsu da hakan ba,
Wayarsa Ya ɗauko yama rasa abunda zai danna a ciki,numbernta da yayi saving da Heartthrob
Ya shiga yana tantama na Ya kirata ko a'a ,daga bisani kuma zuciyarsa da abunda yake so yaci
galabar sa yayi dialing numbern nata ba tare da yayi tunanin dare ne ba domin a lokaci karfe
sha biyu na dare ,a ringing ɗin farko ta dauka cikin baccin da Ya fara ɗaukarta Kaɗan
tace"Assalamu alaikum"
Ƴar ajiyar zuciya yayi daga ɗayan bangaren yace "wa'alaikis salam,na tasheki ko ?"Kimun
afuwa nakasa samun nutsuwa ne sannan baccin yaƙi yazo wanda na alkantashi da rashin jin
muryarki Mai daɗi da sanyi,ina fatan banyi laifi ba
Murmushi tayi kamar yana ganinta tace "aikam Bakayi laifi ba domin ni kaina baccin ne kawai
Ya sace ne amma tsorone fal raina kar matar Hamma Nameer ta zo ta dakani cikin ɗaki babu
wanda Ya sani.
Dariya yayi yace "bazata ma fara ba ,idan kuma ta fara daka mun abar kaunata to tabbas zata
ga fushin Abdallah sosai,"
Cikin rashin sanin abunda zata faɗa kuma tace "Ai nama kulle ko ina and Aunty Nadiya ma ta
jima kafun ta wuce sannan ta daɗe tana min hira a waya har na samu nayi baccin nan.
A hankali Ya ƙwantar mata da hankali sannan