Showing 72001 words to 73196 words out of 73196 words

Chapter 25 - AHALINA (Aure uke series)na chuchu.pdf

Advertisement

08 Jul 2025

2288

rage wanda shine kuyi hakuri ku karbi Aurenta domin kuwa a tare da ita
akwai rabon shi Nameer din,gashi nan bayan wautar da suka aikata bashi da wani aibu sannan
ba wai dan yana jikana Bane kuje kuyi bincike idan kukaga halayyarsa ta banza to ni da kaina
zan saka 'ya sauwakewa ita Jamaimah ɗin,a yanzu kuwa gata nan yarda kukace haka za'ayi
domin hakkin ku ne.

A yarda sukayi tunani iyayen Jamaimah zasu dauki abun ba haka Bane domin kuwa sosai suka
nuna farin cikinsu da 'ya zamana Jamaimah ta faɗa hannunsu sannan suka

Nuna mutuƙar dana sani wajen hanyar da suka ɗauka na nuna mata soyayyar banza da izzar
mulki wanda 'ya so kaita ga hallaka.

Bayan sadda zumunci wanda 'ya wakana tsakanin AHALIN biyu iyayen, da samun
daidaituwa iyaye Nameer suka wuce suka barshi nan da matarsa akan su kwana biyu inyaso
idan zasu koma NIGERIA iyayenta su bisu suga inda ɗiyarsu take.

Bayan komawarsu gida tafiyar Abdallah da matarsa Hafsa ta kama zuwa saudiyya inda 'ya
saka ranar zuwa Katsina domin gaida iyayenta duk da kuwa mahaifinta yace kar 'ya damu
amma ganin chanchantar hakan yaga 'ya kamata ace sunje ɗin,

Yan uku suka fara wucewa Newyork kana Abdallah da hafsa da Aunty shatuh suka tafi garinsu
Hafsa,

Sanin zuwansu 'yasaka Malam Balarabe yin nan da nan ganin 'ya nemawa yarinyarsa mutunci
dan bayan bikinta har gyaran gida yayi,abinci 'ya bada akayi masa a waje sanin wacece laure
matar da bata sake hali,habaici kuwa da zage zage Babu wanda bata saki ba amma yayi mata
banza tunda yasan a wannan gejin sai dai tayi zagin domin kuwa yafi karfinta sannan duk wani
abu da take masa kuwa ya karye domin ɗiyarsa yake san dama 'ya nutsar gidan miji yayi Aure
kuma burinsa 'ya cika Alhamdulillah Auren kawai 'ya rage masa 'dan har mata 'ya samu.

Tarba ta mutunci yayi musu kamar shine macen gidan ,kafun kace mene labarin Zuwan Hafsat
'ya karaɗe gari wanda 'ya jawo yan tsurku zuwa ganin ta,Hasiya dake zaman zawarci gida kuwa
babu abuunda take ma Abdallah sai shisshigi tanan addua Allah yasa cikin shishshiginta tayi
wuff da wani abokinsa,
Motel Abdallah 'ya samawa kansa da kyar duk yarda kuwa Malam Balarabe yayi ya kwana
gidan 'dan suna da masauki amma yarda Hasiya ke shige masa hankalinsa bai kwanta da
yarinyar ba 'dan haka 'ya tafi akan da safe zai dawo inda a ranar dama zasu wuce,Ƙawayen
Hafsa da dama sunzo ciki kuwa harda hauwa da Lawisa da tayi aure a doro,tsokananta hauwa
ta ringayi akan ta kwace mata crush dama shi tabi Adamawa.

Washe gari da rana suka wuce bayan sha tara ta arziki da Abdallah yayi ma yan gidan da
yan gari,bayan komawarsu Adamawa kuma da kwana biyu suka wuce Mecca inda suka bude
sabuwar rayuwarsu cikin Aminci da ƙauna.

****************************

FOUR YEARS LATER.

NEWYORK CITY.

Green Sea palace .

Organized gurine wanda Sai ka tara zaka kamashi saboda tsadarsa,ammaa a guri na zuri'ar

Tasu its just a piece of cake ,baki daya AHALINSU na gurin wannan ƙaramun taro da Grandpa
Bulama 'ya haɗawa yan uku dan murnar gama karatunsu a cewarsa "a kasar 'da suka kare
karatu anan 'ya kamata a tayasu murna ba wani guri ba dan haka suna gama taronsu na
makaranta wanda kwansu da kwarkwatarsu suka je suka nufi Green Sea ,Nameer yazo da
Twins ɗinsa"Afra da Afreen,Abdallah yazo da yaransa Muhammad,Nadiya tazo da yarinyar ta
Fatima,yayin da Abbu,Ummu ,Affan da Afnan ƙannen Imam paki baki daya suka halarta,ciki
kuwa harda gayyar gidan Grandpa Bulama da masu so da wanda babu yarda zasuyi amma a
fuska bazaka ce ba,dama ko wanne AHALI ya ƙunshi hakan addu'ar mu kawai shine Allah ya
sake haɗe mana kan zuri'a baki ɗaya, "

Washe gari suka wuce Nigeria baki ɗayansu .

Zazzaune suke lokacin dinner baki ɗayasu da ƙarin jikoki domin yin break fast,Afra yarinya yar
kimanin shekara huɗuce ta kalli Muhammad Wanda ke tsaye cike da iyayi tace "Ya Muhammad
ijlis mana "

Baki ɗayansu suka saka mata dariya banda ita da ta haɗe rai,cike da pouting lips ɗinta irina
mahaifiyarta Jamaimah cos ita take kama da ita tace"mene kuma kuke mun dariya ai kunsan ba
wani hausa yake ji ba, "

Zama yayi yana mai kallanta cikin hausarsa da bata fita da kyau yace "Ummi na bani hausa"

Dariya sosai sauran jikokin suka saka suna tsokanarsa har sai da Mami tasa musu baki suka
bari kana suka nutsu suka fara cin abincinsu gwanin ban sha'awa.

Rayuwar cikin Ahalinsu rayuwace gwanin ban sha'awa da zaman lafiya duk da kuwa ko wacce
zuri'a ta kunshi up and downs nata amma Alhamdulillah bangaren haɗe kansu abun gwanin
burgewa,a gidan Nameer Yana zaunne lafiya da matarshi da yaransa wanda bayan haihuwansu
ta fara aiki a company dinsa yayin da Nadiya da mijinta Ahmad da yarinyarsu suma suke aiki
cikin haɗaka,bangaren Su Abdallah kuwa bayan haihuwarta 'ya maida ta makaranta nan cikin
garin Mecca inda ta cigaba da karatunta wanda ta dauko farko,

A haka rayuwa ta cigaba da tafiyar musu in which they live happily ever After.

ALHAMDULILLAH anan na sauke biro na daga kan takardar littafin AHALINA ,

Ina mai mutukar nuna godiyata gareku masoya da irin dumbin kaunar da kuke nuna mun,ina
sanku fisabillilah sannan na sadaukar da wannna littafi daga AURE UKU zuwa AHALINA
gareku masoya domin idan baku Babu ni,

My wattpad family mafari na ,ina mutuƙar maku godiya inda kuka kaimun AURE UKU
12.5k,AHALINA 2.2K ah cikin kwanaki kaɗan fa my series book 'ya samu view haka ,i cant
thank you less,nagode.

Kuskuren dake cikin Allah ya yafe mun idan kuma rubutuna 'ya bata maka ta Wata sigar ina
neman afuwa cikin rashin sanine,

Ida kuma ya amfaneka ko ya nishaɗantar da kai komai kankantarsa to kamun addua .

Yauwa kafun na manta zan amfani da wannan damar wajen sanar daku zuwan sabon littafina
amma na kuɗine, amma fa a wannan karan a complete zaizo ma'ana zaka iya siyan complete
idan baka san page by page ,book 1 free book 2 na kuɗi,

Sannan a wannan page din inasan jinjinawa masu tsayawa suyi comment inajin daɗi sosai
Allahu ya barmu tare,wadda kuma ya cinye comment section baki ɗaya itace UMMU SUBAI'A
sharhinta yana mun daɗi kuma yana karamun zeal na sake dagewa wajen rubuta abunda nake
rubutawa ,daki daki sharhinta yake fita yake sani gyara abubuwa da dama,nagode sannan
tukuicinki shine littafin gaba da zaki karanantashi baki ɗaya a kyauta idan Allah ya aramana
rayuwa bayan sallah insha Allah.

Asha ruwa lafiya and barka da Sallah 'in advance

Nice taku a kullum

Amina Jamil Adam

Mrs Buhari

Ommu Mahnoor

CHUCHUJAY ✍️

Duk ni ɗaya��.

Follow me on my media platforms

Wattpad page:CHUCHUJAY

X:Ameenatourh_jay

IG:Chapter_green_

Fb:Ameeatourh jameel

Ku huta lafiya❤

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login