Showing 48001 words to 51000 words out of 73196 words
Chapter 17 - AHALINA (Aure uke series)na chuchu.pdf
yace wani abu Nadiya yace "Ai hamma yama samu".
Buɗe baki Nameer yayi kana Ya saka dariya yana Mai miƙawa Ahmed (Evans )hannu yace
"shikenan ta koreni ,Allah Ya bada sa'a abokina dan na fahimci ƙanwata nan ta gama faɗawa,"
Gaisawa sukayi inda Ahmed ke faman washe masa haƙora ,sallama yayi musu yana Mai faɗin
"sai kinzo Nadiya da yarinyar da kikayi magana ".
********************
Bayan komawar Nadiya gida da dare bayan sun gama dinner tabi mami dakinta danyi mata
maganar Evans,
Kallanta Mami tayi lokacin da tayi sallama a ɗakinta,
Cigaba tayi da cire agogan hannunta tana Mai fadin"idan kinsan maganar Nameer ce ta kawo ki
spare me,
Shigowa tayi ciki ta zauna tana Mai matsa mata hannunta Kana tace"Mamina yau ba maganar
hamma bace maganan tawace sannan nasan zakiyi farin ciki sosai da ita,"Ɗan kallanta mami
tayi tace "inaji sannan kiyi magana softly kar ki tashi mahmood yanzu yayi bacci"
Kallansa Nadiya tayi ganin yarda yayi bul bul abunsa tace"yaran Mami sai wani fresh yake yi
abunsa ."
Cikin rage murya tace"Mami kinsan yanzu im 29 ba?"
Sannan nayi achieving komai da yakamata mutum a shekaruna yayi ko?
Kallanta da kyau Mami tayi tana Mai san fahimtar inda maganar Nadiya kesan tafiya kafin
tace"kin samu mijin aure kenan,to kice Ya turo".
Yar karamar dariya Nadiya tayi cike da jin kunya tace "Kai Mami "
"Ehen ai idan kaji budurwar yarinyan ka ta fara magana haka to Aure take so ,yanzu haka nima
tawa budurwar dake gabana Aure take so,juyowa Mami tayi tana Mai faɗaɗa fara'ar da Rabon
da tayi ta kwana biyu ,daga mata gira ɗaya tayi tace "uhum ina sauraranki wanene lucky guy
din". Ƙasa tayi da idanunta tace "Mami na ta kaina you got me,sunansa Ahmed and ghanian ne
mahaifiyarsa kuma yar Nageria ce amma inyamura ce".
Ɗan shiru mami tayi na wani lokaci cikin fuskar da zakace abun Ya daki mutum tace"Mai ya faru
da dukkan Hausawa da fulanin Nigerian da sai Kinje har ghana kin zaƙulo mana ɗan ghana irin
inyamurai ni Umaimah ,"
Cije lebe Nadiya tayi tace "Ai mami bama wannan ba ,he was a Christian amma Ya musulunta
sannan yanzu haka suna nan Nigeria da mahaifiyarsa akan tana san ganin iyayena"
Gyara zama Mami tayi tace "interesting,yanzu maganar da kuke yazo da Mamansa nan dan
taga iyayenki ,ita ma musulmarce sannan a danginsu mace ke zuwa ganawa da iyayan mace
,bani nasha".
Sosa ƙeyarta tayi tace "ita ba musulma bace 'infact dukkan iyayensa ma babu musulmai shi
kaɗai ne musulmi shima kuma haɗuwa dani Ya saka Ya musulunta".
"Uhum ,kice saboda ke Ya musulunta,abun gwanin dadi na kwana biyu banji labari Mai ban
dariya da daɗin wannan ba,na kasa yarda Nadiyata ta faɗa tarkon mayaudara,dama da popcorn
munayi munaci cos this is hilarious, "
Ganin da gaske Mami bata ɗauki abun gaske ba Ya saka Nadiya saka serious face tace "mami
da gaske nake ba wasa ba Allah,Bana boye miki komai 'dan baki koya mun yi miki boye boye
ba shiyasa a wannan karan bazan fara ba,na amince da shi Mami sannan na gamsu da cewa
musuluncinsa ba domin Ya yaudareni bane Allah ne Ya kirasa Ya zabesa And Sanin wacece ni
yasaka ban tab'a bashi dama ko na nuna masa amincewata da soyayyarsa ba har saida na
tabbatar da cewa ni dashi akwai hallarci,
Bugu da ƙari kuma nasan AHALINA ba mutane bane masu duba banbanci na Al'ada muddin
kuwa addinin mu abu ɗaya ne dashi kawai nayi amfani wajen zuwa sanar dake kai tsaye ba tare
da Naji wani abu ba Mami.
Shiru Mami tayi tana kallan ta Kana tace"daɗina dake akwai iya tsara zance muddin kuwa
Kina san abu,Naji dai yanzu gobe idan Papanku Ya dawo tunda bazani asibiti ba zamu zauna
mu tattauna akan maganar sannan mu samu Daddy muyi magana dashi bayan haka sai su zo
mu gansu nan da kwana biyu nasan dole Papanku bazai taba bada goyan bayansa ba ɗari bisa
ɗari muddin baiyyi bincike sosai akansa ba da kuma danginsa".
Rungume ta Nadiya tayi tace "Allah Ya saka maki da gidan Aljanna Mamina uwa ta gari,"
Shafa bayanta mami tayi tace "uhum uchenna "
Dariya suka saka a tare inda Mami ta daɗe tana nazarin wannan baban al'amarin da Nadiya
tazo dashi.
Kamar yarda tace sai tayi magana da Papa bayan dawowarsa kuwa ta zauna tana Mai
zayyana masa abunda ke a aƙasa ,ɗan jim yayi kafun yace"kuma tace tana san yaran?"
Kaɗa kai mami tayi tace "haka nan tace sannan a idanunta ma na gano hakan ,kawai dai ina
jin tsoron Abunda zaije Ya dawo ne wanda Ya shafi banbancin al'ada da kuma addini wanda
kaga 'fa yaran nan shi kaɗai ne musulmi a danginsu wanda kuma sanadiyar ita Nadiya ɗin Ya
musulunta". Tabbas yasan maganarta da ƙamshin gaskiya,amma komai a rayuwa idan zaka duba ka duba
positive side ɗinsa,
Cikin Hikima ya ƙwantar mata da hankali inda ya sake kwantar mata hankali akan zai yi bincke
Mai kyau akansa 'dan haka suka bawa Nadiya dama akan yazo ɗin kafun su kai maganar gurin
su Daddy,
Ille kuwa kamar yarda Papa ya bukaci ganin Evans haka yazo cikin shiga ta mutunci da
kammala,a hirarsu da sukayi mai tsiya Papa da Mami suka nuna gamsuwatsu da Shi 'dan haka
babu bata lokaci suka kai maganar gurinsu Daddy waɗanda suma bayan ganawa da
mahaifiyarsa suka gane ita ɗin babbar mutum ce Mai fadin zuciya 'dan haka suka rufe babi na
ƙabilanci da banbance Ra'ayoyi da Al'ada suka ƙarbi Evans da zummar zasu fadaɗa bincike
sannan zasu nemesu domin tsayar da magana ɗaya.
Chuchujay✍
[3/6, 5:20 PM] Chuchujay✍️: AHALINA
(Siblings of different father's)
Book two in Aure uku series
By
CHUCHUJAY ✍
EPISODE 4⃣3⃣➡4⃣4⃣
GARABASA GARABASA BONANZA
2024 Shin kuna sane da ban bada garabasa ba?
To ku kwantar da hankalinku ga chuchu dai tazo maku da garabasar sabuwar shekara,
Shin kin fara kin fara karanta YAR AREWA labarin captain Jasmine Bilal shareef da captain
Shuraym Sadauki,
Ta tashi da mafarkin zama pilot a yayinda shi da yake kan aikin yake kusheta Akan tayaya ɗiya
mace Yar Arewa zata zama matuƙiyar jirgin sama?
Soyayyar da ta shiga tsakaninsu ba tsammani wadda take ƙokarin danne kiyayya .
Ko kuwa kin fara karanta littafin ABLA ADNAN ne labari na matashiyar budurwa wadda bata
barin taƙwana ,budurwar da tazamarwa masu kuɗin gaske barazana ,
Shin baki fara karantashi ba ko kin fara kin tsaya saboda kuɗin Ya maki yawa?
Maza zo na maki sauki ki ji yarda soyayyar ABLA take farawa da PRINCE
WASEEMUDDIN,kowa na kiranta karuwa harda shima Shin ita ɗin karuwarce?
Maza garzayo gareni ka samu amsa,
Normal price na YAR Arewa book 1&2 N700
ABLA ADNAN N700 complete amma a wanann lokaci na garabasa kuzo na baku ,Yar arewa
1&2 da ABLA adnan Akan farashin naira N600 dukka biyun ɗari shida kacal ragin N800?
Kamar yayi yawa amma a haka dai Zan baku wannan garabasar ,masu cemun sati yayi kaɗa
ga shi kanan sai 1st February 2024
maza kar ayi baku.
0264267657
Gt bank
Amina jamil adam.
09058191213
Dm me
Wannan page ɗin sadaukarwa ne ga masu comment na wannan littafi wanda ina mutuƙar jin
dadin sharhin ku,kuyi yarda kuka ga dama dashi.❤
Ina mutuƙar kyaunarku.
ِ
مْسِب ِ
هَّللا ِنَمْحَّرلا
ِ
ميِحَّرلا
Adda wai maganar me kikeyi cos wallahi bana fahimta
Kina nufin Hamma Ya Auri Mai Aikin Aunty shatuh fa kike magana ,
Abdallah Ya faɗa da mamaki yana Mai kallan Nameer da Nadiya da Aunty shatuh ,
Dafa sa Nadiya tayi tace "kana san tane sai kayi magana ,beside maganar da ake ba Auranta
Hamma zaiyyi ba illa za'ayi pretending ne akan Ya Aureta d'in amma ba Auren nata zaiyyi ba ka
ƙwantar da hankalinka."
Wani kallo Abdallah ya bata cike da gardamar kalmarta na yana san Hafsa yace"ba wai
maganar ina santa ake ba amma magana ce ta Menene dai dai gudun kar a shiga hakkin Addini
sannan ita hafsan ta amince baza'a shiga hakkinta ba "
Dariya Nameer yasa yace "ka kwantar da hankalinka yallabai ,babu wanda zai shiga hakkin
Addini insha Allahu,"
Shiru yayi bai sake cewa komai ba amma tabbas zuciyar sa bata kwanta da wannan tsarin da
Nadiya ta tsiro ba,
Aunty shatuh wadda ta kula da rashin nutsuwar Abdallah wanda tun tuni tasan yana san
hafsa tace "Nameer wannan abun Ya zamana business ne straight ,ka samu abunda kake
bukata ga matarka ka bama yarinya kuɗinta ta dawo nan cos kasan da kyar na samu ta amince
it took me great effort " Kaɗa kai yayi yana Mai faɗada murmushinsa yace "na baki assurance ɗina Aunty nasan
yarda Jamaimah bata san kishiya bazai dauke mu lokaci Mai tsayi ba zata dawo gurin ki cos
naga alamar ke kanki baki san rabuwa da ita ,ni nama ƙosa naganta yarda Aunty ta gama kafa
mun shariɗai akanta. Suna wannan maganar sallamar Hafsa ta katse su,
Wani irin yanayi Abdallah Ya tsinci kansa ciki lokacin da Ya saka idanunsa akanta domin ganin
yarda ta sake yi masa wani irin kyau Mai ɗaukar hankali ,."
"Masha Allah "
Cewan Nameer wanda shima hafsa ɗin yake kalla wadda keda wani irin sassanyan kyau,
Da sauri Abdallah ya kalle sa ganin yana kallanta,haka kawai yaji wani irin kulu a wuyansa Ya
tsaya cos shi kansa bai san yana san Hafsa har haka ba sai yanzu da aka kawo wannan
maganar ta zuwan Hafsa gidan Nameer ,
Zama tayi kasa bayan shigowarta tana Mai gaida kowa cikin jin nauyinsu,
Kallanta Aunty shatuh tayi tace "yarinyata taso kizo kusa dani ki zauna,"
Cike da jin kunya tace "Aunty nan ma yayi".
Sanin bazata dawo ɗin bane Ya saka Aunty shatuh cewa,zan baki kuɗi kuje ke da Nadiya ki
zabi kayan da kike so saboda wannan aikin yana bukatar chanjin wardrobe kinga a matsayin
Mata zakije gidan,kar ki ɗauke shi matsayin kayanki basuyi ba ,kinga Ai amarya da sabon kaya
aka santa, Sannan zaku tsaya ku siya waya domin naga ta hannunki karamace dama tun tuni ina da niyyar
siyan maki waya,Mai ne kuma kike buƙata?
Dan shiru Hafsa tayi ba tare da ta gamsu da maganar kuɗin da zasu kashe mata ba
tace"Aunty nagode da komai Allah Ya saka da Alheri,amma Aunty bana san kashe kudin da
zakuyi akaina ,iya kulawarku ma kawai ta wadatar sannan ni zanyi aikin nan ne badan abiyani
ba Ai alherinki gareni yafi kudi duk yawansa,siyan kayan kuma tunda kince dole ne ni 'ina gani
ba sai na bita ba komene aka siya dai dai ne,sannan ina san kafun naje gidan naje gurin inna
na gansu tunda kince kar na faɗa mata wanda nima nasan baza taji daɗi ba."
Cikin ƙwantar mata da Hankali Aunty shatuh tace"shikenan Nadiya zata je idan yaso sai
Nameer Ya kaiki gida daga chan ki wuce."
Charaf kamar Abdallah na jira yace"Ya bari Aunty zan kaita idan yaso sai na aje ma Nadiya ita
sai ta wuce da ita gidan Hamma cos kinsan baiyyi ace shi Ya tafi da ita gida ba"
Sanin hankalin Abdallah ba kwance yake ba da wannan tsarin yasa Aunty shatuh cewa"kaga
shikenan ma hakan ma dabara ce".
Nameer ne Ya fara tashi yana Mai faɗin"dama kuwa ina da wani Aiki Mai muhimmanci tare da
Fadil bari na fara wucewa,kallan hafsa yayi cike da sigar tsokanarta yace "sai mun hadu a gida
amaryata sannan kisa 'fa aranki matata lioness ce Allah yasa kin shirya"
Dariya Aunty shatuh da Nadiya suka saka banda Abdallah wanda maganar Nameer ta tsaya
masa a wuya duk da kuwa Yasan maganar gaibu ce,
Sallama Nadiya ma tayi musu inda Abdallah Ya tashi yana Mai cewa Hafsa ta samesa a mota,
Ya daɗe yana shawara a zuciyarsa akan ya faɗa mata yana santa wata zuciyar kuma na faɗa
masa Ya jira ta gama aikinta gidan Nameer,
Yana wannan shawarar Ya hangota cikin milk hijab ɗinta wanda yasha guga duk da kuwa ya
sha jiki,tafiya take cikin nutsuwa wadda ke ɗaukar hankali Mai kallo,
Fitowa yayi da sauri Ya buɗe mata kofa,cike da kunya ta shiga tana Mai faɗin "na gode."
Rufewa yayi Ya zagaya Ya shiga seat ɗinsa Ya zauna,rufe idanunsa a hankali yayi kana yayiwa
motar key Ya tashe ta suka fita a cikin gidan.
Tunda suka fita titi babu wanda yayi magana ,a karo na farko ya Kalleta yace ina zamuje hajiya,
Murmushi tayi a karo na farko tace "da naga ka ɗauki hanya nazata kasan unguwan namu
Ai,tudun wada ne,"
Shafa sajensa yayi yace "kinga kuma na dauki hanya dai dai wanda zuciyata ta bani hakan,Mai
kike tunani akan zuwa gidan Hamma? "
Ya jefa mata tambayar cikin maganar.
Kallan waje tayi tace "to gani nan dai ,babu abunda Aunty zata nema gurina na kasa yi mata
domin a iya zamana gidan ta babu cuta sai Alheri,shi yasa da ta mun magana na yarda tunda
nasan bazata cutar dani ba.
Kaɗa kai yayi yace "Yayi,nasan dai baki da saurayi,Mai zai hana ni nazama saurayinki tunda
kinga ni Abdallah na kamu da sanki mara misaltuwa,ina sanki da yawa hafsa sannan san da
nake miki soyyayace wadda nake so muzama guda ta hanyar Auren sunna'ar ma'aiki,banyi
niyyar faɗa miki ba amma ganin yanzu zaki wani gurin da babu damar naje kar na b'atawa
hamma na plan dinsa Ya saka nake sanar dake mene ke cikin zuciyata ,sannan ban ce dole ki
amsa mini yanzu ba ,kije kiyi tunani koda kuwa zuwa lokacin da zaki bar gidan Hamma ne,ina
san ki je gidan ne da sanin ina fitinar sanki Hafsat ".
Wani irin maƙwat ɗin yawo ta haɗiya da ya kai Ayar maganar domin jinta take kamar a
mafarkin da idan akace ta tashi zata firgita ta miƙe,wai ita Abdallah Hafiz ke furtawa kalmar
so,baki ɗaya jinta tayi kamar a saman ruwa ,
Dan leko fuskarta yayi,da sauri ta Juyar da kanta tana Mai yin ƙaramun murmushi,
Murmushin shima yayi yace "gamu dai mun shiga tudun wada ina zamuyi,"?
Cikin kwatance suka isa gidan nasu,tana ƙokarin buɗe kofar ta ɗago ta kallesa tace"bazaka
shiga ba?"
Girgiza mata kai yayi yace "Inajin kunyane ,zan shiga amma ba yanzu ba sai ranar da kika
amsa mun soyayya ta kinga sai na shiga kaina a sama Ina da soyayyar Hafsa na."
Saurin bude kofar tayi cike da jin kunyarsa ta shiga gidan.
Girgiza kai yayi yana Mai binta da kallo yana jin wani nishaɗi yana ratsasa,ko ba'a faɗa masa
ba yasan cewa shi Mai sa'a ne gurin hafsa .
Baya wasu mintuna ta fito da Muhammad yana rike da yar karamar Jakarta wadda ta karba
kafun su karaso bakin motar tana Mai dagaa masa hannu,
Koda ta iso motan Ya kunna sautin qur'ani yana saurare,da sallama a bakinta ta shiga,
Ido Ya ƙura mata,dauke kanta tayi cikin wata irin murya da ta tafi dashi tace "ni kadai na kallo
na haka bana so".
Daga hannunsa yayi cikin surrender yace na bari gimbiya,key yayiwa motar suka bar gurin,
Kai tsaye gurin siyan waya suka nufa Ya siya mata tsaleliyan waya da sim card wanda a take
akayi register,
Da kyar ta karbi wayar shima sai da Ya haɗa da dabara,bayan sun gama Ya kaita office d'in
Nadiya ,kamar kar Ya wuce Ya barta ,amma hakan nan gudin kar Nadiya ta gano wani abun Ya
wuce.
****************************
Kai tsaye Nadiya da Hafsa suka nufi gidan Nameer wanda kafun suje ta kirasa ta sanar masa
da zuwansu,
Dama kafun su wuce sai da ta kaita aka gyarata tasha lalle sannan tasa wani mayyar TURKISH
abaya Mai shegen kyau
Already dama ko wanne daki a gida a gyare yake 'dan haka yace ta kaita dakin dake gefen
nasa ,
Suna isa kuwa bata tsaya wani knocking ba ta buɗe gidan suka shiga ,babu wani sallama ko
magana ta ja akwatin Hafsa ta buɗe dakin da Nameer yace ta zauna ta shiga da kayan,
Biye da ita hafsa take zuciyarta na ɗari ɗari domin tana tsoran haɗuwa da Jamaimah 'dan taji
ance yar sarkice,
Kama hannunta Nadiya tayi ta zaunar da ita tace"Hafsa kalli nan,jikinki 'fa Zaki saki idan ba
haka ba Jamaimah zata raina ki sosai cos yar rainin wayauce na fitina ,nasan Abun da wuya
,amma a yanayin Jamaimah tana da gasa ,nasan ganinki a nan zai saka tayi duk abunda zatayi
domin ganin ta samo kan Nameer." Kaɗa kai Hafsa tayi tace "Aunty ina jin kawai gabana na faɗuwane amma insha Allahu zan
ƙokari ,amma zakina zuwa ko?"
Murmushi Nadiya tayi tana Mai jin san hafsa cikin ranta,she's just another word of
simplicity,kaɗa mata kai tayi tace"insha Allahu zan rinka zuwa,amma dole fa kizama jajirtatta
wannan sanyin ki ajesa saboda idan kikace sanyi zakiyi zaki sha wahala."
Ajiyar zuciya tayi tace zan ƙokari.
Suna cikin aje kaya jamaimah ta shigo ɗakin kamar wata barauniyya,
Turus tayi tace "to lafiya?"
Tashi Nadiya tayi tace"lafiya uwar gidan Hamma ,nayi tunanin kar nayi knocking ne ki kasa tashi
ki buɗe gudun kar na baki wahala ya saka na ƙarbo key hannun Hamma cos zuwan nan bana
san bata lokaci.
Ɗaga hannu Jamaimah tayi tace "gyara zan maki ,bana san kirarin uwargidan Nameer ,saboda
ni Uwargida ce kuma amarya ,daga ni babu ƙari,kallanta ta mayar kan Hafsa tace "wannan
kuma 'fa,sannan Mai kukeyi ɗakin nan?"
Yar ƙaramar dariya Nadiya tayi tace "Allah sarki,shi yasa nace uwargidan Hamma saboda
yanzu yayi amarya,"
Nuna Hafsa wadda gabanta yayi mugun faɗuwar ganin haɗuwar Jamaima tayi tace "gata nan
,amaryar Hamma kenan wadda aka ɗaura Aurenta da Hamma a yau sannan iyayanmu sun
shaida,sannan abun daɗin shine yar danginmu ce wadda tasan darajar iyayanmu da kuma
mijinta da yan uwansa,Abu Mai daɗin kuma shine ta iya girki chef ce ,sannan tazo da niyyar
girkawa mijinta da kulawa dashi wanda shine ibadar Aure.,"