Showing 18001 words to 21000 words out of 73196 words

Chapter 7 - AHALINA (Aure uke series)na chuchu.pdf

Advertisement

08 Jul 2025

2278

ɗora kanta Akan cinyarta kana ta shagwabe fuska tace "Dada
wai shi kam lamido bai gajiya da magana ɗaya?"

Ki samu lokaci fa ki faɗa masa nikam ina da miji a Nijeriya sannan ban Aura ba sai da na
dirje,sannan nayi hakuri dada da har Yanzu banbi mijina ba abisa umarninki na 'in sake hakuri
,yakusa karewa fa Dada kifaɗa musu.

"Shafa yalwataccen gashinta mai santsin gaske Da Ya fito ta baya dadan nata ta fara tana Mai
cewa"Jamaimah na faɗa miki Aurenki da yaran chan na Nigeria ba Aure bane ba,kaddararki
itace ki maida Harith Lamiɗo wanda dole zakiyi,'dan haka gudun karmu sab'awa mahalicci muyi
Aure kan Aure Ya kamata aje Nigeria a kamo yaran nan ko kuyi magana tunda akwai hanyoyi
na zamani a kashe auren kizo ki bawa Harith Lamiɗo kiyi addua ke ki haifi diya kamar ki ta
bawa wani Lamiɗo cikin Ahalimu bana san rigima surbajona,."

    Tashi Jamaimah tayi a cinyar Dadan nata ba tare da tace komai ba dan idan tayi magana
rashin ɗa'ane zai fito sannan a rayuwarta duk da fitsara da izza irinta mulki jininta take bata so
koda yayane tab'atawa mahaifiyarta ,amma 'fa itama bazata bari a b'ata mata ba ,

Tana mutuwar san Nameer wanda shine babban dalili da yasa ta Auresa sannan tayi imani da
Allah koshi bai isa Ya raba kansa da ita ba sai dai Allah Ya rabasu ,saboda a yarda take jinta
babu wani namiji da zai kalleta yace wai yau baya santa zai rabu da ita ,tabbas 'dan kuwa duk
inda kake jin kyau Jamaimah takai,
Takanas ta miƙe tana Mai faɗin ma Dadan nata "na barki lafiya sarauniya babba",

Sanin maganar ce bata so a ja yasaka mahaifiyar tata rabuwa da ita tunda duk guje gujenta
tasan sai ta Auri harith,

    Tunda ta fito 'dan nufa sashen ta take neman mai rabon shan wulaƙanci bata samu ba har ta
shiga sashenta,

Zaune ta tarar da Harith a dining ɗinta yana Mai shafawa wata kuyangata ɗuwawu,

Ƙaramar dariya tayi lokacin da idanunta suka sauka Akan wanga al'amari,

Da sauri yarinyar ta matsa daga gefensa jikinta na ƙarma inda shikuma Ya lashe leb'ensa na
ƙasa yana Mai kallan JAMAIMA da maita.


Ya kukaji character ɗin Jamaimah?

Shine mene ra'ayoyinku bisa rayuwarta?

Shin Mai kuke tunanin kan Fadil?

CHUCHUJAY

Tbc
[3/6, 5:11 PM] Chuchujay✍️: AHALINA

(Siblings of different father's)

Book two 'in Aure Uku series

        By

chuchujay

Episode 1⃣7⃣➡1⃣8⃣

  Tasowa Harith yayi yana Takowa ga Jamaima kamar babu abunda ta kamasa ya nayi,

Yana ɗaya daga cikin abunda Ya saka ta tsanesa ,a kullum idan zai ganta sai Ya nuna a fili
jikinta yake so.

Kallan kuyangar dake ƙarma tayi tace "idan ma nace zan miki wani abu maine zan miki,kije
kanki kike cuta saboda shi Yarima Harith ɗin da kike biyewa babu inda zai kaiki sai dai Ya
baroki,sannan wani abu Mai daɗi da nake so ki sani,kinyi babbar sa'a da Ya zamana ba nawa
bane kuma bazai zama nawa ba,'dan haka ki bace mun a guri sannan idan kika kuskura na
sake ganinki sashe na sai na yagaki ,Alƙwarin gimbiya jamaima kenan,kinsan zanyi fiye da
haka,"

Bace mun a guri stinky whore .

    Da gudu yarinyar ta fita har tana tuntube 'dan tagama sawa aranta ta mutu kawai a sanin
halayyar jamaima ,amma ga mamakin ta sai taga akasin haka,

Daf da ita harith Ya matso ,bata matsa ba sannan batayi gizau ba ,jira kawai take taga ƙarshen
iskancinsa ƙugunta Ya kamo ya jawota jikinsa yana Mai mata wani irin shafa a ƙugu,

Wani karamin dariya tayi tana mamakin ƙarfin guts ɗin Harith,tayi imani da Allah idan baiyyi
wasa ba akan jikinta shi zata fara kashewa,

Kansa Ya sako dai dai saitin kunnenta yace "Ki daina wancan furucin na ni ba naki bane ba
kuma Zan zamo naki ba,ƙaddarar mu a haɗe take gimbiyata,Nan da ƙwana uku ki shirya mayar
dani lamiɗon ki domin hakan zai faru ko Kina so ko baki so,a yayin da nikuma nake kan murnar
da bana tunanin da wani Lamiɗo da zai Kaini,saboda na farko Zan samu masarautar nan
sannan na biyu Zan samu sarauniya Mai kyau da diri na jiki nayi yarda nake so da ita Akan
gadon milkina,ina mutukar kwadayin jikin ki Gimbiya jamaima ,sannan kar ki damu 6 inch ne
D*ck ɗina kinsan babban goro sai magogar ƙarfe., "

    Kafun yayi Aune tayi wani irin Hankaɗe sa ta ban mamaki da Kafarta inda Ya faɗi kasa
wanwar,binsa tayi ta ɗora Kafarta kan kirjinsa ta taka da karfi kana tace "Abu na farko da nake
so ka sani saboda yan iska irin ka koda naje china ba karatu kawai na tsaya ba sai da na samu
Black belt a taekwondo ,idan na maka wani dukan sai  anyi tunanin hatsarin mota ne kayi,
Kana daukar kanka jarumi ba?

To kai da b'awan gyada a gurina baka da banbanci ,b'awan gyaɗa wanda zanyiwa b'ara ɗaya ya
fashe ,gwanda da kasan cewa babban goro sai magogin ƙarfe domin jikina yafi karfin wannan
abun dake gabanka da kake bin low life kuyangu dashi ,be guided Next time idan ka kuma tab'a
mun jiki Zan saka takobi nasare dukkan hannun ka da Ya taba ni,
Stupid scumbag ,

Yawu ta tofa masa a fuskasa ta bar gurin,

Mikawa yayi yana binta da kallo yana tunanin hanyoyi da dama da zaibi Ya wulakantata ,tabbas
da ace baya san zama sarkin garin da babu abunda Zai hanasa yi mata fyaɗe tuntuni 'dan shi
jikinta yake so ba ita ba,

Amma yazama dole Ya ƙwantar da wuya muddin yana san cimma burinsa guda biyu,na samun
jikinta da kuma zaman sarkin DILAH,."

Tashi yayi daga ƙasan da yake yabar sashen da Tunanin kala kala.

    Jamaima kuwa bayan ta shiga ɗakinta Gadonta ta hau ta ƙwanta ta jawo system ɗinta,

Maiyi mata tausace ta shigo,alamu tayi mata da ta tafi ,babu musu ta koma cikin girmamawa,

Page d'in Nameer na Instagram ta shiga,sababbin hotunan sa ta gani da Fadil,

Murmushi tayi tana Mai jin wani irin masifaffan sansa a cikin zuciyarta ,tayaya ma zata iya zama
a raba ta da Nameer wanda take jinsa shine rayuwarta?

Tayaya?

Zumbur tayi ta miƙe da ta tuna maganar Harith na cewa nan da kwana uku zata zama tashi,

Dole tasan abunyi domin ta fahimci idan ta tsaya a gwiwowinta za'ayi mata shirme ne a
masarautar,dan haka idea ɗin guduwa taje gurin Nameer shine kawai Ya faɗo mata,

Passport ɗinta ta nemo tare da ID cards ɗinta,

Take tayi Booking flight d'in da zai tashi Nigeria da yamma,

Aƙwatinta ƙarami ta haɗa da dukkan wani jewelry nata da kuɗaɗe masu yawa aje gefe tana
tunanin ta yarda zata gudu,

Driver ɗinta ta kirawo,

Babu daɗewa yazo ,ƙaramun akwatinta ta bashi yayin da ta dauko kit din tabi bayan sa,

Kai tsaye Airport Ya kaita,suna zuwa ta wani haɗe rai ta kallesa tace "Zan kiraka anjima kazo ka
ɗauke ni amma for now zaka iya tafiya,"Babu musu yace to cike da girmamawa,wani daɗi taji
lokacin da Ya bar Airport d'in tana Mai jin wata iskar freedom na shigar ta ,atleast har ta bar
kasar babu wanda zai san guduwa tayi,

Zama tayi dan jiran akirasu idan lokaci yayi,

A hankali ta rufe idanunta tana Mai fadin "Nameer gani  nan zuwa gareka."


*************************

    Tunda Hafsatu ta iso garin Adamawa taji hankalinta yayi wani irin ƙwanciya da bata iya
misaltawa,bata tab'a zuwa garin ba amma a karo na farko ɗin nan taji baki daya komai nata Ya
aminta da garin,

    Samun gidan innan mahaifinta bai mata wahala ba saboda tunda ta taso suke
communicating da juna,

Ƙauna babu irin wadda Inna talle bata nunawa Hafsa ba ,ba sai ta faɗa ba Babanta yana ɗaya
daga cikin abubuwa mafi soyuwa a gareta,abu ɗayane wanda ta kula Innar tata tana cikin shine
hali irin na talauci sosai ,bata da kowa sai yaranta Muhammad shi ɗaya wanda yake sayar da
rake a ƙofar gidan ,dukanin shekarun sa bazasu wuce Goma sha ɗaya ba,kamata yayi ace
yana makaranta a wannan shekarun ba wai zama saida rake ba wanda ƙwataƙwata ribar tasa
nawa Take,

Sawa tayi a ranta bazata bari ta zamar masu wani karin nauyi ba ,ko aiki ne zata nema tayi dan
basu nata tallafin duk da kuwa itama tana da burin nata karatun ,bari tayi sai ta ɗan kwana biyu
zata wa Innar tata maganar Aikin nata ,

Ille kuwa bayan ƙwanakinta Huɗu a gidan wata safiya bayan ta gama karyawa da ɗan kunu da
alala ɗin da Muhammad ya fita Ya siyo mata,

Kallan ta tayi tace "Inna wai ni kam babu wani aiki da Zan iyayi a garin nan koda wanke wanke
ne da shara,kinga muhammad ma ya kamata ace yana zuwa makaranta Kema kuma gaki Ana
ɗan fama da jiki idan na fara aikin wani abun Ya ragu.

    Dan shiru Inna tayi tana nazari kafun tace "a yi haka kuwa Hafsatu,yau duka ƙwananki nawa
a garin nan da har kika fara maganar aikatau,haba dan Allah,kar ki wani sakawa kanki damuwa
,muhammadu nan kawuna dake kano yayi Alƙwarin daukar nauyin karatunsa wanda dai nasan
abunda yasaka baiyyi magana ba ƙilan wani abu ne yayi masa yawa,"
Karki damu Allah zai rufa asiri ,ke dai ki zauna ki huta babu abunda zai gagara.

    Dan shiru Hafsa tayi kafun ta kuma cewa"Inna na dai dage ,sannan ba wai dan an Gaza ɗin
bane,ni kaina zaman guri ɗayan zai dameni da yawa,"

Shiru Inna tayi a karo na biyu tana Mai juya maganar Hafsa,tabbas suna buƙatar taimako tunda
dai ita a yanzu karfinta Ya ƙare,ga tsufa ga kuma yan ciwace ciwace da baza'a rasa ba,

    Ajiyar zuciya tayi tace"shikenan hafsatu Zan kira Balarabe idan yaso ko Mai yace hakan
za'ayi,bazan so ace daga zuwan ki kuma kin fara aikatau ba ba tare da yasani ba,"

    Kamar yarda inna tayi suggesting su kira Baban hafsa haka kuwa akayi inda shima yayi
na'am da maganar aikin Sannan yana Mai yin alfahari da ɗiyarsa,

Bayan ƙwana biyu da maganar Inna tayima wata ƙawarta magana wadda dama sana'arta
kenan raba yan aiki,cikin murna da jin daɗi matar ta cewa Inna dama kuwa akwai matar da tayi
mata magana tana san yar Aiki budurwa Mai nutsuwa ,ina ganin Hafsatu zata dace da aikin
kuma matar bata da matsala ,kawai dai abu ɗayane,ki jamata kunne babu idanunta kan mijinta,
    Godia sosai Inna tayi mata sannan ta tabbatar mata insha Allahu bazata samu wata matsala
daga Hafsa ba ,

a haka suka tsaya inda aka yanke washe gari zasuje gurin hajiyar,

Washe gari da Inna da Hafsa da ƙawar inna hajiya mai yara suka nufi gidan da zatayi
aikin,Bayan isarsu gidan Akayi masu iso zuwa falo,

Kallan gidan Hafsa take a hankali tana Mai yaba irin arzikin da Allah yayi musu dan tunda Take
bata tab'a shiga Gida Mai kyau irin haka ba,

Suna zaune suna zaman jiran Hajjiyar ta sauko daga benenta wanda matattakalar kawai abun
kallo ne,

Zama tayi tana Mai amsa gaisuwarsu wadda suke mata kamar suna jira,da fara'ata fal fuska ta
amsa su ,

Hajiya Mai yarace tace "Hajiya Shatuh ga dai Mai aiki nan an kawo ,idan batayi maki ba to ,gata
nan dai zaune,"

    Kallanta Aunty shatuh tayi tace"Yaya suna ki yan mata ,"

Ƙasa Hafsa tayi da kai tace hafsa,

"Kice tsohuwa ce ,to ina fatan dai kunyi magana da maman yara ,sannan gaskiya Mai kwana
nake So ba wadda zatana jeka ka dawo ba,"

Shiru sukayi baki ɗayansu dan maman yara bata faɗa musu ƙwana zata nayi ba,

Kafun Inna tayi magana Hafsa ta rigata ta hanyar faɗin "Babu komai Hajiya amma ina san amun
alfarma ranar asabar ina zuwa gida ,"

Murmushi Aunty shatuh tayi tace"baki da damuwa sannan duk wata zan na baki dubu talatin".

    Jin kuɗin yasakasu fara mata godia yayin da daga bisani Inna da Hajiya mai Yara suka wuce
Akan washe gari za'a kawo mata kayanta tunda sun tafi ne bada niyyar aikin kwana ba.


*********************

   Kai tsaye Nadiya na isa gida ɗakin Nameer ta nufa da Fawha ta tabbatar mata yana ɗaki,

Knocking tayi har sau uku kafun yabata izini ta shigo,

Zaune ta tarar dashi kan abun sallah,

Zama tayi kan couch ɗin dake ɗakin tana mai yi masa ƙaramun murmushi,ninke abun sallan
yayi yana Mai kallanta yace "yau Baby Sis kin tuna da hamman ki kenan ,hope im safe ,"

Wasa ta farayi da Kafarta kafin tace"i dont think you are actually,"

Wayarta kunna ta shiga kan Information ɗin Aneesa ta miƙa masa 'dan Ya karanta ,

Da mamaki Ya gama karantawa a yayin da wani chilled tsoro Ya shigesa musamman da ya san
cewa Anisa ɗin  na tsamo tsamo cikin AHALINSA,

Kallan Nadiya yayi yace "Nadiya mai yasa kike ajiyan wannan Info ɗin a hannunki ba tare da an
kaima police ba sunyi arresting ɗinta,kinsan she's dangerous amma kika yi shiru?

Tashi yayi yace "dole mu san abunyi,"Bari na kira commissioner Hadi.

    Ƙarb'ar wayar tayi ta haɗa da tashin da yake ƙokarin yin wayan tace "kana tunanin zai solving
komai?"

Mai yasa Bakayi tunanin abunda Ya saka take yawo freely ba har Allah Ya kawota gidan mu,

Bro tana da masu mata cover ,sannan tana da haɗarin gaske ,and na zo na faɗa makane
badan ka tada wani tarzoma ba ko kayi wani abu da zata gane cewa mun san ita wacece,

A hankali zamu saka mata trap d'in da zata kama saboda dukkan wani wayau da kake tunanin
Anisa na dashi,After all akan wayan aka basu horo,

I told you dan ka zama alerted .

  Zama yayi yana Mai dafa kansa yace "Ya rabbi,

Sis Mai yasa nazama nine silar wannan dilemma d'in da muke ciki,bana tuna b'atawa wani da
har zai kai ga tura mun assassin har cikin gida sannan da ƙazafi mafi muni,what's going on ?

    Kama hannunsa Nadiya tayi tace "ƙwantar da hankalinka Hamma zamu zo dai dai nan gurin
cos a yanzu maganar da nake maka ana bincike Akan motive ɗinta na zuwa wanda nasan za'a
gano ,"

Juyowa tayi ta Kama hannunsa tana Mai kallan cikin idanunsa tace"Hamma ,im your sister
sannan duk wani abu da zanyi bazan tab'a yin wanda zai cutar da kai ba,hasalima farin cikin ka
a kullum shine abu na gaba a gurina ,babu wani abu da kake boye mun?"

    Dan shiru yayi yana kallanta cikin nazari kafin yace "abu kamar me ?,bana tunanin akwai
wani abu da nake boye miki Nadiya trust me.

Kafarta ta ɗora kan ɗaya tana Mai saka fuskar damuwa tace "Hamma akwai,sannan Ya kamata
ace kayi magana musan abunda zamuyi saboda muddin mami taji maganar nan kaima kasan
gidan nan zai haɗe sama da ƙasa ,so talk to me".

    Shiru yayi still 'dan shi har a lokacin baiyyi tunanin tasan maganar Jamaimah ba ,sannan
ƙwataƙwata bai kawo ma maganar bace domin yasan babu yarda za'ayi ta sani,sannan
haɗuwarta da Fadil ma ba sani ba ,kallanta yayi yace "just tell me Sis bani da wani tunani na
abunda nake boyewa.
Ganin Ya kasa ganewa ne Ya sakata cewa"maganar Auren ka da Jamaimah ,"

Kamar saukar aradu haka yaji maganar dan 'in his wildest dream bai tab'a tunanin Nadiya zata
san maganar nan ba,cike a mamaki yace "ina kikaji maganar nan".

    Dauke kai tayi bata san haɗa ido dashi tace "ina kan binciken Anisa ne da san gane gaskiyar
abunda tazo dashi  na fara bincike akanka rayuwarka a china,im Sorry ban faɗa maka ba,so 'in
the process na gano Auren ka ,Hamma wannan ba abu bane na boyewa ,yes kayi ba dai dai ba
sannan kun yi wasa da girman Aure amma bashine yake nufin za'ayi shiru da abunda,we All
know that babu wanda Ya wuce mistake and you made one,duk kaifin tunanin mu iyayenmu sun
fimu tunani da hagen nesa,so mu faɗa musu koda zasuyi fada suji ba daiɗi amma su zasu zo
da solution."

    Kamo hannunta yayi cike da tsoro fal ransa yace "Nadiya ke da wa kuka san maganar nan,?"

"Abdallah,"ta bashi amsa.

Wani yawu Ya haɗiya wanda Ya saka Adam Apple ɗinsa motsawa yace "Nadiya please lets not
tell mami about this,kinsan yarda take ba,musamman da case ɗin Anisa a ƙasa ,inajin ƙarshe
disowning ɗina zata yi. "

    Cike da tausayinsa tace"Hamma amma Ai bazamuyi ta boyan maganar nan ba har abada
,idan ita kuma yarinyar tazo fa?"

Da sauri yace "nasan Jamaimah bazata taba zuwa mana ba cos kilan ma ta manta da wani
Aure tunda bet ta ɗaukesa,'dan Allah Nadiya kafin mu gama maganar Anisa kiyi shiru tukuna
sannan shima Abdallah kisa yayi shiru 'in yaso After that na maki Alƙawari da kaina Zan faɗawa
mami da Papa. "
Ganin yarda ya marairaice mata yasa Nadiya kaɗa kai tace "i Trust you Hamma and namaka
Alƙwari duk wani yanayi da ka tsinci kanka ina tare da kai."

Suna cikin wannan moment ɗin aka ban kaɗo kofar ɗakin aka shigo,

"Anisa?"

Nameer Ya faɗa da ɗan duburburce sanin maganar da yake da Nadiya.


CHUCHUJAY ✍

TBC
[3/6, 5:12 PM] Chuchujay✍️: AHALINA

(Siblings Of different Father's)

Book two 'in Aure uku series

    By

   CHUCHUJAY

Episode 1⃣9⃣➡2⃣0⃣

 

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login