Showing 1 words to 3000 words out of 73304 words

Chapter 1 - A GIDAN TA NA GIRMA COMPLELET. BY UMMU IHSAN.pdf

*GIDANTA NA GIRMA*


*BY NANA: KHADEEJATU*

_*UMMU IHSAN*_


*SADAUKAR WA GA:- DUKKANIN MASOYA NA NA BOYE DANA BAYYANE INA SONKU
SOSAI SON FISABILILLAH*


*YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA
SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.*


_*Bismillahir Rahmanin Rahim*_

1~5

"Wayyo Allah Mamar mu kin tafi kin barmu cikin kuncin rayuwa wallahi sai na bikii... "

Kawai bata 'karasa ba ta shed'e ko motsi babu, duk ilahir mutanen gidan gaisuwar nan akayo
kan ta, ruwa aka fara zuba mata amman bata motsa ba.

Rudewa yayar ta tayi, da gudu tafita kofar gidan tana ihu, mazan dake kofar gidan sukayo kanta
da gudu, tambayar sukeyi miye yake faruwa amman ta kasa magana sai cikin gidan take muna
masu, ai kuwa basuyi kasa a gwiwa ba suka shiga cikin gidan da gudun su.


Hankalin su ne yayi mugun tashi ganin abunda ke faruwa, wani dattijo ne wanda daga gani
kasan shine mahaifin su, dan sunyi matukar kammani dashi, ya duk kusa a kusa da yariyar
wadda bazata wuce shekara Tara ba, ya duka ya d'auke ta idon sa cike da hawaye amman
kuma hawayen ya'ki barin su, su zubo masa 'kofar gidan ya nufa da ita, wani mutume ne ya
d'auke su a mota harda yayar tata, sai asibity.


Taimakon gaggawa aka bata, su kuma duk suna waje a tsaye sai jeka dawo sukeyi.

Doctor ne ya fito yace, "ga wannan takardar a nemo wannan maganin da sauri".


Mutunen ne ya amsa ai kuwa sai gashi da magani da ruwa ya kai aka ansa, cikin ikon Allah, sai

gashi ta falka da kuka.

Allurar bacci yayi mata, ya fito, hannu ya baiwa mutanen yace, "ta falka amman nayi mata
allurar bacci, saboda haka insha Allah data falka zata dawo cikin hayyacin ta".

Sai doctor yace, "amman dan Allah miye ya firgita ta haka gashi zuciyar ta tafara kumbura dan
gab take da kamuwa da ciwon zuciya mai tsananin gaske ".

Sharce hawayen sa dattijon yayi, yace, "ai dole Husnah ta fir gita tayi kamar zata hauka ce,
mutuwar uwa ai babban rashi ne, koda ciwo ballema mutuwar cotsom d'aya".


Shi kamshi doctor ya tsorata sosai a take yaji tausayin yarinyar ya 'kara kama sa, Addu'a yayi
masu tare da ta'aziyya.

Godiya sukayi masa, ya wuce su.

Zaman sukayi na d'an wani lokacin kafin dattijon ya tashi yazo gurin yar sa d'aya yace mata,
"Zara ku sanya hakuri da juriya a cikin zuciyar ku ki zauna da yar uwar ki, lallashe ta, ki sanar
da ita, mahaifiyar ku Addu'a take bu'kata ba kuka ba, zan je gurin ansar gaisuwar ne.

Gyad`a masa kai takeyi hawaye na zubar mata a ido.

Tafiya sukayi su biyu ita kuma ta zauna har sai da nurse tazo ta kirata sannan ta shiga cikin
d'akin, gin cire yarinyar take a jikin gadon da Karin ruwa jone a hannun ta.

Kujera taja ta zauna a kusa da ita tana kallon ta, tausayin kansu ne ya'kara kama ta.

Tace, "Husnah muyi wa Mamar mu Addu'a ba kuka ba, nasani Mama duk da koda tana a raye
bata iya hana a cutar damu kuma, duk azabtar war da akeyi muna tare da ita akeyi muna shi,
uwa_uwa ce bare ma uwar da ta koyar damu hakuri da dan gana, ko kin manta da cewar,
kullum sai tayi muna nasahar mu d'auki kaddara mai kyau ko marar kyau?, Husnah kin ga gashi
doctor yace, kin kusa kamuwa da ciwon zuciya dan Allah ki rufa mani asiri kin san nice kawai
zan shiga cikin wani halin idan kika samu wata matsalar".

Hawaye sukeyi, babu mai lallashin su, sai mutanen dake gurin da yaran suka cika zuciyar su da
tausayi, duk rashin tausayi irin na nurse amman sunji tausayin yaran.

Daket Husnah tace, "Aunty Zarah shike nan Mama ta tafi ta barmu ko? Kuma sai da nace
mata, kada ta tafi ta barmu gashi kuma Baban mu baya son mu, baya kulamu".

Rufe mata baki Zarah tayi tace, "haba Husnah kada kice haka kiyi shirun ki kawai Baban mu
yana son mu".

Da sauri Husnah tace, "shine ya kawo mu nan ya gudu ya barmu ko? Kuma kice yana son mu,
ko ya bar maki kud'in da, zaki siya muna abinci ne, nifa Mamar mu kawai zanbi".

Kuka Aunty Zarah takeyi sosai, ganin hakane yasaka Husnah kuka itama sai tayi shiru da
masifar ta.

Tun 'karfe goma na safe suke asibityn nan har la'asar babu wani abunda ya shigo hannun su,
ganin sun gala baita ne yasaka wata matar dake kusa dasu ta basu abinci da ruwa.

Godiya sukayi mata, Zarah ce, take baiwa Husnah abincin a baki har sai da takoshi, sannan
itama tace shinkafar jalof.

Har dare babu Baban su babu labarin sa kuma babu wanda ya leko su, mutane sai ala waddai
da irin wannan halin sukeyi.

Mutanen gurin kowa basu abinci yakeyi da kayan mar mari iri daban_daban.

Da safe 'karfe takwas da rabi, doctor ya duba Husnah yace, "zan sallame ta a yanzun dan Allah
ku kula da maganin ta dan gab take da kamuwa da ciwon zuciya mai tsanani, amman idan an
kula da damuwar ta da maganin ta Insha Allah komai zai zama dai dai kuma naga harda Olsar
ke gareta dan Allah ku kula kunji ko? ".

Gyad'a masa kai Zarah takeyi tace, "mun gode sosai".

Sallama ya basu Husnah fad'ar takeyi, "Anty Zarah muyi zaman mu anan inda babu wanda
yake takura muna kuma muna samun abinci mai yawa muna ci ko? ".

Gir giza mata kai tayi tace mata, "dole ne mu koma gida mu zauna kawai dai musaka hakuri a
lamarin mu".

Wayau tayi mata, suka bar asibityn tare da wasu kud'in da wasu mutane suka basu, da murna
Husnah ta anshi kud'in tana godiya tare da farin ciki, suna fita Husnah ta kwance zanen ta, ta
nade kud'in ta kullesu a habar zanen ta, ita dai Zarah kallon ta kawai takeyi abun hawa suka
hau suka sauka unguwar su.
Mutane sai gaisuwa sukeyi masu, a take kuma mutuwar mahaifiyar su ta dawo masu sabuwa.

'kofar gidan su babu kowa duk mutane sun watse cikin gidan suka shiga wanda suke jin kamar
kada su shiga cikin gidan.

Addu'a d'auke a bakin su suka shiga cikin gidan sallama sukayi aka kyalesu ga mutane

zazzaune kamar itace basu amsa Sallama.

Baban sune zaune yana cin tuwo ya kallesu kallo d'aya, ya watsar, kawai cikin masifa wata
mata tace, "to gan talali harda mutuwar uwar baisa kun natsu ba, sai da kukaje yawon karuwan
cin, ai dama nasani tun jiya kuka baro asibityn sai yanzun kuka ga damar dawowa gidan nan
ko!? ".

Fashewa sukayi da kuka kamar ransu zai fita.

Tace, "kukayi banza dani ko bada ku nake ba ne? "

Cikin rawar baki Zarah tace, "kiyi hakuri Goggo wallahi daga asibity muka fito" cikin kuka take
maganar.

Tsawa ta daka masu tace, "kai..! Kada ku maida mu mahaukata ko kuma makafi mana! Dubi
yanda kukayi mul mul abunku dubi yanda kuka dawo kamar ba masu jinya ba, anya ma kuwa
kunji ciwon mutuwar uwar ku kuwa? ".

Kukan makirci ta fashe dashi tanayi tana fad'ar, "Allah na tuba yaran nan zasu sakani bakin
mutane bayan mutuwar uwar su, shine zasu fara biyar maza duka yau kwana d'aya da mutuwar
uwar su, wai nikam yaya zanyi da y'ay'an Allah bani? ".

Kukan takeyi tana fyace majina da habar zanen ta.

Cikin 'bacin rai da masifa Baban ya jefo su da kwanon da yake cin tuwon sa yana fad'ar,
"wallahi 'karya kukeyi ku saka ni kuka, tun kuna yaran ku, wato abun da uwar ku ta koyar daku
ke nan ko? ".

Da gudu suka shige cikin d'akin su suka rufe jikin su sai rawa yakeyi dan sun san yan zun nan
za a had'a masu jini da majina.

A bakin gado suka zauna sai rusa kuka sukeyi Zarah ce ta goge hawayen ta kwantadda
Husnah akan kafafun ta, tana lallashi, dukan 'kofar yakeyi kamar zai 'karya ta yana fad'ar, "kuzo
ku bud'e 'kofar nan kafin na balla ta na shigo ciki".

`Kin bud`ewa, sukayi har sai da ya gaji yayi tafiyar sa.

Basu fito ba sai bayan magrib suka bud'e sukayo alwala suka dawo d'akin sukayi sallah, suna
zaune har 'karfe goma na dare babu abunda suka saka a bakin su, dabara ce ta fad'o masu,
suka lallaba suka d'auki kwano, sukaje suka siyo tuwo suka dawo cikin ikon Allah babu wanda
ya gansu.

Tuwon sukaci, Zarah ta baiwa Husnah maganin ta suka kwanta.

Sai kukan kewar mahaifiyar su sukeyi a haka bacci 'barawo ya sace su.

Tun da asuba suka tashi, sukayi sallah sannan suka fita tsakar gida zaunar da Husnah Zarah
tayi, ai kuwa a take tafara wanke_wanke da share_share sannan ta d'ora ruwan dafuwar kuko.

Suna tafasa kawai ta dama kokon ta ajiye masu suka dawo cikin d'akin su.

Fitowa uwar ikon tayi zata fara masifa sai hamma takeyi daga gani ko sallah batayi ba, gashi
koda take ta zabga hamma babu Addu'a, abun da yabata mamaki shine duk aikin da take son
taci masu mutumci idan basuyi ba, sunyi har sun gama, dube_dube ta somayi ko zataga wata
matsalar ta daban amman bata gani ba.
Tsaki tayi ta wuce ta d'auki buta, ta shiga cikin bayi ta fito ta wanke baki ta debi kokon tasha, ta
zabga sugar sai da tayi biyu da robar koko san nan ta tashi ta fara `dauraye jikin ta ta shiga
cikin d'akin ta sanyo hijab ta d'auko charbi ta shiga d'akin Baban su Husnah, ta gaishe shi
sannan ta fito ta zuba masa kokon, ta kai masa, yaran ta ne suka fito su ukku mace biyu na miji
d'aya babu sallah babu salati, kawai suka wanke baki suka zubo kokon suka 'koshi ragin da
sukayi ne aka zuba wa su Zarah aka kira su suka zo suka d'auka, da sanyin sa suka sha.

Misalin 'karfe sha d'aya gidan ya cika da ba'ki na ban mamaki.

A take jikin su Goggo ya d'auki mazari sai ta samu guri d'aya tayi zaune ta rafka uban tagumi.

Su Husnah kuwa farin ciki ne ya kamasu a take taje gurin mutanen ta shige cikin su.

Bayan duk sun zazzauna ne, wani dattijo wanda yadara Baban su Husnah tsufa kadan kuma
gashi kamar su d'aya, yace......



*Comment and share*

_*Yin comment din ku da sharhin ku shine zai bani damar ci gaba da wannan labarin kuma
shine zai bani tabbacin cewar kuna son labarin*_


*A GIDAN TA NA GIRMA*

*BY NANA: KHADEEJATU*

_*UMMU IHSAN*_


*SADAUKAR WA GA:- DUKKANIN MASOYA NA NA BOYE DANA BAYYANE INA SONKU
SOSAI SON FISABILILLAH*


*YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA
SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.*


_*Alhamdulillah Allah ya dawo dani lafiya na samu sau'kin jiki na ina godiya a gare ku masu
kirana kuji ya na 'kara ji da jiki na Alhamdulillah Nasamu sau'ki sosai nagode da kulawar ku a
kaina*_



_*Bismillahir Rahmanin Rahim*_

6~10

Mutumen yace, "Allah ya jikan ki Hinde mutuniyar kirki a gaskiya anyi babban rashi a gaskiya
mutuwar Hinde tabar gurbi mai wuyar cikewa ya Allah kayi mata rahma"

Ya madaida kallon sa gurin Baban su Zahra yace, "zan dauki Zahra na had'ata da sauran
yarana har zuwa lokacin Auren ta, Amina kuma tace itace zata dauki Husnah".

Da kuru ruwa da har gowa delu tazo a gaban mutamen tana fad'ar, "dan Allah kada ku rabani
da yarana wallahi ina son su zanyi masu ri'ko na amana da gaskiya" hawaye kawai take zubar
wa tayi kwance ta rike 'kafar dattijon tana kuka.

Kallon ta kowa yakeyi Zarah da Husnah kuwa sakin baki sukayi suna kallon salon makirci irin na
marka.

Girgiza kansa dattijon yayi yace, "nasani zaki iya ri'kesu a gurin ki bawai bazaki iya bane
malka, ko dan ganin mahaifin su Amman gaskiya kiyi hakuri kuma ba yanzun zan dau'ke suba
sai angama ansar gaisuwa duk da naga kamar angama ansar gaisuwar ace kwana d'aya har
anwatse kamar daman an matsu mutum ya mutu? ".
Babu wanda yace uffan daga cikin su Malka da Baban su Husnah.

Yan uwan girgiza kansu kawai sukayi suna jin zafin wannan mugun halin na mutanen gidan
nan, Malka kuwa tunda taji abunda wannan dattijon ya fada sai ta tashi zaune na matso hawaye
dan yaji tausayin ta, amman ya dauke idon sa yana kallon su Zarah yana 'kara tausaya masu.

Addu'a sukayi suka tashi tsaye dattijon yace, "Sa'idu kaji dai hukun cin dana yanke a matsayina
na yayan ka kuma koda wasa kada naji kada nagani, Allah ya jikan ta da rahma Allah ya baku
hakurin jure rashin ta".

Kallon sa ya maida akan Zarah da Husnah yace, "to muntafi sai mun dawo ku kara hakuri kuma
kuyita yiwa mahaifiyar ku addu'a kunji ko? Domin addu'ar ku tana isa a gareta ".

Gyada masu kai sukayi.

Rakiyar su, sukayi sai da suka ga tafiyar su suka dawo gida suka tarad da Malka ta balbale
Baban su da fada tana fad'ar, "ai wannan tozarci ne wallahi dan mutum yana gaba dakai shine
har yake da ikon zar tar da hukunci akanka da iyalan ka? Abu sai kace wanda ya haifeka ako
dai koda wanda ya haifeka ne banyi zaton zaka kasa ce masa komai ba, wallahi malam ka bani
kunya wallahi, yaran ka matane fa kasan irin abunda ya tsara a ransa kuwa a kansu ? nifa ban
ma yarda da wannan salon nasa ba".

Tashi mahaifin su Husnah yayi ya fita yabar mata gidan, dan ya kasa musawa Yayan nasa dan
ko iya hada ido dashi bayayi ballema har takai ga yayi musu dashi.

Da ido tabisa ta ri'ke ha'ba tace, "ikon Allah wato dai malam indai a kan zancen Yayan san nan
ne bazai iya attaka komai ba, haka kawai mutum ya shanye kowa a cikin dan ginsa dan yafisu
kud'i wallahi indai nice Malka sai na hana yaran nan jin dad'in rayuwar su".

Kallon ta kawai su Husnah keyi kuma itama tana kallon su amman ta'ki daina fad'ar abunda
take fad'a a gaban idon su.


Bokiti kawai suka d'auka suka fita d'ebo ruwa, koda suka kawo masifar takeyi bata daina ba
yaranta ne zaune sun d'aura kafa d'aya a kan d'aya suna zaman kashe wando.

Ajiye ruwan sukayi suka hada kayan wanke_wanke Zarah ke wankawa Husnah na d'auraya,
suna gamawa suka d'aura girki sukayi alwala suka nufi daki Malka cikin masifar ta tace,
"munafukan banza uban waye kuke nunawa cewar ku musulmai ne , ita kanta uwar taku a
lokacin karuwa ce sai da aka 'ka'kabawa Malam ita sannan ta daina a cewar ta amman bafa
barin tayi ba, ina kallon yanda take fita zuwa yawon karuwan cin ta, asirin tane kawai bai tonu
ba har ta mutu, kunga ke nan ku kan ku ba kuda ya'kinin cewar ku masu tsalki ne ko masu
kazanta ne?".

Wannan maganar kam ta shigesu musam man ma Zarah wadda take yar shekara sha biyar
hawaye kawai ke zubo mata tana sharewa har suka gama sallar.

Husnah tace, "Anty ki daina yiwa muguwar nan kuka wallahi idan nayi kud'i sai na rama
muguntar da takeyi muna da zagin mahaifiyar mu harda su kazafi wallahi bamu yafe ba, ko
kuma itama nayi mata Addu'a ta mutu kowa ma yafuta".

Murmushi Zarah tayi tare da shafa fuskar kanwata, sai kuma ta tuno da itama Husnar an kusa
rabasu, kawai ta sake sakin sabon kuka tana fad'ar, "mutuwa mai tonon asiri yau gashi rashin
uwa zai saka a raba mu nida 'Kanwata ya Allah ka bamu hakuri ya Allah kabamu kariyar ka a
duk inda muka tsinci kanmu ya Allah kada ka baiwa wani azzalumi cin nasara a kanmu ya Allah
kasani yan zun bamuda wanda zai kwabemu idan muka aikata ba dai_dai ba,ya Allah ka d'ora
marayun ka a kan dai_dai ya Allah kada kabarmu da dubarar mu!".

Cikin kuka Husnah ke cewa,"amin ya Allah Anty ai kema ba mutuwa zakiyi ba kibarni ko?
kamar yanda Mamar mu ta tafi tabar mu ".

Kiran da akayi masu ne ya sakasu fita ni'kan gari suka kai sai kuma cefane, Husnah ce ke 'kul
'kule Zarah kuma ita ke girkin.

Haka rayuwar su ke tafiya har akayi sati ukku da rasuwar mahaifiyar su .

Du'ke Zarah take tana yiwa Malka da yaran ta wanki Husnah na zuwa d'ebo mata ruwa duk sun
gaji, Baban nasu na zaune yana sauraren Radio yaran Malka ukku Ashiru da Nafi da indo suna
zaune suna cin abinci dan basuda aiki sai wannan.

Malka kuwa ta kasa ta tsare tana iya bakin 'karfin ta tana zabga bala'i, "wai wankin 'keta ne
Zarah keyi masu bata murza kayan sufita".

Sallamar da akayi aka shigo ne ya hanata ci gaba da masifar su Alhaji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login