Showing 27001 words to 30000 words out of 73304 words
Chapter 10 - A GIDAN TA NA GIRMA COMPLELET. BY UMMU IHSAN.pdf
Alhajin ne ya yi gyaran murya ya ce, "ada naso mubi komai a sannu a hankali amman na rasa
mi yasa kwatsam wasu abubuwa suke faru, shin Husnah mike faruwa ne, kuma da kika gudo,
ina zaki tafi ne?.
Shiru Husnah tayi sai kawai ta saki kuka kamar ranta zai fi, shiru sukayi suna kallon ta, Husain
ya ce, inafa zata tafi bayan sana'ar ta, ta karuwan ci! ".
Cikin fushi, Daddy yace, "Husain!! " tare da daka masa tsawa, "kayi wa mutane shiru waye ya
ce maka wasa muka zauna yi a gurin nan?.
Shiru Husain yayi bai sake magana ba, Hajiyar tace, mubar ta har ta dawo cikin hayyacin ta,
muyi magana da ita, cikin kwanciyar hankali ".
Alhajin ya ce, "ok babu komai Anisah ku shiga da ita cikin d'akin ku, kuma ku barta sai ta futa,
kada wanda ya dameta, oya tashi Husnah ku tafi ".
Ri'ka hannun Husnah sukayi suka bar gurin da ita, bayan su Husnah sun bar gurin ne, Alhaji
yace, "Husain ya kama ta ka iya bakin ka, ka daina ai banta yarinyar nan, kasan irin yanda nake
son ta, dan haka na gar_gad'e ka akan ta kaji ko? ".
Gyada kai Husain yayi ya tashi yabar gurin.
Yaya Yusuf ya ce, "dan Allah Daddy nikam ina jin kamar Husnah jini nace, bana kaunar na
ganta cikin damuwa, wallahi idan naga yanda take zubar da hawaye sai naga kamar zan tuno
wani abun, amman kuma na rasa miye?".
Daddy ya ce, "Yusuf kada ka damu muci gaba, da biyar komai a sannu Insha Allah komai zai
dai_dai ta, sai dai nikam a tsanin Husain da Husnah na rasa miye Allah shine mafi sani, amman
ni bana son ganin suna samun sa'bani"
Hajiya ta ce, "ni wallahi idan na kalle su har wani abun yake dar suwa a raina amman ina tunda
ina ganin yan zun da Auren wani a kan ta ".
Shaheed ya ce, "Insha Allah babu Auren kowa a kan ta amman mubi komai a sannu ".
Haka dai su Alhajin sukayi ta tattaunawa akai.
Husnah kuwa bata dai na kuka ba, sai taga su Anisah duk sun fara taya ta kukan kawai sai ta
bar nata kukan, ta dawo tana kallon su".
Wayar ta ce tayi ringing sai kawai Husnah ta shiga cikin mamakin ya ya akayi wayar ta, tazo
nan gidan, dariya Anisah tayi tace, "wayar ki tun jiya take hannu na, amman na rasa taya zan
maida maki wayar ki a gurin ki ba, shi yasa na ajiye ta a guri na".
'karfe ukku da rabi nayi, Husnah ta anshi wayar ta, ta soma dan na wayar tana shafar wayar,
suna labarin su, suna saka Husnah dariya, dan burin su Suhailah su saka Husnah cikin farin
cikin.
A can gidan su Zubaidah kuwa, suna ta chashe war su, ba bu ji ba bu gani, wasu dai sun ga
fitar Husnah amman basu kawo komai a ran su ba, har sai da aka kira wayar Zubaidah, tana fita
cikin mutane ta d'aga wayar tace, "hello yallabai an d'aura Auren kuwa? ".
Daga can d'aya ban garen, yalla'bai d'in yace, "a a an kusa dai akwai wan da muke jira, manyan
ba'kin mu, ina fatan dai Amaryar tawa, tana kusa, dan yau ina son jin muryar ta, ki bani ita muyi
magana naji wannan zazza 'kar muryar ta ta, kamar yanda nasaba jin ta idan kuna waya da ita,
yau nima nad'an d'ana mana kafin tazo gida na, ta zama ni d'aya zan ri'ka jin muryar ta".
Dariya Zubaidah tayi ta ce, "to ranka ya dad'e bari na kira maka ita, na bata wayar ".
Da wayar a hannun ta ta nufi cikin gidan bata ga Husnah gurin da ta bat taba, ta nufi d'akin
Husnah nan ma babu labarin Husnah, haka tayi ta zaga gidan kamar da wasa abu ya zama
gaske gidan kowa ya shiga cikin tashin hankalin neman Husnah wasu suce, sun ga fitar ta,
wasu kuma suce basu ga kowa ba, ai kuwa gidan biki ya zama jaje da neman inda Husnah ta
shiga.
Shi kuwa yalla'bai d'in ya ce, "wallahi sai an nemo ta kuma wallahi kar wadda ta yarda tabar
gidan namiji ne ko mace".
Zubaidah ku ka kawai takeyi kukan gaskiya takeyi bana wasa ba, test message ne ya shigo a
cikin wayar ta, ai kuwa cikin rawar jiki ta duba kawai ta tashi tsaye ta kurma uban ihu ta fad'i
'kasa babu rai a tattare da ita.
To mike nan Zubaidah ko ta mutu ko tana raye!
Shin wane sa'kon ne ya firgita Zubaidah har haka?
Kudai ci gaba da bin Ummu IHSAN dan wal_wale maku wannan 'kullin
*Comment and share*
*Ummu Ihsan ce*ğ¹ğ¹ğ¹ğ¹ğ¹ğ¹ğ¹ğ¹ğ¹ğ¹ğ¹ğ¹ğ¹ğ¹ğ¹
8/25/21, 7:20 PM - Ummu Ihsan ce ğ¹âğ?: ğ®ğ®ğ®ğ®ğ®ğ®ğ®ğ®
*°â¢Â°A GIDANTA NA GIRMA°â¢Â?*
ğ®ğ®ğ®ğ®ğ®ğ®ğ®ğ®
*BY NANA: KHADEEJATU*
*_UMMU IHSAN_*
*SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU
SOSAI SON FISABILILLAH*
*YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA
SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.*
*YA ALLAH KA BAIWA MAMANA LAFIYA KA BAIWA DUK KANNIN WANDA BAIDA LAFIYA
NA GIDA DANA ASIBITI ALLAH KA BASHI LAFIYA AMIN YA ALLAH*
*Hahhhh wayyo ciki na wallahi duk kun bani dariya masoya, ita mommy Zubaidah kukeyi
wannan mugun fatan? .*
*Kai Djamila idan nice na turowa mommy Zubaidah sa'ko ai sai na sanar da ita inda kuka 'boye
mata "ya.*
Ina godiya sosai da Comment din ku da sharhin ku masoya.
*Nafsy a gaskiya shar hinki na sakani farin ciki ina godiya sosai*
*Kamar irin kowa da kowa duk ina godiya sosai da addu'ar ku*
My takwara jin jina da ban girma a gareki*
*A GIDANTA NA GIRMA*
*_Bismillahir Rahmanin Rahim_*
61~65
Duk kan nin mutanen dake gurin sai sukayo a kan Zubaidah suna fad'ar, "Zuby! Zuby!!
Zuby!! " suna gir giza ta amman inaa ko motsi Zubaidah batayi ba.
Wani guy ne ya yi dabarar d'ebo ruwa ya yayyafa mata a take ta saki ajiyar zuciya, da 'karfi, ta
kurma uban ihu, ta tashi tsaye tana dube_dube, ta ce, "na shiga ukku ni Zubaidah Husnah ta
gudu ya ya zanyi da rayuwa ta ne? Gashi Husnah harda su turo mani sa'ko wai ita tabar ni, ni a
daura Auren dani! "
Yaya zanyi da rayuwa ne ni Zubaidah Husnah ta tona mani asiri a idon duniya, Husnah yan zun
ne na kejin takai cin rashin hankalin da nayi, na yarda da fitowar ki, bayan nasan nayi, nayi ki
tashi kiyi hakuri ki shirya tun waye war gari, amman kika 'ki yarda, sai yanzun ne, daga baya
kika nuna mani kin fini iya bariki nida na haifeki da ciki na, amman kizo ki fini, kwarewa a gurin
bariki, na d'auki alwashin duk inda kika shiga sai na gano ki!
"Zubaidah" ke nan take magana a cikin fushi da nuna 'bacin rai, su kuwa mutanen dake gurin,
duk sunyi zuru_zuru suna kallon ta, wayar tace, ta d'auki 'kara, bata ko duba mai kiran ba, ta
d'auka ta saka hans free, kawai sukaji, muryar yallabai yana fad'ar, "Zuby kin raina mani da
wayau dake da "yar ki da 'kawayen na baki to, kusani, dukan ku wanda yake cikin gidan da yar
ki, da ke kanki, zanyi maganin ku, kuma ku saurari sharri na d'aya bayan d'aya kuma duk wani
abu nawa wanda ki ku san cewar nawa ne, ni na baku ku dawo mani dashi, daga nan zuwa
gobe, kuma kad'in da na turawa Husnah ko naira, ban yarda ba, ace ta 'bata, kuma kusani ba
iya nan na tsaya ba, sai kunyi nadamar sa ni na a rayuwar ku, kuma na koreku aiki ga baki
d'aya ".
Tunda suka fara sauraren wayar, har aka gama wasu na kuka hawaye sha re_sha re a idon su,
wasu kuma hannun su, suka d'aura a kai, dan kowa yasan waye yake magana kuma sun san
zai aikata duk abunda ta fad'a, ba bu fashi.
Tsine wa Husnah kawai sukeyi tare da Zubaidah tunda kowa sakacin Zubaidah yake gani, kowa
ya manta da nasa laifin.
Husnah kuwa hankalin ta, kwance, yake, har tama manta, da cewar ta baro fitina a gidan su.
Tun lokacin da Husnah tazo gidan har dare bata fito cikin falon gidan ba, haka Husain, duk abun
da Husnah take bu'katar sa, a take ake kawo mata shi, Husnah ta zama kamar wata yar gidan.
Hankalin Husnah a kwance ta shari baccin ta, tun 'karfe tara na dare take bacci sai 'karfe goma
na safe ta falka, su Anisah mamakin irin wannan baccin na Husnah sukeyi, amman ita hankali
kwance take yin abin ta.
Husnah na falkawa, ta shiga toilet, tun suna hakurin jiran ta, har sai da Suhailat, ta nufi bikin
'kafar bayin ta soma, kiran, "wallahi ki fito haka nan dubi mutum kamar wadda bacci ya d'auka a
ciki"
Husnah dake cikin bayin ta ce, "ke malama, son kikeyi na fito a ji jikina, na tsamin d'aud'a, haka
kawai, kawai dai ki barni, idan na gama son rai na, sai na fito, zaki saka, ni na fito ban wanke
wani gurin ba, ko na fito, wani gurin bai ma san anyi wasar ruwa ba".
Ai kuwa ga baki d'aya suka, had'a baki gurin fad'ar, "Allahu akbar jaa muje muslima".
Ai kuwa sai ganin Husnah sukayi ta fito d'aure da towel a jikin ta, sai dariya takeyi, kamar wata
hauka sabon kamu harda hawayen ta, dan dariya.
Kallon ta, kawai suka tsaya suna yi, Anisah ta kasa hakuri ta ce, "Anty Husnah lafiyar ki kuwa
wan nan dariyar haka? "
Husnah ta ce, "ku dan jira na gama shirya wa, zan baku amsa d'aya bayan d'aya".
mai da hankalin su sukayi gurin Husnah suna kallon yanda take shirya wa komai cikin tsari
kuma hankali kwance, trolley d'in ta, ta d'auko ta bud'e ta, mugun mamaki sukeyi ganin yanda
duk kayan Husnah suke 'kananan kaya, babu atamfa ko d'aya a cikin kayan, ita kuwa hankalin
ta a kwance ta saka riga da wando, rigar pink da kwalliyar yellow, sai wando, jeans blue, ta
gyara gashin kanta, ta saka ribom pink da yellow, mai kawai ta shafa, da yar powder ta, sai
turare kusan biyar sannan taje ta d'auki hijab ta saka, ta d'auki sallaya, ta shimfida ta, tayar da
sallar Asubah.
Duk suka rungume hannun su, suna kallon Husnah har ta kammala, bayan ta idar ta dad'e a
zaune kafin ta, tashi, tayo gurin su, cikin murmushi Husnah ta ce, dasu, "antashi lafiya ya
gidan? ".
A tare suka amsa mata da, "Lafiya lau Alhamdulillah dafatan kin tashi lafiya ".
Dariya kawai Husnah tayi bata amsa masu ba, suna dai ta bin Husnah da, ido ganin irin yanda
kayan suka kama mata jiki, suna cikin kallon Husnah, kawai Husnah ta ce, dasu, "to muje kuci
abinci ko? Dan nikam sai 'karfe sha biyu nake karyawa".
Duk suka zaro mata ido, suna fad'ar "wane irin sha biyu? Mukam tun 'karfe tara munci abinci, ki
dai chanza shawara, kije kici abinci kuma ku gaisa dasu Ummey".
Husnah tace, muje kawai mu gaisa amman abinci ba yanzun ba".
Haka suka kama hanya, amman su kunyar shigar da Husnah tayi sukeyi, amman kuma, abun
mamaki Husnah harda takalmin ta, masu uban tsini ta saka, kuma hankalin ta, kwance take
tafiyar ta.
A falo suka sami su Hajiyar Husnah Kawai ta 'karasa gurin Hajiyar ta rungume ta, cikin so da
kauna, Husnah tace, "ina kaunar ki Ummey, barka da safiya da fatan kin tashi lafiya ? ".
ajiyar zuciya Hajiyar tayi, cikin tausayin Husnah wadda tun fitowar su, Hajiyar ta kafe su da ido,
ita ma ta rungume ta, ta ce, "lafiya lau Alhamdulillah Husnah da fatan kin tashi lafiya, ya ba'kun
ta, ya kika kwana ina fatan dai su Anisah basu takura maki ba? ".
Dariya Husnah tayi ta ce, " a a ba suyi mani komai ba, sai tattalina, dai_dai da shigowar su
Husain da Shaheed da Yaya Yusuf da Baby, ai kuwa Babyn tayo kan Husnah da gudun ta, ta
rungume Husnah, itama Husnah cikin jin dad'in ganin Babyn kawai ta saki Ummey ta rungume
Babyn suka sanya dariya, su Shaheed sakin baki sukayi suna kallon Ikon Allah.
Husain kuwa cikin zafin zuciya ya ce, "kee! Uban waye ya baki damar da zaki ri'ka yiwa mutane
wannan muguwar shigar, ta karuwai, ko an fad'a maki nan ma gidan karuwan ne!?.
Ba Husnah ba, hatta Ummy da duk wani wanda yake gurin yaji ciwon wannan maganar da
Husain yayi wa, Husnah wadda suka fahimci cewar ita bata da laifi, saboda abun da ta taso ta
ga an koyar dai ta , to shine itama take amfani dashi, amman sun d'auki alkawarin taimakon ta,
su maida ita tamkar yar gidan kowa.
Ko kallon inda yake Husnah batayi ba, kawai taci gaba da, fad'ar "Baby nayi kewar ki, tun da
nazo gidan nan ban gane ki ba, kawai dai yau ki kasan ce tare dani muyi firar mu ko? ".
Yarinyar dakewa tayi dan tsawar da Husain ya doka wa Husnah, duk sun fir gita da ita.
Husnah kuwa lura da kallon da Husain ke jifan ta da shine ya saka ta fad'ar, "nikam na tsani
yawan shiga cikin mutane masu yawan surutu kawai aje a fasawa mutum dodon kunne a kaisa
a baro, shi mutum idan yasan iska ya kad'a to mi zai saka shi shiga gurin mutane masu
natsuwa? , ke Baby zo mubar gurin nan muje cikin d'akin can muyi firar mu".
Tashi Husnah tayi, ta ja hannun Babyn suka bar gurin, ai kuwa kallon tsana kawai Husain ke
jifan ta dashi gashi ta sakar masa magana Ummey ta galla masa harara, ta hana shi ya d'auki
wani mataki, duk sai yaji ya 'kara tsanar Husnah.
Yaya Yusuf ya ce, "dan Allah Husain kada ka hawa kanka raini a gurin yarinyar nan, kana jifa
sai da ta rama abun da kayi mata ".
Share sa Husain yayi sai cika yake yana batsewa, Shaheed ya ce, "Hajiya Auren nan fa ya fasu
ba'ayi sa ba, acewar wani aboki na, amman kuma ita mahaifiyar Husnah tana kwance bata da
lafiya dan yau tun safe aka kaita asibiti, hawan jinin ta ya taso, yan zun yaya ya kama ta ayi ne?
"
Ummey ta ce, "Ajiye wannan maganar Shaheed bari har Daddyn ku ya dawo, nasan zaiyi
magana akai cikin hanciyar hankali, kai kuma Husain nadawo kanka, ka kiyaye ni fa! , kai wai
ma, tun da ka gama ginin gidan ka, ka saka komai, tun shekaru biyu da suka wuce, to yaushe
ne zaka kawo mani, matar da zaka Aura dan son nakeyi naga naka jikokin ga Shaheed nan
cikin satin nan zamuje mu kai kud'in hidimar bikin sa, amman kai 'katon banza, kana nan kana
ta kurawa 'kannen ka, to kasani, daga yanzun zan matsawa mahaifin ka, ayi gaggawar matsa
maka ka fito da matar Aure haka nan! ".
Zufa ce, take zubo wa Husain ta ko'ina, amman sai gun_guni yakeyi, zuwa can ya ce, "Ummey
nifa har yanzun ban samu budurwa ba, duk yan matan yan zun basu da hankali ".
Dariya kawai suka sanya masa, Hajiyar kuwa tace, "zakayi bayani ne Husain kwanan nan".
Haka dai su yini Husnah sai 'karfe goma sha biyu tasha shayi da biredi tace shine kawai take
ra'ayin ci.
Daddy na dawo wa Hajiyar ta sanar dashi halin da ake ciki, a take ya kira Husnah yace, ta
shirya yau zasu je gidan su.
Zufa ce Husnah take zubo mata, sai yan zun ne ta tuno da Auren da aka shirya yi mata, to
miyasa Daddy yace sai sunje gidan su cikin tsakiyar rana, ita kam taga ta kanta.
Babu yan da Husnah ta iya haka ta shirya suka nufi gidan batare da tasan dalilin zuwan nasu
ba.
Suna shiga cikin gidan zuciyar Husnah kamar ta fashe saboda far gaba, suna yin parking suka
fito dukan su, Husnah kuwa cikin sanyin jiki take takawa, har suka shiga cikin falon gidan suna
rafka, sallama amman basu ji a anmsa masu ba, Husnah dai tana baya ita d'aya kuma tasan
daman babu wanda zai iya amsawa, acikin tawagar Mommy, sannan kuma ai taga ba'kin motoci
harda wanda ta sani, da wanda bata sani ba.
Zazzaune suka sami mutane maza da mata dukan su babu mai shigar mutumci, a cikin su,
Husain jin yakeyi kamar ya kashe su, saboda tsabar takaicin da yakeji nasu.
Zubaidah ce kwance sai fifita akeyi mata, Husnah na d'aga idon ta, kawai ta hango Zubaidah a
kwance duk ta rame tayi ba'ki kamar ba Mommy yar gayun nan ba.
Da gudu Husnah