Showing 54001 words to 57000 words out of 73304 words
Chapter 19 - A GIDAN TA NA GIRMA COMPLELET. BY UMMU IHSAN.pdf
bayane na wannan
mutanen sannan sai kunyi hakuri dan zan dad'e ban zo ba, kudai kuci gaba da yi masu addu'a
".
Amsa mata sukayi badan sun yarda da ita ba, suka koma gida suka sanar da kowa abunda ya
faru har had'uwar su da Tk, su Daddy sun jin jina al'amarin, haka sukaci gaba da addu'a.
A can wani gurin kuwa?
Husnah na ce kwance jikin ta da bandeji kwance take akan wata jibgegiyar kujera mai kamar
gado kuma ba gado bane sai laushi, ga sanyin A/c na ratsa ta tako ina gurin sai 'kamshi ke
tashi.
Motsawa ta soma yi ta saka hannun ta, ta dafe hannun ta, ta bud'e idon ta ta soma biyar ko ina
da ido tashi zaune tayi a zabure, ganin gurin da take kwance a halin yan zun sai ta shiga cikin
mummunan tashin hankalin saboda tsin tar kanta tayi a 'kasar da tasu ba, duk irin had'uwar
gidan su sai taga ba komai bane, sauka tayi a 'kasa d'akin duk glass ne ta ko ina, hankalin
Husnah ya kai matu'kar tashi, jin zugin da hannun ta yakeyi ne ya saka Husnah duba hannun a
take ta tuno abunda ya faru kawai ta dur'kusa 'kasa ta fashe da kuka ".
Husain kuwa bud'e idon sa ke da wuya ya soma ganin hazo_hazo jiri_jiri duhu_duhu fankar
dake li'ke a sama ita ce ke juyawa, shi kuwa jin yakeyi kansa na juyawa dafe goshin sa yayi
kansa na yi masa mugun ciwo kan nasa nad'e yake da bandeji, tashi zaune yayi gurin da ya
tsinci kansa ne ya 'kara d'aure masa kai dube_dube ya farayi d'akin glass ne kuma inda yake
zaune carfet ne tsanwa mai ruwan ciyayi, mamaki ne fal ransa, dafe kan nasa yayi da hannun
sa duka biyun.
Wata 'yar 'kara ce ya jiyo daga bayan sa kawai ya d'ago kansa a hankali ya juyo, mutane ne su
biyu murtu'ke da fuska jibga_jibga dasu babu alamar tausayi ko nan da can, suna 'karasowa
kawai suka saka hannuwan su suka tallabe Husain wanda yake ta kokarin su sauke shi 'kasa
amman ina ko sauraren sa basuyi ba , sukayi waje dashi, gashi sunyi masa ri'kon bawa da
maigida basu ajiye sa ko ina ba har sai da suka shiga wani katafaren hadden falo ma girman
gaske, a gaban wani mutum ne suka sauke sa da 'karfin gaske har sai da yace wash!.
Husnah kuwa tana cikin kukan ta, wata tsohowa ce ta ce, "yata taso muje kiga wani abu".
Husnah na ganin wannan matar kawai ta tsare ta da ido dan ganin takeyi kamar mafalki takeyi,
hannun Husnah ta kama ganin Husnar ta zama status da ita, cikin falon akayo da ita inda aka
ajiye Husain a nan aka ajiye ta, a gaban wani mutum wanda bai d'aga fuskar sa ba amman
mutanen daga ganin sa kasan babu imani a tattare dashi.
Sun dad'e da zama babu um ba um_um, Husnah bata san da akwai mutane a gurin ba illah
mutanen da tagani an ajiye ta a gaban sa sai kirjin ta ke dukan uku_uku.
Husain kuwa tun isowar Husnah ya maida hankalin sa akan ta, har ta zauna yanda take kallon
mutanen ne yasaka shi maida hankalin sa, a can gurin.
Mutanen ne ya cire malfar da ya rufe fuskar sa da ita yana kallon su ya kalli Husnah ya kalli
Husain, idon mutumen jawur dasu gashi ba'k'ki 'kirin dashi kamar bayan tukunya.
Wata irin dariyar keta ce ya bushe da ita ba bu dad'in sauraren ta hahhhhh, yace, "Husnah yau
gaki ga mijin ki wanda baki da wani mijin bayan sa, nine yalla'bai d'in da kikaji zuby na fad'a
nine wanda na tashi Auren ki, a ranar kika gudu, gidan su saurayin ki wannan kika 'bata mani
suna a gurin abokan hulda ta" ya nuna gurin da Husain yake da hannun sa.
Gurin da yayi mata isharar ne ta maida hankalin ta, waye zata gani inba Husain ba, suna had'a
ido dashi take suka d'auke idon su suka mayar akan mutanen.
Mutanen yace ya naga kunyi kamar baku san junan ku ba? Bayan nasan tunda ku ka zauna a
guri d'aya har tsayin wattani bakwai ai nasan kun murji anarci da kyau tunda gashi har yan zun
baku tashi haihuwa ba, nida naso na ganki da ciki, sannan na d'auke ki tare da mijin na saka a
ciro mani dan a gaban idon ku, na saka wu'ka ta na yanka jin jirin nasha jinin sa, nasa a kaiku
kichin a gaban idon ku a dafa mani naman nacinye duka, akan idon ku, amman kash! Hakan
bai samu ba, to yan zun zan yi maku hukun ci irin wanda ya dace, kai goga! Ka saita Bindigar
nan ka kawo mani ita a nan! ".
Da sauri wanda aka kira da goga ya cika aiki, ya kawo bindigogi guda biyu, ya ansa ya saita su
ya halbi yaran sa guda biyu a hannun, ji kake darammm_darammm, su kuwa cewa sukayi
washi, suka dafe gurin, sai jini ke zuba ido yayi kamar an watsa masu barkono.
Husnah da Husain duk sai da suka zabura, mutanen da yaran sa cike da d'akin suka bushe da
dariya harda doka 'kafa.
Sai da sukayi dariyar su mai isar su, sannan mutanen yasha mur ya had'e rai yace, "Husnah
keda wannan munafukin ku ri'ka kowa ya halbi dan uwan sa, gurin da yake so"
Mika masu Bindigar yayi yana d'aure da fuska, kin amsar Bindigar sukayi, kawai ya ce, "to ni
zan halbe ku da kaina ta inda naga yafi burgeni ".
Mur yasha, ya saita Husnah a goshin ta, ya saita Bindigar d'aya a saiti da zuciyar Husain ya
gyara zai halba da sauri suka anshi Bindigar suka tashi tsaye suna ri'ke da bindigogin a hannun
su, tsawa ya daka masu wadda sai da Husnah ta zabura kamar zata fad'i 'kasa, daket ta saita
kan ta, tayi tsaye, tsawar ya 'kara daka masu ya anso wata Bindigar zai halbesu, kawai sukayi
saurin sai ta junan su da bindigogin Husain ya sai ta Bindigar sa a kan Husnah, itama Husnah
ta saita Bindigar ta akan Husain, sai zufa ke zubo masu kawai Husain ya ce da Husnah, "
daman nace sai na kashe ki da hannu na yau ga dama ta samu, kinga babu mai yi maki magiya
ballema a hana ni aikata hakan " ya bushe da dariya.
Husnah kuwa dariya ta bushe da ita, tace, "to kai ka manta yanda akayi har na yarda na zauna
dakai? To ka sani daga yau sai nabar tarihi nice mace ta farko wadda ta fara kashe mijin da ya
damu da ita"
'kara saita Bindigar sukayi a take suka halba, jin kake
darammmmmmmmm_darammmmmmmmm.....
Dai dai saiti da shigowar su Anisah Tk Zubaidah Yaya Yusuf, wata irin 'kara suka fasa, suka
dafe kai.......
*Comment and share*
*A GIDANTA NA GIRMA*
*BY NANA: KHADEEJATU*
*_UMMU IHSAN_*
*SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU
SOSAI SON FISABILILLAH*
*YA ALLAH KAJIKAN BABA NA DA MAMA NA KAYI MASU RAHMA KA KYAUTATA
MAKWANCIN SU KA SANYA SU A ALJANNAR KA TA FIRDAUSI BIGAIRI HISAB SU DA YAN
UWA MUSULMI BAKI `DAYA.*
*AMIN YA ALLAH*
*To Alhdulillah Allah ya nufeni da dawowa gashi zamuci gaba daga inda muka tsaya*
*_Bismillahir Rahmanin Rahim_*
95~100
Wani irin uban ihu duk mutanen gurin sukayi, babu kamar yallabai wanda ya fad'i kwance 'kasa
cikin jini yana zabga uban ihu hannun sa d'aya dafe da ka fadar sa, d'aya hannun kuma dafe da
cinyar sa, sai jini ke zuba, mutanen gurin cike da mugun mamaki suke kallon Husnah da Husain
da yallabai wanda ya fita cikin hayyacin sa, abunda ya 'kara baiwa mutanen mamaki shine
ganin Husain da Husnah a tsaye ri'ke da bindigogin suna a jere da junan su, sun 'kara saita
Bindigar akan yalla'bai kuma Husnah itace ta saita zuciyar yalla'bai Husain kuwa ya saita
Bindigar sa akan yalla'bai, duk cikin jin haushin abunda su Husain da Husnah suka aikata wa
ogan su, kawai suma suka d'auki bindigogin su suka saita su Husnah da su.
Husain yace, "ashe dai ku duk kidahumai ne tunda har kukayi tunanin zamu iya kashe kan mu
da kan mu mu aikata kusan kai, amman gaskiya na kara raina maku da wayau tunda har kukayi
sakacin zama baku sha maganin bindiga ba, ai kuwa zamu 'karasa kashe mugun iri inyaso
kuma sai ku kashe mu"
Husnah tace, "yalla'bai kaga yaran nan naka basu damu da abunda muka aikata maka ba,
tunda ka gan su nan kowa ya nemi Bindigar sa dan ya kare kansa kai kuma indan ta sune mu
'karasa kashe ka, ko suma sun gaji da goyon bayan ba, saboda haka kasan nayi fa, daga yau
kayi ban kwana da wannan izzar taka da mulkin zalluncin al'uma".
'kara saita har sashen su Husnah da Husain sukayi zasu sake halbawa, cikin tsawa da
rad'ad'in aza yalla'bai yace, "ku... da... Kata... Dan.... Allah, kada ku kashe.... Ni..... , ku fad'i
abunda..... Kuke da bu'katar sa.... koma miye koda duka dukiyar... Dana tara ne.... ".
Da sauri Husain ya ce, "dakata! An gaya maka cewar mu shasha sune da zaka bamu dukiyar
haram mu ansa? To idan bacci ma kakeyi yanzun ka falka fansar a d'aya ce, ka basu umarnin
su kawo bindigogin su anan su ajiye su a gaban mu kuma duk su durkusa 'kasa kai suma
kwanta su rufe ido indai har suna bu'katar ganin ka a raye!,
Kuma wannan yan uwan nawa da suka shigo a yanzun nan ka bada umarnin a maida su gida
lafiya ba tare da wata damuwa ba"
Cikin tsawa da a zabar da yalla'bai yake ji ya basu umarnin yanda Husain yake bukatar ai kuwa
sukayi tsalle suka dire suka ce, "mufa sam bamu yarda da wannan maganar ta gamam min
ha'kori ba kawai dai ka bar mu dasu mu kashe su dama kasan muna da haushin su a can baya
lokacin da ka saka su goga gadin wannan masifar lokacin da suka suka saka muka rasa
mutanen mu suka saka aka kaisu a gaban hukuma dan haka gara kabar mu mu kashe makiyan
mu! "
Husnah tace, yalla'bai kaga sun nuna maka shedar sun fi kowa farin ciki da ganin bayan ka,
tunda sukeyi maka fatan barin duniyar nan".
Cikin masifa yalla'bai yace, "idan kuka yarda suka sake aikata mani irin wannan raunin saboda
gardamar ku, to ba kuba har dan ginku sai na 'karar dasu..."
Tunda suka fahimci da gaske yalla'bai zai iya aikata fiye da abunda ya fad'a duk sai suka
saduda sukayi yanda su Husain suka bada umarni aka fita dasu Yaya Yusuf ta wata hanya
wadda Zubaidah ta nuna masu tace, "indai da gaske ne gidan zasu kaimu to nan ne kawai
hanya mafi sau'kin bi".
Anisah da Tk da Shaheed wanda suke cike da mamakin taya su Husain da Husnah suka koyi
irin wannan aikin suda ba training din koyon halbi sukayi ba, daket suka ajiye tunanin suka ce,
"kai gaskiya babu inda zamu saboda mutseratar da rayuwar mu, mubar ta yan uwan mu a cikin
hatsari"
Husain da Husnah cikin masifa sukace dallah ku tafi so kukeyi ayi mutuwar kasko anan ne?
Iye? ".
Tafiya sukayi badan sun soba sai dan ganin irin yanda su Husnah da Husain suka hasala, suna
shiga hanyar kamar labule suka wuce zuwa wanda suka kaisu suka dawo suka nuna masu
video sun kai su, murmushi su Husnah sukayi.
Husain yace, "to ranka ya dad'e sun aikata yanda muke so, amman kuma wani hanzari ba gudu
ba, nasan halin ka gaba da baya zaka iya idan mun barka a raye zaka iya biyar mu da dangin
mu ka kashe kaga kuwa mun kashe wutsiyar maciji mun bar kai da gan_gar jiki, kaga kuwa da
sauran Rina a kaba ke nan ".
Husnah ta ce, "dan haka gara mu fara kashe ka kaida yaran ka, tun kafin ka kashe muna kowa
namu, muma ka kashe mu".
Cikin zabura wani yazo tashi ya d'auki Bindigar sa, Husnah ta dawo da Bindigar akan sa, tace,
wato kaine kake son zama farkon mutuwar ko? ".
Jin Bindiga a akan sane ya saka shi fasawa, cikin rawar jiki yaja baya Husnah tasa 'kafar ta, ta
ri'ka tura bindigogin nesa dasu, sannan ta gyara tsayuwar ta ta ce, " yalla'bai ina da bukatar
aron waya, dan ba zamu rabu da ku haka kawai kuji dad'in ganin bayan mu ba, dan haka gara
musan nayi tun kafin lokaci ya 'kure muna ".
Yalla'bai ya ce, "dan Allah kada ku had'a mu da hukuma d'an sun dad'e suna nema na basu
ganni ba, amman ni ina ganin su, kuma koda sun ganni a lokacin ba zasu iya aikata komai a
kaina ba, yau ita ce rana mafi muni a gareni domin kuwa tun kafin hakan ta faru masu yi mani
duba sun sheda mani wata rana sai na d'auko wa kaina wanda zasu ga baya na, kuma duk
tsafina baya aiki akan su, ni kuma shine na na saka akayi mani duba ga duk yara na, amman
sam ba su bane wasu ne can na daban mace da namiji kuma babu wanda yake ganin fuskar
su, shi yasa nake ta kashe duk wanda na d'auko koda kuwa a ce mace mai tsohon ciki ce, da
mijin ta sai na kashe su, gudu ni su kashe ni".
Kuka Husnah ta saka ta ce, "shi.. Ke.. Nan ka yarda da tsafin ka sabawa Allah kake kashe
mutanen da baine ka kawo su duniyar nan ba, kuma shine kaso ka 'bata mani rayuwar ka Aure
ni, ka kashe ni da raina..! "
Kuka kawai Husnah keyi, "Husain cikin tsan_tsar tsana ya dubi mutanen gurin a wulance, yace,
"tir da rayuwa irin wannan, wallahi kun daukar wa kanku kaya, kuma tunda har masu tsafin ku
sun sheda maku cewar mune zamu kashe ku, mun fasa, idan kun so mu ku kashe mu, amman
mu bamu yarda da tsafi ba, ballema mu zamo masu cika umarnin matsafa, kawai Husain ya
jefawa yalla'bai Bindigar, ya juya gurin Husnah ya anshi Bindigar hannun ta ya ajiye sukayi
zaune a 'kasa suna dafe da kai Husnah na kuka harda hawaye da majina Husain kuwa kukan
zucci yakeyi idon sa yayi mugun ja, jijiyoyin kansa duk sun tashi saboda tsabar shiga cikin
tashin hankalin.
Su kuwa yaran yalla'bai suna ganin haka da sauri suka d'auki bindigogin su suka sai ta su
Husain dasu, yalla'bai ne ya basu umarnin da su rabu dasu su kai sa d'akin sa, ayi masa aiki.
Ya bada umarnin a fita dasu Husnah daga cikin gidan.
Cika umarnin sa sukayi suka tasa Husnah da Husain a gaba suka fitar dasu daga gidan su
Husnah na fita mutanen ya koma tanga menen gidan dan baiwa ogan su kulawa, sauran kattin
dake harabar gidan ko kallon su Husnah basuyi ba, saboda suna lokacin da aka fito dasu duk
da cike suke da mamakin wannan shine karon farkon da aka ta'ba shiga gidan da mutane kuma
suka fito da ransu da kafafuwan su, har suka isa bakin get maigadin gidan suka bud'e masu get
din cike da mamaki, su Husnah da Husain ba fita daga cikin gidan aka rufe get din kawai suka
ga ashe ma cikin uban jeji suke kallon_kallo aka shiga yi, tsakanin Husnah da Husain, sai duba
gurin da suke sukeyi.
Rasa ma wace hanyar ce zasu kama, sukayi tunda gurin duk itace ne da shikko ki babu alamar
gurin da mota ko mashin suke bi.
Tsaye suke sun ri'ke 'kugu suna dube_dube, wata murya sukaji marar dad'in saurare daga
bayan su ana fad'ar, tunda kuka ki kashe sa, to kusani ba zaku iya fita cikin jejin nan ba, idan
kuma kuka dawo zaku shiga cikin gidan ku kashe shi da hannun su, to zaku sami hanyar fita
daga cikin jejin nan cikin sau'ki".
Husain ya ce, "mu ba jahillai bane kuma ba zamu cika umarnin wani banza ba, sha katafi, kuma
mun dogara ga Allah shine zaiyi muna mafita! ".
Husnah tace, "idan su kun samu damar batar dasu, to mu munyi imani da Allah kuma munyi
imani da kaddara mai kyau ko marar kyau dan haka insha Allah yau a gida zamu kwana".
Husnah harda su Murgud'a baki kamar irin taga mai maganar nan.
Tafiya suka fara yi a jere duk sun gaji har suka bar kofar gidan kawai sukaji wani uban ihu da
gir_giza sai kuma sukaji wani irin dammm kamar bom ya tashi sai hasken wuta suka gani ga
iska mai 'karfi gaske ya taso da 'kura itacen gurin kamar su karye da wani irin 'karfin gaske
Husain ya janyo Husnah ya rungume suka kama wani icce suka ri'ke sai addu'a sukeyi duk
wadda tazo bakin su, aikuwa sannu a hankali har iskan ya daina jan su, kawai ma suka daina
jin iskan a jikin su iskan yayi gaba, kawai sai zafin wuta ga hasken ta, kafin su Husnah su
'karasa mamaki sai kawai sukaga itace sun 'bace, gidan da suka baro ne keci da wuta
bal_bal_bal cike