Showing 3001 words to 6000 words out of 73304 words
Chapter 2 - A GIDAN TA NA GIRMA COMPLELET. BY UMMU IHSAN.pdf
Audu ne wato Yayan
malam Sa'idu shida wasu yan uwan sa harda mata a cikin su sun kai dai su biyar.
Kallon su Zarah sukeyi da suketa zufa ga gajiyar wanki ga zafin rana ga yunwa, girgiza kan su
sukeyi tare da kallon yaran Malka dake cin abinci a kusa da dan uwan su.
'Kara sowa sukayi cikin gidan Malka duk ta tsure karyar ta ta 'kare yau sai tayi mutuwar zaune
dan batayi zaton cewar maganar daukar su Zarah tana nan ba dan har ta manta da wannan zan
cen.
Alhaji Audu ya kalli d'an uwan sa yace, "anyi walkiya mun gano komai Zarah had'o kayan ki mu
tafi Amina kuma zata zo ta d'auki Husnah zuwa gobe".
Wani kukan ne ya kama su Zarah da Husnah ai kuwa sunci kuka da ket aka raba su aka tafi da
Zarah.
Husnah sai ta dawo abar tausayi yanzun kam ta zama marainiya ga rashin uwa ga rashin Yayar
ta kuma abun takaici babu mai janyo ta jikin sa yayi lallashin ta.
Gabaki d'aya gidan zama yayi shiru saboda Malka yan zun han kalin ta yayi mugun tashi
saboda taga alamar fa yaran nan za suyi gaba fa ita kuma ta d'auki alwashin wula'kan ta
rayuwar su sai sun zama abun kwatance.
Baban kuwa kamar baya gurin haka ya zama.
Da dare Husnah batada abunda zataci abinci dole ta kwanta bacci ya kasa 'daukar ta gashi
tsoro takeji babu mahaifiyar su babu Anty Zarah, sai yanzun takara yarda da cewar itama fa tafi
kowa maraici kaka kawai takeyi ta dun kule guri daya, har bacci ya d'auke ta baccin wahala.
Run sanyi aka kwalaya mata, a take jikin ta ya d'auki mazari da rawar sanyi.
Malka ce a tsaye sai cika take tana batsewa ri'ke take da bokitin ta a hannun ta tana harar
Husnah tace, "uwar kice zata fito ramin tazo ta hura wuta ta d'ora Abinci tayi mani shara da
wanke_wanke Iye? "
Girgiza mata kai kawai Husnah keyi, sai rawar sanyi takeyi Malka tace, "tsohuwar munafuka
karuwa lalatacciya shegiya maza jeki kifara yi mani aiki tun kafin na kasheki da hannu na! ".
Ai kuwa da gudu Husnah tabar d'akin taje ta had'o kayan wanke_wanke ta ajiye ta d'auki
tsintsiya ta soma shara tana kuka ga iska na bugowa ga sanyi na shiga cikin jikin ta, tana
'karasa sharar cikin rashin kwarewa ta d'auki bokiti taje ta d'ebo mata ruwan sai da ta cika
komai tafara kiciniyar d'ora girki gashi bata iya ba, ko itacen bata iya had'awa ba, Malka kuwa
duk abunda takeyi akan idon tane, kuma tayi kamar bata ganta ba, ganin har tara tayi ne yasa
kata zuwa gurin tasa hannu ta turata ta fad'i 'kasa, hannun ta ya daki dotsen murhun taji zafi
sosai, da sauri ta tashi ta bata guri tayi gurin wanke_wanke tana gamawa taje tayo alwala ta
shiga cikin d'akin nasu ta cire kayan jikin ta wanda ya soma bushe wa a jikin ta, ta tsane ruwan
dake kwance a tsakiyar d'akin san nan tayi sallar asubahi.
Har wucewar sha d'aya sannan aka kirata Malka tace, "dan uwar ki jeki ga ragin koko can 'kuda
nabi ki d'auka kisha dan kawai naji ance babu kyau horo da yunwa dana haneki kokon nan.
Allah sarki cikin rawar jiki da sauri Husnah ta d'auki kokon duk yayi 'kasa saboda iska gashi duk
yayi kakka'bi abun dai zar tausayi haka ta zauna ta shanye kokon har tana sarkewa, harda
sud'e kofin sai da Malka tace mata, "shegiya kada ki fasa mani kofi jeki kwaso sauran kayan ki
wanke mani su kuma akwai kayan da Zarah bata 'karasa wankewa ba jiya yanzun ki 'karasa
wanke su, dan uwarki dan baki sha kokon banza ba".
Babu digon tausayi haka ta kwaso mata kayan nasu harda su zanen gado wanda akayiwa
fitsarin kwance.
Har Husnah ta d'uka zata fara wan kewa aka doko 'kofar gidan aka shigo ko sallama babu da
ido kowa yake biyar su Baban ne ya fito daga cikin d'akin sa cike da mamaki yake kallon su,
haka Malka da yaran ta duk sun saki baki da hanci suna kallon 'kofar gidan.
Kallon kallo akeyi tsakanin Malka da Malam da yaran gidan Husnah kuwa kallo d'aya tayiwa
gurin ta d'auke kan ta ta soma jika kayan dan kayan sunfi 'karfin ta bata iyawa dasu sai dai
ji'ka_ji'ka.
'karaso mutanen biyu sukayi d'ayar tace, "bakwa bu'katar sallama da munyo maku, Am ba
zamu 'bata lokaci ba, nasani sarai wannan gidan shine gidan Sa'idu kuma mijin mataciya da
musaka, am batare da 'bata lokaci ba, munzo ne zamu d'auki "yar mataciya Husnah take ba? ".
Malka tace, "uban waye ya turo kune yace kuzo kuyi wa mutane fitsara 'kana nan yara daku?".
Kawai d'ayar tace, "ubanki ne ya turo mu kaji shegiyar mata ana magana da wanda yake
matsayin uban yarinya shine zaki wani sakawa mutane baki? Kuma idan kika 'kara kwatantamu
da 'kana nan yara sai mun nuna maki cewar munfi ma inda kike tuna nin kaimu".
Malam yace, "waye ya turo kune gidan nan? ".
Kai tsaye sukace, "Amina ce 'Kanwar ka ga photon ta, ansar photon yayi yace masu, "ga
Husnah can ke kizo kibisu".
Malka tayi tsalle ta dire tace masu, "babu inda zata, sai dai su d'auki Indo ko Nafi".
Kallon inda takeyi masu nuni sukayi suka bushe da dariya, d'ayar wadda tun zuwan su batayi
magana ba, tana dai kallon sune d'aya bayan d'aya tace, "Husnah muka zo d'auka kuma ita
zamu d'auki dan haka kubamu Husnah ta bud'e jakar ta ta d'auko bandir din yan naira dari biyar
biyar ta isa gaban Malka ta janyo hannun ta ta d'ora mata, ta wuce ta isa inda Husnah ta janyo
hannun ta suka zo zasu fita Husnah da sauri ta kwace hannun ta tayi cikin d'akin su da gudu
jakar da Zarah ta shirya mata jiya itace ta kama ta run gume, tayi zaune tana zabga kukan da
tarasa na miye ma takeyi, saukar lafiyayyen mari taji wanda ya d'aga mata hankali ya rud'ata da
sauri ta tashi tsaye Baban sune tsaye yana fuci kamar wani wanda yayi gamo da kumurcin
maciji, ya janyo hannun ta da 'karfin gaske ya fito d'akin da ita ya dan kawa matan nan su biyu
ita yace gata nan baiwar kuce duk irin hukunci da kuka ga damar yi mata kuyi mata shi saboda
ta 'bata maku lokacin ku kuma ku sani ita din baiwar kuce duk irin hukunci da kuka ga damar yi
mata koda laifi ko babu kuyi mata ai dai kun biya kud'in ta tunda kun bani dubu dari da goma
kun baiwa Malka dubu hamsin yaran gidan nan kowa dubu ukku ukku".
Dariya sukayi suka ja hannun Husnah wadda maganar da Baban yayi taka ma yi mata yawo a
'kwa'kwalwa sai kawai ta saki jikin ta tabisu babu wanda yayi yun 'kurin biyar bayan su babu
wanda ya tambayi sunan su kawai dai sun sayar da marainiya ne.
A cikin motar su suka saka ta suma suka shiga driver ne kejan taxi din, 'yan unguwar kuwa cike
da mamaki yaran da suka labe lokacin da suka ga zuwan wannan mutanen duk sunji abunda ya
faru ai kuwa suka sanar wa mutanen unguwar, ai kuwa mutanen na shiga motar har sun fara
tafiya aka bisu da jifa.
Da gudu suka bar unguwar suka d'auki hanya sai wani dajin a bakin titi suka tsaya, suka fito
suka sallami mai taxi din suka shiga tasu motar suka d'auki hanya tun sha biyun rana sai 'karfe
shida suka tsaya suka sayi abinci a wani hotel suka baiwa Husnah baiwar Allah Leda d'aya
suka d'auki nasu suna tafe sunaci ita kuwa Husnah ta 'kasa wani dogon motsi dan ta tabbatar
da wannan mutanen masu yanka kan mutane ne.
Jin jikin ta na rawa, gashi har 'karfe tara na dare yayi ne ya sakata yin saduda ta bud'e ledar ta
d'auko robar ciki ta lemo da naman kazar dake ciki ta soma ci, cin yuwa sai da ta 'koshi zuwa
dare misalin 'karfe sha d'ayan dare suka 'karaso inda suka tsaya a bakin titi matar d'aya ta
bud'e motar ta fito ta zago gurin Husnah ta bud'e motar ta janyo hannun ta daman Husnah ri'ke
take da jakar ta, fitowa tayi sukayi sallama tace mata jirani na kawo maki naki kason, ai kuwa da
murna matar ta sara mata, hannun Husnah ta ja suka tsallake titin a gurin wata 'katuwar mota
fara suka tsaya ta janyo remote ta bud'e motar ta saka Husnah a kujerar mai zaman banza ta
rufe, ita kuma ta zagayo ta bud'e motar ta d'auki wata jakar ta tsallaka titin ta kaiwa matar,
aikuwa da farin ciki ta ansa ta bud'e jakar cike da kud'i, sukayi sallama suka rabu.
Tana bud'e motar ta shiga kawai ta tayar da motar suka d'auki hanya tana tu'kin motar tana
kallon Husnah ganin duk ta takure guri d'aya sanyi yayi mata yawa sai tayi dariya tace.......
*Comment and share*
*GIDAN TA NA GIRMA*
*SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU
SOSAI SON FISABILILLAH*
*YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA
SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.*
*Alhamdulillah Allah muna godiya a gareka daka nuna muna sallah lafiya ya Allah ka karbi
ibadun mu ka yafe muna kura kuren mu amin*
*Ina yiwa kowa barka da sallah Allah ya mai_maita muna amin*
*_Bismillahir Rahmanin Rahim_*
11~15
Tayi dariya tace, "idan ma zaki saki jikin ki yarinya to ki saki jikin ki dan duk duniyar nan babu
wanda yasan wace ce ni kuma daga Ina nake sai Allah dan ko wannan matar ko sati d'aya ba
muyi da haduwa da ita ba, ke ko sunana na gaskiya bata sani ba, ballema wata Amina
gwaggon ki dan haka yariya sai kiyi mani biyayyah kamar yanda tsohon ki yace, idan kuma ba
haka nan ba him! ".
Ita dai Husnah da ido kawai take bin ta dan ba kowane irin zance take ganewa ba da manufar
zancen saboda karancin shekarun ta da kuma uban baccin da takeji Amman kalmar ta da
tafurta cewar, "gwaggo Amina bata santa ba ta bata tsoro matu'kar tsoro, tunanin ta ya bata
saceta kawai akayi, sai kuka takeyi tana kiran Aunty Zarah.
Wata uwar tsawa ta daka mata a take kukan ya bacewa Husnah sai ta kara firgita kamar kace
mata ar ta gudu sai zarar ido takeyi, Abu da kuruciya idan an natsu guri daya sai bacci ai kuwa
bacci ne ya dauketa mai cike da tsoro sai firgita takeyi acikin bacci, ita kuwa matar duk abunda
Husnah keyi akan idon tane kuma tsab tayi kamar bata sanda ita ba hankalin ta na akan titi sai
gab da asubahi suka iso cikin gari tayi tafiya sosai a cikin garin kafin ta 'karasa a wata unguwar
wani katon gidane ta nufa tayi horn aka bude mata ta shiga da motar a cikin gidan a gaskiya
duk da duhun asuba gidan kyawun sa yana nan daram bud'e motar tayi ta dauko Husnah tayi
cikin gidan da ita a kujerar falo tree star ta kwantadda Husnar ita kuma ta haye up.
Husnah sai 'karfe shidda ta samu falkawa ahan kali ta soma biyar falon da ido a figice kawai
idon ta na 'karasa sauka akan katowar plasma kawai ta zun duma uban ihu wanda sai da duk
wanda yake gidan ya firgita a tamanin duk suka karaso cikin falon harda matar da tazo da
Husnar ganin iri yanda duk ta rudene bataji bata gani sai ihun takeyi ne gashi su basuga komai
ba kawai da sauri matar ta karaso gurin Husnar ta riketa tana girgizawa tana fadar, "kee Husnah
lafiyar ki kuwa uban miye kika gani wanda ya tsorata ki da har kike rafka wa mutane irin wannan
ihun iye!? "
A cikin masifa take zancen wanda ya kara firgita Husnah kawai tayi luuu ta some a take aikuwa
duk mutanen dake gurin suka kara tsorata ganin karamar yariya a firgice gashi har ta kaita da
somewa cikin zafin nama wasu maza masu uniform iri d'aya su biyu suka karaso da robar swan
suka yayyafa mata ruwan a fuska da jiki atake ta sauke ajiyar zuciya ta dawo cikin hayyacin ta,
ahankali ta soma bud'e idon ta.
Da kallo take biyar su har idon ta yadawo a kan matar da tazo da ita hara rar da matar takeyi
matane yasaka ta sauke idon a 'kasa.
Matar tace, "zaku iya tafiya" tana nuna masu hanya, dukan su babu musu suka fita, kallon
Husnah tayi tace, "bazan iya daukar maki kauyenci ba, kuma daga yau daga rana mai kamar ta
yau kada na sake ganin kin tara mani mutane acikin falo kuma duk wani 'kauyenci naki ya 'kare
daga yau saboda haka tashi ga kayanki nan ki dauka mushiga ciki na nuna maki masaukin ki
koma nace muhallin ki, haka Husnah ta tashi jiki ba wani 'kwari suka shiga cikin d'a kunan
dasuke acikin falon ta kaita wani d'akin mai dauke da gado madai_daici da way drop fentin
d'akin purple ne da green akwai rowel na labulai ash color haka kayan d'akin ash color ne, nuna
mata komai tayi da amfanin sa, sannan ta bud'e mata kofar toilet da take gurin ta 'karasa nuna
mata da koyar da ita yanda zatayi amfani da komai dan bata son yawan tambaya, da gida danci
tana gama koyar da Husnah komai sai ta fita tabarta a gurin wanka tayo da alwala cikin rashin
iya amfani da komai sosai amman tayi 'kokari gaskiya, sauya kayan jikin ta tayi tayi sallah tayi
zaune ta rafka uban tagumi kamar wata babbar mace, ahaka matar tashigo mata da abinci ta
ajiye mata a gaban ta tace, "ga abinci nan kici idan kin 'karasa ki sameni a falo" bata jira amsar
Husnah ba kawai tasaka kai ta fita.
Da sauri Husnah ta soma shan tea mai kaurin gaske sai kamshin kayan yaji yakeyi har tana
kone baki amman taki ajiye wa har sai da ta shanye coffin duka san na ta lura da wainar kwai
aikuwa kamar an aikota kawai ta soma ci kamar wani zai kwace mata haka tazo akan arish
amman ta kasa iya cin sa, loma d'aya tayi ta ajiye sa a gefe tana fadar, "wannan abun babu
dad'i gaskiya dama nasani da banci ba na 'bata bakina, kuma fa na 'koshi sosai kamar zanyi
amai wai Allah inda ma anty nanan ko mamar mu wai da sunci wannan dad'in wallahi amman
ko yanzu ai nasha lama dan nakusa cinye komai bari dai naje na kai masu sauran kilama shike
nan ni take jira na kawo mata sauran itama taci, kilama duk kurine irin na wannan aljanar matar
ai wallahi tunda aka fara kawo mani dole ne naci yanda nakeso na rama irin yanda su Gwaggo
marka da Baba da yaran su suke yi muna nida Anty Zarah da mamar mu".
Haka dai Husnah tayi ta zabga shirme har sai da matar ta gaji da jiran ta tazo ta sakota a gaba
tare da kwaso kayan da taci abincin, har kitchen ta raka Husnah takai kayan suka dawo cikin
falon ta zaunar da Husnah a 'kasa ita kuma tana akan kujera ta d'ora 'kafa d'aya akan d'aya
tana girgizawa tace, "Husnah ki bud'e kunnen ki, ki saurari abunda zan sanar maki, da kyau"
"Husnah ban dauko ki dan narasa yar aiki ba, ban dauko ki dan bani da kanwa ba ko yan uwa
ba aa kuma ban dauko kiba dan bazan iya haifuwa aa, kawai dai na d'auki kine, saboda wani
dalili wanda bazan iya sanar dake ba ko wane irin dalili ne, amman zan iya sanar dake sunana
da wasu abubuwa wanda babu wani mahalukin da yasan haka, tun bayan sauyuwar da nayi,
Husnah Sunana Zubaidah Ashir mu hudu ne a gurin iyayen mu duk kannin mu matane nice ta
ukku Asma'u ce babba sai Ruma sai ni sai kanwata Zulai, kowa daga cikin yan uwana yanada
kamun kai nice kawai daban dasu, inada shekara sha hud'u na bata rayuwa ta iyayena sunyi
kukan bakin ciki sunyi mani nasiha da lurar dani akan illar abun amman ni ban wani damu ba,
sai itayen nawa suka rika sanya mani ido sam sun hanani fita, ko nan da kofar gida atakaice dai
sun sanya ni kulle, nikuwa cikin dare nake tserewa tun basu gane ba har suka gane sunyi sunyi
amman abun yacitura sai dai suka sanya mani ido tare da addu'ar shirya a lokacin inada girman
jiki sosai babu wanda zai iya yarda da cewar Asma'u yayata ce, duk ganin akeyi nice babba,
inada shekara sha biyar nasoma zubar da ciki tunda iyaye na suka fuskaci haka suka fara
neman su auraddani ni kuwa na shammace su na gudu, akikacin inada shekara sha bakwai a
gaskiya bariki tayi babu mai hanani babu mai takurani, bariki ta karbeni da bariki nayi kud'i
natara manyan gidaje da motoci da manyan kadarori dan haka kema zan d'ora ki a wannan
harkar idan kinason kiyi kud'i ki rama abunda matar Baban ku da Baban ku sukayi maku keda
mamar ku da Antyn ki zan wayar dake fiye da tunanin mai tunani".
"Nabaki wannan labarin ne Husnah dan nasan bakida wayau ballema 'kwa'kwal warki ta rike
wannan sirrin nawa, ballema kisan duk abun da na aikata yanada kyau ko baida kyau dan bana
bukatar zuwa gaba kiyi mani wata tambayar kwatan kwacin hakan".