Showing 69001 words to 72000 words out of 73304 words

Chapter 24 - A GIDAN TA NA GIRMA COMPLELET. BY UMMU IHSAN.pdf

zazzauna Husnah da Anisah sai firar yaushe gamo suke, su Anty
Zarah ne suka katse masu firar da fad'ar, "A Husnah haka akayi ko? An biyo miji batare da
sanin muba ana nan ana shan soyayya".

Dariya suka saka mata, Husnah tace, "kai Anty Zarah satoni fa yayi kuma ku ko kuzo nema na,
ai babu komai, koda yake taya ma zaki zo nema ba bayan dan gaban goshin kine ya sato ni,
gashi nasan baya laifi, gashi daga zuwan ki har kin nemo laifi na".



Dariya sukeyi, Husain ya ce, "yau Anty Zarah dan Allah dubeta ki gani ai itace ta ce na sato ta
ta gaji da zama gidan Ummey kuma tana jin kunyar tace wa Ummey zata biyo ni, shine na
taimaka mata, ai kin san ni da taimako ko? "


Da sauri Husnah ta ce, "wallahi mutum ya fad'i gaskiya ai dai naga yanda lokaci d'aya mutum
ya dawo wani iri dashi ya rame yayi d'an wuya tunda na baro masa gidan sa, shine kullum cikin
zama gidan Ummey ".



Husain ya ce, "yauwa dan Allah halan wane gurin kika tafi, kika sa ina ta wahalar neman ki,
gashi Ummey ta'ki bani damar da zan tambaye ta ko na tambayi wani, Anty Zarah dai nasan
bata sani ba tunda inda ta sani da ta sanar dani dan kar na wahala da yawa kamar yanda
nasha ba'kar wahalar neman gurin da kike, har gidan Anty Zubaidah naje da sunan nazo gaishe
ta".



Dariya duk aka sanya harda Husnah Anty Zarah ta ce, "wannan dariyar ta nuna muna cewar
duk kun san inda take ko? ".


Anisah ta ce, "kai ne baka kwantadda hankalin ka ba, amman da ka kwan tadda hankalin ka da
ka gano inda take".


Husnah tace, "nikam ina gidan Shaheed ina futawa ta".


Husain ya ce, "Shaheed munafuki ashe kina gidan sa, shine yake ce mani nabashi number ki ko
na sanar dashi inda kike? ".


Dariya akeyi, Husain ya ce, "ina zuwa".

Tashi yayi ya nufi d'akin sa, yana d'an dad'e kafin ya dawo, da wani babban littafi ya dorashi a
jikin Husnah ya ce, "Baby na ki duba wannan littafin yau zakiji abunda baki ta'ba jiba keda yan
uwa na, nabaku wannan damar ".


Gefe ya koma Husnah sake da baki take kallon littafin wanda aka rubuta, sirrin zuciyar Husain,
mijin Husnah.


Duk sai suka sauka 'kasa suka ajiye littafin a tsakiyar su, Husnah ce ta fara bud'e littafin, kawai
photon Husnah wanda takai Daddy asibiti ya bayya na, cike da mamaki Husnah ta d'aga idon ta
tana kallon Husain gashi tana d'aukar photon taga rubutu kamar haka:->


_Wannan itace wadda tayi zarra acikin matan duniya muryar ta kawai naji, sai naji zuciya ta, ta
amince da ita sai naji cewar kawai itace mata bugun numfashi na_


D'aga mata gira yayi, sai ta sake bud'e wani shafin shi kuma an rubuta,

_ceton mahaifina tayi amman nikam nasan wannan ni aka aikowa da ita, domin na Aure ta,
tabbas nikam Allah yayi mani gata, da ya had'a ni da wannan kyakykyawar yarinyar ajin farko,
lallai nasamu babban rabo_


Wani shafin ta duba taga an rubuta,


_"ya ilahi na shiga cikin mawuyacin halin 'batan masoyiya ta, na rasa mike damuna, farin ciki na
ya gushe, Allah ya kawo mani wannan yar baiwa, wadda duk taku d'aya nata yake bugawa tare
da zuciya ta!"_



Haka ta sake duba wani fejin, taga an rubuta,

_Ciwon son wadda bata ma san dani ba a rayuwar ta zai kashe ni, ya Allah koda sau d'aya ne
ka bayyana mani ita, damuwa ta Aure ni, nikam ya ya zanyi da rayuwa ta ne!?_

Haka dai sukayi ta dubawa duk na damuwa suke gani, suna zuwa tsakiyar sukaci karo da:-


_Alhamdulillah Alhamdulillah yau Allah ya amshi addu'a ta, Baby Husnah 'yata ta kawo muna
shawara munbi kuma gashi nayi nasarar samun jin muryar da ko a cikin mafalki na ba zata
'bace mani ba, ni Husain ina daga cikin masu rabo, abar kauna ta zata kawo kanta guri na.. Ina
cikin farin ciki"_

Photon Husnah ne wanda take cikin motar ta tana driving ta sako kan motar ta a gidan su, da
wanda ta bud'e motar da wanda ta zuro 'kafar ta, tana murmushi da wanda ta fito a jikin motar
da wanda ta rungume Daddy da Ummey da wanda ta fara takawa kai har cikin falon gidan nasu
da wanda tazo dai 'kofar d'akin su Anisah taji suna maganar ta, ta tsaya tana murmushi da
wanda sukayi fad'a gurin cin abinci da wanda ta fito zata tafi gida har bayan motar sai da akayi
masa photo.


D'ago idon ta ta sakeyi tace, "amman taya duk ka d'auki wannan photon haka kuma duk ban
san anyi su ba, kuma lokacin da zani koma gida baka nan".


Murmushi yayi yace, "ki bari ki 'karasa mana".


Murmushi Husnah tayi taci gaba da dubawa, photon da tagani ne wanda yafi bata mamaki
shine ta fito 'kofar gidan Zubaidah da niyar zata 'boye trolley d'in ta, kafin ta gudo shine ta gani
da sauri tace, "wannan ya bani tabbacin cewar kai ne ka sauya wa trolley d'ina gurin ajiya ko? ".


Dariya ya yi babu amsa, tana duba wani shafin taga an rubuta,

_guduwa guduwa guduwa, yan mata na ai guduwa indai ba a gida na ba ban ga gurin da zaki
jeba, kiji dad'in sa, dole gida na ne mafakar ki domin nine suturar ki sirrin ki, kuma duk wan nan
shirmen na had'in wannan Auren ba zaiyi amfani ba, saboda an ginawa zuciyar ki da tawa
mafaka d'aya wato gidan Husain da Husnah zuciya d'aya"_


_Alhamdulillah ga Husain ga Husnah a gida d'aya zuciyoyi biyu a guri d'aya, a gaskiya ina jin
dad'in yanda Husnah take biye mani muna fafata soyayya a dabai baye, ni ina nuna mata
soyayya ba tare da sanin wani ba itama tana amsa, ba tare da sanin yanayi da girman soyayyar
ba, kuma ina gamsu wa da yanda naga sa'kon yana isa a gareki masoyiya ta_

_"Tabbas soyayya tana dad'i musamman ma akanki Husnah, saboda akan kine nasan mine ne
farin ciki mine ne ba'kin ciki_


_ya ilaihi wai nine za'a had'a Aure na da Husnah kuma harda su fad'ar sai kayi muna biyyaya
dole, lallai ne nayi fice, Husnah ta yarda har zuciyar ta, amman kishi ya hanata bayyana, hakan,
abun farin cikin anan kuwa shine, ta yanda Husnah taje gurin dinner din biki na ta soke abun tun
alokacin ne na yarda da cewar komai 'boye soyayya wata rana sai ta bayyana tun da gashi,
soyayya ta ta bayana akan idon ki Husnah da kuma gan_, gar jikin ki, tabbas ni mai nasara ne,
Husnah saboda ki 'kara sona na yarda da cewar zan Auri Mardiyya amman sam ni ko son ganin
fuskar ta bana yi_



_zaman Aure na da Husnah nine kawai nasan amfanin hakan kuma ni ba gangar jikin Husnah
nake muradi ba ita kanta Husnah da zuciyar ta nake muradi banyi Auren sha'awa da Husnah
ba, kuma nayi alkawarin sai idan ita ce naga tana bu'katar hakan amman ni kam nasan
soyayyar Husnah halitta tace a hakan, ba zan takura mata ba duk kuwa da yanda nake bu'katar
mata ta tabbas sai na tabbar da Husnah ta cika da sona ta yanda bani da wani aibu a gurin ta,
sai soyayya zallar ta_


_Haa kashe ni aka zoyi Husnah ta kawo jikin ta, aka halbe ta, tun a wannan lokacin na fahimci
cewar soyayya ta tayi tsiro a zuciyar ki Husnah, kasan cewar zuciyar mu d'aya shi yasa aka
had'a dani dake aka d'auke wai har abamu bindiga ace na kashe kaina, toh idan na kashe
Husnah ai kaina na kashe, haka Husnah idan ta kashe ni kanta ta kashe, to kasan cewar da
zuciya d'aya muke amfani, da ido muka tsara komai da zuciyar mu sai gashi lokaci d'aya, mun
kaiwa abokin tabar mu bari, kai amman yayan gata ne a soyayya ta da Husnah_


_Daddy kuci gaba da bamu hakuri amman duk da gan hanci muke abun mu, kasan cewar ina
son na 'kara tan tance ya zurfin soyayya ta yake a yan zun a gurin Husnah shine na Auri Zee
na Aura kuma nayi nadamar Auren nata dan taso ta kashe ni, ta rabani da ruhi na_



_Husnah ina son ki ina kaunar ki ina jiran ranar da kema zaki ce dani mijin ki soyayya ta har
abada Allah ya azurta mu da zuri'a ta gari_

ajiye littafin Husnah tayi tace, "muna son 'karin baya nin ka"

Husain ya ce, "Sai kuma abunda nine kawai nasan sirrin sa da fassarar sa shine wanda yake ci
maku tuwo a kwarya Husnah shine ina kiranki da Karuwa ".


Husnah tsakani da Allah ni dai wallahi tun lokacin da nafa ganin ki komai naki yana burgeni,
amman dalilin da yasa nake cewa haka, shine idan na kiraki da wannan sunan idon ki na nuna
mani wanni sirrin wanda na barwa kaina sani, kuma ba zan iya sanar da kowa ba, Husnah ke
sheda ce ranar da naji Mardiyya ta ambaci sunan da nine kawai nake kiran ki dashi, na dake ta
har na korata gidan su, Husnah wallahi ni har a zuciya ta bana zar gin ki da komai dan haka ni
ban 'bata Aure na ba"


"Husnah ina sonki ina sonki ina sonki ina sonki bana son ganin kukan ki ina kaunar ganin farin
cikin ki ha 'karshen rayuwa ta dan Allah Husnah ki soni kada ki bani na rasa ki kada ki barni
nayi kuka akan rasa soyayyar ki".



Da gudu Husnah taje ta rungume mijin ta, tace, "ina sonka mijina".


Tafi aka sanya masu kowa dad'i yake ji ganin yau su Husnah da Husain sun shirya a gaban su.


Haka gidan ya kasan ce masu cikin farin ciki sai dare suka tafi, haka su Anisah suka sanar da
Ummey sosai Ummey tayi farin cikin haka daddy, su Yaya Yusuf da Shaheed ma sunyi farin ciki
sosai.
Haka rayuwar su Husnah da Husain ta kasan ce cikin so da kaunar junan su da kulawa ta
soyayya.


Sai da sukayi wata ukku suka koma gidan su, Zee na ganin yanda suka dawo kawai ta tattara
kayan ta tace ya zalunce ta ya muna funceta ashe dama yana can tare da Husnah yayi mata
maganar wayau ya bata kud'i yaci gaba da zama da Husnah wallahi sai ya sake ta, Husnah
tace, hubby kada ka yarda ka sake ta share ta kawa, ita ta manta cewar ita da kanta, tace ita
tagaji da zaman ka kai da ita, kawai ka bata kud'i kayi tafiya mai nisa itama ta futa, to kanki kika
yiwa".


Cikin zafin nama ta kawo wa Husnah mari, amman kafin hannun ta ya sauka a kan fuskar
Husnah tuni Husain ya ri'ke hannun yayi mata mari biyu masu kyau.

Ya ce, "ban za kawai ke har kin isa ki mari mata ta bugun numfashi na a gaba na? "


Hannun Husnah yaja sukayi d'akin Husnah, da 'kamshi kawai ke tashi, cikin mamaki Husnah
tace, waye yayi wannan aikin? "


Dariya Husain yayi yace, Suhailah ce, kuma idan kin futa kwana biyu, sai kije gidan Ummey kiyi
sati biyu saboda bikin Anisah da Tk Suhailah da Muktar sai Safiya da Ahmad"



Sosai Husnah taji dad'in wannan maganar.

Haka kuwa kwanan su biyu da wowa suka nufi gidan Ummey, sosai Ummey tayi farin cikin
ganin Husnah da Husain da sauyin da aka samu, jin takeyi kamar ta maida Husnah da Husain
cikin ta, Daddy ma wani irin farin ciki yakeji, ganin wannan sauyin su Anty Zarah dasu Yaya
Yusuf Shaheed matar Shaheed su Anisah kowa cikin farin ciki yake, tabbas Husnah da Husain
sun dace da juna.


Daddy ne yace su shirya yau zasuje ziya gidan baffah daga nan zasu je gurin baban su Husnah
a take Husnah da Anty Zarah sukace su ba zasu ba, Husnah ma harda fad'ar, ai Baban mu ya
dade da rasuwa ni ban ma san shi ba".


Lallashin duniya sunce ba zasu ba, gidan baffah ma da akayi maganar cewa sukayi ba zasu ba,
har sai da Daddy yace Yusuf Husain wannan aikin kune, dole a ranar aka fasa tafiyar.


Husain ne ya zainar da Husnah yana lallaba ta amman ta'ki yarda, tun yana lallashin har ya
hasala yayi fushi ya daina kulata ya koma gurin matar sa, har sati d'aya, ai kuwa Husnah ta
'kara hasala, tana fitowa daga cikin d'akin ta zata shiga kichen kawai Zee ta saka wa Husnah
'kafa dan ita sam saboda abunda Husain yayi mata tana cikin zafi ta share su shida matar sa ta
daina shiga lamarin su, to bata kula da suna zaune a gurin ba kawai taji an tadiyeta, a take tayi
luu zata fad'i cikin zafi nama Husain ya janyo ta, suka fad'a akan kujerar da yake zaune a kan
ta, shine a 'kasa Husnah a saman sa, a take Husnah ta bud'e ido ganin ta kwance a jikin mutum
kawai tayi yun kurin tashi, da sauri ya ri'ke ta, yace, "ina fatan baki samu rauni ba"


D'aure fuskar ta tayi tace, "zan tashi ka kyaleni malam nayi abunda yake gaba na, kuma miye

naka aciki koda raunin ne na samu ai dai naga ba jikin ka ba ko? "


Dariya yayi yace, "Husnah nine fa kika yiwa laifi kamata yayi Husnah kizo ki bani hakuri ki
lallasheni ko".


Shiru tayi masa shi kuwa gyara mata kwanciya yayi a jikin sa, ita kuma ta daura kanta a jikin
sa,.


Wani wawan tsaki, Zee ta saka, tace bariki kawai, Husain ya daga idon sa, yace, oh tunda burin
ki bai cika ba, ai ina kallon yanda kika saka mata kafa ni kuma kin san abunda ba zan d'auka ba
ke nan, akan yar karuw... Da sauri Husnah ta rufe masa baki tace, "um umm nidai bana son
wannan Sunan Allah".


Cizon wasa yayi mata, ihu ta saka, cikin takaici Zee tabar gurin, anan gurin ya lallashi Husnah
har ta yarda, da sauri yace to tashi muje gida tun yanzun dan da zafi_zafi akan daki 'karfe "



Shiryawa sukayi suka bar gidan suna zuwa ashe daman su ake jira daman yayi niyar yau kam
dole ya shawo kan Husnah.

Hanya suka d'auka tare dasu baffah, shine ma ke nuna masu hanya cikin ikon Allah koda tara
ba dare yayi sun kusa isa garin hotel suka kama suka kwana tun da safe suka d'auki hanyar
shiga garin, zuwa 'karfe biyu na rana suka isa, ita dai Husnah da Anty Zarah cike suke da
mamakin ganin gidajen guri duk sauya masu hanyar da suka sani ma taso 'bace masu, ko
baffah sai da yayi tambayar gidan su Marka wanda aka tambaya yace, "kuce gidan barayin
kauyen nan" ai kuwa a take aka nuna masu, hanyar tafe suke da mamakin barayin Kauyen, taro
suka gani ana ta rafka bala'i mutane ne suka taru ko wane da makamin sa, a hannun ana dukan
wasu mutane a gurin, Husnah kuwa bud'e motar tayi, ba tare da wata wata ba, a take Husain ya
biyo ta yana kiran ta amman sai ture mutane takeyi tana shiga itama Anty Zarah da sauri ta
shigo gurin, Husnah turus tayi ganin ana dukan matar da har ta mutu ba zata iya mantawa da
ita ba,


Anty Zarah ce ta dafa Husnah tace, "Husnah kin ga kuwa abun da nake gani da ido na kuwa? ".


Husnah ce, tace Alhamdulillah duk sai mutane suka jiyo suna kallon baki duk sai aka matsa

masu, akayi shiru Husnah tace, " *HAJIYA MARKA*!! ke nan to Alhamdulillah gamu da ran mu
Allah ta nufa bamu mutu ba kuma bamu wukanta ba kamar yanda kikayi muna fatan gani, ki
dubemu da kyau ki gani".


Tun lokacin da Husnah ta ambaci sunan Marka kawai sa Marka ta saki ido da baki ita da wanda
suke gurin suka zubawa su Husnah ido.


Anty Zarah ta ce, "Marka ki duba da kyau ki gani ko idon ki daya zai iya gane mu, amman koda
yake, bari abaki amsa, ta dubi Husnah.


Husnah tace, "Anty Zarah ce da Husnah makinyanki mune nan a gaban ki, lafiya lau cikin
kwanciyar hankalin amman ke dibeki keda "ya'yan ki "ya'yan so, kun dawo abun tausayi, yan
mune zamu taima ke ku, Marka nazo da niyar d'aukar fansa amman Allah ya bi muna hakkin
mu dan haka mun barki da halin da kike ciki".


Anty Zarah ta ce, "hum Marka mune kikayi wa farar kasan cewa haka, a yanda kike a yanzun
sai gashi kin ga, Ikon Allah wanda babu wani mahalukin da ya isa ya chanza kaddarar Allah da
hukunci sa, dube ki dubi yanda wani mummunan wari yake fita daga jikin ki dubi yanda kika
maiyar da yaran ki wata da ciki wani an toye masa rabin fuskar wata kuwa da Alama ba zata
sake amfani da hauren bakin ta ba ko d'aya, Marka ina bokayen naki ina tsafin da kike takama
da shi?, wanda mutuwar maman mu bata zame maki ishara ba, mahaifin mu da kika mai dashi
jela, yan zun nasan kin 'karasa kashe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login